Showing 15001 words to 18000 words out of 145203 words

Chapter 6 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25685

gode, kamar kin san abinda ke raina kenan , dama banɗaki na ke nema"...

Fita su ka yi Sister Munibat ta nuna ma ta inda banɗakin mata ya ke, sannan su ka sauko su ka wuce masallaci. Anan Farida ta ga wa su ma'aikata matan duk wanda tacewa ita sakatariyar Sir Najeeb ce sai su ce "Hmmm, Allah ya sa ki iya dan Sir Najeeb Sai a hankali"

Ita kam ba ta ce komai ba dan tun kafin su faɗi haka ta ji a wajen Yakubu da Anas.
Daga masallaci canteen ɗin kamfanin su ka wuce, su na shiga Farida ta hango Yakubu da wasu su na cin abinci dan haka ta yi saurin ƙarasawa wajen table ɗin su.

"Yaya Yakubu ka siya min abinci yunwa na ke ji"
Yakubu ya harareta ya ce " idan ba ki da kuɗin siya ki je ki karɓi ruwa, ruwa is free for all the workers here"

"Haba dan Allah, na ce ma Yayan ma ba za siya mun ba"

"Yayan ai ba na Allah Annabi bane. Na cin hanci ne"

Engr Mathew da ke gefe ya ce " sister ki zauna za'a siya miki abinci. You are our beautiful sister ai"

Farida ta je ta jawo kujera ta zauna. Yakubu ya ce "Matt, wannan yarinyar ci ta ke kamar gara ga ta da shegen son bati. Idan za ka bi shawarata ka barta ta siya da kanta idan ba haka ba kullum kai za ta maƙalewa"

"No problem, this beauty deserve to be serve like a Queen"

Farida ta yiwa Yakubu gwalo...

Su na cin abinci Najeeb da Anas su ka shigo, nan wajen yai tsit. Kai tsaye wani gefe su ka je su ka zauna inda wajene da aka tanada ɗan gefe da sauran mutane. Kujerun wajen da table ɗin ya fi sauran ƙayatuwa. Wajen cin abincin Sir Najeeb kenan, da ke Anas shi ne na hannun daman sa sai ya zamana tare su ke zama su ci a wajen.

Jin wajen yai shiru ba kamar yadda ta fara shigowa ba ya sa Farida cewa " ni kam mutuwa ce ta wuce ne? Na ga kowa yai shiru sai ƙaran sokala da fork kawai"

Yakubu ya taƙaleta ya mata nuni da ido. Sir Najeeb da Anas ta hango su na cin abinci.
Ta gane saboda Sir Najeeb ne kowa ya nitsu a wajen. Sakamakon da da ake cin abincin ana hira yanzu kam kowa abincin ya ke ci baki gum.

"Ya Anas...Ya Anas" muryarta ya karaɗe wajen.

Anas da ya ke kurɓan juice ya ajiye glass ɗin ya juyo da sauri. "A'a 'yar uwa ke ce, ya aiki"

"Lafiya yayana. Yaya wai ni an saka dokan hana magana ne anan? na ga anyi shiru"

Anas ya ce " ni ma ban sani ba amma ki tambayi Ogan ki"

Farida ta maida kallonta wajen Najeeb da ya cika ya kumbura kamar zai fashe. Ta ce " Sir Najeeb ka hana magana a nan ne??" Tambayar ta fi kama da gatse ko shaƙiyanci kuma da gangan ta yi hakan. Tashi Najeeb yai ya bar wajen. Yana fita daga canteen ɗin aka sa ihu. Wasu sai a lokacin su ka san miye aikin Farida, ta burge kowa, sai dai dayawa sun ji tausayinta dan a tunaninsu ƙarshen aikinta ya zo kenan. Harta Anas sai da yai dariya, shi kam sai da ya cinye abincinsa kafin ya tafi.

Suna fitowa a canteen ɗin Yakubu ya ce " tunda aikin ne bakyaso shikenan. Idan ya koreki za ki san zafin neman aiki ai"

"Haba Yakubu, mutumin nan fa mutum ne amma yadda ku ke zuzuta shi ku ke tsoronsa sai ka ce wani ifritun Aljani"

"Ni dai na gaya mi ki"

Wai da su ka taho da Sister Munibat ma harda ba ta addua'ar da za ta yi idan ta shiga office, ita kan dariya kawai ta yi ta wuce.

