Showing 138001 words to 141000 words out of 145203 words

Chapter 47 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25716

son ɗaukan sa...

Bayan wata biyar Aneesa ta haiho yarinyar ta mace. Yadda bata wahala a renon cikin ba sai ya zamana ta wahala wajen haihuwa, dan awa takwas ta yi tana labour ƙarshe sai da aka sa mata ruwan naƙuda kafin haihuwan ya taso gadan-gadan.

Itama wannan jaririyar a Kano aka yi sunanta, yarinyar ta ci suna Khadijah su ka sa ma ta inkiyar Mujahida...


............................

Ummi ma ta haihu namiji amma kwanan sa biyu yaron ya koma. Farida sai da ta yi kuka ranan tamkar ita ta yi haihuwan.
Baffa Musa ma ya ji mutuwar yaron dan yadda ya ke ji da Ummi to haka ya ke jin son abinda za ta haifo ma sa. Sai dai ƙaddara ce da ta riga fata...



Yau Jumma'a da wuri ya dawo daga office. Ɗakinsa ya fara shiga amma ba ta nan. Ya rage kayan jikin sa sannan ya wuce ɗakin ta. Abin mamaki sai ya ganta durƙushe bakin gado tana kuka. Da sauri ya ƙaraso wajenta dan tunanin sa wani abu ne ya samu Yaman.

"My Queen mi ya faru? Ina Yaman?"

Ɗaga hannu ta yi ta nuna wajen gadon yaron. Ya ƙarasa gadon da sauri, ya kalli Yaman na bacci hankalin sa kwance, sai a lokacin ya ji hankalin sa ya kwanta. Ya shafa kan yaron sannan ya koma wajen Farida da ke kuka.


Ya jima yana rarrashin ta kafin ta yi shiru ta miƙa ma sa PT strip ba tareda ta ce ma sa ƙala ba. Bai gane ba ya tambayeta " what is it?"

Ta ɗago jajayen idanun ta ta kalleshi ta ce " i'm pregnant"

Allahu Akbar Najeeb ya faɗa tareda yin sujjada a gefenta. Har ya ɗago ba ta dena kallon sa ba.

"Kai i'm happy Aysherh, kin min komai a rayuwa ban san mi zan miki na saka miki ba"

Hararansa ta yi ta ce "it seems ka manta shayarwa na ke. Yaman is only 7months"

"So?"

"Da ke ba kai za ka yi wahalan ba ai"

Jawota jikinsa yai ya ce " Aysherh aren't you happy, mutane nawa su ke neman haihuwa ido a rufe amma Allah bai ba su ba. Amma ke kin samu kina kuka, let me ask you something. Kuɗin kula da su ne ba mu da shi ko kuma me ne?"



Skt 59


Maimakon ta bashi amsar maganar sa sai ta fashe da kuka. Har cikin ransa ya ke jin haushin kukan ta, dan shi bai ga abin kuka a nan ba.

"Ban yi aure da wuri ba Aysherh, i had my first child at 37yrs. Ina da abokai da 'ya'yan su na fari suke shekara goma, takwas, bakwai. Kai Cousin ɗina Bilyamin da ke Gombe, shekara ɗaya aka haife mu, but his first daughter will be thirteen this year. Ba kya son haihuwa da ni ne?"

Shiru ta yi dan ba ta da abin cewa. Ita dai ta san tana son hutu, haihuwa ba wasa ba ne.

"Shekarun baya cikin wauta na tsara wa kai na iya 'ya'ya biyu na ke so. Amma yanzu i've changed, ina son 'ya'ya dayawa. Allah ya kawo mana ko nawa ne, da taimakon Ar-Rahman za mu kula da su, mu tarbiyantar da su bisa tafarkin addini, za mu yi komai dan mu inganta rayuwar su in har muna raye"


"Dole ka ce in haihu dayawa ai, salon nan da 'yan shekaru kaɗan idan na gama yin laushi ka je ka ce za ka auro wata sabuwa tunda na tsufa. Wallahi lokacin ne za ka san Aisha Farida ka auro"


Lallai Farida har yanzu da sauran shirmenta, abin da ya ke hanga daban abin da ta ke hangowa daban. Cigaba da magana da ita a wannan lokacin ma shirme ne.
Miƙewa yai ya je ya ɗau Yaman da ke bacci ya ce "ka da abinda ya samu baby na Aysherh. Or else..." ya sa kai ya fita ba tareda ya jira mi za ta ce ba.

