Showing 60001 words to 63000 words out of 124686 words

Chapter 21 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

86

saninta a zahiri. Idan ya kwanta bacci, ba abin da yake mafarki sai wannan yarinyar. A duk lokacin da ya farka, sai ya din ga jin akwai wani abu mai muhimmanci da yake son haɗuwa da shi, duk a duniyar da ya farka, babu wanda ya sani, banda iya mutanen da yake iya gani.
Gurin mai magani na farko da suka fara zuwa da su Habu, wata yarinya ta gifta shi, ya ji wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, ya din ga jin tamkar ya koma ya bi inda ya ji sanyin nan.
Haka da suka sake haɗuwa a gidan Sarkin baka, bai ga fuskarta ba, amma sanyin nan ya ƙara neman ya zauta shi.
Sai dai ya sha mamaki, da ganin wani zanƙalelen mutum yana bin ta a baya, sai dai baya iya ganin iyakar tsawon mutumin.
Gaba ɗaya ya lura, gane-gane da yake yi,  shikaɗai yake ganin abun sa. Lokaci lokaci ya kan yi mafarki da gidan tarihi, sai dai ya kasa tuna ina ne gurin.
Duk lokacin da ya yi mafarkin yarinyar nan, ya kan tashi da matsanancin farin ciki mara misaltuwa, ya kan ji dama su dauwwama a cikin baccin nasa ba sai ya farka ba.
Tun da suka fara aiki a gidan Alhaji Zailani, duk lokacin da zai gan shi, yana ganin jini yana bin sa, da wasu ƙanan yara, da wasu mutane su na kuka, amma Alhaji Zailani ba ya ganinsu, sauran mutane ma ba sa ganinsu, sai shikaɗai. Hakan ya jefa shi a cikin damuwa, da jin cewa shi wata halittar ne daban, da sauran mutane.
Sai dai babu zato babu tsammani, ya yi ido huɗu da ita, da wani yammaci ta fito daga cikin gidan, wannan dogon mutumin yana biye da ita, sai dai ya ga wannan tsohon ne ya dawo matashi, bai bayyana a suffarsa ta tsohon da ya saba fitowa ba.
Sanyin da ya ji ya ratsa shi ya sanya ya rikice, ya ƙudurce a ransa akwai wani abu da bai sani ba, ko yakamata ya sani, kuma wataƙila wannan da suke tare zai iya gaya masa waye shi, kuma daga ina yake!.

