Showing 21001 words to 24000 words out of 124686 words
shigo ɗakin da sallama, ta kalle su ta gaishe su cikin girmamawa suka amsa mata baki ɗaya.
Cikin damuwa ta ce "Abie yau ma bai farka ba ko?"
Sultan ya jinjina kai ya ce "Bai farka ba Asal"
Daga nesa inda take tsaya take ɗan leƙa shi ta ce "Baccin dai yake yi?"
Matawalle ya ce "Ƙaraso ki gan shi mana"
Ta girgiza kai ta ce "A'a shaƙe ni yake yi ya kusa kashe ni, daga nan ma ina hango shi"
Babu babban abin da yake sake ɗaga wa Sultan hankali, sama da wannan azababben zafin da jikinsa yake yi mai ban tsoro, kamar ba jikin ɗan Adam ba.
Da yamma Sultan na cikin ɗakinsa, yana ta kai komo, ya rasa mene ne mafita, ya san muddin batun ciwon nan na Hammad ya fita, ba su da wata mafita.
Aka sanar masa da isowar Imam Zahradeen. Ya bayar da iznin ya shiga. Bayan shigarsa suka gaisa. Ya dubi Sultan ya ce "Abie, wai ko ka aiki Imam Hammad wani gurin ne? Ya saka ni wani aiki, na je gidansa Gimbiya Asal ta ce "Baya nan, kuma a iya sanina ban san ya yi wata tafiya ba"
Sultan ya ce "Haka ne, yana ƙarƙashin takunkumi na hana shi zuwa ko ina ne".
Ya ce "Na sani, ina son ganinsa ne, a yi mini alfarmar nan, wani saƙo zan isar masa na aikin da ya sanya ni"
Sultan ya dubi Zahradeen ya ce "Aikin me kenan?" Zahradeen ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Sultan ya ce "Shikenan na fahimta, amma a yanzu dai ka yi haƙuri ba zaka samu ganinsa ba, yana ƙarƙashin takunkumi "
Imam Zahradeen ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Shikenan, godiya nake ranka ya daɗe" Daga haka ya tashi ya bar sashen. Ya san iya takunkumin hana fita aka ƙaƙaba masa, banda na killace shi a hana ganinsa gaba ɗaya, amma lokaci ɗaya an ce har ganinsa ma ba zai yiwu ba.
*****
Nana ce zaune ta saka kwanon abinci a gaba ta yi shiru, Nene ta taɓa ta ta ce "Ki ci Abincin mana, kin bari yana ta shan iska"
Nana ta numfasa ta ce "Nene wai zuwa yaushe zan je na karɓo ɗa na ne, ci gaba da zama fa bai kamace ni a garin nan ba, ni duk hankalina ya yi gida wallahi"
"Nana na san duk abin da nake yi, ba na son ki faɗa komar mutanen nan, su ci moriyar ganga su yada kwaronta. Mutane ne masu bala'in son kansu fiye da yadda ki ke tunani, dan haka ki ɗan yi haƙuri. Sai dai Nene na rufe baki, wayarta ta fara ringing.
Nene ta ɗauki wayar ta saka a kunnenta tare da yin sallama.
"Barka da wannan lokaci Ummana"
Ta amsa da "Barkanmu dai"
"Umma dan Allah Nana tana tare da ke ne? Idan ke ki ka ɗauke ta ki taimaka ki sanar mini inda ki ka kaita, kan Imam Hammad ya farga ba ta nan, wallahi ban san me zan ce masa ba"
Nene ta ce "Idan ya fargan me ya yi saura a tsakaninsu? Ba dai ɗanku ba ne kun ƙwace? Takardar sakinta kawai muke jira, zan mayar da ita Nigeria har gidansu"
Mahmoudu ya ce "Ummana, wannan wani abu ne da ya shafi Nana da Imam da iyalinshi. Ni fa kamar ya san za a yi haka ya haɗa ni da Imam Zahradeen ya sanya aka killace ku a wannan gidan, kuma lokaci guda sai ki ɗauke ta ki tafi na neme ki na rasa. Dan girman Allah da buwayarsa ki taimaka ki gaya mini inda ku ke"
"Kai ka kiyaye ni, ba zan faɗa ba ɗin, ba ku da wani haɗi da Nana, ka gaya wa ubangidanka ya aiko mini da takardar yarinyata, zan mayar da ita gaban iyayenta ta nemi gafararsu" Ta katse wayar.
