Showing 57001 words to 60000 words out of 124686 words

Chapter 20 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

89

Asal, ƙarshe ta kore ta daga sashen girke-girken gidan, zuwa wani abin daban.

Asal ta saka masa kukan, dan me zai kula wannan hadimar, sannan ya yabi jikinta. Ya din ga rarrashinta ya ce shi ba da wani abu ya yi ba.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ana tursasa Hammad jure abubuwa da dama Saboda Asal.
Kwatsam Tafawa ya kira Asal, ya ce ta je ta same shi, sai da gabanta ya faɗi tana zaton ko wani laifin ta yi. Ya kira ta cikin turakarsa. Ya ɗaukko mata wata 'yar ƙaramar laya, ya ba ta ya ce ta je ta samu wani guri da ido ba zai kai kanta ba, inda Hammad yake zama ta saƙale ta.
Ta yi shiru tana kallon layar, amma babu yadda ta iya haka ta karɓa ta tafi da ita. Ta din ga tunani ta saka ko kar ta saka. Saboda ba ta san ta mece ce ba. A iya zaman da suka yi tsawon shekaru tare, ba za ta iya cewa ga wani abu na cutarwa da Hammad ya yi mata ba, sai ma shi da yake shanye abubuwa da dama take yi masa, komai cutarwar hakan a gare shi.
Cikin dare yana tsaka da barci, ya ji tamkar ana girgiza gadon da yake kai, ya din ga ganin wasu irin halittu marasa kyan gani da tsoratarwa. A haka ya wayi gari kansa na neman juyewa, tun gari ya waye ya daina magana. Asal kanta sai da ta tsorata. Sai da suka kwana biyu da kyar yake iya cin abinci, sai ya din ga abu kamar baya cikin hayyacinsa. Tafawa kuma ya din ga kiranta yana tambayarta duk halin da ake ciki.
Sai da ta ga da gaske baya magana, ko majalisa baya fita, ta tsorata ta sanar da Sultan halin da ake ciki. Aka kai shi Asibiti amma aka kasa gane abin da yake damunsa. Sai dai jininsa da yake hawa fiye da kima. Ya yi jinya sosai da sosai.
Da kyar ya warke, sai dai Tafawa bai haƙura ba, gefe babar Asal ta bazama neman maganin haihuwa tana ba wa Asal. Sai dai kwatsam! Ita ma ta haɗu da jinya, ciwon suga ba ta san tana da shi ba ya yi ajalinta. Asal ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba, da rasuwar mahaifiyarta tamkar za ta zare. Hammad ya yi ta rarrashinta yana ba ta baki.
Tafawa bai samu zama ba, ya tashi nan ya faɗi can, duk domin ganin burinsa ya cika, gaba ɗaya rayuwarsa ba shi da cikakken sukuni, haka nan ya hana Asal ta zauna lafiya tare da mijinta.
Ya zamana ku san kullum ba shi da cikakkiyar lafiya, yau da lafiya gobe babu.
Tafawa ya fara magantuwa a kan yawan rashin lafiya da Hammad yake yi, yakamata ya sauka daga kan shugabancin Majilisar Imam, a bawa wani. A majalisar Sultan aka soke maganar da ya kawo.
Hammad kawai yana tafiya ana ganinsa, amma a cikin jikinsa shikaɗai ya san abin yake ji. Ko Asal bai fiye sakin jiki da ita ya gaya mata damuwarsa ba, saboda sam ba ta da alƙibla, kuma tsawon shekaru da suka shafe tare, ba ta iya fahimtar damuwarsa rashin lafiya kai tsaye, sai idan tana da buƙatar wani abu a gurinsa.
A haka ta sake neman komawa karatu, lokacin Hammad ya karaya da neman haihuwa. Idan yana salla har kuka yake yi, abin yana burge shi ya ga mutum da ɗan uwansa sun haɗa kai, shi kuma ba shi da wanda suke ciki ɗaya. Mahaifinsa kuma ayyuka sun yi masa yawa, matarsa kuma bai gama gane kanta ba. Dan haka duk wani rikicinsa, shi kuma ba ya gajiya. Wasu lokutan ya na jin daɗin ya bi Mahmoudu gurin Ummansa, su je su wuni, su ci abinci tare. Duk da yana matuƙar jin nauyinta, na abin da aka yi mata a masarautarsu, sai dai bai taɓa ganin hakan a fuskarta ba.

