Showing 75001 words to 78000 words out of 145203 words
na" ta fito da wayarta daga jaka ta fara kiran Najeeb sai dai da ke inda su ke ba service sai bai shiga ba. Jikin Farida yai sanyi, ta tura ma sa text kawai ta bi police ɗin nan...
Bai duba wayar sa ba sai ƙarfe biyar da rabi bayan sun dawo kamfani. Yana duba missed call ya ga har da numbar Farida ga kuma text ɗin ta. Ya buɗe text ɗin ya ga ta rubuta *Sabreen ta arresting ɗi na*
"Arrest?" Yai saurin kiran numbar Faridan ya ji ta a kashe. Da sauri ya fara dialling numbar Anas ya na fita daga office ɗin da gudu...
Shi da Anas su ka isa gida dan numbar Sabreen ɗin da Najdah ta turo mu su an ƙi ɗaga kiran su.
Hankali kwance su ka samu Sabreen tana zaune a falo tana cin apple.
"Where's she?" Ya daka ma ta tsawa
" who?"
"Dont be stupid Sabreen, where is she?"
Juyar da kai ta yi gefe ba ta amsa ba.
Ƙarasawa yai wajen ya fincikota yai waje da ita Anas ya bi bayan sa...
............
Tun da su ka shiga mota ya ke faɗa abin mamaki Sabreen ta ce ba za a fitar da Farida ba saboda abin da ta ma ta...
'Yan station ɗin ma sai da su ka san sun taɓo matar babban mutum. Tun da su ka shiga Najeeb ke ta masifa. Anas ne ma ya ke ƙoƙarin bashi haƙuri dan kar a samu matsala a wajen.
Ba'a jima ba aka taho da Farida. Yana ganin ta ya ƙarasa wajen ta da sauri. Ya riƙe hannunta kawai sai ta faɗa jikin sa ta fara kuka.
Duk wani formalities Anas ne ya tsaya zai yi, dan Najeeb kan jan hannun matar sa yai su ka bar wajen. Sabreen ta bi bayan su tana faɗin ba zai yiwu Farida ta tafi haka ba bayan abinda ta yi ma ta. Najeeb bai kulata ba har su ka isa bakin mota. Zai taimakawa Farida ta shiga Sabreen ta riƙe ma sa riga, ta fara kukan munafurci.
"Noory she wanted to kill me, ita ta sa min yaji a gado jiya. I almost died Noory"
Bai yi yunƙurin yafce hannunsa daga riƙon da ta ma sa ba illa matsawa yai kusa da Farida ya ɗan sukuyo dai dai saitin fiskarta. Ba tareda wani tantama ba ya haɗe bakin su. Farida ta ƙwalalo ido saboda mamaki da shock da ta ji lokaci guda.
Sabreen ta sake rigan Najeeb tana kallon yadda Najeeb ke kissing Farida zuciyarta na tafarfasa, ji ta ke kamar zuciyar zai bulluƙo ya fito.
Farida ta yi saurin janye bakin ta saboda tunowa da ta yi a public place su ke. Da rinannun idanun sa da su ka ƙanƙance ya ce "kiss me" ba ta san ya akayi ta jefar da kunyar ba kawai ta tsinci kan ta da haɗe bakin su not minding a inda su ke...
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣3️⃣0️⃣
Murmushi kawai ta ke yi tunda su ka fara tafiya. Idon ta na gefen titi amma hankalin ta ba a titin ya ke ba. Har yanzu tana jin taste ɗin zaƙin bakin sa a nata bakin. Ba ta taɓa sanin haka kiss ke da daɗi ba sai yau. Lokacin su na soyayya da Lukman ya taɓa kissing hannun ta da goshi amma banda lip to lip kiss. Shi kam Rayyan ba su taɓa irin haka ba, Rayyan ya na tsoro da shakkar Farida shi ya sa ko hannun ta bai taɓa riƙewa ba sai dai ko a rashin sani.
Yau ta samu first kiss ɗin ta, kuma da Sir Najeeb, Sir Najeeb fa. Ta sa hannu ta rufe bakin ta saboda tsikar jikan ta da ya tashi lokacin da ta tuna abinda ya ce "kiss me".