Nana ta ce "Nene to idan ya sake ni ba su bani Muhsin ɗin ba fa?"
"Shi Muhsin ɗin da shi aka haife ki ne?"
Idon Nana fal hawaye ta ce "Ni dai a bani ɗa na kan ya sake ni"
Nene ta girgiza kai ta ce "Nana kina cikin jarrabawa, wannan ɗan shi zai sanya ki lalata komai ki kasa ƙwatarwa kanki 'yanci, ai sai ki yi"
Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Amma Nene, ya aka yi aka saki Mahmoudu na ji sun ce wai sai sun hukunta shi, sun ɗora masa laifin aurenmu, sun sake shi kenan sun fasa hukunta shi?"
Nene ta ce "Oho musu, su kashe shi ma kar su bar shi da rai."
Nana ta waro ido ta ce "Nene wai ke ba kya son ɗan nan naki ne?"
"To Nana idan ma ina son nasa, zan goya shi ne?"
"To Nene dama mutum yana daina son ɗansa ne?"
Nene kawai ta yi murmushi, ta tashi ta bar Nana da wasi-wasi.
*****
Wasa-wasa aka shafe kwana uku curr ba a ga 'yar gidan Doctor Sharif ba, ga matarsa a Asibiti, hankalinsa ya tashi kamar zai haukace. Ga jikin matarsa kullum babu afuwa ga shi ta fara damuwa da ina Hafsa take. Sai dai ya ce mata tana gida ba ta da lafiya.
Ya din ga yawo gurin 'yan sanda da gidajen radio, yana bayar da cigiya ko za a ganta. Ya din ga jin tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu. Gefe guda ga mummunan mafarkin da yake yi da Shukura babu ƙaƙƙautawa har fargabar kwanciya bacci yake yi. Saboda munanan mafarkai ne marasa daɗi.
Ya shiga Asibiti ya tarar da wata katoɓara, an yi wa matarsa insulin allurar sauke sugar, fiye da kima suganta ya yi mummunan sauka, har ta shiga shock.
Tare da sauran abokan aikinsa likitoci, suka yi ta fafutuka ƙoƙarin ganin sun ceto ranta. Yana tsaka da wannan tashin hankalin 'yan sanda suka kira shi, ya tafi cike da fatan 'yarsa Hafsa aka gani. Sai dai 'yan sanda suka ce masa Asibiti za su je ya ga wata yarinya da aka tsinta aka kaita domin a duba lafiyarta. Suka ɗauke shi a mota suka tafi. Sai dai suna zuwa aka tafi da shi ɗakin adana gawarwaki. Sam bai kawo komai a ransa ba, idonsa ya rufe kawai Hafsansa za a nuna masa. Sai dai aka fito da gawarwaki biyu. Ɗaya a kango a ka tsince ta, an fafe cikinta an kwashe wasu sassa na jikinta a can wata unguwa. Yarinyar sanye da Uniform ɗin makarantar da ya fasaltawa 'yan sanda.
Tamkar ba Namiji ba, haka ya kurma uban ihu ya faɗi ƙasa sumamme, bayan ganin 'yarsa Hafsa a wannan mumman yanayi.
Bangaren Sagir ma bai fitar da rai ba, yana ta addu'a, da ji a jikinsa Yusransa za ta dawo. Ga shi satin haihuwarta ya kama. Ya daure ya lallaɓa ya je duba Yusra. Wadda ita ma jiki yake a rikice.
Sai dai da yaje ya tarar da jikinta da ɗan sauƙi, dan har suka ɗan fara hirar hankali.
Ta ce "Haryanzu ba a ga matarka ba ko?"
"Haryanzu Yusra, amma kina yi mata addu'a Allah ya bayyanata?"
Ta ce "Ina yi mana, ina so Allah ya sanya a ganta, kuma fa a satin nan za ta haihu, dan ta ma fara naƙuda kaɗan-kaɗan"
Ya ce "Yaya aka yi ki ka sani?"
