Showing 141001 words to 144000 words out of 145203 words

Chapter 48 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25696

sa duk wayoyin su a kashe.
Daddy dai baya nan dan ya fita kai report ko zai ji labari ko anyi hatsari hanyar Kano to Kaduna.

Najma na jijjiga ɗan ta Bobo da ke kuka wayar Farida ta fara ringing Farida ta yi saurin tashi ta ɗau wayar da ke kan centre table. Ganin My Champion ke kira ya sa ta fara murmushi.

"My Champ saura kaɗan na mutu yau, ina ka shiga? Are you Ok"

"Yana nan lafiya idan har kun amince da sharuɗɗan mu" muryan wani ƙato ya doki kunnen ta.

"Waye, mi kuka yiwa mijina? Ina mijina?" Tambayoyin da ta fara jerowa kenan.

Jin maganarta ya sa Mom tashi da sauri ta amshi wayar ta sa a speaker tana faɗin " ina Najeeb?, mi ku ke so"

Mutumin yai wata mahaukaciyar dariya sannan ya ce " Najeeb Adam Jibo yana nan lafiya until kun fanshi ran sa a wajen mu"

" what do you want?" Mom ta faɗa tana danne hawayen ta.

"200million" ya faɗa a taƙaice.

"Ka bawa ɗana mu yi magana"

Mutumin ya sawa Najeeb waya a kunne.

"Mom i'm ok, ku kwantar da hankalin ku." Jin kukan Farida ya sa shi cewa " My Queen dan Allah ki dena kuka"

Mutumin ya ƙarɓe wayan ya ce " kun ji shi dai yana raye, nan da 24hrs idan ba mu ga kuɗi ba za mu aika shi lahira" daga haka ya kashe wayan.

"Hello Hello" Mom ta faɗa amma shiru, sake kiran numbar ta yi amma ta ji shi a kashe.

Farida ta dafa kafaɗan Mom tana faɗin "Kashe shi za su yi ko? Kashe min shi za su yi ko?"

Ƙoƙarin faɗuwa ta ke yi Mom ta riƙota tana kiran sunan ta amma....



*Jirgin SAKATARIYA TA yana shirin sauka jama'a, jirgin ya yi wata ɗaya da 'yan kwanaki yana lulawa a sararin samaniya kuma Alhamdulillah yana daf da sauka da daren yau Insha Allah. Da fatan Team Najeeb da Team Farida za su yi cincirindo a filin jirgi su ga saukan mu sannan su bamu masauki mai kyau. Wanda su ka supporting ɗina by paying to read this novel Jazakumullahu khairan. Wanda su ka karanta ta bayan fage kuma...*




Skt 60


Haihuwa ne ya taso wa Farida gadan-gadan bayan sun kaita asibiti wurjanjan. Ba ƙaramin wahala ta sha ba kafin ta haihu dan sau biyu tana suma a wajen. Lokacin da 'yar ta fito gaba ɗaya ta gama galabaita jinin ta ya hau sosai, ga azabar haihuwa ga kuma tashin hankali.

Saboda yadda ta rikice dole sai da su ka ma ta allurar bacci.
Tun a asibiti Mom ta kira Daddy ta sanar da shi halin da ake ciki daurewa yai ya ƙaraso asibitin dan hankalinsa ya mugun tashi.
Lokacin da ya iso Mom na ɗauke da jaririyar da ke kama da uwar ta sak. Ya karɓi jinjirar yana ma ta addu'a...

Bayan an tabbatar ma sa da lafiyar Farida ƙalau sannan ya bar asibitin saboda ya je ya sanar da jami'an tsaro...

Wannan karan waɗanda su ka kama Najeeb da Abdullahi ba ƙananun kidnappers ba ne domin duk yadda ake ƙoƙarin gano inda su ke abin ya faskara. Washe gari Daddy ya je bank aka fara ƙoƙarin cire kuɗi, abu da manyan mutane cikin abinda bai fi awa uku ba aka gama haɗa 200million...


......................


Ummi ce ke zaune gefen Farida tana riƙe da baby tana ɗan shafa bayanta saboda kuka da ta ke yi. Yarinyar ba dai kuka ba, ga shi uwar ta ko ta kan ta ba ta yi, damuwar da ke ranta ya isheta.

