Showing 18001 words to 21000 words out of 145203 words
je"
Ta fita daga office ɗin...
Anas ne ya shigo office ɗin ta da sauri "'yar uwa mi ya faru? Najeeb ya kira ni yanata kwarwa"
"Ce ma sa na yi bai isa ya koreni ba"
"Barin shiga na ji mi zai ce" ya shige office ɗin Najeeb da sauri...
Yadda Anas ya ɗau alamarin fa ba da sauƙi bane. Domin Najeeb faɗa ya ke ma sa kamar tsohon zaki, cewa yai ya kawo ma sa mahaukaciya, yarinyar ba ta ganin girma ko darajar sa.
"Amma Najeeb we've talked about this ai, na roƙeƙa ka bata wani chance ɗin"
"To hell with her. I dont want to work with her, can you imagine wannan yarinya ta creating documents ta sa na signing ba tareda na san miye a ciki ba. The girl is a crook, she's just...."
"Haba yallaɓai. Duk wannan tashin hankalin akan mace, ban sanka da haka ba"
Najeeb ya kalli Anas ido cikin ido ya ce " get her out of this office or i will use force, and you know i will do it"
Ganin yadda Najeeb ya bircike ya sa ya fita ya samu Farida ya ce dan Allah ta koma gida zuwa gobe idan Najeeb ya huce zai kirata sai ta dawo. Farida ta tafa hannu ta riƙe ƙugu ta ce "Ya Anas ba inda zan je. Ai yau idan bai haƙura ba zai ga haukata muraratan. Ba ri ma kaga"
Ta wuce office ɗin Najeeb.
"Ka ga Sir Najeeb kar ka bari na nuna ma ka haukata anan, kai shikenan ba dama mutum ya ɗan yi ƙaramin laifi sai ka ce kora, to yau ka gamu da gamonka. Ba inda zan je idan ka takura kuma na shigar da kai ƙara tunda da izininka na tafi hutu" ta san hakan zai iya faruwa shiyasa ranan laraba da ta zo ta typing documents ɗin ta haɗa cikin wasu da zai signing shi kuwa ko dubawa bai yi ba ya dinga signing ɗin su.
"Well lets see how tough you are" ya faɗi tareda ɗaukar waya ya kira security.
Anas da ya shigo office ɗin ya fara bashi haƙuri. "please dont do this. Ba girmanka bane wallahi. Za ta bar maka aiki amma banda koran walaƙanci dan Allah"
Farida ta ce " Ya Anas ka barshi, security ɗin su zo ina nan ba inda zan je"
"Farida ki yi shiru ki fita, i'll handle this"
"Yadda ya ke ji da taurinkai ni nawa ya ninka na shi. Mun fafata da arnan Jos ma balle shi"
Ana haka sai ga wasu murɗaɗɗun security sun shigo, dukkan su biyu da ka gansu ka san basu da mutunci da alama ma ba musulmai ba ne.
Najeeb ya tashi ya zo gaban Farida ya ce " for the last time, LEAVE"
"Allankatafir ba inda zan je"
Shi kam Anas baza ido kawai yai yana kallon wannan dramar.
Najeeb ya dubi securities ɗin ya ce " throw her out of my company, i dont want to see her here again"
Ɗaya daga cikin securities ɗin ya nufo ta yana ƙoƙarin riƙe ta, aikuwa ta yi tsalle ta faɗa jikin Najeeb ta cukwuikuyeshi tana ihu tana faɗin wallahi ba zan fita ba ko za a kashe ni.
Najeeb ya rintse ido lokaci guda kuma hankalinsa ya tashi. Cikin zuciyarsa ya ke mamakin abinda ya faru, ba wai rungumeshin da ta yi ba, sai dai effect ɗin da rungumar ya jawo ma sa. He cant believe he got erection because of this crazy girl.
Security ɗin ya kai hannu zai janyo Farida daga jikin Najeeb, Anas ya daka ma sa tsawa ya ce su fita daga office ɗin.
Najeeb har lokacin idonsa a rufe, ya rasa ya zai yi, he's afraid of pushing her away saboda Anas da securities za su ga yadda engine ɗinsa ta miƙe. He cant embarrass himself infront of this crazy girl dan haka cikin hikima ya sa hannu ya turata da ƙarfi before you knew it ya juya da sauri yai hanyar banɗaki.