Ta ce "Mafarkinta na yi mana, tana kulle a wani ɗaki mai duhu, ta ce mini ba ta jin daɗin zaman gurin, baka gani ba abin tausayi"
Idonsa fal ƙwalla ya ce "Duk a mafarkin ki ka ga haka?"
"Eh mana, tana ta kuka ma"
Ya ce "Shikenan, ya isa haka. Ki ci gaba da yi mata addu'a bari na je gida. Amma yaushe za ki zo mu koma gida, ina fama da kaɗaici"
Ta ce "Ko yau ka yi wa Anty magana sai na bika mu tafi"
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi"
Shukura kuwa tana kwance a ƙasa, zama babu daɗi, kwanciya babu daɗi duk inda ta motsa cikin nan sai ya tokare ta. Ga ciwon baya da na ƙafafuwa da take yi da take kyautata zaton naƙuda ta fara a tsaitsaye.
Sai dai tana yawan ganin Nana cikin mafarki, tana nanata mata ta yawaita addua babu ƙaƙƙautawa babu ji babu gani. Duk da tana yi ɗin amma ta ƙara ƙaimi gurin yi.
*****
Ko da aka shiga kwana na biyar da shigar Hammad halin da yake ciki, Sultan ya gama tsurewa babban tashin hankalinsa rashin cin komai da ba ya yi ga abin kullum gaba yake yi.
Tafawa ya samu Sultan a kan lallai a sake zaman majalissa, a ji bayanin Hammad a gaban kowa da kowa a kan yadda aka yi yake da ɗa kamar yadda ya faɗa."
Matawalle ne ya amsa masa da cewar "A tunanina wannan maganar ai ta wuce ko?"
"Ta wuce ta je ina? Kun san zata wuce ku ka dakatar da ni daga majalissa. Ya faɗi abin da dole sai ya fito ya kare maganar da ya yi. Ya ce yana da ɗa, ina ɗan yake? Kuma wacece uwar yaron? Idan kuma shaci faɗi ne to ta tabatta ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa da na faɗa ku ke ɓoyewa"
Matawalle ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ka san abin da zaka din ga furtawa a kansa, ko babu alaƙar jini a tsakaninku shi shugaba ne."
"Eh Hammad ɗa na ne, kuma shugaba ne, amma ba zai yiwu na zuba ido ina ganin ba daidai ba, a ce yana shugaba babu cikakkiyar lafiya ba kuma ku na dannewa ku ɓoyewa ba. Ita larura ai ba abin kunya ba ce, kuma abu ne da yakamata a sani domin a nemi lafiya"
Cikin nutsuwa Sultan ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ban sna meyasa ka ke aibata shi da da wannan larurar ba"
"Allah ya taimake ka, idan ba haka ba ne, mene ne gaskiyar batun ɗan da ya ce yana da shi?" Tafawa ya yi maganar yana tsare Sultan da ido.
"Abu ne da muke kan bincike a kai, koma mene ne zaka ji daga baya"
Ya ce "Shikenan na ji wannan, ina son zan yi magana da shi, magana ce a kan ɗiyata Asal"
Sultan ya kalli Tafawa cike da takaici, ya san yana sane yake wannan bin ƙwaƙƙwafin da bin diddigin a kan lallai sai ya ga Hammad."
Sultan ya ce "Za ka gan shi, amma nan da wani ɗan lokaci" Hakan ya sanya Tafawa sake tabattar da maganganun Asal.
A ransa ya ce "Idan ka san wata baka san wata ba Jalaludeen"
*****
Tun washegarin dawowar Nana daga gidan su Hammad, yanayin jikinta take jin babu daɗi, kamar akwai wani abu mara daɗi da yake faruwa. Sai dai ta danganta hakan da kewa da kuma tashin hankali da take ciki a kan Muhsin. Amma idan ta nutsu sai ta ji wannan damuwar daban ce, wannan a cikin jikinta da ruhinta take jin damuwar, sai dai ta yi iya ƙoƙarinta gurin danne damuwar, da duƙufa da addu'a Allah ya dawo mata da ɗanta.
Yau da safe Nana ta fito ta tarar da Nana, ta ɗora tukkwane daban-daban har uku a kan murhu, tana ta harhaɗa wasu irin saiwoyi da sassaƙe-sassaƙe tana ta zubawa tana dafawa.
