Showing 1 words to 3000 words out of 87802 words
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 1*
Acikin wani irin katafaren parlour ne mai k'unshe da kayan alatu ko'ina acikinsa zad tsari da k'awatuwa, matashin magidanci ne zaune saman cushion d'in dake malale cikin parlourn yayi tagumi cikin tsantsar damuwa kallo d'aya zakayi masa ka hango tsagwaron takaici da bak'in ciki cikin k'wayar idanunsa saboda sun kad'a sunyi jajir akan matsananciyar damuwa, wani irin tururin d'aci da zogi zuciyarsa keyi asanadiyar rashin samun abokiyar rayuwa ta gari, yayi shiru yana sak'e sak'e cikin zuciyarsa domin abin duniya yasha masa kai saboda matarsa Nazifa kwata kwata bata basa hak'k'insa dake rataye awuyanta ita dai babu abinda ta sawa gaba illa ta zamo hamshak'iyar mai arzik'i duk dayake babu abinda ta nema ta rasa awurin mijinta Yaseer.
Ya fad'a cikin duniyar tunani saiga sallamar Nazifa rik'e da hannun 'ya'yanta Sameer da Sameera sun shigo tsakiyar parlourn, firgigit ya dawo cikin natsuwarsa tareda had'iye wani irin abu mai matuk'ar d'aci azuciyarsa kallonsu kawai yakeyi batare da yace uffan ba, Sameer dayake yafi wayo ya iso wurin dad d'insa ya fad'a ajikinsa rungumeshi yayi cikin tsantsar k'aunar d'ansa yana shafa kansa yana murmushin da baikai zuci ba dak'yar ya bud'i baki yace"Sameer ina fatar kun samu su hajiya lafiya?".
"lafiyarsu k'alau dad sunce ma agaisheka".
Yaseer ya saukar da numfashi yana kallon Nazifa yace"ina amsawa".
Alokacin ne Nazifa ta k'araso wurinsa ta zauna tana murmushin dake k'ayatar da fuskarta tace"daddyn Sameer mun bar ka kai d'aya cikin gida kayi hak'uri wani uzuri ne ya tsayar dani"..
Murmushin dake bayyanar da tsantsar bak'in ciki da takaici yayi yace mata"karki damu Nazifa bakiyimin wani laifi ba ai Fauzeeya bata dad'e da fita daga cikin gidan nan ba".
Cire gyalenta tayi tana fuskantarsa tace"ayyah da fatar dai ta baka abinci kaci bata barmin kai da yunwa ba? ".
Yaseer ya nisa yace"gaskiya alhamdulillahi yarinyar tana iyakar bakin k'ok'arinta batada son jiki ko matsala".
"masha Allahu haka nakeson ji yanzu dai bari in shiga ciki inyi wanka in d'an kwanta na gaji sosai wlh".Ta fad'a ayangace.
"ba damuwa zaki iya tafiya".
"To".Ta fad'a tareda mik'ewa tsaye baby Sameera ta tashi tsaye tana shagwab'e fuskarta kamar zatayi kuka.
Nazifa ta kalleta cikin so da k'auna tace"babyna ya akayi ne kike fushi?".
Sameera ta zumb'ura baki tace"nima zan biki a d'aki".
"to yayi wannan ba abin fushi bane 'yata".Tana rufe bakinta taja hannun Sameera suka fice daga cikin parlourn suka nufi cikin d'akinta.
Ganin sun fice daga cikin parlourn yasa Yaseer yaja tsoki zuciyarsa sai k'una da tsantsar tafasa takeyi masa, ya rasa abinda yakeyi masa dad'i aduniya domin yana buk'atar kulawar Nazifa amma ita babu ruwanta dashi hatta da gyaran gado Fauzeeya 'yar aikinta ce keyi masa, ya rasa miyasa matarsa batada sirri babu abinda take b'oyewa Fauzeeya ta amince da ita tareda bata amana d'ari bisa d'ari.