Anas da ke recording abinda ke faruwa yai kan Farida da ta faɗi ƙasa warwas. " sorry 'yar uwa, tashi" da ƙyar ta miƙe da taimakon Anas saboda ƙugunta da ya bugu sosai...
Ya ƙara zuba ruwa a fiskarsa a karo na ba adadi. Ya kalli kan sa a madubi sai lokacin ya ga yadda jacket na shi ya ɓace da janbakinta.
"This girl is a witch. How could this possibly happen?"Rabon shi da shiga yanayi irin wannan ma ya manta....
"Oga ka fito ayi magana, ka haƙuran ne ko dai" muryan Anas ya katse shi.
Ajiyar zuciya yai sannan ya fito riƙe da jacket a hannunsa yadda ya riƙe ka ce kashi ne ajikin jacket ɗin. Yana fitowa Anas ya sa dariya.
"Get out Anas, i dont want to see anyone"
"Ka huta mutumina irin wannan al'amari sai da hutu ai"
Najeeb ya wurga ma sa jacket ɗin. Anas ya chafe ya ce " wannan jacket ɗin ta tarihi ce"
Sai da ya kai bakin ƙofa ya ce " kar ka manta za ka saurari presentation daga Team D ƙarfe goma. Zan sa sakatariyarka ta tuna ma ka idan lokaci ya yi"
Najeeb ya ce " Anas i'll kill you"....
Anas na fita ya samu Farida ya ce " gaskiyar Yaks da ya ce ke da Najeeb fire and fire ne sai dai gaskiya ta ki wutar ta fi tasa zafi. Kar ki bari kowa ya shiga office ɗin sa sai nan da 1hr kafin nan ya huce"
Farida ta amsa da " ok"
Ko ajikinta dan ta san haƙarta ya cimma ruwa...
Yana zaune ya sa hannu a ƙirjinsa yana shafawa ashe yarinyar nan har cizonsa ta yi, da ya duba wajen a madubi yai wani jaa abinka da farin mutum.
"She'll pay for this, i'm not sending her away. Not until she suffer, i'll make sure she cry and cry and cry"
Yana zaune ya kunna laptop ɗin sa " lets see what the witch is doing"
Tana zaune tana danna waya ga biscuit agefe tana ci. Har zai kashe sai ya tsaya saboda shigowar Khalidah da ya gani. " another bitch" ya faɗi a ran sa...
Kai tsaye hanyar office ɗin Najeeb ta yi Farida ta ce " Malama tsaya"
A gadarance Khalidah ta juyo "and who are you?"
"Idon ki dai bai makance ba ina?. Kin san dai aikin wanda ke zama a kujeran nan ko"
"Ya kamata ki sani, matsayin ki bai kai ya hanani shiga office ɗin Najeeb ba"
Farida ta taso " Sir Najeeb ya ce bai son ganin kowa sai nan da awa ɗaya dan haka. Ko ke wacece sai dai ki dawo anjima"
"Ki hanani shiga idan kin isa?" Khalidah ta faɗi tana ƙoƙarin shiga. Farida ta sa hannu ta jawota da ƙarfi.
"Ki riƙe matsayinki Malama, ko kuma wallahi ni da ke sai mun kwashi 'yan kallo"
"Ki matsa na shiga. Ke kin ma san ni wacece a kamfanin nan?"
"Najeeb constructions na gani ba Najeeba constructions ba dan haka duk matsayinki a ƙarƙashin mai kamfanin nan ki ke"
"Hmmm za ki sha mamaki yarinya, ko kwana ɗaya ba za ki ƙara anan ba Najeeb zai koreki, wanda su ka fi ki nitsuwa ma ba sa daɗewa balle ke shashasha"
"Eh na ji dai. A bi doka a zauna lafiya"
Khalidah ta yi tsaki ta fita. Sai da ta tafi Farida ta ja numfashi ta ce " wai! na sha da ƙyar. Wannan matar fa ta riƙe ni ba ƙaramin jin jiki zan yi ba. Allah ya yi halitta anan"
Najeeb da ke kallon komai ya ce "scary bitch"...
..............