"Did they hurt you?"
Ai ta tafi duniyar tunani ba ta ma ji abinda ya ce ba. Duk wani cin mutunci da ta shirya za ta yiwa Sabreen lokacin ta na cell ta watsar da shi. Ƙwaƙwalwarta ba abinda ya ke tunowa sai wannan moment ɗin.
Chan ƙasan zuciyar sa ya ke neman dalilin da ya sa ya kissing ɗin ta amma ya rasa. Chan ya baiwa kan sa amsa da Sabreen. Yes ya yi haka ne saboda Sabreen, saboda ta gane cewa he's over her now. Amma must he resort to kissing her? Yanzu sai ta rena shi. Wata zuciyar ta ce but it was the best kiss you ever had. Ko dan ya jima bai yi kiss ba ne, dama da Sabreen ne kawai, no one else. First kiss na shi in 8yrs felt different. Kaman wani ƙaramin yaro haka ya lashe lips ɗin sa da harshe. Garin haka ma saura kaɗan ya buge wani mai Keke.
Har su ka isa gida ba wanda yai magana. Farida ce ta fara shigowa dan ta fita ta bar shi a mota. Tana tafiya tana jin ta a sama fiskar ta ɗauke da murmushi.
Najdah ne da wata tsohuwa a falon lokacin da ta shigo. Ba ta ma lura da su ba sai da tsohuwar ta ce "amarya lafiya?" Farida ta juyo sai ta ga tsohuwar duk da kuwa kuɗi sun ɗan ɓoye tsufan, amma kuma a yadda ta gan ta za ta haifi Daddy.
Ta yi saurin ƙarasawa wajen ta ta tsugunna "Hajiyata dan Allah ki yi haƙuri ban gan ki ba ne"
"Na ga alama ai, kin tafi birnin soyayya ko. Ina angon" kafin ta ba ta amsa sai ga Najeeb ya shigo.
Yana ganin Hajiya Mama ya washe baki " tsohuwa yaushe a gari?"
Yana ƙarasowa wajen ta ta ɗauki sandarta ta ɗaga sama za ta kwaɗa ma sa ya ja baya da sauri.
" ke fa tsohuwa kin dawo kenan za ki fara cin zalin mutane"
"Ungo na ka Najeebullahi, tun jiya na dawo amma shi ne ba za ka kawo min amarya na gan ta ba"
"To ke kiji da ƙafar ki ma na, amma sai shegen yawo"
Farida dai kallon Najeeb da Hajia Mama ta ke da su ke dramar su na Kaka da Jika. Najeeb was jovial amma ba kaman tsakanin sa da Mom ba wanda tun zuwan ta abin ke ɗaure ma ta kai.
Hajia Mama ta kalli Farida ta ce "kin ga mijin kin nan ke ce rufin asirin sa. Haka yai ta yawo ƙaton tuzuru da shi, sai da Allah ya kawo ki"
Farida ta yi murmushi.
"Sai ki kula da shi sosai dan ɗan duniya ne"....
Ta fito daga wanka bayan sallar Isha ta fara jin hayaniya a ƙasa. Ba ta tantance ko muryan su waye ba ne amma daga yadda maganar ta ke haɗakar larabci da turanci ta san ba zai wuce Sabreen ba ne...
"Big B mi ya sa ka ke bin bayan ta, kai kan ka ka san ita ta yi wannan abin and she needs to be punished for that"
" walau ita ta yi walau ba ita ba, dukkan ku biyu babu wanda ya ke da ikon arresting ɗin ta, especially you Sabreen. Ina so ki nisanci iyalina"
"Big B amma..."
"Najdah!" Ya daka ma ta tsawa. Kallon shi ta yi sannan ta haura sama da gudu.
Ya juyo ya kalli Sabreen ya ce "next time ki ka yi ƙoƙarin taɓa lafiyar mata ta, i wont take it lightly"
Cike da tuƙuƙin baƙin ciki ta ce "you dont love her, do you"
Haɗiye miyau yai sannan ya ce "go back to Hollywood you dont belong here"...
