Showing 15001 words to 18000 words out of 124686 words
ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haɗe rai.
Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi haƙuri"
Ya miƙe ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa.
Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya ɗauki wayarsa ya kira Tafawa.
Tafawa ya ɗaga tare da yin sallama.
Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daɗe"
"Barka dai" Ya amsa a taƙaice.
"Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta"
"Hammad, ni ka ke gaya wa haka?"
"Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba ɗaya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan.
A zaune ya tarar da Nana a ɗakin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu ɗan kwali. Ta yi parking ɗin black natural hair ɗin ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa riƙe da ledoji, ya ƙarasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaɗai ko?"
"Dama can ai nikaɗai ɗin nake rayuwata"
Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni ɗin ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta ɗauki ɗan kwalin kayan, za ga ɗaure kanta. Ya janye ɗan kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai"
"Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taɓa tasiri a kaina ba, ka bani ɗana kawai na kama gabana"
"Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid. Ga abinci na kawo miki, ki ci"
Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni ɗa na?"
"Kin ci, amma ba kamar yadda nake buƙata ba, sonake ki ƙara ƙiba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki ƙoshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi."
Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri.
Ya zauna a kusa da ita ta ɗago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya ɗago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa.
Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi"
"Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daɗi. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taɓa aikata shi sai ni."
Ayshercool.
08081012143
81
Nana ta taɓe baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haɗa ni da masarautarku, kawai a bani ɗa na na tafi"
Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?"
"Eh" ta faɗa tana kawar da kanta gefe.
"Shikenan, zan ƙara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu ɓatawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan banƙara na aikata, domin ganin ba ki suɓuce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata ɗin na nufin ƙara miki ƙiyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguɗa baki ta sake kawar da kanta gefe.
Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau ɗaya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da roƙonsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wulaƙanci ne aka yi masa.
Ganin ya ƙi tashi ya bata guri, ya sanya ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta.
Ta sake kai hannu ta ɗauki ɗankwalinta, amma ya jefa shi bayansa.
Wannan kallon da yake ƙanƙance ido ya fara yi mata, ta ƙara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi.
Baƙi ƙirin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma yaƙi barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi.
Duk wani abu da Nana za ta yi ta baƙanta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita.
Sai da ya bar ɗakin ta samu ta ci abinci, ta tura ƙofar ɗakin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse ƙofar dan kar ya shigo mata.
Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita.
*****
Doctor Sharif ne ya tashi a razane, bayan mummunan mafarkin da ya yi da Shukura, ta biyo shi tana kuka jikinta duk jinin haihuwa, da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana, ya ba ta jaririnta.
Ya din ga gudu yana ihu, ya ɗan tsaya ya waiwaya kawai ya ganta a tsaye a kan matarsa, da wannan wuƙar a hannunta, tana kallon cikin tana kallonsa tana faɗin "Ka zo ka bani jaririna, ko na farka cikin matarka na ɗauke nata, ka ji abin da na ji" A daidai nan ya tashi cikin razani, ya haɗa uban gumi.
Ya kalli agogon ɗakinsa ya ga ƙarfe biyu da kwata na dare, kawai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, so yake ya je ya ga halin da matarsa take ciki, amma ya tuna wa zai fita ya bar wa yaransa mata su biyu da suke bacci. Doctor Sharif bai samu haihuwa da wuri ba bayan ya yi aure, sai da suka shekara goma sannan ta haifi yara mata biyu, yanzu za ta yi na uku ciki yana ta wahalar da ita. Tun da ya haɗa kai da Alhaji Zailani ya ba shi jaririn Shukura abin yake damunsa, amma tun da Alhaji Zailani ya shaƙa masa kuɗi, sai ya manta sai kuma yau da ya yi wannan mummunan mafarkin.
****
Yau ma Nana a kan gadon rannan ta hango Ƙaisar, lulluɓe da mayafi, hannunsa kawai ya ziro ta ƙasan mayafin yana rubutu a kan wani littafi.
Ya ɗago kai ya kalle ta, ya ci gaba da rubutunsa.
"Ƙaisar"
"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Wai dan Allah me ya same ka?"
"A ina?"
