Showing 27001 words to 30000 words out of 145203 words

Chapter 10 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25680

bari ba"

"Eh yayana, zan ajiye aiki da ku"

"Gaskiya ban yarda ba. Ai hutu kawai za ki yi na sati zuwa kwana goma ki dawo bakin aikin ki"

"Ya Anas Ummi na ba ta so, ta ce na ajiye aikin"

"No Farida, Najeeb needs you. Ki ba wa Ummi haƙuri ta barki ki dawo dan Allah"


" to bari mu ga ni dai. Na gode Yaya"

Sai da za ta fita daga motar ta ce " Ya Anas ya jikin Sir Najeeb?"
" da sauƙi ƙanwata" ya faɗi yana murmushi...

Ita ɗin ma da ta shiga gida sai ta ji kamar ba za ta iya haƙura da aikin ba. Musamman idan ta tuna bikinta da Rayyan zai iya kaiwa wata shida ma su zuwa...

Washe gari su ka wuce Jos ita da Ummi bayan ta yi welcome back ɗin layinta.


.....................



Yana zaune a kujerar sa yana duba wasu files amma hankalin sa na kan wayar sa, jira ya ke ya ga ko an turo ma sa saƙo. Sai yanzu yai da na sanin ƙin bin Anas da yai ranan. Ko ba komai da ya ganta ya tabbatar lafiyar ta ƙalau.

Duk da ya san ba ta da numbar da ya tura saƙon. Ya ja dogon tsaki ganin har awa ɗaya kenan da tura saƙon na shi amma ba amsa, saboda ka da ta gano shi ma ya sa ya ke rubuta saƙonnin da Hausa. Da ya gama duba files da takardun da ke gaban sa ya tashi ya fita a office ɗin. Ganin kujerarta wayam ba kowa ya sa shi jin wani abu a zuciyar sa, ba dai da gaske barin aiki za ta yi ba. Kai tsaye office ɗin Anas ya wuce wanda ba nisa da na shi office ɗin.

Waya ya samu Anas na yi lokacin da ya shigo, ya samu waje ya zauna yana kallon sa.

"Miss Salihu ta bar aiki ne?" Ya faɗa da harshen ko in kula lokacin da Anas ya gama wayar.

"Ka fara kewar ta ne?" Anas ya amsa ma sa

"Oh please, ka amsa min tambayata ba na son shirme"

Dariya Anas yai sannan ya ce " well, ta ce za ta dawo amma sai Monday"

"Monday is too far"

"Mutumina da alama ka ƙagu ka ganta ko?"

Tashi Najeeb yai ya ce " idan ba ta dawo Monday ɗin ba, ka nemo min wata sakatariyar"

Anas ya ɗan yi dariya ya ce " kamar da gaske"......


...........


Ghana-must-go manya guda biyu ne a gabanta tana faman jera kayan gwanjo da ta saro da za ta kai Kano.


Adiyya wata jikar Nanna ta miƙo ma ta waya wai ana ta kiranta tun ɗazu.
Amsa wayar ta yi ta ranƙwashi kan yarinyar wadda ba za ta wuce shekara takwas zuwa tara ba. "Na hana ki ɗaukan wayata ba kya ji ko. Yanzu jiba yadda kuka cinye min chaji"

"Allah Anty ba ni kaɗai bane har da Mubashshir, shi ne ya ke game, ni kallon hotuna kawai na ke yi" yarinyar ta faɗa tana shafa wajen da Farida ta ranƙwasa.

Duba wayar ta yi ta ga missed call ɗin Maijiddah ne da na sister Munibat sai saƙo guda ɗaya wanda wani number ya turo. Numbar na yawan damunta da saƙo tun lokacin da ta yi welcome back ɗin layinta. Ta buɗe saƙon ta karanta kamar haka.

*fatan ki na lafiya Aysherh? Ina so ki yadda da ƙaddarar da ta same ki, ki ɗauke shi a matsayin jarrabawar Ubangiji. Zai fi ki koma al'amuran rayuwar ki kamar da, ba tareda wani tsoro ba. N J*


Tsaki ta yi ta ce " shi wannan N J ɗin sai shegen naci, ka kira ba za ka kira ba, sai gatan tura saƙo kamar kamfanin Airtel."