Ɗakin Najdah ya fara zuwa Lokacin da ya haura sama, amma ta ki buɗe ma sa ƙofa. Dan haka ya juya ya shiga ɗakin su.
Yana shiga ɗakin ya gan ta bakin gado tana kuka. Jikin sa yai sanyi ya ƙarasa wajen ta yana tambayar minene dan a tunanin sa ko a cell ɗin an mata wani abu ne.
"Mi ya faru?"
Tana kuka tana jan majina ta ce "Baba ya rasu"
Kan sa ya ɗaure dan Anas ya taɓa ce ma sa Farida marainiya ce to yanzu kuma wani Baban ne ya rasu.
"Your father?" Ya sake tambaya.
"Kaka na ne"
Ya jawota jikin sa yana lallashin ta.
"Yanzu Ummi ta kira ni, dan Allah Sir Najeeb zan je Jos gobe"
Ya gyaɗa kai ya ce "its ok"
Sun jima tana kwance a jikin sa tana hawaye tana faɗa ma sa kyawawan halayen Baba. Bai bar wajen ta ba sai da ta yi bacci, lokacin kusan sha biyu saura na dare. Da ya gyara ma ta kwanciya sannan ya je yai wanka ya shirya cikin kayan bacci sannan ya zo ya kwanta amma kafin yai bacci sai kusan ƙarfe biyu. Tunani ya cika ma sa kwanya.
Washe gari da sassafe ta shirya, ya sa Iliya ya kaita har Jos. Lokacin da motar ta bar cikin compound ɗin ƙarfe shida da rabi na safe. Yana shigowa cikin gida Daddy ya kira shi, da ya je tambayar sa yai gameda abinda ya faru jiya dan ya ji maganar a wajen Mom.
Bayan ya ma sa bayani sai Daddy ya ce " ka yi katanga tsakanin ka da Sabreen, ban hana ka ƙara mace ba idan ka ga ba za ka iya zama da Aisha ita kaɗai ba, amma ka sani. Ba zan taɓa amincewa da Sabreen a matsayin suruka ba. Ba wai dan ta rabu da kai ta dawo ba, sai dan ba zan bari ka haɗa zuri'a da macen da zata iya gurɓata ma ka rayuwa ba. Ina sane da lokacin da Mahaifiyar ka ta ke kuka kullum saboda Sabreen ta na shirin auren wani kafiri ɗan ƙwallon ƙafa har ta ke sukan addinin musulunci da ya hana aure tsakanin kafiri namiji da mace musulma. A hira da aka yi da ita shekaru uku da su ka wuce, cewa ta yi sallah na takura ta, wai anata abu ɗaya kullum ba hutu. Wannan ba macen aure ba ne. Idan har ka nuna za ka auri Sabreen to za ka yi nisa da ni da iyalina. Za ta zauna a nan ne kawai saboda alaƙa ta jini da su ke da shi da Nabilah amma bayan nan ba na so wani abu ya kuma shiga tsakanin mu"
Najeeb ya gyaɗa kai.
"Ya maganan gidan ka, anyi interior decoration ɗin?"
"An kusa a gama"
"Ok Allah ya nuna ma na"...
Yau dai throughout a office jin sa ya ke wanni iri. Musamman idan ya zo fita ya ga ba ta kan kujeran ta.
Da ke Jummu'a ne kuma ranan hutu ne an haɗa ƙwarya-ƙwaryan party amma bai iya tsayawa a wajen ba. Anas ne ya tsaya ya wakilce shi, daga sallar jummu'a gida ya wuce yana jin jikin sa ba daɗi. Ba wai ba shi da lafiya ba ne amma kuma jikin sa is weak.
Yana shiga ɗakin sai ya ji ɗakin ya ma sa faɗi kaman ba ɗakin sa ba, there's something missing. Ƙanshin ɗakin ya sauya tun zuwan Farida saboda haɗuwar turarukan sa da na ta kalolin turaren. Har ta fasalin ɗakin ya sauya. Ya tuna ranan da ya shigo ya ga tana chanja arrangement na wasu abubuwan a ɗakin.
"Sir Najeeb ɗakin ka yana buƙatan polish"
Ya tuna yadda yai ta gwaleta yana cewa ta hargitsa ma sa ɗaki.