"Na ga yanzu kullum ka na kan gadon nan, kuma a lulluɓe. Giyaz ne ya yi maka wani abin ne?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a me ki ka gani?"
"Na san shikaɗai ne yake iya cutar da kai" Ta yi maganar a sanyaye.
"In ji wa? Akwai Aljanu masu ƙarfi da suka fi ni ƙarfi da za su iya cutar da ni. Kawai ni ba na shiga harkar kowa ne, ina gefe ina jin daɗin rayuwar kaɗaicina da litattafaina da haɗa magunguna na"
Nana ta yi murmushi ta ce "Yaushe za ka yi aure ne kai?"
"Sai na girma"
"Au yanzu baka girma ba? Ina Haula ne?"
Tsuke fuska ya yi ya ce "Je ki ɗakin magungunana, akwai wata kwalba taswirarta kamar zanen Duniya, ki ɗaukko ki kawo mini"
Nana ta ce "To" Ta nufi ɗakin da yake ajiye-ajiyen kayan maganinsa.
Ta tsaya tana ta kallon kwalaben, da yadda wasu magungunan suke yawo a cikin kwalaben, tamkar abubuwa masu rai.
Ta ga wanda ya ce ta ɗaukko ta waiwayo kawai ta ga Giyaz a tsaye a bayanta.
"A'uzubikalimatillahi tammat" Ta furta cike da tsoro, a suffarsa ta tsoho tukuf ya bayyana a gabanta.
Ya buɗe baki ya ce "Ban taɓa ganin halittar da na tsana a doron ƙasa ba sama da ke, sai na sabauta rayuwarki, sai na kashe ki na ƙarar da zuriyarku na huta da wannan bala'in. Ya ja da baya ya nuna ta da sandarsa, da take ci da wata irin wuta mai tartsatsi.
Nana ta ja da baya, ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, tana jiran jin wutar ta fara ƙona ta, amma ta ji shiru. Ta buɗe idanunta a hankali ta ga Ƙaisar ya shiga tsakiyarsu, tartsatsin wutar ya ƙona shi, ya faɗi a gefe jikinsa yana hayaƙi.
Nana ta saki kwalbar ta nufe shi da gudu. Cikin tashin hankali da tsoro ta ce "Ƙaisar, me ya same ka?" Sai a lokacin ta ga tarin raunukan da suke jikinsa, ga ƙonewar da ya yi yanzu.
Giyaz ya ƙaraso kan Ƙaisar da sauri, ya saka hannunsa ya ɗago shi, amma ya ga jikinsa ya saki.
"Wallahi muddin ɗa na ya mutu sai na kashe ki har lahira"
Cikin dakiya da kawar da tsoro ta ce "Me ka yi masa? Kai wane irin azzalumar halitta ne wai, kowane abu yana alfahari da ɗansa da ƙoƙarin ba shi kariya, amma kai kullum cikin ƙoƙarin cutar da shi ka ke. Ƙaisar ka tashi dan Allah. Ta yi maganar cikin kuka tana ƙoƙarin taɓa shi, amma wani irin matsanancin sanyi ya ratsa ta.
Ta buɗe idanunta a hankali cikin sheshsheƙar kuka, har da majina kawai ta ganta a jikin Sayyid ya riƙe ta gam yana kallonta cikin tausayawa.
Ta yinƙura za ta tashi amma ya hana ta, ya ce "Ki bari ki ɗan nutsu. Me ya same shi ki ke wannan uban kukan haka? Idan komai ya lafa mini, dole na ɗauki mataki a kansa, dan ba zai yiwu ya din ga bibiyar matata ba, ina baƙin ciki da hakan"
"Ba za ka yi masa komai ba, babu ruwanka da shi, tun da dai duk da tsana da abubuwan da nake yi masa, shi bai gudu ya bar ni ba, kamar yadda ka yi mini ba"
Ya ɗan zura mata ido har zai yi magana sai kuma ya fasa.
Ta zame daga jikinsa ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa da tashin hankali, tare da fatan Allah ya sanya ba wata mummunar illar Giyaz ya yi masa ba. Ya tashi ya bar mata ɗakin, dama kukanta da sheshsheƙarta ya jiyo, shi yasa ya fito ya je ɗakin nata.