Cikin zuciyarsa sai cewa yakeyi Nazifa batada wani amfani awurinsa daga taci ta kwanta sai neman kud'i babu abinda ta iya, shi ya rasa wace irin mace ce wadda batada sirri da kulawa arayuwa hak'ik'a ya tabbatar baiyi dace da mace ta gari ba, numfashin takaici ya sauke ya kalli Sameer yace"my boy je wurin mom d'inka ni fita zanyi yanzu".
Sameer ya mak'e kafad'arsa yace"dad zan bika muje".
Yaseer ya dafe goshinsa cikin damuwa yace"ohh ni kaina Sameer ka cika yawan damuwa".
"yi hak'uri dad zan bika".
Yaseer ya sakar masa murmushi yace"ok tashi muje d'in tunda ka matsa".
Sameer ya mik'e tsaye yayinda Yaseer yaja hannunsa suka nufi parking lot, suna isa Yaseer ya sanya d'ansa cikin mota sannan shima ya zagayo mazaunin driver ya zauna, yana zama ya danna horn getman ya wangale musu get suka fito daga cikin gidan tareda nufar gidan iyayen Yaseer.
____________________
Nazifa tana shiga cikin d'aki ta zaunar da Sameera saman gado tana kallonta, cire tufafinta tayi ta d'aura towel ajikinta ta fad'a cikin bathroom da nufin wanka ta dad'e sosai tana gurza jikinta ko'ina sannan ta fito d'aure da towel ta nufi wurin dressing mirror, kujerar dake fuskantar mirror ta jawo ta zauna ta fara shafa lotions ajikinta kayan kwalliya ta d'auko ta fara tsantsara kwalliyarta mai k'yau da gani, bayan ta gama ta ciro atamfarta orange colour ta sanya ajikinta sannan ta feshe jikinta da turare mai k'amshin dad'i.
Tana kammala shiryawa ta dawo wurin Sameera ta zauna alokacin ne baby Sameera ta kalli mahaifiyarta tace"mom kinyi matuk'ar k'yawo".
Murmushi Nazifa tayi tace"da gaske nayi k'yawo?".
"eh mom da gaske nake fad'a".
Nazifa zata sake magana kenan wayarta tayi ruri alamar ana kiranta da sauri ta d'auko phone d'inta tayi receiving tace"hello besty Safiya".
Ab'angaren Safiya ta musk'uta tace"ya kike Nazifa yasu Sameer?".
"Lafiya k'alau suke Safiya ya naki yaran?".
"k'alau suke Nazifa dama dalilin dayasa na kiraki shine sak'on kayan da muka basuwa asiyo mana sun iso yanzu saboda haka ki shirya zuwa gobe zamu had'u shago".
"OK ba damuwa Safiya kamar da k'arfe nawa zamu had'u goben?".
Safiya tayi ajiyar zuciya tace"da k'arfe takwas na safe zamu had'u".
"karki damu zanzo insha Allahu".
"OK sai anjima".
"sai anjima d'in".Tana k'arasa maganarta ta katse wayar tareda saukar da numfashi yayinda Sameera sai kallon mahaifiyarta takeyi tana murmushi.
**********************
Yaseer yana isowa bakin tangamemen get d'in gidansu ya danna horn da k'arfi maigadi yazo da gudu ya wangale masa get d'in ya kunna hancin motarsa cikin tsakiyar filin gidan,direct wurin parking lot ya nufa ya parker motarsa yana parkerwa ya fito daga cikin motar ya nufi gefen Sameer ya bud'e masa k'ofar ya fito, yana fitowa Yaseer ya sanya key ya kulle motarsa tareda jan hannun Sameer suka nufi cikin parlour.