Ya yi shiru yana kallon Nana, da ta yi shiru tana saurarensa.
"Ya ka yi shiru kuma?"

"Na gaji, kuma bacci nake ji"

Ta ce "A'a wannan wayo ne na kar ka ƙarasa mini, dama ni ƙarsheƙarshen nan, ba jin daɗinsa na yi ba, gara ma farkon labarin tun da tarihi ne."

"Saboda zancen Asal ne?"

"Zan iya cewa eh ɗin ma, saboda mutane kaɗan na tsana a Duniya, kuma ta shiga cikinsu" Ta yi maganar tana tsuke fuska.

"Amma meyasa?"

Nana ta ce "Kawai ba ta yi mini ba"

Hammad ya yi shiru ya ce "Ba na tunanin kishi ne kawai ya sanya ki ka faɗi haka, akwai wani dalili, ba kya faɗar magana haka kurum mara ma'ana"

Ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Ba mai ma'anar ba ce gaskiya, mu je a haka kawai, kishi ne ya sanya na faɗi haka. Yanzu dai ni ka tsallake nan, ka gaya mini yadda aka yi ka din ga wasa da hankalina, da yadda ka gane ni amma ka share ni, nake yi wa matarka aiki cikin ƙasƙanci da wulaƙanci. Kuma alhalin ka na iƙirarin ka na so na. Har kuka na yi mata, da ta ce za ta kawo ni Agadez na ce mata ina da jariri, amma buɗar bakin matar nan ta ce ni ta shafa, tun da talaka ce ni dole na yi abin da take so. Ba zan manta wasu abubuwan da ta yi mini ba na cin mutunci har abada"

Ya ɗago da fuskar Nana tana kallonsa ya ce "Ba wannan ne dalilin da ya sanya ki ka ce ba kya sonta ba, akwai dalili. Wannan ba halinki ba ne, idan wannan dalili ne da abin da na yi miki ba za ki sake zuwa inda nake ba"

AREWABOOKS

Ta kawar da kanta gefe ta ce "Ka ƙarasa mini kawai, mu bar wannan maganar"

"Asmy, Asal ko ba aure tsakanina da ita matata ce, ban kuma gaya miki halin da muke ciki, domin na tozartata ba, iya abin da na sani na sanar da ke game da zamantakewar mu, saboda shi ne mahaɗin labarin rayuwata da ke"

"Ai dama ban ce kar ka so ta ba, ka je ka yi ta son nata"

Ya ce "Ai ba zancen so muka yi da ke ba, ki yi shiru mu ƙarasa an kusa fara kiran Asuba"

"Ba na son ji" Ta yi maganar tana kifa kanta tare da tsuke fuska.

"Merci ma viee, ba na son ki din ga ɓata ranki, mun bar wannan maganar tun da ba kya so, yadda ba na son kowa ya raɓe ki, ke ma haka ne na sani, kuma na san kin yi ƙoƙari kin yi haƙuri sosai da sosai da juriyar da ki ka cancanci a sara miki, amma ki yi haƙuri mu ƙarasa maganar, daga ƙarshe duk hukuncin da ki ka yanke mini, zan karɓa"

Ta ɗago kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, azababben kishin Asal yana taso mata, babu abin da yake ƙara ɓata rai irin cin mutuncin da Asal ta din ga yi mata a matsayin kishiyarta.

"Kin huce mu ci gaba?" Ta yi masa shiru.

Ya ce "Matso na rungume ki, ki nutsu sai mu ci gaba" Ya ƙara matsawa kusa da ita, ya rungumota jikinsa, yana murmushi. Ta kwanta lamo a jikinsa yana shafa bayanta a hankali.
A ransa ya ce "Asmy, ba za ki taɓa jin rabi a kwatankwacin abin da nake ji a kan ki ba, ina ƙaunarki ina kishinki, Allah ya bamu haƙurin zama da juna"