Ranan gaba ɗaya ɗauke ma ta wuta yai dan har raba wajen kwana su ka yi, ya kwana a ɗakin sa ita ma ta kwana a na ta.

Washe gari ma ko kulata bai yi ba. Tana gaishe shi ma sama-sama ya amsa ma ta. Haka su ka ci breakfast ba tareda wani ya yi wa ɗan uwan sa magana ba. Yana gamawa ya tashi ya fita...

.............................


Yau kwana biyu kenan ma'auratan ba sa wani magana da junan su. Najeeb na dawowa daga office zai maƙalewa Yaman yana wasa da shi. Idan ya lura yana jin yunwa kuwa Tasallah zai kira ko matar Abdullahi su miƙawa Farida.

Najeeb na dawowa daga sallar Maghrib ya ga su Tasallah na fito da kayan Yaman ana sawa a boot ɗin mota. Farida na tsaye ɗauke da Yaman wanda ya sha kayan sanyi ma su kyau saboda yanayin garin akwai sanyi, itama Faridan da ganin shigarta fita za ta yi. Bai ce komai ba ya tsaya yana kallon ikon Allah. Farida ma kau da kai ta yi kaman ba ta gan shi ba tana jira su Tasallah su ƙarasa fito da kayan.
Sai da su ka gama Farida ta ce " ba'a manta komai ba ko?"

Tasallah ta ce duk kayan da ta ce a ɗauko an ɗauko.
Farida ta sa kai ta shiga mota dreba ya ja mota su ka fita a compound ɗin. Najeeb na tsaye a wajen yana ganin ikon Allah. Ran sa kuwa yai matuƙar ɓaci, mi Farida ke nufi da shi.

Ya isa cikin gidan da ƙyar saboda ciwon kai da ya fara ji saboda ɓacin rai. A hankali ya ke maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun saboda ya samu nitsuwa...


........................


Farida kam gidan su Najeeb ta wuce da Yaman. Da ta je a falo ta samu Mom da Najdah suna hira, itama ta zo gida.

"Oyoyo angona" Mom ta faɗa tana ƙarɓan Yaman a hannun Farida.

Shigowa da kaya da Danliti ya farayi ne ya sa Mom tambayar ko lafiya.

"Na kawo miki ɗan yaye ne"

"Ɗan yaye?" Mom ta faɗa tana sake kallon Yaman da ke hannunta. Yaron da watan shi bakwai da sati biyu ne a duniya.

"Mom yaron bai damu da nono ba, shima rashin son cin abinci kaman uban sa. Shi ne na ce gara na yaye shi"

"Amma Anty Farida da kin bari ya cika shekara ɗaya, Yaman fa bai da wani ƙwari" Najdah ta faɗa tana kallon Yaman ɗin da ke murmushi saboda Mom da ke ma sa wasa.

"Kema kina hanya ai za ki ji yadda ake ji. Allah ya kaimu nan da wata biyu lafiya"

Najdah ta yi shiru dan itama fama ta ke yi da kanta. Ta wahala sosai da wannan cikin tun yana ƙaramin sa har yanzu kuwa.

"'yata ki bari Yaman ya kai 10 months mana, Najeeb ma a wata goma na yayeshi"

"Mom ki yi haƙuri dan gaskiya na yaye shi daga yau"

Mom ta kalli Faridan da kyau ta yi murmushi dan ta lura kaman Faridan na ɗauke da ciki ne...

Sai bayan sallar Isha Farida ta dawo gida. A falon sama ta samu Najeeb yana zaune sanye da baƙar jallabiya yana jan carbi.

"Barka da hutawa" ta faɗa tana ƙoƙarin tafiya ɗaki tunda har yanzu ba wai sun shirya ba ne.

"Aysherh" ya kira sunan ta a hankali.

Tsayawa ta yi tana jiran mi zai ce.

"Zo ki zauna?"

Ba musu ta dawo ta zauna a gefen sa.