"Farida ki karɓe ta ki ba ta nono dan Allah. Ba ta da wani ƙwari fa"

"Ummi idan su ka kashe shi mutuwa zan yi, ba zan iya rayuwa babu shi ba" ta faɗa hawaye na bin kumatunta.

"Ba na son kina magana kamar wacce ba ta da imani. Rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah ya ke kuma zai kuɓutar da mijin ki Insha Allahu. Tashi ma za ki bata nono dan Allah"

Da ƙyar Farida ta iya miƙewa zaune tana jin duk gaɓoɓin jikinta na ma ta ciwo, ta amshi jinjirar daga hannun Ummi ta fara ba ta nono har lokacin ba ta dena zub da hawaye ba.
Ummin ma tausayin 'yartata ne ya cika ta amma dole ne ta dinga ƙarfafawa 'yarta gwiwa saboda halin da ta ke ciki...

A kwana na uku da haihuwar aka sallameta su ka dawo gida. Yau ɗin ne kuma kidnappers ɗin su ka ce za su sake Najeeb dan jiya aka aika mu su da kuɗin su. Ƙarfe goma Mom, Farida da Ummi su ka iso gidan wanda ke cike da 'yan uwa. Kowa a wajen yana jimamin abinda ya faru ne ana kuma jiran dawowar Najeeb...

A hankali Mom ta taimaka ma ta ta zauna a bakin gado, har yanzu ba wai tana da ƙarfin jiki ba ne kawai dai dauriya ta ke yi.

"Mom zan sha ruwa" ta faɗi tana ƙoƙarin kwantawa akan gadon.
Mom ta ce tana zuwa. Ummi ta kwantar da baby a gefen Farida tana faɗin "ta ma yi bacci ashe"


Tun safe ake jiran dawowar Najeeb har yamma shiru.
Ihun da gidan ya karaɗe da shi ne ya farkar da Farida da ke bacci. A hankali ta buɗe ido tana maida hankalin ta ga abinda ta ke jiyowa. Jin ana kabbara da faɗin Alhamdulillah ya sa ta miƙe tsaye zumɓur ta fita da gudu duk da kuwa yadda jikin ta ya ke very weak.


Tun daga stairs ta hango shi yana murmushi, an yi cirko-cirko ana kallon shi ana kabbara, gefen sa Daddy ne riƙe da hannun sa ɗaya, shima ɗin fiskar sa ɗauke da murmushi. Tun da ta gan shi ta rage saurin da ta ke yi ta koma saukowa a hankali. Hajiya Fatima ce ta fara kallon ta ta ke cewa " Farida Alhamdulillah kin ga sun sake shi ko"

Tsayawa ta yi tana ƙarewa mijin na ta kallo, kayan jikin sa ne tun na ranan da ya fita, kayan sun ɗan yi bututu, akwai tabon ciwo a goshin sa da gefen bakin sa. Sai duhu da yai da alama bai ga ruwa ba a 'yan kwanakin nan.

Ɗago ido da zai yi ya kalleta tsaye ta zuba ma sa manyan idanun ta. A hankali ya cire hannun sa daga jikin na Daddy ya taka zuwa wajenta yana zuwa ya rungumeta tsam ajikin sa kamar zai shigar da ita ƙirjin sa ne. Sun jima a haka kafin Farida ta iya cewa "it's a girl, your princess is born"

"Alhamdulillah ala kulli Haal" ya furta ya na sauke ajiyar zuciya.

Aƙalla sun yi minti biyu rungume da junan su. Hawayen da ya gani a fiskarta ne ya sa shi sa hannunsa duka biyu yana goge ma ta su yana faɗin "Queen ba na son kuka please" sake shigewa ta yi jikin sa tana murmushi...

.......................

Su na shiga ɗaki ta sa key ta kulle. Kafin ma ta gama kullewa ya je wajen gado ya ɗau 'yar sa da ke kwance tana bacci. Ya kissing goshin ta yana yi ma ta addu'o'i.