Ta tura masa reply kamar haka *" Malam NJ ko Mr NJ, koma wa ka ke dai, ina ma ka gargaɗi da ka dena turomin saƙo, saboda ni matar aure ce. Idan ka cigaba kuwa duk inda ka ke, mijina zai nemoka kuma ba za ku wanye lafiya ba"*

Sai da ta tura saƙon ta ke ƙara alhinin wannan NJ ɗin wanda take tunanin ƙila cikin abokan Yakubu ne da su ke aiki tare a Najeeb constructions. Idan ba haka ba ta ya NJ zai san an kidnapping ɗin ta har ma ya san ta ji ciwo a ƙafa. Ƙafarta ya fara tambaya ranan da ya fara turo saƙonsa wanda kuma ta san idan ba Yakubu da Anas ba ba wanda ya san ta ji ciwo a wajen aikin su. Ta kawar da tunanin ta hanyar kiran Maijiddah dan ta ji mi ye labari...

Yana zaune ya ji ƙarar shigowar saƙo. Ya ɗauki waya ya duba, sai da ya karanta sannan yai murmushi dan ya san yanzu kam ta samu lafiya tunda har ta iya ma sa reply.


.........................


Yau sammako yai a office dan ko mai shara ba ta yi aikinta ba lokacin da ya shigo. Fakewa yai da cewa wasu ayyuka zai ƙarasa a office ɗin lokacin da Najdah ta tambayi dalilin fitarsa da wurwuri haka. Duk da kuwa dama shi ɗin mai fitar wuri ne amma na yau daban ne...

Har ƙarfe takwas da rabi ba ita ba alamarta. Haka dai ya ke aikin na shi ba tareda samun kwanciyar hankali ba...

Tun takwas saura ta zo, ta fara biyawa tana tallen gwanjon da ta saro a office-office da ke hawa na farko da na biyu. Sannan ga uwa uba labarin kidnapping ɗin su da ta ke bayarwa ga duk wanda ya ma ta jaje. Ba ta ankara ba tana office ɗin sister Munibat ta ga ƙarfe tara har da kwata.

"Kai ashe haka lokacin ya tafi barin je na kama aiki kafin Sir Najeeb yai ƙuli-ƙulin Kubra da ni"...



"Najeeb na samo ma ka wani secretary, he's a good guy idan ka amince zai fara aiki gobe"

Ya kalli Khalidah kallon ki na da hankali kuwa.

"Ban sa ki wannan aikin ba. Idan ina buƙatar secretary na san inda zan nema"

"Najeeb, sati ɗaya kenan wancar shashashar ba ta zuwa. Na san abinda ya faru ne ya sa ta ƙi dawowa, ni wallahi da da su...."

"Out"

"Najeeb.."

" i said get out"

Khalidah ta kai maƙura wajen ɓacin rai amma ba yadda ta iya dole ta kwantar da kai idan tana son samun Najeeb.

"Shi kenan zan fita amma ka yi tunani"

Tsaki ya ja sannan ya cigaba da aikin da ya ke akan system ɗin sa.

Shigowar Farida kenan Khalidah ta fito daga office ɗin Najeeb.

"Ina kwana Anty" Farida ta faɗa dan abinda ta ke kiran Khalidar da shi kenan idan tana son tunzurata. Khalidah irin matan nan ne da Allah yai wa baiwar jiki da tsayi.

" da kin rufawa kan ki asiri kin bar aikin nan da zai fi mi ki, dan ni Khalidah sai na sa Najeeb ya kore ki daga aiki"

"haba Anty! daga zuwa na. Ba ga ruwa balle ya hanya?" Farida ta faɗi tana farfari da ido.

Khalidah tai tsaki ta tafi...



"Sir Najeeb Ina kwana" ta faɗi lokacin da ta shigo office ɗin sa. Bai ce komai ba bai kuma ɗago ba.

"Miss Salihu you are late"

" na san ba ka son latti Sir, a min afuwa na yau ne kawai"

Sai a lokacin ya ɗago idon sa ya kalleta.
Shigar riga kalar maroon ta yi sai wando kalar ash da jacket shima kalar ash, ta yi ɗaurin turban da ɗankwali kalar maroon.