Asal kuwa na can a tsaye, tamkar ta haɗiyi taɓarya, idanunta suka sauka a kan agogon bangon ɗakin. Idanunta sun bushe, zuciyarta ta ƙeƙashe sai raɗaɗi da idanun kawai suke yi mata.
Haryanzu ta kasa yadda Hammad ne yake da wata matar, matar ma baƙar fata da a kyau ba ta kai ta komai ba. Babban abin da ya ƙara rikita ta bai wuce batun ɗa da Tafawa ya tabattar mata da Hammad yana da shi ba, har ɗan shekaru biyu ba.
Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri da sauri, tsawon lokacin nan ba ta taɓa tunanin son da take yi wa Hammad ya kai haka ba, ashe duk abin da take yi bonono take rufe ƙofa da ɓarawo. Tana zaman zamanta ta janyo masifa da kanta jikinta. Ta din ga tunanin ko dai wata ƙulla-ƙullar ce ta daban aka yi. Sai kuma ta tuna babu yadda za a yi Nana ta samu zarafin shiga har sashen Sultan, su keɓe da Hammad idan ba matarsa ba ce ba. Kenan Sultan ya goyi bayan abin da Hammad ya yi na auren baƙar fata da ba ƙabilarsu ba?. Kawai ta ɗora hannu a ka ta rushe da kuka, hawaye ya ƙi zubo mata sai azabar zafi da zuciyarta take yi.
Gimbiya Bilkisu ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Asal lafiya kuwa?"

"Na shiga uku na lalace Gimbiya, wallahi Hammad ya cuce ni ba zan yafe masa ba. Kuma wallahi sai ya rabu da ita, an cuce ni an cuci rayuwata"

Ta rungume Asal tana rarrashinta, ta ce "Ki yi haƙuri, ki daina wannan kukan kar ki samu matsala, ki kwantar da hankalinki na san Sultan ba zai ƙyale shi ba, zai ɗauki mataki" Asal ta ci gaba da kuka da babu abin da yake ƙara mata sai nauyin zuciya.

*****
Imam Hammad kuwa a hankali ya ɗan ɗago fuskar Nana ya ce "Bacci ki ke yi ne?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"To tashi mu ci gaba" Ta noƙe kafaɗa tana ƙara rungume shi.
Ta ce "Imam ka ci gaba mu yi mu bar gurin nan, Aljanun gurin nan sun fara tsorata ni, kar a samu matsala"

"Kina ganinsu ne?"

"Su na bayyana a siffofi daban-daban, tsofaffi tukuf da matasa da wasu halittun daban, duk ina ganinsu addu'a kawai nake yi tun ɗazu"

"Ni da ke duniyarm daban take, ƙalubale iri ɗaya, Ubangiji Allah ya bamu lafiya rayuwar Hammad".
Ta sake lafewa a jikinsa ta ce "Ka ci gaba to"