Ƙarfe goma saura minti biyar ya fito daga office ɗin sa.
"Sir na biyo ka ne?"
Bai kulata ba ya fita bayan ya harareta.
Da ya tafi ta ce " ka ji dashi, ni kam kujeran nan tawa ce ina nan daram da kai"
Lokacin da zai dawo tare su ka dawo da Khalidah. Su na shiga office ta cigaba da bayanin abinda Farida ta ma ta sai dai hankalin sa ma baya gareta yanaga takardun da ya shigo da su.
"Najeeb ba ka ce komai ba"
"She's doing her job" ya faɗi ba tareda ya kalleta ba
"Najeeb yarinyar nan 'yar iska ce, ƙila ma 'yar ƙwaya ce kaga ɗazu wai za ta yi kokawa da ni idan na ce zan shiga office ɗinka"
"So?"
"Najeeb ka koreta, ina wancan Joseph ɗin nan da ya ke aiki da kai kafin na yi tafiya"
"Look Khalidah, i fire who i want to. For now that girl stays"
"Najeeb i demand you to sack that girl"
Da ƙarfi ya buga desk ɗin gaban shi.
"Look Khalidah, dan mahaifinki yanada 8% share a kamfanin nan doesnt mean you can make rules here. I owned 75%, i make the rules here. Understand that or ask your father, he'll explain to you. Now get the hell out of my office"
Khalidah ta fice fuuu cikin fishi.
.............
Cikin sati uku da Farida ta fara aiki a Najeeb constructions ba wanda bai santa ba. Wanda su ke tunanin ba za ta jima ba sai gashi har sati uku, shi kan sa Anas yai mamakin yadda Najeeb ya haƙura da Farida. A zuciyarsa kuma yana ganin kamar akwai lauje cikin naɗi.
Babban matsalar Farida a office ita ce Khalidah, a second floor ta ke amma kusan koyaushe tana third floor. Magulmatan kamfani su ka sanar da Farida cewa Khalidah son Najeeb ta ke, lokacin da ta zo ta yi service ɗin ta a Kamfanin ta haɗu da Najeeb tun daga lokacin kuma ta ƙi tafiya, da ke dama mahaifinta na da share a kamfanin sai ta samu ɗaurin gindi. Shekararta uku a Najeeb constructions amma ba alamar nasara sai dai ta ƙi haƙura...
Ta gaji da cin abincin canteen kullum sai kashe kuɗi ga abincin a zuba ma ka kamar kana roƙo duk da ma mafi yawancin lokuta Engr Mathew ko Arch Hamza wani cikin abokan Yakubu ke siya ma ta. Ba ma wannan ba abincin ma bai ma ta yadda ta ke so ba.
Ta zuba faten doya da ya ji ganyen alayyaho da kifi a plate. Gaba ɗaya ƙanshi ya baɗe office ɗin, ta na ci tana korawa da zoɓonta mai sanyi a haka Najeeb ya shigo. Bai ma ta magana ba ya shige office ɗin sa, yana shiga ta ji kira. Tsaki ta yi ta ce " yana gani fa abinci na ke ci" haka ta ajiye ta shiga office ɗin sa.
"Miss Salihu. The next time you eat in the office, 10% zan cire a albashin ki. Is that clear?"
"Ok Sir " ta faɗi ta fita tana ƙunƙuni...
.....................
Farida ta zaunar da Baaba Sabuwa ta yi ma ta bayanin abinda ke faruwa tsakanin AbdulWahab da Maijiddah. Da kuma ƙudurin AbdulWahab ɗin na son turo iyayen sa.
Baaba Sabuwa ta ce idan dai da gaske ne za ta sanar da Baffa Musa sai ya basu lokaci.
Farida ta ce " yanzu Baaba Sabuwa ba ki yarda ba kenan?"