Nana ta ce "Umman Muhsin, yau kuma baya aka tuna wa ake dafa wa magani"
Nene ta yi murmushi ta ce "Ba kula ki zan yi ba ai ki ƙarata, daɗin abin ƙwaryar sama ce ke dukan ta ƙasa daga ni har ke"
Nana ta yi dariya ta ce "Yasin ni ban bayar da magani ba"
"A'a tuna dai, tuna dai yarinya"
"To ai Sayyid kawai na yi wa"
Nene ta ce "Kash, an zo gurin dan haka ki yi mini shiru" Ta ƙarasa maganar tana janyo wayarta da ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta tsuke fuska ta kira Mahmoudu a waya. Ya amsa tare da gaishe ta.
Bayan ta amsa ta ce "Wannan uban kuɗin fa da ka sako mini?"
"A'a ki yi haƙuri ai ba naki ba ne, na kula da Gimbiyar Imam ne"
"Da can ku kuke bani abin kula da ita? Lokacin da take gararambar neman taimakon ba ku neme ta ba ba barin ta ku ka yi tana gantali a titi ba?"
Ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ba zan iya gaya masa haka ba. Haryanzu fa ma ni ban sake ganinsa ba tun ranar da ya je tare da ita. Ba ya gidansa baya fitowa zaman majillisa, ko hawa ba ya fitowa. Duk da na san an saka masa takunkumi shige da fice amma an tsaurara masa sosai. Ki yi haƙuri har gida za mu zo ban haƙuri. Dan Allah ki taya mu rarrashinta dan ta ƙi saurararsa gaba ɗaya, kuma wallahi hankalinsa a tashe yake nesa ba kusa ba. Ga tarin magauta da yake da su a cikin gidan su ma da ba barinsa suka yi ba. Dan Allah ku yi haƙuri Umma ke kin san sha'anin gidan sarauta kin san komai"
"Ni rabu da ni sai daɗin bakin tsiya, ai ko mutum zai danne ya yanka sai ka kare shi"
Yayi dariya ya ce "Ai ɗanki ne, kin san ba zai aikata haka ba, tuba muke ranki ya daɗe. Wallahi ina ta faɗi tashin na gan shi ne ma, na san halin da yake ciki. Amma a ƙara ba wa Gimbiyar Imam haƙuri"
"A'a babu ruwana, idan ku ka zo kwa bata da kanku" Suka yi sallama ta kashe wayar.
Ta kalli Nana ta ce "Kafin ki yi wanka, fara ɗibar ruwan maganin nan, ki je ki yi wanka ki gama, sai ki yi wanka da shi. Ki fito ki sha wannan maganin sai ki karya.
Nana ta ce "Shi kuma Nene na mene ne?"
"Na tsarin jiki da kariya ne, saboda kariya ne" Ta yi maganar tana basarwa, tare da tsuke fuska dan kar Nana ta addabe ta da tambayoyi.
Ganin hakan ya sanya Nana amsawa Nene, ba dan tana so ba.
*****
Mahmoudu ne ya iske Sultan a gurin shan iskarsa da yamma. Kasancewar shi ma ba shi da iyaka a shiga da fita a gidan Sultan, saboda Hammad, dan haka ganinsa ba wahala yake yi masa ba.
Sai dai yau kasancewar Sultan shikaɗai ne, ya fi sakin jiki da shi.
"Barka da wannan yammaci Sultan"
"Barkanmu dai Mahmoudu, kuna lafiya?"
Ya amsa da "Alhamdillah. Alfarma nake nema daga gare ka Sultan"
"Ina sauraren ka"
"Dan Allah a yi mini izini na ga Imam Hammad ne.
Sultan ya numfasa ya ce "Hammad babu lafiya. Ta so muje ka gani"
Ya tashi cikin ladabi, ya bi bayan Sultan. Suka yi tafiya mai nisa a sashinsa, can cikin wani ɗaki suka je ya buɗe masa ɗakin.