"Ina ki ka kai min ɗa na?"

"Gidan kakannin sa"

"Why?" Ya faɗa yana ma ta kallon tuhuma.

"Na yaye shi ne, shi ne na kai mu su shi"

"Da izinin wa?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi.

"Kai ne fa ka ce kar abinda ya samu cikin ka, lafiyata da lafiyar Yaman ya sa na yaye shi dan na kula da wanda ke cikina yanzu"


"And you made the decision without me"

"Ya ka ke so na yi, fushi ka ke da ni, ba ka min magana balle na gaya ma ka zan yayi Yaman"

Yana son yin magana amma idan yai hankalin sa ne zai tashi saboda ɓacin rai da ke cin sa.

Miƙewa yai ya ce " tunda banida matsayin da za a yanke shawara tare da ni, shikenan ki yi duk abinda ki ke so. Wanda ya ke cikin ki ma idan ba kya son sa ki yi waje da shi kar ya takura ki ya sa ki tsufa da wuri"...

"Ba haka ba ne My Champ, Wallahi..." ta tsayar da maganar saboda wucewa da yai ɗakin sa ba tareda ya kalleta ba...

Yadda ya ke magana ta san ran sa a ɓace ya ke. To ba ya ma ta magana ya yake son ta sanar da shi shawaran da ta yanke...
............


Waɗannan kwanaki huɗun sun fi kowani rana zafi a gareta. Idan ka cire lokacin da Naomi ta ma sa asiri, Najeeb bai taɓa shareta kaman na wannan kwanakin ba. Ba ya dawowa daga office sai ƙarfe goma ranan da ta je office kuma yadda ka san kwandon shara haka ya maidata ko kalma ɗaya bai ma ta ba. Lokacin da ta ke bashi haƙuri ma miƙewa yai ya bar ma ta office ɗin.

Shi kam Najeeb daga office gidan su ya ke wucewa ya je ya zauna da ɗan sa. A kwana na biyu Mom ta ma sa maganar ko zai tafi da Yaman ne, ya ce ta bar shi Farida na da ciki shiyasa ta kawo shi...


Ba abin da ya kai zaman lafiya tsakanin miji da mata daɗi. Farida har rama ta yi saboda fushin da Najeeb yai da ita. Yana dawowa da dare zai shiga ɗaki ya kulle sai kuma da safe.

Yau kam ta watsar da duk makaman yaƙin ta, ta ɗaga farar tuta. Tana son mijin ta, ga shi ko cikin ne ko minene dai 'yan kwanakin nan da su ka yi ba sa tare ba ƙaramin kewar shimfiɗar mijin ta ta ke yi ba.

Zuwa ta yi aka ma ta ƙananun ƙitson bare-bari saboda Najeeb ya fi son ya ga ta yi ƙitso compared to barin gashin haka nan ba kitso, aka ma ta jan lalle mai kyau ya fito da kyaun ƙafarta da hannun ta.

Ta haɗa madara zuma da lalle ta shafe jikin ta da shi, da yai awa ɗaya ta shiga banɗaki ta kakkaɓe sannan ta yi wanka da shower cream mai ƙanshi.
Dama tunda rana ta blending kankana da apple da lemon ta sa a fridge yai sanyi. Da ta gama shiryawa ta sa dogon hijab ta sauƙa ƙasa ta je ta ɗauko juice ɗin ta, tana zaune bayan sallan Isha tana shan juice ɗin tana kallon wayarta ko za ta ga saƙon sa amma shiru. Tun ƙarfe biyar ta tura ma sa text akan dan Allah ya dawo da wuri, sai dai bai ma ta reply ba.
Ƙarfe tara da rabi ta ji horn ɗin mota ta yi hamdala a zuciyarta...


.......

Ya fito daga wanka kenan ya ji ana buga ma sa ƙofar ɗaki. Ya sani sarai ita ce amma ya share. Ganin ancigaba da bugun ba a daina ba ya sa ya je ya buɗe.
Tsaye ta ke ta sha light make up a fiskarta, jikinta na fidda wani ƙanshi mai jan hankali, tana sanye da doguwar night robe baƙa.