..........................

Tana zama a kujerar ta aka kira, as usual dai cewa yai ta zo.

"Sir gani"

Kallon walaƙanci ya ma ta sannan ya jefa ma ta takardar da ke hannunsa.
"Read it"
Tsugunnawa ta yi ta ɗauko takardar ta fara karantawa a zuciyarta.

"Read it loud" ya daka ma ta tsawa

Haka ta fara karanta ma sa daga farko har ƙarshe. Sai da ta tsaya sannan ya ce " i'm sure lokacin da aka baki takardar ɗaukan aiki an haɗa mi ki da wannan takardar, but you are so dumb to not have read it. Now, daga gobe ki fara shiga irin yadda aka tsara a dress code ɗin nan. This is a construction company not a fashion show"

"Sir, ni banda kuɗin siyan kaya irin wannan, kuma dai yau na fara aiki balle ace zan samu albashi dan haka sai ka yi hakuri har na karɓa albashi tukunna"

"Miss Salihu you are stepping beyond your limits, dont you dare talk back to me again" ya nuna ta da yatsa

"I gave you a week to find cooperate clothes. A week Miss Salihu"


"Ok Sir"

Hannu ya ɗaga ma ta ta juya ta tafi.
Ta ɗauka zai ma ta maganar abinda ya faru a wajen canteen sai ga shi bai yi ba. Ita kan bonus ɗin ta dama ta riga ta tanadi amsar da za ta bashi idan ya ma ta magana...

Aiki dai ta aikatu dan da gayya ma ya ke sata wasu ayyukan. Sai dai tunda ranar farko ce haka ta haƙura ta dinga binshi a hankali kar ya ce ma ta lazy.

A haka su ka ƙare aikin ranan, ƙarfe huɗu za su dinga tashi dan haka ƙarfe huɗu saura kwata ta fara haɗa kayanta. Kiririnkiririn sai ga telephone na ƙara.
"Mtsww sarkin naci" ta ɗauka fiska ɗaure kamar tana gaban Sir Najeeb ɗin.

Ajiye wayar ta yi ta shiga office ɗin sa. A ranta tana ayyana abin da za ta ce idan wani aikin zai ba ta.
Tana shigowa ya nuna ma ta wata laptop ya ce ta ɗauka ta tafi da shi gida wanda za ta dinga ƙarasa aiki da shi a gida kenan.

"O'o ni Aisha, wato agidan ma ba hutu za kai ba"

"What do you say?"

"Babu, na ce Thank you Sir"

Sai da ta juya za ta fita ya ce "Miss Salihu"
Haɗiye miyau ta yi tareda dunkule hannunta ɗaya ta juyo.

"Fix a meeting with the Sudanese tomorrow"

Wa su Sudanese kuma? Ta faɗi a zuciyarta a fili kuma ta ce "Ok sir"

Ta san ko ta tambaye shi ma ba gaya ma ta zai yi ba dan haka ta bari akan za ta samu Anas ya ma ta bayani...



......................


Gaba ɗaya a gajiye ta isa gida, Yakubu sai dariya ya ke ma ta wai indai a haka za ta ci gaba ba za ta jima da Sir Najeeb ba dan shi kam aiki ya ke so a mishi tuƙuru.

Bayan Maghrib ta kira numbar da Anas ya bata na wasu Sudanese da ke son haɗa hannun jari da Najeeb. Ta faɗa mu su meeting ɗin su da Najeeb gobe ƙarfe goma.

Su na cin abincin dare Baffa Musa ya aiko a kirata. A falonsa ta sameshi yana aikin lissafi a takarda. Ɗan nesa da shi ta zauna a ƙasa ta gaishe shi.

"Ya aikin dai"

"Alhamdulillah Baffa"

"Allah ya taimaka, iyayen yaron nan sun sameni kuma mun tattauna da su. Na ce su bani lokaci na yi bincike saboda kar a samu matsala irin na baya"
Farida ta rintse ido tana tuno abinda ya faru a baya. Ta ya za ta manta wannan babban al'amari daya faru a rayuwarta.
Maganar Baffa ya dawo da ita.