"She's beautiful, just like you"
Ya faɗa yana kallon Farida. Ganin ba shi da niyyar ajiye yarinyar ya sa ta amshi 'yar a hannunsa ta ce mu je na ma ka wanka. Ta maida yarinyar kan gado kafin ta ja hannunsa su ka shiga banɗaki. Ita ta sa hannu ta cire ma sa duk kayan jikin sa wanda ta san daga yau sun gama aiki dan ƙona su za ayi. Yana tsaye yana binta da kallo ta fara murza ma sa shower cream a jikin sa tana dirje dukkan jikin sa da shi. Da ta gama ta kunna shower ya wanke duk kumfan. Ta tsiyayi shampoo ta sawa gashin sa tana dirza ma sa especially scalp ɗin sa, ɗan rankwafowa yai da kan saboda ta samu daman wankewa da kyau cause ya fi ta tsayi. Sai da ta wanke shi sau biyu a bakin shower kafin ta tara ma sa ruwan zafi a bathtube ta ce ya shiga ciki. Ya ji daɗin ruwan zafin da ya shiga dan dama jikin sa na ma sa ciwo.

"I'm sorry my Queen" ya faɗa ganin hawaye da ta ke yi.

"Ni ce zan ba ka haƙuri miji na. I'm sorry you are married to a crazy woman"

Dariya ya fara yi yana faɗin "and i love my crazy wife"

Dariya itama ta yi tana cigaba da yiwa kafaɗun sa massage...


..........................


Duk ƙoƙarin 'yan sanda ganin an kama wanɗanda su ka kidnapping Najeeb abin ya ci tura. Kidnappers dai sun tafi da miliyan ɗari biyu wanda biya kam sai dai a lahira.

Ranan suna anyi ƙasaitacciyar walima, duk da anyi shagali amma bai kai lokacin sunan Yaman ba. Ko dan saboda abinda ya faru, oho.
Yarinya dai ta ci sunan Mom, an raɗa ma ta *Nabeelah Zafreen*

Wannan karon a gidan Daddy aka yi suna, infact sai da aka yi sati uku da sunan ma kafin su ka koma gidan su.


.........................


Yau Monday ta fara fita aiki bayan Zafreen ta cika wata biyu a duniya. Tana duba wassu takardu Zafreen da ke kwance a gadon yara da ke office ɗin ta hau kuka.

"Kayya 'yar nan Allah ya miki albarka, shegen kukan kin nan ban san ya zan yi da ke ba." Ta faɗa tana ɗaukan yarinyar.

Wayar office ɗin aka fara kira ta ɗauki kiran.

"Hajiya, Architect Fauziyya na son ganin Ki" muryan Kabiru sakatare ya doki kunnen ta.

Kabiru ƙanin mahaifiyar Anas ne. A ƙalla zai kai shekaru talatin da takwas zuwa da tara. Sakandare kawai ya karanta, yana aikin masinja a wata makaranta kafin Anas ya ma sa maganar aiki a Najeeb constructions tunda Najeeb ya rufe ɗaukan sakatariya ma ce. Wata ɗaya ana ma sa training na aiki kuma ya ɗauka sosai gaskiya, kafin ya fara yi mu su aiki.

Farida ta ce "ka ce ta shigo"...

Najeeb ba ya gari ya tafi Lagos wani taro.

Fauziyya ta gaida Farida a ladafce kafin ta ce " Ma ya jiki?"

"Da sauƙi" Farida ta faɗa fiskarta a sake dan yanzu ta yi wa kan ta faɗa. Dama cikin Zafreen ne ya sake tunzura ta.

Fauziyya ta fito da IV daga jakarta ta miƙawa Farida. Farida ta amshi IV ɗin tana karantawa. Ta ɗago ido da sauri ganin sunan da ke jiki.

Fauziyya ta yi murmushi ta ce " Ma, you have every reason to be jealous, ko ni na ke auren Sir Najeeb ba ƙaramin kishin sa zan yi ba. He's handsome, rich and successful. Amma ki sani ban taɓa son mijin ki ba, tun kafin na fara aiki anan an riga an ba da ni, lokaci kawai mu ke jira and now the wedding is in 12 days"

Cike da kunya Farida ta ce " ba dai za ki bar aiki da mu ba"

"No, i love my job, kuma dear ya amince na yi aiki anan matuƙar za a maida lokacin tashi na ƙarfe ɗaya ko biyu"

"Kar ki damu za a rage miki. Wannan kamfani yana buƙatar ma su ƙwazo irin ki"

Fauziyya ta miƙe tana faɗin " na gode Ma"

Farida ta ce " dan Allah ki yi haƙuri abinda ya faru baya"

Fauziyya ta ce ba komai ya wuce...