Ya na shiga wajen closet ya tuna ranan da ya ke chanja kaya ta shigo lokacin gajeren wando na jeans ne a jikin sa ba riga.
" Sir Najeeb, idan ka na gida sai ka yi ta sa gajerun wanduna kaman wani ɗan firamare"
Yai murmushi tunowa da yai da kalolin tusa da ta lissafto ma sa ranan...
Lokacin da ya gama abubuwan da zai yi yana kishingiɗe a kan gado ya ji gadon ya ma sa daban. Tun da ta zo kullum za su kwanta akwai pillow a tsakanin su, jiya ne kawai su ka kwana ba pillow.
A hankali ya sa hannu ya fara shafa gefen da ta ke kwana wanda ya ke empty yanzu. Ya tuno ranan farko da za su kwana a kan gadon faɗan da su ka yi, daga ƙarshe da tunanin kissing ɗin da su ka yi jiya bacci ya tafi da shi.
Washe gari da safe Daddy ya ce su je su yiwa Baffa Musa ta'aziya. Tare su ka je a chan ne ana taɗi wanda tsakanin Daddy da Baffa Musan ne dan shi banda ya haƙuri da ya ce bai kuma cewa komai ba. Cikin taɗin su Baffa Musa ke kawo rayuwar da Farida ta yi. Daga wannan gida zuwa wannan gida kafin daga baya ta zauna a wajen Kakannin ta.
Daddy ya tambayeshi ko miyasa bai ɗauki Farida tun da wuri ba. Baffa Musa ya ce "Hmm Faridan, tun tana yarinya ta ke da baki. Ko hutu aka kawota sai ta yi ta ƙorafi, Baffa garin ku akwai zafi, ba zan zauna ba"...
Lokacin da za su tafi Baffa ya ce da Najeeb " ka kula min da ita dan Allah. Ka da ranan gobe Ubanta ya ce ban riƙe amanar tilon 'yar sa ba"
Najeeb ya ce Insha Allah...
........................
Yau sati ɗaya kenan da ba ta nan. Cikin sati ɗayan nan ya rasa ganewa kan sa. Bai ma cika son fita ba, dama wajen aiki ke ɗebe ma sa lokaci to yanzu ana hutu. Sabreen washe garin da Farida ta tafi itama ta yi tafiya, bai san inda ta je ba kuma bai damu ba dan shi idan ta tashi ne to kar ta ƙara dawowa.
Yau da ya je wajen Hajia Mama ne ta ke cewa ya kira ma ta Farida ta ma ta ta'aziya.
Kwana uku da Farida ta yi a Jos ta yi su cikin rashin jin daɗi, na farko ga rashi da su ka yi, na biyu kuma Sir Najeeb da ya shareta. Kullum da tunanin sa ta ke kwana ta tashi, amma shi ko text bai ma ta ba balle ya kira ya ma ta ta'aziya. Duk da kuwa ranan da ta taho ta tura ma sa text akan sun isa lafiya amma ko reply bai yi ba. Wasu lokutan har mafarkin suna tare ta ke, haka kawai tana zaune sai ta ji kaman muryarsa a kunnen ta yana faɗin "kiss me" har tunanin ko ta fara hauka ta ke yadda waɗannan kalmomin biyu ke sa ta jin wani nishaɗi da farin ciki...
Tana ganin wanda ya kirata mamaki haɗe da wani farin ciki ya mamayeta, sai da wayar ta kusa katsewa sannan ta ɗauka.
"Sir Najeeb shi ne sai yau?"
"Aishatu, kuna lafiya ya haƙuri?" Muryan Hajia Mama ya doki kunnen ta maimakon muryan Najeeb...
Hajia Mama na kashe wayan ta kaiwa Najeeb sanda.
"Ashe ko ta'aziya ba ka je mu su ba. Kakan matar ta kan"
"Kai Tsohuwa, ba munje gidan uncle ɗin ta ba. Miye sai mun je har Jos. Will that bring back the dead?"
Hajia ta sa ke ɗaga sanda yai gefe da sauri yana dariya...