Cikin damuwa ya ce "Mahmoudu ya tabatta Hammad hauka yake yi, haukan ma irin wanda ban taɓa ganin kalarsa ba. Na ce ko a Nigeria da ku ka zauna ya yi irin wannan? Yanzu idan ka je kusa da shi zai iya shaƙe ka, tsawon wannan lokacin bai ci abinci ba, a haka kawai yake"
Cikin tashin hankali ya ce "Yayi ciwo daban-daban, amma ban ga ya yi irin wannan ba, ina kyautata zaton mutum ɗaya ne ya san matsalolinsa ciki da waje, ya san bakin zaren wannan ciwon nasa"
"Wane ne? Mahmoudu ba ma son asirinmu ya tonu fa"
"Da asirinmu zai tonu da tuni ta tona, sai dai a zo da Mahaifiyar Muhsin"
AREWABOOKS
Cikin rashin fahimta Sultan ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba?"
Cikin girmamawa ya ce "Matarsa da ya zauna da ita a Nigeria, saboda ni kaina na fuskanci wasu abubuwa masu ban mamaki a tsakanin su, bayan sun yi aure." Ya yi maganar yana kallon inda Imam Hammad yake ta mimmiƙewa yana kakari, kamar ana yanka rago.
Cikin damuwa ya ce "Yanzu tun wancan lokacin a haka yake?" Sultan ya jinjina masa kai ya ce "Ko ruwa bai sake sha ba, hankalina a tashe yake. Ga Tafawa ya sako ni gaba a kan Imam Hammad sosai da sosai; Yanzu dai mu je ka yi mini bayani gwari-gwari na fahimta"
Bayan sun fito, suka zauna tare da Mahmoudu.
Mahmoudu ya numfasa ya ce "Idan ban manta ba, bayan mun dawo daga bikin buɗe gidan cin abincin Imam na Maraɗi, mun dawo ka sanar masa da batun tafiya Damagaran ya wakilceka a taron sarakuna da za a yi a Zinder. Ba zan manta ba an kai ruwa rana sosai a kan tafiyar.
A tsukin lokacin ya kan gaya mini cewa, shi gaba ɗaya ji yake yi baya ƙaunar zaman ƙasar nan, yana jin kamar a cikin wani bala'i da masifa yake. Da fari na zata da wasa yake yi, amma sai na fuskanci da gaske yake a lokacin. Na ce masa mu sanar maka ko ɗaga tafiyar za a yi, amma ya ce mini a'a kar na gaya wa kowa, baya son ya ɗaga wa kowa hankali.
Tare muke kwana da shi a cikin gidan nan, muna shirin tafiya , kawai ya ce mini na same shi a ɗaya gidan nasa na kusa da gidan tarihi da yamma, mu yi tafiyar. Na ce masa mu tafi tare amma ya ce mini a'a.
Haka kurum bayan tafiyarsa hankalina ya ƙi kwanciya.
Kawai na kira shi na ce masa yana ina? Ya ce mini ya tafi zagaye can wajen gidan adana kayan tarihi na Agadez. Kawai na hau raƙumi na bi shi.
Sai dai na je gidan adana kayan tarihi na tarar bayanan, aka kira ni da ɓoyayyiyar lamba, aka ce mini an san Imam Hammad nake nema, ya bi cikin sahara. Ba tunanin komai na kewaya bayan gidan inda Sahrar nan take.
Na yi tafiya ta kai ta awa huɗu, saboda ina ganin sahun raƙumi a gurin. A tsakiyar sahara na ci karo da Imam Hammad cikin fita hayyaci a sume. Abin ya bani mamaki, na ciro shimfiɗa a jikin raƙumina, na yi na kwantar da shi na dudduba jikinsa na ga babu wata alama ta ciwo. Na jira ya farfaɗo ko na ɗauke shi mu koma gida.
Cikin ikon Allah ya farfaɗo, na ce masa meyasa ya taho cikin sahara haka? Ko ba shi da lafiya ne?" Ya yi mini shiru. Na ba shi ruwa ya karɓa ya sha.
Na ɗora shi a raƙumina ina mamakin yadda yanayinsa ya canza.
Muka doshi dawowa, sai dai muna nufo Agadez ya din ga wani irin ihu, ya faɗi a cikin sahara daga kan raƙumin ya din ga burgima yana kururuwa. Na sauka na riƙe shi ina tambayar ko lafiya? Amma ba ya iya magana sai ihu kawai.
Hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi da shi. Da mun nausa cikin sahara sosai sai ya yi shiru da mun nufo gida, sai ya rikice. Na rasa yadda zan yi ga yamma tana yi. Ba zai yiwu na