"Farida na fi kowa damuwa da rashin auren Maijiddah, sai dai maganar AbdulWahab ɗin ne ta zo kamar almara"
"Addu'arta ne ya ƙarbu. Kin san tunda na zo gidan nan kullum dare Maijiddah sai ta fi awa ɗaya tana sallah tana roƙon Allah ya bata miji. Ko ba ta sallah sai ta tashi ta roƙeshi. To Ubangiji mai jin ƙan bayinsa sai ya kawo ma ta wanda ba ta taɓa tsammani ba. Baaba Sabuwa ki godewa Allah kawai ki cigaba da yi ma ta addu'a"
Cikin satin Alhaji Bello Hassan Kachako da wa su wakilan AbdulWahab su ka zo. Bakin Baffa Musa kasa rufuwa yai, shi ba dan ya gani zahiri ba ko lokacin da Baaba Sabuwa ta gaya ma sa bai gama yarda ba. Su zuwan da su ka yi idan an basu Maijiddah su na so bikin kar ya ɗau lokaci.
Baffa Musa kam zani ne ta tadda muje. Dan haka ya amince da sauri.
Sati na zagayowa aka kawo sadakin Maijiddah, dubu ɗari da hamsin. Wata uku aka sa biki su ka nemi a dawo da shi wata biyu Baffa Musa ya amince. Duk da kuwa bashida kuɗi a ƙasa dan ya gama kashe kuɗi wajen bikin su Salima. Sai dai ba zai bari damar da ya ke nema tun da jimawa ya kuɓuce ma sa ba. Allah na gani ya so a haɗa bikin Maijiddah da Farida sai dai hakan bai yiwu ba. 'Yan uwan Rayyan sun ce Rayyan yana so ya haɗa ginin sa kafin ayi biki...
Wannan babban al'amari ya sa kishiyoyin Baaba Sabuwa kowa yai tsit dan abin ya ba su mamaki, duk cikin yaran da aka aurar ba mai sa'an Maijiddah. A gaba ɗaya yaran ma Yayar Maijiddah wadda ita Maijiddan ta biyo wato Bilkisu ita kaɗai ta auri wanda yai boko sosai kuma ya ke da hali yana aiki a kamfanin insurance, sai gara-gara mijin Kulthum wanda shima ma'aikacin Kamfanin Airtel ne.
Abu kamar mafarki fa yadda su ke tsokanarta da Matar Custom sai ga shi har sadakinta an bayar saura a ɗaura aure kawai.
......................
Tana kwance wayarta ya fara ringing tana ɗagawa ta ga Sir Najeeb. Mi zai sa ya kira a wannan lokaci? Ta dai ɗauki kiran.
"Miss Salihu, i asked you to send me a copy of the proposal before you leave. What happen?"
"Ya Allah! Na manta zan turo ma ka yanzu"...
Yana zaune yana sipping tea ɗin sa ta turo ma sa saƙon. Sai da ya duba ya ga aikin bai yi kyau ba akwai gyararraki. Nan ya sake kiran ta.
Tana amsa waya ya fara faɗa "Miss Salihu what is this? Mi ki ka turomin? Haka na ce ki yi?" Jin ƙorafin yai yawa ya sa ta ce
"Domin kai ƙorafi danna ɗaya, domin neman ƙarin bayani gameda aikin da aka maka danna biyu, domin magana da Aisha Farida kai tsaye danna uku...."
Ba ta gama ba ya kashe wayar.
Farida ta yi tsaki, " shi agidan ma ba za ka huta ba aiki, ya san da ya na yi wannan ɗin. Wallahi ba za ka kasheni da aiki ba"
Najeeb ya cillar da wayar yana cize leɓen sa na ƙasa. He's waiting for the perfect time ya aiwatar da ƙudurinsa, just a perfect time. Yarinyar nan sai ta raina kanta...
*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0️⃣0️⃣8️⃣
Washegari a office Najeeb bai ma ta maganar shaƙiyancin da ta ma sa ba, iya kaci tana nuna ma sa proposal ɗin ya ce ta je ta gyara.
Tana aiki sai ga Sister Munibat ta shigo.
"Sister Farida ya aiki"
"Alhamdulillah"
"Sir Najeeb yana ciki?"
"Eh ki shiga"
Minti biyar sai ga ta ta fito har za ta wuce ta ce " Sister Farida ɗan bani ruwa mai sanyi ma na, fridge ɗin office ɗina ya ɓaci"
Farida ta miƙa ma ta satchet water mai sanyi.
"Na gode sister" har za ta tafi Farida ta ce " yawwa idan kina son zoɓo ko kunun aya, gobe zan fara zuwa da shi"
Sister Munibat ta ɗan yi dariya ta ce " a cafeteria za ki dinga ajiyewa?"