Ya numfasa.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Hammad na fuskantar suka da ƙalubale kala-kala. A kwana a tashi ya haɗu da larurar zafin jiki, idan jikinsa ya ɗauki zafi tamkar an hura wuta. Babu wanda ya sani sai Asal, dan ya fi kama shi cikin dare, ita ta ɗauka kawai normal zazzaɓi yake yi sai ta yi masa sannu kawai ta ci gaba da sabgoginta.
Sultan ya mallaka masa wannan jakar fatar mai kama da laya, wadda ita ma a cewarsa ta tsari ce, kuma tana ɗauke da aljanun da suke yi wa mamallakanta hidima. Duk lokacin da ya murza zobensa, ya kan gansu a suffar tsuntsaye, irin wanda bai taɓa gani ba a duniya, ko suffar wani abun daban. Wasu lokutan ko be murza zoben ba, ya kan gansu, ko ya din ga ganinsu a barci. Duk da ba shiri suke yi da Yayansa Zahradeen ba, saboda Gimbiya Bilkisu ta shiga tsakaninsu, amma ya taɓa tambayarsa, ko yana ganin wannan tsuntsayen shi ma idan ya murza zobunansa. Zahradeen ya ce masa baya ganin komai, an ce duk mai zoben yana iya ta'amalli da aljanun jikin zoben, amma shi baya ganin komai. Ya tambayi Hammad ko yana gani shi. Ya ce masa aa saboda ya karanta tarihin zobunan a littafin Kundin Agadez ne ya sanya ya tambaye shi. Haka ya tambayi sauran Imam ɗin, su ma dai bai ji alamun akwai wanda yake ganin wani abu ba. Abin da bai sani ba, tun zamanin kakansa, aka canza zobunan, na hannunsa ne kawai na ƙwaran da babu wanda ya sani, sai mahaifinsa da kakansa, sai kuma marigayi Matawalle.
Kwatsam tafiya ta kama Sultan, ga taron sarakuna da za a yi. Sai ya wakilta Hammad ya ce yaje ya wakilce shi. Nan da nan aka hau surutun da me bai wakilta kowa a majalisar sa ba, zai wakilta yaro ƙarami, maimakon ma a ce a cikin Imam ɗin a zaɓi wanda suka fi shi shekaru.
A lokacin Hammad bai daɗe da buɗe sabon branch ɗin gidan abincinsa a Maraɗi ba, ya wakilta cousins ɗin sa Hasna da Al Hussain a matsayin masu kula da gidan cin abincin.
Babban abin da yake ƙara ɗaga wa masu son ganin bayansa hankali, bai wuce yadda mutane suke son sa ba. Saboda ya iya shugabanci, shi wannan ƙyamar ma da ake nuna wa baƙaƙen buzaye ba ya yi. Yana damuwa da lamuran na ƙarƙashinsa sosai da sosai, wasu lokutan ma kamar ba basarake ba, saboda yadda yake alaƙa da su. Ga kuma girmama shi da suke yi tamkar Sarki. Hasali ya fi nuna saurata da izzarsa a lokacin da yake cikin 'yan uwansa masu Sarauta. Ga shi manyan mutane na son sa, su na son mu'amala da shi, saboda ladabinsa, da iya magana, fiye da sauran Imam, har ma da 'yan majalisar Sultan ɗin, mussaman da duk wanda ya ga Sultan ya ga Hammad, ya san jininsa ne.
Yana ta shirye-shiryen tafiyar taron nan Niemey, a lokacin ga shi nan ne kawai, kansa kamar zai ɓare saboda ciwo.
Yana kwance cikin dare tare da Asal su na bacci, ya yi mafarkin wani sanye da baƙaƙen kaya, yana soka masa allura a ka.
Ya farka a razane, sai dai ya din ga jin raɗaɗin allurar nan a zahiri. Ya sanya hannayensa biyu ya dafe kansa, yana rintse idanunsa yana ambaton Allah, amma kan tamkar zai yi bindiga. Ya tashi zaune da kyar ya yaye bargon da ya rufe jikinsa kawai ya ga wata takarda. Ya ɗauki takardar ya duba sai ya ga hoton ƙwarangwal na ci da wuta, ga sunansa a jiki. Hakan ya yi daidai da sake jin kamar kwanyarsa za ta zazzago.
Ya kifo daga kan gadon ya a rirriƙe kansa, ga jikinsa ya fara wannan zafin. Kawai ya din ga jin idan bai bar garin nan ba, mutuwa zai yi saboda wata irin azaba da yake ji mara misaltuwa.
Ya yinƙura ya tashi da kyar, ya ga Asal a zaune a kan gadon tana kallonsa, ya nufi hanyar fita jikinsa na tsuma, amma kasancewar dishi-dishi yake gani, ya faɗi a gurin.
Washegari ya tashi normal, sai dai jin da yake yi idan bai bar inda yake ba, kamar zai zauce.