Kaman yadda Hajia Mama ta nema kuma ta sa Daddy ya ma sa magana dole ya shirya zai je Jos. Shi sau ɗaya ya taɓa zuwa garin kuma aiki ne ya kaishi.
Ya fito kenan ya tarar da Anas da Najdah a falo su na magana.
"Kai ba na son takurawa fa, she's still in school" Najeeb ya faɗa yana hararan Anas.
Anas ya ce " an gaya ma ka ni irin ka ne da sai na zauna har 35yrs. Ai ni kafin watan shidan sabuwar shekaran nan zan angonce"
"Shege, to Baby sai ta ƙare karatu tukunna"
"Wallahi ba ka isa ba, ka san tun yaushe mu ke shan ruwan kanwa kuwa"
"Ɗan iska, to ka bi ni a hankali ko in hanaka, dama Musty yana gaba dani saboda na hana shi, ka ga idan ka yi wasa sai na bashi ita"
"Kai na a ƙasa babban yaya, mu na neman tubarrakin ku"...
Sai da su ka jima su na wasa da dariya kafin daga baya bayan Najdah ta bar falon Anas ya shiga bayanin abinda ya kawoshi.
"Najeeb, Farida ita ke da gaskiya da kai da kamfani you owed her apology"
Najeeb ya gyara zama yana sauraron sa.
"Khalidah da Alhaji Matawalle su su ka kitsa komai. The money from VESTAC inc. Alhaji Matawalle ne ya sa aka tura supported by Khalidah. Shi ya shirya yadda za a sace ma ka takardun zanen ka a kuma ɓata modelling da ka yi. On the other hand kuma Khalidah ita ta kawo shawaran a framing Farida. Duka evidences da mu ka haɗa yana nan" ya miƙa ma sa wata ƙatuwar envelope.
Idon Najeeb ya rine yai ja tsanar Khalidah da Alhaji Matawalle na ƙara shiga ran sa.
"Kai ka san wani mataki ko hukunci za ka ɗauka idan aka koma aiki ranan monday" ...
..............
Ba dan ya riga ya shirya tafiya ba da ba abin da zai sa ya tafi. Ƙusan ƙarfe uku ya isa Jos, address ɗin da Yakubu ya bashi ya bi, da tambaya kuma ya isa har layin su. Bai gama shan mamakin layin ba sai da ya isa gidan. He cant believe a irin wannan gida Farida ta yi rayuwa. Ba wai dan bai saba ganin gidaje haka ba a'a sai dan yadda Farida ke gudanar da rayuwar ta with boldness and cofidence, ba ta shayin shiga ko'ina. A ko yaushe ji ta ke dai-dai ta ke da kowa, duk daraja ko kuɗin ka kuwa.
Yaro ya kira ya ce a ma sa magana da Farida dan tun a bakin layi ya ajiye mota saboda mota ba ta shiga layin.
Ana yiwa Farida kitso yaro ya shigo wai ana sallama da Anty Farida.
"Ni kuma? Waye?"
"Bai gaya min ba"
"Ya yake" Farida ta sake tambaya tana sawa ranta kwaɗayin ya kasance Sir Najeeb ne ya zo.
Yaron ya ce " fari ne, dogo, kaman balarabe ya ke amma ya iya Hausa" ai yaro bai gama bayani ba ta tashi daga gaban Umma Binta ƙanwar Ummi da ke ma ta kitso.
"Ka je da gudu ka ce ma sa ina fitowa yanzu"
"O'o amaren zamani kenan, Farida wannan zumuɗi haka"
Ai ba ta ji me Umma Binta ke cewa ba ta riga ta shige ɗaki za ta ɗau hijabi...
Ya bawa ƙofan gidan baya yana tsaye hannayen sa duka biyu su na cikin aljihu, hankalin sa ya tafi wajen wassu yaran Birom da ke wasa a ta wajen kwata yana mamakin yadda yaran ba sa ƙyanƙyamin wajen.
Yana sanye da baƙar shirt da baƙin hoodie jacket sai baƙin jeans.
"Sir Najeeb" muryan ta ya doki kunnen sa. A hankali ya juyo yana kallon ta, ba ta wani chanja ba sai dai idon ta ya ɗan nuna rama may be