"A'a anan office ɗina, mai so sai ya zo ya siya"
"Toooo, ke da Sir Najeeb kunfi kusa, amma bana tunanin zai amince da haka"
"Sister Munibat ke dai ki sanar da 'yan wajen kun nan kawai"
Sister Munibat tace "Allah ya kawo kasuwa" Farida ta amsa da Amin...
Washe gari Farida ta haɗa zoɓo gora shabiyar da kunun aya gora goma. Tun kan ta shigo ta ɗan bibbiya wajen mutanenta ta sanar da su, wasu a lokacin su ka ƙarɓa dan wa ya ke da garajen zuwa har Office ɗin Sir Najeeb siyan zoɓo...
Tana aiki a computer Najeeb da Anas su ka fito.
" 'yar uwa sannu da aiki ko"
"Na gode Yayana"
Har zai shige ta ce " Ya Anas ga zoɓo fa, harda kunun aya"
" ƙanwata kenan, kina sha'aninki"
"Yaya ai mai neman kuɗi kam kowani ƙofar samu ya gani shiga ya ke"
"Well Hakane, Allah ya kawo kasuwa"
"Na kawo ma ka zoɓo ko kunun?"
"Ki bari anjima yanzu zamu fita wani waje nida mutumunki ne"
Kafin ya gama surutun sa Najeeb kam ya yi gaba...
.....................
Tana tsugunne gaban fridge tana duba sauran zoɓonta wanda na Anas ne da na Sir Najeeb da ta ajiye mu su, yanzu Yakubu ya zo ya ƙarɓi na sa.
"Miss Salihu"
A firgice ta juyo dan ba ƙaramin tsorata ta yi ba.
"Ya Allahu! Sir Najeeb ai sai ka sa hawan jinin mutum ya tashi. You scared the hell out of me"
"To my office, Now"
Yana shigewa ta fara mimicking na sa " Miss Salihu, to my office now nnnnnnaa. Mtsww"
Ta ɗau zoɓo ɗaya wanda yai sanyi sosai ta shiga da shi.
Tana zuwa ta ajiye ma sa akan table ta ce "Sir na san kafi son shan tea ko coffee amma wannan zoɓon one in town ne. Albarkacin haƙƙin maƙotaka za ka dinga samun kyautar goran zoɓo ɗaya"
Tunda ta fara magana ya zuba ma ta ido har sai da ta kai aya. Duk yadda ya ke jin tsanar yarinyar nan wannan quality na ta na rashin tsoro yana impressing na shi. Idan ka cire Anas duk girman Kamfanin nan babu wanda ke iya tsayawa gaban sa ya faɗi magana son ransa sai ita. People fear him, but this skinny girl idonta ƙyam ya ke duk lokacin da ta ke gabansa babu tsoro ko fargaba a tattare da ita.
"Sir ka taɓa zoɓon ka ji, Allah sai ka yi santi"
"Miss Salihu, duk wani rules and regulations na wannan Kamfani yana da muhimmanci. But na ga alama ba ki ɗauke su da daraja ba. You dont wear cooperate clothes, you eat in the office you... you... you and only you Miss Salihu"
"Haba Sir, tun ranan da kace na dena cin abinci a Office fa na dena"
"Oh really, and that yellow thing you ate in the morning yersterday?"
"Kai Sir ya akayi ka gani? Ban karya ba na fito shine na karya a office"
"I see. And this" ya nuna goran zoɓo da ta ajiye"
"Alakoro na kawo ma ka fa. Tunda dai Allah ya haɗamu maƙotaka"
"Look Miss Salihu, get this in to your dumb skull. Office ba wajen ciye-ciye ko kasuwanci bane, you keep on doing it i keep on cutting your salary. Now out of my office"
Ji take kaman ta make shi amma ba hali. Ta juya a hankali tana tafiya.
"Miss Salihu" dama a kufule ta ke ta juyo da sauri ta ce " Sir yanzu kuma mi na yi"
"Take this stupid thing out of my sight"
Ta kalli zoɓon ta kalle shi tace "idan ka ga dama ka wanke bahayarka da shi"
"Wait what?" Ai da sauri ta fice