"Sun ce Asalin su 'yan Wudil ne amma kuma tunda Kakansa ya dawo cikin Kano da zama ya zamana 'yan uwan su sunfi yawa anan. Ina so idan komai ya daidaita da yardar Allah da ke da Maijiddah ƙarshen shekara ayi bikin ku tare. Tunda Allah ya sa Saminu ya amince. Na huta da yawan maganganu da ake akanta"

"Baffa wani Saminu kuma?"

"Yaron shagona"

"Baffa auren sadaka za ka yiwa Maijiddah, haba dan Allah sai ka ce wanda ta ke da wani aibu"

"Bance tanada aibu ba. Amma tunda har yanzu shiru ba wanda ya zo neman aurenta kinsan dai ba zan zuba ido ina ganinta haka har a gama auren ƙannenta ba"

"Wallahi Baffa kai bagidaje ne. Wai za ka aurar da ita wa yaron shagonka, irin ta yi kwantai ɗin nan,cab ɗi"

"Tashi ki bani waje. Ba shawararki na nema ba"

"Baffa dan Allah ka saurareni, Wallahi indai ka aurar da ita wa Saminu Jiddah ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba. Walaƙantata zai yi dan ya san sadaka aka bashi ita"

"Ban nemi shawaranki ba. Tashi ki tafi "

"Baffa akwai wanda ya ke sonta fa"

"Waye?"

"AbdulWahab sunan shi, ɗan gidan Hajiya Yelwa wanda Jiddah ke wa kitso"

"Hajiya Yelwa?"

"Cikakken sunan sa AbdulWahab Bello Hassan"

Baffa ya ajiye biro ya kalli Farida da kyau ya ce " na san ki da yawar magana amma ban sanki da sharri ba. Yaushe ɗan gidan Alhaji Bello Kachako ya ce yana son Maijiddah"

"Allah Baffa da gaske na ke, ka tambayi Jiddah"

"Shi kenan, kiramun ita"


Ko da ta shiga ɗaki Maijiddan ta samu tana waya. "Ki je inji Baffa"...

Farida na shirin kwanciya ta jiyo muryan Baffa yana faɗa. Da sauri ta zari hijabi ta fita saboda ƙaramar riga ce a jikinta.

" kin san ko waye shi kuwa?, babban ma'aikacin custom ne fa. Ba na son sharri Maijiddah ki riƙe matsayin ki"
Duka matan sun hallara a falon dan suma faɗan Baffa ya tado su daga matsugunninsu. Maijiddah kam ta kifa kai tana kuka dan ta tsorata da masifar Baban na ta.

"Ikon Allah! Yanzu dan ba ki da mashanshani sai ki yiwa bawan Allah sharri. Ba ki tsaya ma kusa ba sai chan nesa da ke ki ke hangowa. Ni dama na san yawan zuwa gidan Hajiya Yelwan nan kwaɗayi zai sa miki" Anty Hanne ta faɗi tana tafa hannu.

"Munafukai anzo gulma. To ta Allah ba taku ba" ta kalli Baffa ta ce "Baffa ina ni na ce ma ka AbdulWahab na son ta, to ka manta da na yi maganar. Idan gaskiya ce ai ba za ta ɓuya ba idan ma ƙarya ne za a gani. Jiddah ta shi mu tafi"

Jiddah kam tana tsugunne a wajen ko motsawa ta kasa yi. Haka Farida ta zo ta ja ta su ka bar falon...


"Dan Allah ki bar kukan nan, tukunna kukan mi ki ke yi? Saboda Baffa bai yarda da ke ba? Shareshi idan AbdulWahab ya turo ai za su ga zahiri"

Cikin kuka ta ce "Anty Farida wai Baba cewa yai idan ma asiri na ke son yi akan shi gara na bari. Allah ya bani miji Saminu, ta ya mahaifina zai min wannan zargin. Har rashin miji zai sa na koma asiri"

" Jiddah ki godewa Allah, domin addu'arki ta ƙarbu Insha Allah. Ba ga ni ba, ko kin manta abinda ya faru da ni shekaru uku da su ka wuce, i was exactly your age lokacin. Wani surutu ne ba ayi ba, an zage ni an zagi Ummi, hatta Abbana da ke kabari sai da ya samu kason shi. Dan haka ki cigaba da addu'a kuma ki yi ƙum da bakin ki. Duk lokacin da AbdulWahab ya turo su za su ji kunya ai"

"Na gode Anty"

Ta gode Allah da Anty Farida ta yadda da ita lokacin da ta ji record ɗin hiran da su ka yi a waya. Ta rintse ido tana tuno abinda ya faru tsakaninsu duk da kuwa alokacin ba ta cikin hayyacinta saboda firgicewa da ta yi da ganin kyanwa.