Ya yi tafiyarsa ɗaya gidan nasa, ko zai daina jin abin da yake ji, amma abu ya din ga jin cigaba, ya din ga jin kamar a cikin wata masifa yake.
Ya yi waya da Mahmoudu a kan tafiyar su, ya ce masa su haɗu a ɗaya gidan nasa.
Gaba ɗaya ya ji tashin hankalin na ƙara ƙaruwa, ga wata kururuwa da yake ji a cikin kunnuwansa, ganin wasu irin halittu su na yi masa shawagi a kansa. Su na ta watso masa takardun nan na zanen ƙwarangwal. Yana daga kwance ya din ga jin ana kiransa, ana ya tashi ya je gidan ajiye kayan tarihi ana nemansa. Ya toshe kunnunwansa, amma ya gaza daina jin hayaniyar.
Jin da yayi yana neman ya haukace, kawai ya tashi ya fita ya hau tafiya. Duk da da ɗa  nisa daga gidansa na wajen masaruta, haka ya din ga tafiya har ya je gidan tarihin. Yana zuwa mai tsaron ƙofar ya buɗe masa. Da takardar nan mai hoton ƙwarangwal ya sake cin karo,  muraran a zahiri ya din ga ganin aljanun da ke cikin gidan tarihin nan, muraran a siffofi daban-daban. Su na ta fitowa daga cikin ɗakunan nan, wasu su na ratso bango su na fitowa, suka nufo shi su na yi masa wani irin ihu. Ya toshe kunnunwansa, sai ga waɗanda yake gani a suffar tsuntsaye, sun bayyana su na make masu nufo shin. Wata irin guguwa ta tashi a tsakiyar gurin, aka yi wata irin walƙiya mai ban tsoro sai ga Giyaz ya keto ta tsakiyar gidan tarihin ya bayyana a gabansa.
Giyaz ya nufo shi, wannan tsuntsayen suka yi kansa, shi kuma Hammad ya tashi ya fice daga gurin, jiri yana ɗibarsa, ya san ya fito daga gidan tarihin sai dai bai san ina ya nufa ba, kawai ya buɗe ido ya gan shi a sahara tare da Mahmoudu.
Ya yi shiru yana kallonsa, sai ga Giyaz ya kuma bayyana a cikin saharar, cikin tsofaffin kayan nan tamkar auduga saboda tsufa. Ga wani irin sauti da saharar take yi, tamkar iskar za ta taso.
Wata irin dariya Giyaz yake yi mai ban tsoro.
Ya ce "Ban sani ba, ko haɗuwa da kai ya sanya na ce na fi kowa sa'a a cikin sararin Duniyar nan, saboda aikin da aka bani a kanka, ya sanya na samu 'yanci. Ni ne Giyaz ibn Jaddul Jinn, ɗaya daga cikin aljanun da suka yi wa kakanninka hidima, daga ƙarshe aka kore shi daga fadar, saboda wani laifi da ya aikata da bai taka kara ya karya ba. Ya tattara iyalansa ya koma Nigeria da zama, ya cigaba da hayyayafa, can ma aka samu waɗanda suka ƙara cutar da shi. Duk da na shafe tsawon shekaru ashirin a tsare, yau wani boka ya bani 'yanci, sannan ya damƙa mini aiki a kanka. Dan haka ko zamu mutu tare sai na cika aikin nan da na karɓa a kan ka" Hammad bai gama gane me Giyaz yake faɗa ba, hankalinsa ya gushe.
Bayan ya sake farfaɗowa, ya sake tozali da Habu, sai dai ya manta a inda ya san shi, ko ya taɓa ganinsa.
Duk iya ƙoƙarinsa ya kasa tuna komai game da kansa. Shi dai ya san shi mutum ne, duk wani abu da ya shafi rayuwa yana iya tuna shi, amma duk wani abu da ya shafe shi, ya manta.
Ko da Habu ya yi yinƙurin mayar da shi Agadez, bin sa kawai yake yi, amma bai san waye shi ba, sai dai su na dosar Agadez Giyaz yake bayyana, yana feso mu wata irin wuta mai ban tsoro, a take sai jikinsa ya ƙara rikicewa ya ji tamkar zai zauce kansa yana wani irin gigitaccen ciwo, bugun zuciyarsa ya ƙaru, ya din ga jin zafin wutar da Giyaz yake feso masa a jikinsa ta na ƙona shi. Gaba ɗaya ya rikicewa Habu. A dole suka bar Agadez suka nufi Nigeria. Su na tafe Hammad yana ganin abubuwan da ya lura abokin tafiyarsa wato Mahmoudu ba ya gani. Duk tambayar da ya yi masa a kan waye shi, ya sunansa ya tuna wani abu game da rayuwarsa amma ya kasa.
Da suka shigo Nigeria, suka samu masauki, bai sake ganin Giyaz ba, sai dai lokaci zuwa lokaci wannan zafin jikin yana tayar masa.
Tun da suka shigo Nigeria, yake mafarkin wata matashiyar budurwa, tare a cikin sahara. Sai ya kwaɗaitu da son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login