Washegari da safe, ya kawo mata kayan da za ta saka su tafi. Ya kalle ta cikin magiya ya ce "Ma vie, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki tattara nutsuwarki guri guda, domin mu samu mafita.
Duk abin da za su tambaye ki, ki sanar musu da komai, kar ki ɓoye musu komai saboda makomarmu"
"Ni ba wata makomarmu, kawai ɗa na za a bani na tafi"
Ya ce "To na ji, ga riga da za ki saka, ki je ki yi wanka ki shirya, ina jiran ki" Ta kalli rigar kamar ba zata karɓa ba, sai kuma ta karɓa ta ce "Na gode"
Ya yi murmushi ya ce "Ko mu je ki yi wankan a ɗakina, akwai mayukan shafawa"
"A'a ina da man da zan shafa"
"To su ma nawan ne dai ki ke shafawa, saboda tsabar ƙauna" Ta murguɗa baki ta juya ta ajiye kayan, murmushi ya gaza barin fuskar sa. Ya ce "Kin san me na tuna? Lokacin da ki ke yi mini wanka mu na Nigeria, sauran ki yi mini wanka a Agadez".
"Sai ka je gurin Gimbiya hamshaƙiya, farar fata da take biladama ta yi maka" Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba.
Ko da ta yi yinƙurin juyowa, sai jikinsu ya haɗu, sam ba ta san ya ƙaraso bayanta ba, saboda cikin takunsa mai kama da hawainiya ya ƙaraso. Dan sam ba shi da hayaniya ko karakaina.
Ya saka hannunsa ya zagaye ƙugunta, ƙirjinta ya tsananta bugawa tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta.
"Ma viee banda dalilin soyayyarki, ta sarƙe ni ta ko ina ta hana ni motsi, da sai na saka an sa bulala an zane mini ke. Imam Hammad ki ke yi wa magana a haka? Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina ɗaga mini murya" Ya yi maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai ta ta har su na jin numfashin juna.
Yana murmushi ya ce "Na taɓa yi miki wannan kashedin, kin tuna?" Ya yi maganar yana kashe mata ido.
"Dan haka ke za ki yi mini wanka a Agadez da ma"
"Ni ka cika ni ba na son irin wannan abin" Ta yi maganar kamar numfashinta zai ɗauke.
Ya cika ta ya bar ɗakin, ta zauna tana sauke numfashi.
*****
"Jamila ki yi bayani, na kasa gane kan wannan ciwon naki, na fara jin tsoro ki gaya mini me yake faruwa?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai"
"Wallahi sai kin gaya mini, damuwarki ta yi yawa, ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinyewa mene ne yake faruwa ki ke ɓoye mini" Mama ta yi maganar cikin tashin hankali tana zazzaro ido cikin fargabar abin da Jamilan za ta sanar da ita.
Ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta ta ce "Dan Allah Mama ki yi haƙuri ki ƙyale ni, ni babu abin da yake damuna"
"Wallahi Jamila sai kin gaya mini uban abin da yake damunki, mene ne yake damunki?"
"Ni ma ban sani ba" Ta yi maganar tana kuka mai ƙona zuciya.
"Wallahi kin sani sai kin gaya mini" Ta yi maganar tana ƙara zazzare wa Jamila ido.
Kawai Jamila ta yi mata shiru, ta ci gaba da sheshsheƙar kuka.
"Za ki gaya mini ko sai na shaƙe ki?"
Jamila ta girgiza kai ta ce "Ciki ne da ni"
Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Mama, ta ja da baya ta dafe ƙirjinta, tana wani irin haki, tare da kallon Jamila cike da tsoro.
"Jaa..jam..jamilahh me ki ka ce? Ciki fa a ina? Kuma garin yaya?" Jamila ta ci gaba da sheshsheƙar kuka ba ta yi magana ba.