Hiran su ta tuno wanda ya sa duk wani baƙin ciki ya kau daga zuciyarta.

*" Hauwerh za ki iya auran tsoho?"*

*"Mi zai hana?"*

*"wannan tsohon fa shekarunsa ɗai-ɗai har arba'in da ɗaya, ga yaran sa har biyu"*

*"ai ba tsoho ba kenan"*

*" haka ki dai ki ka ce gimbiya Hauwerh"*

*"zan samu amsata anjima ko?"*

*"sai bayan kwana uku"*

*"wai-wai har 3days. To, Allah ya kaimu"*

*amin*


Gaskiyarsa ya fi komai birgeta. *" ina son matata sosai Hauwerh, sai dai umurnin Hajiyata ne akan lallai in ƙara aure kafin shekara ta ƙare. Kuma kallo ɗaya na mi ki na ji kin birgeni"*

Ta sha ji ana hiran sa idan ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso. A yadda ta fahimta matarsa na aiki a Abuja shi kuma da yara su na Lagos, sai ƙarshen wata ta ke zuwa mu su. Wannan ne dalilin da ya sa Hajiya Yelwa ta sa shi ƙara aure.

Kamar yadda Anty Farida ta ce za ta yi shiru har sai ya aiko gidan su. A da tunanin da ta yi shine gobe da safe ta playing record ɗin hiran su wa Baabar ta ta ji saboda ta yadda da maganarta ta kuma yiwa Baba bayani...


........................


Washe gari ma shigar atamfa ta yi duk da kuwa a dresscode ranar Jumua'a ne kawai aka amince asa kaya native.
Yana shigowa ta bi bayan sa da sauri.

"Sir kana da meeting da Sudanese ƙarfe goma. Sannan akwai wani Mr Habib Olalekan da ya kira ya ce yana buƙatar ganinka na ce ya zo ƙarfe tara"

"What about the files that i asked you to arrange?"

" na gama Sir"

"Bring them here"...

.........


Sati ɗaya kenan da fara zuwa aiki. Duk wani kafa da Sir Najeeb ya ɓullo da shi dan ya muzguna ma ta tana shanyewa, acewarta dole ta jure kar ya ɗauka ta gaza aikinta ne. Tsawa da masifa kam tana shan shi kullum.

A ɓangaren Maijiddah kam tunda sauran 'yan gidan su su ka ji labarin abinda ya faru sai su ka koma tsokanarta da habaici da Matar custom. Abin yana sosa ma ta rai sai dai ba yadda za ta yi tunda dama sun saba tsokanarta. Bisa umurnin Farida ta amince da AbdulWahab. A yadda ya tsara immediately zai tura iyayensa ayi maganar sai dai ta ce ya bari a gama bikin ƙannenta tukunna.

Da sati ta zagayo ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso, kunya duk ya cikata lokacin da Hajiyar ta kira ta da 'surkuwa ta' da kyar ta iya ƙarasa kitson saboda yadda ƙannen AbdulWahab su ka sa ta agaba da tsokana.

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro. Dan asabat za a ɗaura aure...

Kallon rainin hankali ya ma ta sannan ya ce "repeat what you just said"

"Sir Najeeb ina son ɗaukan leave na kwana uku. Ba zan zo aiki ba ranan Laraba Alhamis da kuma Jumma'a"

"You are crazy right? Yaushe ki ka fara aiki da za ki ɗau 3days leave?"

Ta yi shiru

"Answer me!" Ya daka ma ta tsawa.

"Sir, bikin ƙannena za ayi kuma..."

"And so?"

"Sir...."


"Get out of my office"....

Washe gari laraba ya ɗauka ba za ta zo ba sai ya ganta. A zuciyarsa ya ce ashe ta san mi ta ke yi. Sai dai ƙarfe ɗaya na yi da aka fita sallah ta yi tafiyarta.