"Yes, what can i do for you?" Ya faɗa yana kallon ƙwayar idon ta.
Ba ta yi magana ba, ta sa hannu ta zarge igiyar robe ɗin da ta sa, a hankali robe ɗin ya sulluɓo ƙasa.

Idon sa ne ya fara tracing ɗin jikinta tun daga sama har ƙasa. Haɗiyar miyau kawai ya ke saboda yadda ran sa ke ayyana ma sa abubuwa dayawa. Wata arniyar lingerie ta saka, wato yadda ka san an sa igiya an matse ƙasan breast ɗin ta haka nonuwanta su ka ɗago sama su ka cika tam cikin raga-ragar rigan. Riga ce da ta bayyana ko'ina a jikinta.

Da wata mitsitaiyar murya ta ce " in shigo?"

Gyaran murya yai yana ƙoƙarin saita nitsuwar sa, kusan 3 seconds kafin ya matsa daga bakin ƙofar ta shigo. Yana ƙoƙarin janyo ƙofar ya ji ta kwanta a bayan shi.

"Mijin na, abin alfahari na, jarumin namiji" ta faɗa tana wasa da kunnen sa duka biyu. A hankali ya juyo saboda gwiwowin sa da su ka yi sanyi.

"Mi ki k..."

"Shhhhh, ni ce da magana ba kai ba" ta faɗa tana sa yatsar ta ɗaya akan lips ɗin sa tana wasa da shi. Ɗaya hannun kuma ƙasa ta yi dashi tana gaisawa da abunsa da ke ƙoƙarin leƙowa waje ta cikin towel ɗin da aka rufe shi.

"Na yi ba dai-dai ba. Ka na da dukkan dama akan Yaman da ni kai na, ka yi haƙuri dan Allah. Ka yafemin My Crown, My King, My Hero, My Mr BLTD"

Zai yi magana ta rufe bakin sa da na ta. Yayin da hannun ta ya ratsa cikin towel ɗin yana yiwa BLTD wasa.

"Aysherh you know..." ya faɗa lokacin da ya samu damar breaking kiss ɗin.

Hawayen da ya gani a idon ta ya sa ya kasa ƙarasa maganar.

"Ka yafe min dan Allah" ta faɗa da muryan kuka.

Sake haɗe bakin su yai su ka cigaba da abubuwa, tuni Farida ta warware, dama hawayen na kissa ne...


...........................

Wannan cikin kam ya sa Farida cikin yanayi na saurin fushi da faɗa. Da farko farkon cikin dai abin da ɗan sauƙi amma cikin na ƙara girma abin na ƙara gaba. Ba sa sati ba su yi ƙaramin faɗa da Najeeb ba. Ga shegen kishi, sau biyu ta ke zuwa office a sati amma da ƙarfi ta maida shi duka kwana biyar ɗin. Indai ta ga mace ta shigo wajen Najeeb to haka za ta je ta zauna da su ayi duk maganan da za a yi a gaban ta. Tun Najeeb na tanka ma ta har ya haƙura ya daina kulata dan ya lura idan ya kulata ma shine ke ƙara ma ta ƙarfin gwiwa...



Bayan wata biyu da sati ɗaya Najdah ta haifi ɗan ta namiji. Ranan suna aka yiwa Najeeb takwara. A gidan sunan kuwa sai da Farida ta yi halin ta. Fauziyya sabuwar ma'aikaciya ce a Najeeb constructions, Architect ce da ta yi karatu a South Africa, asalin iyayen ta Nupawan Minna ne, amma sun jima suna zaune a Kano. Yarinyar ba ta da girman kai ga ta da yawan fara'a. Guruwa ce dan first class ta fita da shi.

A matsayinta na ma'aikaciya a Najeeb constructions ta zo sunan Najdah tunda Anas Ogan ta ne. Amma daga zuwan ta Farida ta fara yaɓa ma ta magana. Wai ta zo shishshigi da neman suna. Fauziyya ba ta kulata ba haka ta ajiye ledar da ta kawo ta fita ko babyn ba ta ɗauka ba...

Abun bai tsaya a nan ba, da dare da Farida ta dawo gida haka ta kama yiwa Najeeb faɗa wai ya turo budurwarsa ta zo ta yi gaisuwa.