..........................

Tun da su ka dawo daga sunan Zafreen ta ke jin jikin ta ba daɗi. Ba ta son gayawa Lukman saboda kar hankalin sa ya tashi. Ciwon kai idan ta ce tana ji ranan za ka ga Lukman ya rikice yana ƙoƙarin ba ta kulawa na musamman. Yana son ta sosai yana kula da ita, she's really lucky da ta aure shi. Ya iya soyayya ga iya kula da mace, ba shi da zafi kwata-kwata. Cikin zaman auren su za ta iya irga lokutan da ta ga ransa a ɓace hakanan ana ɗaukan wassu awowi za ka ga ya sauko ya koma normal. Itama ɗin ba ƙaramin tattalin sa ta ke ba, cikin 'yan kwanakin nan ma tunanin samun haihuwa ta ke dan ta san shine kaɗai abinda za ta yi ta sa Lukman farin ciki, ga shi har yanzu shiru. Wani lokaci sai ta ga ko dan shekarun ta ne, amma kuma ai mata na haihuwa har a fifties na su balle ita da ke talatin da biyar.

Ta tuno da lokacin da ake tsakiyar shooting wani film hajijiya ya kwashe ta ta faɗi, da aka kaita asibiti aka ce tana da ciki. Baƙin cikin da ta ji a lokacin ba zai misaltu ba. Bayan kwana uku ta sayi wassu pills ta sha ranan ta yi bleeding kamar jinin ta zai ƙare. Ƙarshe sai da ta yi jinyar sati biyu a asibiti Ta rintse ido tana hawaye....

Lukman na fitowa daga asibiti ya haɗu Da Dr Jennifer wanda ta koma Dr Aisha. Ta jima da barin aiki da asibitin da ya ke, few months bayan ta yi aure.

Gaisawa su ka yi sama-sama har zai tafi ta tsayar da shi akan tana son magana da shi.

"Faɗi maganar ki da sauri dan my wife na chan gida tana jira na"

Jikinta yai sanyi da jin kalaman sa amma ta daure ta shiga koro ma sa bayanin yadda mijin ta Dr Faisal ya walaƙantata ya hana ta aiki ga shi ba ya wani kula da ita, ga matan sa da su ka sa ta a gaba akan ita yare ce kuma kafira wacce ta gama yawon titi. Walaƙanci dai iri-iri, yanzu gashi ko wata shida ba ta cika da haihuwa ba ya saketa.

"Sorry ko, ya sunan babyn?" Lukman ya faɗa cikin halin ko in kula.

"Fatima amma ta rasu few days bayan sunan ta"

Lukman ya ce " Allah ya sa me ceto ce amin. Barin je gida kar wife ɗina ta jini shiru"

Ya wuce ya bar Dr Aisha cike da tarin nadama, yau da Dr Lukman ta aura ta tabbata ba zai taɓa walaƙantata haka ba, he'll love her and cherish her for the rest of his life, sai ga shi ta ƙi auren ɗan shege ta auri ɗan asali kuma tana nadama...

Lukman na zuwa gida ya samu Sabreen na kela amai a banɗaki. He's being suspecting pregnancy 'yan kwana biyun nan amma saboda rashin samun isashshen lokaci ya sa bai damu ya tsaya ya tabbatar da zargin sa ba. Bayan ya taimaka ma ta ta gyara jikin ta sannan ya fara duba ta. Daga idanun ta zuwa tafin hannunta kafin ya ɗaga rigarta yana sa hannu a mararta da cikin ta.

"What is it?" Sabreen ta tambaya ganin taɓe-taɓen yai yawa.

With excitement a fiskar sa ya ce " Lets confirm first"

Sai da ya tabbatar ta samu ƙwarin jiki kafin ya fita ya je ya siyo PT strip. Da ya dawo su ka gwada.

Ɗaukan ta yai sama yana juyi da ita yana dariya bayan ya ga reading ɗin strip ɗin ya bada positive...

..........