Da ya dawo daga masallaci ya shiga office ya ga takarda akan desk ɗin sa.

*Sir na tafi, sai Monday zan dawo. Ka yi haƙuri wannan hidimar ta gida ce dole ayi komai da ni*

Duƙunƙuna takardar yai sannan ya cillar " crazy bitch"
Ya ɗau waya ya kira Anas.

"Hello mutumina ya aka yi?"

"Find another secretary"...



*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣7️⃣


Hankali kwance Farida ta ke hidiman biki. Anas dai ya kira ya ma ta faɗa akan tafiyarta, acewarsa kwana uku yai yawa sannan ya sanar da ita Najeeb ya koreta sai dai kar ta damu ta zo ranan Monday ɗin kafin nan zai roƙe shi. Ita kam ko ajikinta dan ta san abinda ta shirya wa Najeeb.

Ranan Jumma'a su Ummi su ka zo daga Jos, murna wajen Farida ba'a magana. Ranan Asabat aka ɗaura auren *Hajara Musa Wase da Haladu Iliyasu* sai *Salima Musa Wase da Jabir Muhammad*

'Yan uwa daga Wase da Giyaɗe duk sun zo, da ke Baffa Musa da Baaba Sabuwa duka 'yan Wase ne. Ita Anty Hanne kuma 'yar Giyaɗe ce.
Haka aka sha hidima lafiya, duk da an ɗan samu rikici ranan yini saboda magulmata wanda su ka tisa Baaba Sabuwa a gaba kan rashin auren 'yarta Maijiddah. Maijiddah ta yi kuka har ta ƙoshi duk da ta san akwai alamun kukan na ta ya kusa ƙarewa amma kuma madamar ba auren ta yi ba, ita ko Baabarta ba wanda zai samu sukuni...

.......................

Shigar Abaya ta yi mai adon duwatsu kalar gold. Gyalensa ta yi rolling da shi sannan ta ɗau jakarta ta fito, gidan dai an watse sai 'yan tsiraru. Ummi ma ta tafi jiya saboda aiki da za ta koma.

"Allah dai ya sa Sir Najeeb ya haƙura idan ba haka ba kuma kin gama aiki kenan a Najeeb constructions"

"Ya ma isa ya koreni. Lallai! ai Yakubu ka zuba ido kawai ka sha kallo amma yau ko ana ha maza ana ha mata bazan ajiye aiki ba"

Yakubu girgiza kai kawai ya yi ya tada machine ɗinsa su ka tafi...


Sandy mai goge office ɗin Najeeb ne ta cewa Farida Najeeb ya zo lokacin da su ka haɗu, za ta shiga lifter ita kuma Faridan ta fito.

Ta na ajiye jaka ta wuce office ɗin sa. Yana duba wa su takardu ta shigo.
"Good morning Sir"
Ya ji shigowarta amma ya share ko ɗagowa bai yi ba.

"Sir akwai aikin da zan yi ne?"

Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta.
"What part of my message did you not understand?"

"Sir na ga saƙo ta email ranan Laraba wai an koreni daga aiki"

Ya ɗaga ido ya ce "and?"

"Ban koru ba mana. Ba laifin da na yi sannan ko na yi laifi ma, tsarin da ka shirya min ya hana ka koreni"

"Listen Miss Salihu. Na san Saboda Anas ki ka dawo, but ki sani. This is my company, just like you Anas is my employee. So, na koreki ba abinda Anas zai iyayi akai. Now get out of this place bitch"

Fita ta yi daga office ɗin ba tareda ta ce ƙala ba. Minti biyu sai ga ta ta zo da takardu a hannunta

"Ga shi nan, wannan takardar shedar amincewarka ce da tafiyata. Wannan kuma kai ka amince zan yi aiki da kai na wata shida ba tareda ka koreni ba, idan har ka koreni to za ka dinga biyana salary har wata shida ta cika kuma......"

"Wait whats this? When did i sign this? I never signed this"

"Ka kalla dai da kyau Sir Najeeb Jibo. Ka san tabbas signature da ke jiki kai ka yi, you stamped and signed it"

"This is bullshit" ya faɗi tareda yaga takardun

Farida ta yi dariya ta ce " na nawa kuma wannan ma ba original ɗin bane. Original ɗin na nan, so ba inda zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login