Suna isa tsakiyar parlourn suka isko hajiya Sadiya zaune saman cushion idanunta sanye da farin glass domin ya zamo mata garkuwa, jin motsin mutane yasa hajiya Sadiya ta d'ago fuskarta ta kallesu cikin sakin fuska, suna isowa wurinta Yaseer ya gaisheta ta amsa masa cikin farin ciki da walwala yayinda taja hannun Sameer ta zaunar dashi kusa gareta tace"'k'aramin maigida kaine ka kawomin ziyara ya mom d'inka da school?".
Sameer yayi mata murmushi yace"lafiya k'alau take hajiya".
"masha Allahu ubangiji ya k'ara rufa mana asiri".
"Amin amin Ummi".Inji Yaseer bak'in ciki k'unshe cikin zuciyarsa.
Alokacin ne hajiya Sadiya ta tsurawa d'anta idanu na tsawon lokaci tana nazari da karantar abinda yake cikin k'wayar idanunsa, damuwa da tsantsar takaici ne ta hango kwance cikin k'wayar idanunsa cikin natsuwa da tausayi tace"Yaseer mi yake damunka?".
Yaseer ya marairaice fuskarsa yace mata"babu abinda yake damuna Ummi".
Hajiya Sadiya ta girgiza kanta alamar rashin yarda da maganarsa wani irin abu ta had'iye mak'wat cikin mak'oshinta mai d'aci tace"wannan maganar taka ba gaskiya bane Yaseer har kanada damuwar da zaka b'oyemin cikin zuciyarka, nifa mahaifiyarka ce aduniya babu wadda ta dace tasan matsalarka fiye dani haba d'ana ka gayamini mi yake damunka?".
Kwallar zallar takaici ne ta cika masa idanu dak'yar ya had'iye ruwan hawayensa yace"kema Ummi kinsan matsalar bata wuce Nazifa akullum batada wani buri illa taga ta samu kud'i babu wani kulawa da tsantsar soyayyar gaskiya da take nunamin, komai nawa Fauzeeya ce keyimin ta yaya rayuwa zata cigaba da kasancewa haka?".
hajiya Sadiya ta kallesa cikin tausayawa da tsantsar k'aunar d'anta bak'in ciki da damuwa ne shimfid'e afuskarta zad tausayi tace"ka cigaba da hak'uri Yaseer ubangiji yana tareda bayinsa".
Yaseer ya gyad'a kansa kamar k'adangare yace"Ummi ina iya bakin k'ok'arina wurin ganin nayi hakuri da halayyar Nazifa amma na fara gajiya da halinta na rashin nuna halin ko inkula game dani, gaskiya bazan b'oye miki ba hakuri ya fara kai k'arshe".
"subahanillah!Ka daina cewa hak'urinka ya k'are Yaseer duk abinda Nazifa takeyi maka ka daure ka cigaba da hak'uri tabbas wata rana zakaga ribar hak'urinka anan gaba, sannan kada ka kuskura ka gayawa abokinka sirrinka domin ba kowane aboki ake fayyacewa sirrin zuciya ba".
Yaseer ya girgiza kansa alamar gamsuwa da maganarta yace"to babu damuwa Ummi zan cigaba da hakuri da halayyar Nazifa da yardar Allah ni zan wuce gida".
"to shikenan ka gaidamin da Nazifa".
"zataji da yardar Allah".Yana rufe bakinsa yasa hannu cikin aljihunsa ya ciro kud'i masu kauri ya mik'awa mahaifiyarsa yace"Ummi ga wannan ba yawa ayi hak'uri sannan idan Alhaji ya dawo ki mik'a sak'on gaisuwata zuwa garesa".
Hajiya Sadiya tayi murmushi tace"ubangiji yayi maka albarka Yaseer idan Alhajin ya dawo zan gaya masa sak'on gaisuwarka,kai Sameer tashi ku tafi zuwa gida kar ya manta dakai ".