"My Goodness Aysherh. Fauziyya is a staff @ the Company. Ta je gaishe da matar Ogan ta miye laifi a ciki?"

"Ni dan Allah ka koreta, ba ta min ba. Idan ta zo wajen ka ta dinga buɗe haƙora kenan tana ma ka tallan open teeth ɗin ta dan wannan ya fi ƙarfin wushirya"

"Fauziyya is good, wata biyu da ta fara aiki da mu i saw potential in her, i saw raw talent. Kuma kin san ba na ɗaukan ma'aikata sai ma su ƙwazo"

"Ni gaskiya ka koreta, ba ta min ba. Idan ba za ka iya ba ni zan koreta"

Rasa abin cewa yai ya tashi a falon ya ba ta waje...


Kwanaki su na tafiya, lokaci na gudu. Fauziyya kam tana shan magana a wajen Farida sai dai abu bai kawota office ɗin Najeeb ba. Yarinyar ba ta taɓa tankawa Farida ba, tana mugun respecting ɗin ta. Domin ta ji labarin bajintar da Faridan ta nuna lokacin da Najeeb ya ke kwance a asibiti...

..............

Yau ma Najeeb shiryawa ya ke zai je wani taro Kaduna. Saboda faɗan da su ka yi ɗazu ya sa bai ce ta haɗa ma sa kayaba ya fara haɗawa da kan sa.
Har ta shigo ta zauna bai yi alamar ya gan ta ba.

"Wannan karan ma da Fauziyyar za ka tafi?"

Ya cigaba da abinda ya ke ba tareda ya tanka ma ta ba.

"Tambaya fa na ke dan na ga Fauziyya ce 'yar gaban goshi a Kamfani yanzu"

" Aysherh please, ba na son tashin hankali"

"Wallahi indai da ita za ka je sai dai mu tafi tare. Ba za ayi irin tafiyar ku Portharcort ba"

Sai a lokacin ya ɗago yana kallon matar ta sa. Cikin ya sa ta yi ƙiba ga baƙi da ta yi. Ba kaman lokacin cikin Yaman ba da ta yi haske ta yi kyau, wannan kam banda faɗa ba abinda ya ke sata whilst cikinta na farko ya sa ta cin abinci kamar gara.

"Queen Aysherh, my heart belongs to you, my love is only for you. Mun je Portharcort as a team ba wai na ɗau mace na tafi Portharcort ba. Ni, Yakubu, Hassan, Peter and Fauziyya. As a team Aysherh, ki dena yi min mummunan fassara"

Ta turo baki ta ce " to ai a hotel kuka kwana, Allah kaɗai ya san mi ya faru a wajen"

Maganar ta ma sa ɗaci, amma ya shanye dan yana ƙara magana ɗaya anan sai ta Allah, dan Farida idan ta fara masifa ka ɗauka dukan sa za ta yi. Yai shiru kawai yana sauraron maganganun ta wanda su ka fi kama da tuhuma...

..........


Washegari da sassafe ya fita, ruwan tea kawai ya sha ya fita har ya kusa kai wa bakin ƙofa ya dawo ya manna ma ta kiss a goshi ya ce " sai na dawo"

Sai alokacin Farida ta saki ranta ta ce " Allah ya kiyaye hanya ya dawo da kai lafiya" ya amsa da amin sannan ya fita...

Shiru- shiru har ƙarfe uku Najeeb bai kira ba bai kuma turo text ba. Ina Kano da Kaduna ace tun bakwai saura da ya tafi bai isa ba. Da farko ta ɗauka ko dan maganar jiya ne amma yanzu kam hankalinta ya tashi dan duk faɗan da su ka yi ko text zai tura ma ta ya ce ya isa.
Ta fara kiran numbar sa switch off, ta kira numbar Abdullahi dreba shima switch off. Nan jikinta ya hau rawa ta shiga kiran Mom. Tambayar Mom ta yi ko Najeeb ya kirata ta ce ma ta a'a.
Cikin kuka ta ce "Mom ki tambayamin Daddy ko sun yi magana da shi"...


Zaune su ke a falon kowa yai jugum saboda rashin sanin halin da Najeeb ya ke, da shi da dreban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login