"Sir Najeeb ka gama kallon da kyau. Duk haɗuwar da na yin nan gwanjo ne ajikina, grade one ma kuwa. Kuma akwai irin su-irin su da na saro ko da za ka ɗaukawa ƙanwar ka ko..."

"Miss Salihu, go back to your office" ya faɗi yana sauke idon sa

"Haba Sir, ba sannu, ba ya jiki, ba..."

Wani file ya miƙa ma ta ya ce " ina son aikin nan cikin minti goma"

Ƙarɓan file ɗin ta yi a hannunsa tana kumbure-kumbure har ta fice daga office ɗin...


*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣1️⃣1️⃣








A kishingiɗe ta ke a kan kujerarta bacci ya sace ta. Tun ƙarfe goma da ta gama aiki ba abin da ta ke yi, chatting ta ke yi a waya baccin ya sace ta.

"Miss Salihu...Miss Salihu" ta yi firgigit ta farka. Kallon sa ta farayi tana murza ido.

"Biyo ni"

Kafin ta wartsake ta tattara office ɗin tuni ya fita.
A hawa na farko ta sameshi yana yiwa wasu bayani. Anas ne ya ce ma ta yana ƙasa, dan da ba ta san inda yai ba.

Tana tsaye tana ƙoƙarin saita kan ta saboda har lokacin ba ta gama wartsakewa ba ta ga yai hanyar parking lot na kamfanin. Da sauri ta bi bayan shi tana jiran ƙarin bayani amma bai ce komai ba. Sai da su ka iso wajen motar sa ta ce "Sir fita za mu yi ne?"

"Shiga mota" abinda ya iya cewa kenan. Sai da ta zauna da kyau sannan ta kalleshi ta ce "Sir da ka gayamin fita za mu yi ai da na ɗan gyara fiskata ko. Yanzu ko ɗan hodan nan ban ƙara tisawa fiskata ba, fiskata ta yi wani bauu"

" Miss Salihu ina so ki sa a ran ki cewa wannan kamfani ba fashion industry ba ne inda ake gudanar da fashion shows. This is a constructions comp...."

"Daɗina da kai Sir Najeeb akwai wasge mutum. Kuma dan ina aiki a kamfani irin wannan sai ba zan yi ado ba. Yanzu idan a yamutse na ke fitowa kai kan ka ba za ka ji daɗin aiki da ni ba, balle ma su zuwa wajenka kullum"

"Miss Salihu..." ya faɗa da ɗan ƙarfi

"Sir Najeeb ina neman alfarma dan Allah"

Ɗan juyowa yai ya kalleta na ɗan daƙiƙai sannan ya maida hankalin sa ga tuƙin da ya ke yi.

"Sir dan Allah ka dena kirana da Miss Salihun nan. Shi fa Salihun nan yana chan kwance cikin kabari amma ka dinga kirana da sunan sa. Ga Aisha ga Farida duk bai maka ba, sai ka kirani da Salihu" ta ɗan yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce "Salihun ma fa a hoto kawai na ganshi ban ganshi a zahiri ba, amma abi a dameni da Miss Salihu Miss Salihu"

Wannan karan muryarsa a kausashe ya ce " our relationship is strickly formal Miss Salihu. So ba abinda zai sa na kira ki da first name na ki"


"Abin ai son kai ne. Ita sister Munibat ai Miss Munibat ka ke kiranta ba Miss AbdulHamid ba. Ga wancan ƙatuwar nan Khalidah, itama sunan ta ka ke kira. Sai ni ne za a raina a dinga wani yaɓa mani Miss Salihu kamar wata marar suna. Gaskiya Sir ka dinga kirana da suna na nima"

"Or what?" Ya faɗi yana kallon ta

"Sir ni dai ka gyara dan Allah"

Bai sake cewa komai ba har sai da su ka iso inda za su je. Ya ce ta fito kuma ta kimtsa kan ta baya son yawan surutu. Wani ɗakin taro ya shiga ya barta a reception wai ta jira shi.