Sameer ya zumb'ura baki tareda b'ata fuska yace"ni bana zuwa anan zan zauna wurinki ".
hajiya Sadiya ta kalli Yaseer cikin matuk'ar mamakin zancen Sameer tace"kaji yace baya zuwa gidanku".
Yaseer yayi ajiyar zuciya cikin kamala yace"dama Ummi na gaya miki Nazifa batada kulawa da tarairaiyar yaranta shiyasa kikaga yace baya zuwa, saboda haka babu matsala idan yayi miki kwana biyu zanzo da kaina in d'aukeshi".
"hakan yayi Yaseer ubangiji ya kaika gida lafiya".
"Amin ya rabbi ".Yana kai k'arshen maganarsa yaja k'afafunsa ya fice daga cikin parlourn direct parking lot ya nufa wurin motarsa, maigadi yana hango fitowarsa ya wangale masa get tadda motarsa yayi ya nufi hanyar fita daga cikin gidan yayinda ya iso wurin maigadi ya ciro kud'i ya basa, godiya maigadi yayi masa Yaseer ya fisgi motarsa da sauri ya nufi unguwarsu babban amininsa Abduljalal........
_Shin ko ya zamantakewar rayuwar aurensu Yaseer zata kasance, shin Nazifa zata gyara halayyarta ta kula da mijinta Yaseer, shin wane irin k'alubalen rayuwa zasu fuskanta? Sai ku cigaba da bina sannu ahankali domin jin yadda zata kasance atsakaninsu._
_Mugirat Musa_
~I love you my fans~.🥰
. 💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 2*
Yaseer yana isa bakin get d'in gidan Abduljalal ya parker motarsa yana zaune yayi dialling nombar abokinsa,wayar tana shiga ta fara ringing d'id'id'id'i Abduljalal yana ganin kira sunan Yaseer ne b'aro b'aro akan phone d'insa receiving call yayi yace"hello Yaseer".
Yaseer yayi doguwar ajiyar zuciya yace"kai ba wani hello ka fito daga cikin gida gani a k'ofar get d'in gidanka".
Abduljalal dayake kwance saman gadonsa yayi zumbur ya tashi zaune yace"da gaske kake fad'a kana k'ofar gidana?".
"auuu zanyi maka k'arya ko kana kusa ga madam Rufaila shiyasa ka kasa fitowa?".Yace azolaye.
Abduljalal ya mik'e tsaye tareda jawo jalabiyarsa ya sanya yace"hmmm friend baka rabo da zolaya fa bana kusa gareta to ina d'akina da nufin inyi barci saiga kiranka ya shigo".
"naji dai ina jiranka yanzun nan awaje".
"haba mizai hana ka shigo daga ciki Yaseer tunda gidan ba bak'onka bane?".
"kaga banason dogon surutu sauri nakeyi akwai abinda zanyi agida".
"OK ba matsala ganinan zuwa abokina".
K'it Yaseer ya katse wayar murmushi k'unshe afuskarsa babu wani jimawa can ya hango Abduljalal ya fito daga cikin gidan sanye da jalabiyarsa, yana isowa wurin Yaseer ya bud'e k'ofar ya shigo ya zauna yace"gani Yaseer two days ka b'oye ina fatar dai lafiya k'alau?".
"lafiya k'alau Abduljalal saidai abinda ba'a rasa ba".
Abduljalal ya mayarda hankalinsa kacokam wurin Yaseer yana masa kallon k'walelecewa can yace"mi nene matsalar Yaseer kardai kacemin har yanzu babu wani chanji daga wurin Nazifa?".
Hucin takaici yayi damuwa da tsantsar bak'in ciki ne shimfid'e afuskarsa yace"har yanzu bata chanza ba friend nidai agaskiya banyi sa'ar samun mace ta gari ba kuma bazan b'oye maka abinda yake cikin zuciyata ba tabbas nayi nadamar auren Nazifa arayuwata! ".