Mama ta shaƙe Jamila ta ce "Ki gaya mini uban waye ya yi miki ciki kafin na take ki na kashe, da ki janyo mini abin kunya"
"Ke Rabi, kina ina ne? Waye yake yi mini kuka, kuma maganar me na ji ana yi?" Muryar Baba ta katse ta. Da hanzari ta saki wuyan Jamila, ta ja da baya tana hararta cikin ƙunar rai. Ta yi ƙwafa ta fito daga ɗakin su Jamila.
"Me yake faruwa ne?"
"Babu komai, jikinta na shiga na duba"
Baba ya ce "Kuma shi ne take ta kuka haka? Ni na gaji da larurar nan ta Jamila, wannan banke-banken hayaƙin da ki ke yi mata duk ba ne ba"
Ta ce "To in sha Allah za mu je. Ka san mun je, mun kuma zuwa amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, amma za mu koma"
*****
Nana ta tsaya tsuru da rigar nan a jikinta, ita kanta ta san ba dan albarkacin kaza ƙandagare kan sha ruwan kasko ba, ta san ba ta kai ta saka wannan rigar ba.
Ta jikin mudubi ta hango shigowarsa, kayansa royal blue, kalar rigar jikinta.
Ya ƙaraso gabanta, ya fesa mata turare, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro zobuna da abin hannu ya saka mata. Ta yi ƙuri da ido tana kallon hannun nata, rabon da ta sanya wani abu na ado, har ta manta.
A tsorace ta ce "Ni dai zan cire wannan abin tsoro nake ji"
Banza ya yi mata ya gyara zaman mayafin rigar a kanta. Ya din ga ƙare mata kallo yana mamakin yadda Asal take aibata Nana da muni, dan kawai baƙar fata ce.
Idanunta manya sexy eyes, farare ƙal da su, gwanin ban sha'awa, ga shi rigar tamkar dan jikinta aka yi ta.
Ya numfasa ya ce "Ina ƙara tuna miki, duk wani abu da za a tambaye ki, kar wanda ya baki tsoro, kar kuma ki rufa komai, muddin ki na son Muhsin ya dawo hannunki"
"Meyasa kai ba za ka yi musu bayani ba kawai?"
"Da bayanina ya wadatar, ba zan bari a zo wannan gaɓar ba". Ya ciro niƙab ya saka mata.
Sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarta daga aljihun rigarsa.
Nana ta waro ido ta ce "Wayata, ya aka yi ta zo hannunka? Dama kai ka ɗauka?"
"Eh ni na ɗauka, kin ƙi saurarata, balle na yi miki bayanin komai, mu je" Ya yi maganar yana nuna mata hanya.
Bakinta fal magana, amma ya yi mursisi, ya yi mata shiru. Ta tarar da takalma a falon gidan. Nana ta din ga ganin abin tamkar a mafarki.
Su na zaune a baya ita da shi, ana jan su a motar. Ta yi shiru tana zabga addu'a Ubangiji Allah ya bata nasarar karɓar ɗanta, dan ko kaɗan ba ta sha'awar gidan nan, ɗan zamanta a gidan kawai ta fuskanci akwai kitimurmura a gidan.
Tun da aka doshi gidan gaban Nana yake tsananta faɗuwa, haka kurum take jin ba ta ƙaunar gidan. Gefe guda kuma Nana tana ta tunanin halin da Ƙaisar yake ciki.
Tun da aka yi parking suka fito, hadimai suke gaida Imam Hammad yana ɗaga musu hannu. Ya riƙe hannun Nana yana ratsa cikin gidan da ita. Gaba ɗaya aka zubo musu ido, ana son sanin wacece wannan ya riƙo hannunta, saboda kowa ya san ba Asal ba ce, saboda ba ta kai Asal tsawo ba, kuma Asal ba ma'abociyar niƙab ba ce, ko kanta ma ba ta damu da rufewa ba.
Jikin Nana ya hau rawa, bayan da suka shiga ɗakin zama na musamman na cikin fadar Sultan.
A can suka tarar da Sultan ɗin, ga Matawalle ga Sardauna, su na jiran isowarsu.
Nana ta ja ta tsaya jikinta yana wata irin rawa, har ƙafafuwanta, gabanta ya din ga faɗuwa. Duk ta kowacwa kusurwar ɗakin, akaai na'urar sanyaya ɗaki, amma Nana ta kasa gane