Kusan awa ɗaya yai a wajen sannan ya fito. Tunda su ka bar wajen su ke tafiya tun tana shiru-shiru har dai ta kasa jurewa ta ce "Sir Najeeb wai garin za mu bari ne kam?" Bai kulata ba sai ma ƙara volume ɗin kiɗan da ke tashi a motar da yai.
Haka ta haƙura ta yi shiru har su ka isa wajen. Tana fitowa a mota ta fara miƙa tana cewa " kai! yau na zaunu gaskiya. Irin wannan nisan waje haka"

Wani site ne da kamfanin su ke ginawa ya zo dubawa. Bayan zaunuwa to Farida ta taku domin kaf wajen sai da su ka zaga duk girman shi. Su kan tsaya da wasu ma'akata yai mu su tambayoyi da 'yan bayanai. Anan ta ke ɗan rubuta wa su abubuwa kamar yadda ya buƙata.

Ƙarfe uku sai ga kiran Anas ya shigo wayar sa. Lokacin su na hanyar dawowa. Yana ajiye wayar ya kalli Farida da ta yi lanƙwas a motar ya fara faɗa.

"Miss Salihu are you nuts?"
(Miss Salihu kin yi hauka ne?"

"Kin fixing meeting da Mr Abraham ƙarfe uku ba tareda kin gayamin ba a wani dalilin?"

"Sir, ba ka ce min za ka fita ba ai. Kuma mantawa na yi"


"To hell with mantuwar ki. Miss Salihu, akwai dubban mutane da su ke neman aikin nan, idan ba za ki yi aiki da kyau ba zan kore ki"

Shi kan sa sai abin ya zamo ma sa banbaraƙwai wai 'zan kore ki' ba ma 'na kore ki ba' kamar yadda ya saba faɗi.

"Sir Najeeb dan Allah ka dena ɗaga min hankali, dududu yaushe na dawo aiki bayan wannan iftila'in da ya sa me mu. Irin wannan rashin godiyar ne ya sa wallahi aikin nan ke fita min a ka. Ga shi mutum duk ya fiffige saboda aiki amma ba ka gani. Ni mutum ce kuma ba abun aibi ba ne ace na yi mantuwa tunda yana kan kowa"

Yana son maida ma ta martani amma ya rasa me zai ce. Yawan maganarta shi ne abu na farko da ya ja hankalinsa ranan da ya fara ganinta a restaurant, haka nan har yau bakin nan na nan. A kowani lokaci tana da abin faɗi choichoichoi. Tunowa da yai da kama su da aka yi da irin surutun da ya sha, ya sa ya san wannan Aisha Faridan a ko ina sai ta yi magana ba ta iya yin shiru......



............................

Tana zaune tana typing memo Anas ya shigo office ɗin ta.
Sir Najeeb ya jima da fita kuma a yadda ya ce ya tashi kenan saboda zai daɗe. So ta ke ta ƙarasa abinda ta ke yi ta tafi itama duk da kuwa ƙarfe biyu ne saura. Ciwon cikin period ke damunta tun safe shiyasa ta ke nan laƙwas ba kuzari sosai duk da kuwa ta sha magani ya lafa ma ta kaɗan.

" 'yar uwa yau ba zoɓo ne? Kin san i'm addicted to your zoɓo"

" Ya Anas ban yi ba yau. Ni zoɓon ma zan dena gaba ɗaya tunda Sir Najeeb ya nuna indai na cigaba da sana'a a office to cikin albashina"

"Ya Najeeb zai ma na haka kuma?"

"Hmm kaman ba ka san shi ba, watan da ya wuce da ya zare 40% ai har yau shiru ka ke ji. Wai jiya Halima tana duba gwanjo anan da ya shigo ya gani haka ya dinga faɗa har da cewa wai ya ƙara ganin na buɗe hajata a office zai cire 10% a cikin albashina. Kuma fa ya Anas lokacin break ne ba wai a lokacin aiki ba"

Anas yai murmushi ya ce " kin fara gajiya da shi ne Farida? Ko za ki bar aikin?"