Abduljalal yayi wuru wuru da idanunsa yana kallon Yaseer cikin tausayi da tsantsar rad'ad'in abinda yake faruwa ga amininsa yace"ka cigaba da hak'uri Yaseer komai na duniya yanada farko yanada k'arshe tabbas wata rana zata iya yiyuwa Nazifa ta gyara halayyarta".
Yaseer yayi nishi mai tattare da bak'in ciki da takaicin rayuwa yayinda wani irin abu ya tokare masa a k'irji yace"zaiyi wuya Jalal ta gyara halayyarta saboda ta riga tayi nisan kiwo batajin kira".
Abduljalal ya dafa kafad'arta cikin tausayawa rayuwar abokinsa yace"ka daina cewa haka Yaseer saboda ba'a yanke k'auna da samun rahamar ubangiji sannan shiriya ta ubangiji ce shine mai shiriyar da duk wanda ya gadama alokacin da yaso".
Cikin gamsuwa da bayanin Abduljalal Yaseer ya musk'uta yace"haka ne gaskiya ba komai ubangiji yasa tanada rabon gyarawa".
"Amin abokina hakan ya dace ka fad'a tun farko ka rage sawa kanka damuwa da yardar Allah komai zai zama tarihi".
"zan rage Jalal nizan koma gida sai mun sake had'uwa".
"OK Yaseer ka gaidamin da madam".Yace bayan ya fito daga cikin motar Yaseer.
"zataji friend".Yana kammala maganarsa ya tadda motarsa ya fice daga cikin unguwarsu Abduljalal, yayinda Jalal yake tsaye yana kallon bayan motar Yaseer saida yaga b'acewarsa, sannan ya juya ya koma cikin gidansa wurin matarsa Rufaila.
**********************
Yaseer yana barin unguwarsu Abduljalal bai zarce ko'ina ba sai cikin gidansa ya parker motarsa aparking lot, sannan ya fito daga cikin motar ya nufi cikin parlour yana isa tsakiyar parlourn ya hango Fauzeeya budurwa 'yar shekara goma sha shida zaune saman cushion tana kallon TV show, da sallama ya shigo cikin parlourn ta amsa masa cikin sakin fuska tareda yi masa sannu da zuwa, Yaseer ya amsa mata tareda zama nesa da ita saman cushion mik'ewa tayi ta nufi frizer ta ciko masa tire da kayan mak'ulashe ta kawo ta dire agabansa, ruwa kawai ya iya sha saboda kwata kwata bayajin dad'in zuciyarsa kallo d'aya zakayi masa ka gane yana cikin matsananciyar damuwa da tsantsar buk'atar kulawar Nazifa,Fauzeeya ta koma ta zauna saman kujerar data tashi kallonsa tayi atsanake cikin ladabi tace"daddyn Sameer ko akwai abinda kake buk'ata ne yanzu?".
Numfashi ya sauke mai tattare da d'acin rai da tsantsar bak'in cikin rayuwa yace"a'a babu abinda nake buk'ata".
Fauzeeya bata sake cewa uffan ba ta cigaba da kallonta cikin natsuwa yayinda Yaseer yake kallon duk wani motsinta ta wutsiyar idanunsa, wani irin yanayi yakeji acikin zuciyarsa game da ita wanda ya kasa tantance ko miye, ganin cigaba kallonta bazai iya haifar masa da komai ba illa tunani da damuwa dole yasa ya mik'e tsaye cikin mutuwar jiki ya nufi room d'in Nazifa dake kusa ga nashi.