Kwanci tashi cikin Sabreen ya cika wata tara inda ta sha wahala wajen naƙuda ƙarshe aka ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba aka cire ma ta kyakykyawar jaririyar ta. Yarinyar sak ubanta hatta green eyes ɗin sa sai da ta ɗauka, idan ka ɗebe farin Sabreen da ta ɗauko ba abin da ta bari na Lukman.

Murna wajen Lukman ba a magana. Finally shi ma ya samu 'ya, 'ya ta sunnah.

Kwana biyu kafin suna Najeeb da Farida su ka dira a Abuja, tareda yaran su Yaman da Zafreen wanda ƙiriniyar yarinyar yafi ƙarfinta. Yayinda Yaman ya ke so quite ita wannan tun aciki ta ke sa uwarta masifa da ta fito ma tun tana 'yar jinjira ta ke nuna iya shegen ta balle yanzu da ta fara wayo. Idan mutum ya ɗauketa ba ta so har cizo tana yi.

Ranan suna gaskiya anyiwa Sabreen da Lukman kara domin kuwa an zo dayawa, 'yan uwan Lukman ta ɓangaren mahaifiyar sa duk sun zo, ga 'yan uwan su Najeeb da su ma su ka cika wajen.

Tsakanin ma'auratan su ka yanke shawaran sunan da za a sawa yarinyar. Farida kam ba ƙaramin mamaki ta yi ba da Najeeb ya kira ta daga masallaci yana faɗin sai ta kawo kuɗin suna domin an samu *little Aisha Farida*

Bayan sun gama waya ta je ta ɗauki 'yar tana ma ta addu'a. Sabreen da ke kwance sai murmushi ta ke yi...


..........................


Rayuwa na cigaba da tafiya shekaru sun fara ja domin kuwa an samu haɓaka na arziƙi da iyali.
Najdah da Anas sun sake haifan mace inda su ka sawa 'yar su sunan *Aisha Amira* aka yiwa marigayiya Aisha takwara.

Farida ta sake haihuwan namiji bayan Zafreen ta cika shekara biyu su ka yiwa Daddy takwara *Adam * suna kiran sa da *Aasim*

Sabreen ma ta sake haihuwa bayan Little Farida, shima ɗin CS aka ma ta dan ance da wuya ta iya haihuwa da kan ta. Sun samu *Muhammad Mubarak*

Baffa Musa da iyalen sa na zaune lafiya kowacce ƙoƙarin faranta ran ɗan tsoho ta ke. Amma alamu sun nuna Amina ta ci galabar sace zuciyar wannan tsoho, ilimi da wayewa sun sa duk abubuwanta sun banbanta da na sauran matan. Ba ta ganin tsufan sa kwata-kwata, duk ranan girkin ta haka ta ke birkitashi da salon ta na matan zamani wanda ya ke sa ya ji ina matan sa su ka shiga lokacin da sauran mata ke koyan dabarun sarrafa miji. Abubuwan da ya ke yi yanzu da wanda Ummi ke ma sa ko lokacin yana matashi bai samu wannan gatan ba.

Yakubu ma shekara ɗaya bayan haihuwar Zafreen ya angonce da amaryar sa Halima.

A ɓangaren Aneesa da Majiddah ma sun haɗe kan su suna zaune lafiya. Duk da Aneesa na zuwa aiki hakan bai hanata samun lokacin miji da 'ya'yanta ba. Bayan Mujahida haihuwa ta tsaya ma ta amma Maijiddah ta samu Yusuf bayan Al'amin ga kuma tsohon ciki da ta ke da shi yanzu. Shi kam AbdulWahab sai dai yai ta hamdala kawai domin kuwa kwanciyar hankali da nitsuwa sun samu gindin zama a gidan shi...

............

Zama aure sai haƙuri, akwai soyayya, akwai faɗa, akwai matsaloli amma idan kuka san yadda za ku dinga tafiyar da lamuran ku sai ya zamana duk inda matsala ta kunno kai za ku samu mafita cikin ƙanƙanin lokaci.

Najeeb da Farida su na nan su na soyayyar su, su na abubuwan su ma su sanya farin ciki da jin daɗi. Idan ana aiki a office jiki ya buƙaci abubuwa, sai a kashe wuta a rufe ƙofa a cigaba da abubuwa kawai 😂
It wasnt a perfect life, they werent perfect. Su na faɗa suna samun saɓani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login