"Yaya kenan. Ni fa idan ka ga na ajiye aikin nan to aure na yi, na gano take-takensa ai, dama so ya ke na yi wani abu ya koreni. Mutum sai shegen taurin rai"

"Well, ni na ga alamun tun fara aikin ki da shi ya chanja, he's becoming more tolerant now. Allah! Farida da Najeeb ɗin da ne da tuni kin bar aiki a nan"

"Hmm shi ya sani, wai ace mutum yai ta haɗe rai shi kaɗe ya ƙi shiga jama'a. Ai jama'a Rahama ne"

"Kowa da irin rayuwarsa 'yar uwa"

Har zai fita ya ce " ki ji har na manta. Akwai baƙin da za su zo gobe wajen Najeeb, ki scheduling lokacin meeting da su sannan ki sanarwa Najeeb on time kar ayi irin ta ranan"

"Ai ranan na sha kwarwa. Allah, Ya Anas na ɗauka mari na zai yi yadda ya dinga banbamin nan"

"Sai ki kiyaye"...

Yana fita ta cigaba da aiki, tana so ta ƙare ta tafi gida da wuri dan kar ta yi staining dan ba ta zo da pad ba, ta ajiye a bakin gado za ta sa a jaka ta manta shi a wajen.

Minti ishirin ta haɗa komai sannan ta turawa Najeeb lokacin meeting ɗin sa ta email. Tana kan tattare kayanta Halima ta shigo.

Halima Baballe tana aiki a hawa na ɗaya ne a HR department. Halima irin matan nan ne ma su gutsuri tsomi, 'yan haɗa waje. Bazawara ce aurenta biyu tana fitowa. Tun farkon zuwan Farida ta ke ƙoƙarin manne ma ta sai dai Faridan ba ta bata dama ba. Yawanci su ka haɗu a masallaci haka za ka ga tana liƙewa Farida tana kawo gulma da zunɗen mutane duk dan ta samu fada a wajen Farida tunda Farida sakatariyar Sir Najeeb ce, kuma kusan kowa a kamfanin yana son samun kusanci da Sir Najeeb.

"Anty nah Anty nah, ba dai kin tashi ba" ta faɗi tana washe baki

"Zan tafi gida, Sir Najeeb ba zai dawo ba kuma na gama aiki na"

"Sai na ga kin min wani lakwas, lafiya kuwa?"

"Halima yau ba na jin magana. Mi ya kawo ki?"

" Anty na kenan, baƙon wata ya zo kenan"

Farida ta yi tsaki ta saƙale jakarta a kafaɗa ta ce " mi ya kawo ki?"

"Anty na, za a yi bikin 'yar yata nan da sati biyu kuma wallahi adashen da na ke jefawa akwai mutum uku a gabana kafin na amsa shine na zo ko za ki ara min kuɗi?"

Kallon sama da ƙasa Farida ta ma ta sannan ta ce " kar ki kawo min rainin hankali nan wajen. Yaushe mu ka haɗa hanya da ke da har zan ba ki aron kuɗi na?"

Halima ta yi dariya tareda ɗan dafa kafaɗar Farida ta ce "ƙawata kenan..."

"Cire hannun ki a jikina tukunna" Farida ta katse ta

" duk yadda na ɗauke ki da zuciya ɗaya amma ke har yau ba ki ɗauke ni haka ba. Ita Sister Munibat ɗin da ki ke maƙalewa an gaya mi ki son ki ta ke? Kwanaki fa har cewa ta yi ke 'yar ƙwaya ce"

"Dalla gafara daga nan. Ba na son munafurci, halin ki na haɗa guri ya sa ba na son mu'amala da ke, idan da ba ki sani ba ki sani"


Halima ta ɗan haɗa rai ta ce " na rantse da Allah Munibat ta ce wai ke 'yar ƙwaya ce"

Farida ba ta ce komai ba ta ce biyo ni.
Tiryan-Tiryan su ka wuce office ɗin Sister Munibat inda ta ke ta faman aikin zane.

"A'a Sister Aisha ke ce tafe, ban ganki a masallaci ba ko lafiya?"

Farida ta kalli Sister Munibat sannan ta kalli Halima ta ce " maimaita abin da ki ka faɗa a office ɗina"

Halima ta ji ras dan ba ta ɗauka abinda Farida za ta ce ba kenan. Ta ɗauka su na zuwa za ta fara yiwa Sister Munibat masifa.
Sai dai kamar yadda ta ke pro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login