Yana isowa bakin k'ofar d'akinta yaji ta akulle knocking d'in k'ofar yayi yana jiran tazo ta bud'e masa k'ofar, Nazifa tana kwance ta shagala dayin charting taji ana knocking d'in k'ofarta zumb'ura baki tayi kamar zatayi kuka saboda tasan ba kowa bane illa Yaseer mijinta, dak'yar ta isa wurin door d'in ta sanya hannu ta bud'e masa k'ofar tana bud'ewa taga Yaseer tsaye yana kallonta na tsawon lokaci, can dai ta bashi hanya ya shigo ya rufe k'ofar direct wurin gadonta ya nufa yana murmushin takaici, Nazifa tayi tsaye ta rungume hannayenta saman k'irjinta tana kallon mijinta kamar yaune ta fara ganinsa numfashi ta saukar tace"daddyn Sameer ashe ka dawo ban sani ba?".
Yaseer ya kalleta da idanunsa da suka chanza colour yace"ya za'ayi kisan na dawo bayan bak'ya bani kulawar data dace ke kullum cikin fita kasuwanci sai kace gareki aka fara business ".
Nazifa taji zafin maganarsa har azuciyarta amma dayake tasan abinda ya fad'a gaskiya ne, tattaro dauriya da juriya tayi ta sanya azuciyarta sannan tace"haba daddyn Sameer ka cika yawan complain wallahi ka dinga hak'uri dani tabbas wata rana komai zai wuce kamar amafarki ".
Yaseer ya banka mata uwar harara asanadiyar haka saida d'iyan hanjin cikinta suka motsa tsoro k'arara cikin k'wayar idanunta, domin yau ta hango masifa kwance afuskarsa cikin tsinkewar zuciya da fargaba yace" kullum kullum haka kike fad'a Nazifa komai zai wuce kamar amafarki sai yaushe abin zai wuce ki bani kulawa da tsantsar soyayyar gaskiya? Na gaji ina buk'atarki kusa gareni matata ni kad'ai nasan yadda nakeji adalilin rashinki akusa dani ki taimakawa rayuwata ki bani abunda nakeso ".
Nazifa ta langwab'e kanta tayi narai narai da idanunta tace"dan Allah Yaseer ka daure kayimin uzuri na zuwa tsawon lokaci da yardar Allah zan baka tsantsar kulawa na musammam fiyeda misali".
Yaseer ya d'aga mata hannu cikin tsananin takaicin maganarta yace"na gaji da yawo da hankalin da kikeyimin Nazifa akullum bakida burin daya wuce kiga rayuwata ta b'aci, bakida wani fata illa kiga na kasance cikin matsananciyar damuwa da tsantsar bak'in cikin rayuwa".
"ka fahimceni mana mijina.......... ".
Katse mata magana yayi yace"bazan tab'a fahimtarki ba Nazifa har sai kin dawo kamar yadda nasanki afarkon aurenmu".
Nazifa tayi shiru cikin haushinsa domin ita arayuwarta ta tsani mutum mai yawan damuwa da tsantsar ganin laifi, can ta d'ago fararen idanunta tace"gaskiya nace maka ka bani lokaci zanyi tunani akai".
Yaseer ya mik'e tsaye ya nufi wurinta yana isa kusa gareta gab da gab yadda zasuji numfashin juna, kallonta yayi ya kauda kansa gefe domin idan ya cigaba da kallon wani irin tururin d'aci da zogi zuciyarsa keyi dak'yar ya furta cewa"tunda bazaki bari mu fahimci junanmu ba Nazifa taurin kanki ya hana ki saurareni to ki sani duk abinda ya biyo baya banida laifi !".
Nazifa tayi saurin kallonsa cikin matuk'ar mamakin maganarsa tace"babu abinda zai biyo baya sai alkhairi daddyn Sameer".
Yaseer bai sake cewa komai ba yaja k'afafunsa ya dawo cikin parlourn ya zauna, koda yazo ya iske Fauzeeya ta kwanta rigingine, santala-santalan cinyoyinta awaje dayake ita kadaice cikin parlourn jin motsin mutum yasa dole ta gyara sicket d'inta, shiru ne ya biyo baya ak'arshe saida Yaseer ya d'auko newspaper yana duddubawa ko damuwar dayake ciki zata