Ayshercool.
08081012143
LITTAFIN KUƊI NE, VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC
92
Kafin ya yinƙura ya fito daga ɗakin nasu, wanda yake gani ɗin ya ziro sanda ya hankaɗa shi ya faɗi sumamme.
Ya fuskanci mutane kowa yana da ahali, uwa, uba, ɗan uwa, mata 'ya'ya ya san duk abu ne mai muhimmanci game da rayuwar mutum, amma shi ya kasa tuna komai a kan rayuwarsa.
Su Habu da yake gani a tare da shi, ya san su na yi masa ƙoƙari amma ba ya jin su sosai da sosai a ransa, yadda za su iya zama wani ɓangare na rayuwarsa. Wasu lokutan idan maganar ba ta ɗauke ba, ya kan yi musu magana cikin iko da isa, ba tare da jin nauyin hakan ba, shi Mahmoudu sam baya damuwa da hakan, amma su Sule wasu lokutan abin yana sosa musu rai.
Aka ci gaba da tura wa Habu kuɗaɗe cikin asusunsa.
Yana ta tunanin yadda zai sanar da can gida Agadez cewa, ga fa halin da ake ciki, amma aka din ga tura masa saƙonni a kan muddin ya kuskura suka koma Agadez, Hammad zai iya rasa rayuwarsa. Ya tura wa Nene saƙon halin da ake ciki. Ya sanar mata ko an zo an tambayi yana ina ta ce ba ta sani ba kawai. Ya kashe wayarsa ya cire layin ya ajiye, ya samu na Nigeria ya saya ya saka.
Sai bayan kwanaki biyu, aka farga ba a samun lambar Hammad, wayarsa na ajiye a ɗakinsa.
Sultan ya ce wa Asal, kar ta kuskura ta gaya wa wani cewar Hammad ya ɓace ba a san inda yake ba, ana nan ana bincike a kan nemansa.
Hammad kuwa sai ya kintaci lokacin da Nana za ta zo gidan Alhaji Zailani ko kuma ta tafi, sai ya fito harabar gidan ya zauna, ko kuma ya buɗe taga, ya san dole zai ji wannan sanyin. Sai dai duk lokacin da zai ganta, tare da wannan dogon mutumin ne da babu wanda yake ganinsa, sai dai ya fuskanci duk lokacin zai gan shi tare da Nana, ba ya cutar da shi, ko ya yi masa feshin wuta, amma duk lokacin da ya bayyanar masa a suffar tsoho sai ya cutar da shi.
Duk lokacin da zai ga Nana yanayin fuskarta na nuna damuwa, dan haka sai ya din ga jin kamar ya je ya tambaye ta mene ne yake damunta fuskarta babu walwala. Wasu lokutan kuma Ƙaisar yake kallo, ita kuma sai ta din ga ganin tamkar yana addabarta da kallo.
Ranar da Alhaji Zailani kuwa ya biyo ta, haka kurum ya din ga jin jikinsa babu daɗi, tamkar ya bita cikin gidan. Ko da ya ga Nana ta fito a sukwane kuwa, ya san akwai matsala, sai dai Giyaz ya bayyana a lokacin ya shaƙe Alhaji Zailani.
A hankali ya fara lura da tsuntsayen da suke bayyana idan ya murza zoben hannunsa, ko kuma ya matsa jakar fatar da yake ratayawa a wuyansa.
Ya kan tambayi tsuntsayen, ko sun san waye shi? Suwaye iyayensa? Da kuma 'yan uwansa? Tun da su na magana wasu lokutan. Ba sa ce masa komai sai dai su zana masa taswirar gidan tarihin Agadez a ƙasa. Idan ya kalla ya san gurin amma ya manta a ina ne.
Sannu a hankali ya gane, akwai bambanci a tsakanin Giyaz da Ƙaisar ranar da faɗa ya haɗa su, Giyaz ya yi jifa da Ƙaisar sai da ya sha mamaki, ganin tsananin kammanin da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar.
A ranar kuma ya fuskanci Nana ma tana gane-ganen abubuwan da ba kowa ne yake gani ba, hakan ya sanya ya ji a jikinsa ita daidai take da rayuwarsa, ita ce suke iri ɗaya. Amma ta yaya? Tun da yana jin Habu da Sule su na zancen Nigeria da Niger, shi da su irin su ɗaya, ga yarukan da yake iya yi, wanda alamu suka nuna inda suke ba duka yaren da suke yi mutanen gurin suke ji ba.
Ɓangaren Ƙaisar ma, tun da ya ga Giyaz a tare da Sayyid ya rikice, domin bai taɓa tsammanin Giyaz zai dawo ba.
Wataran bayan shafe kwanki biyar Sayyid yana fama da wannan zafin jikin da yake rikita shi. Ga babu magana abinci ma baya iya ci. Ya wayi gari ya ɗan samu sauƙi. Har ya ci abinci ya shiga ya yi wanka da la'asar. Kawai ya ji wannan sanyin yana kusanto shi.
Babu tsammani ya ji muryarta, ta yi sallama sai dai ya yi shiru yana tunanin ko tsabar saka ta a ransa ne ya sanya ya ji muryarta. Yana tsaye cak da matajin hannunsa, ya ji muryar yaro a ɗakin bai ga yaro a ɗakin ba, kawai ya ga ta faɗo ɗakin.
Su na haɗa ido ya ga ta yanke jiki ta faɗi. Ya ga Ƙaisar ya bayyana ya tsaya a kanta yana huci, shi dai ya tsaya yana kallonsa dan bai san abin da ya yi mata ba. Ya gama ya sanya kayansa Nana ta kwance, amma sanyin da yake tattare da ita na saukar masa da wata irin nutsuwa da daidaita zafin jikinsa.
Tun daga lokacin aka fara dambarwar nan, har ta kai ga ɗaura masa aure da Nana, ya din ga jin amincewa da auren, shi ne hukunci mafi daɗi da zai yankewa wannan rayuwar tasa da yake yi mara kan gado. Ba ya jin ko ɗar sanya Habu ya yi masa duk wani abu da yake buƙata.
Bayan aurensa da Nana a  jikinsa yake jin, samun nutsuwa a tattare da wannan duniyar da kuma kwanciyar hankali, idan ya matsa ya tuna wani abu da ya shafe shi game da ainihin waye shi, sai ya ji damuwa da baƙin ciki ya mamaye shi.
Habu kuma bai taɓa gangancin gaya masa waye shi ba, kawai ya ƙyale shi a kan duk lokacin da ya tuna wani abin ya sanar da shi.
Idan ya kwanta bacci baya mafarkin kowa, sai wannan dai gidan tarihin da yake gani, sai kuma ya din ga ganin wasu abubuwan da suka faru a ƙarnukan baya a wannan gidan sarautar, har ma da mutanen da suka yi rayuwa a gidan. Wasu lokutan har a zahiri yana ganinsa a gidan tarihin amma bai taɓa tuna a ina ya san gidan ba, sai dai bai manta abin da ya faru na ƙarshe a gidan ba, na firfitowar wannan halittun daga ɗakunan tarihin. Sai dai yana yawan ganin gidan, sakamakon aljanun da suke tattare da zobensa da kuma jakar fatarsa, ainihinsu mazauna gidan ne, kuma su ma su kan yi kewar gidan, tun da duk inda yake ya murza zoben sai sun zo. Lokacin da aka yi aurensu, aka kai Nana wannan aljanun na zobensa ne suka din ga rangaɗa guɗa.
A duk lokacin da yake son ya yi wasa da hankalin Nana, sai ya murza zoben hannunsa, idan ya danne jijiyar da ke wajen ƙeyarta, sai ta yi bacci. Haka zalika yadda yake ganin gidan tarihin nan, haka ita ma take ganinsa.
Da wannan aljanun yake amfani ya burkita mata lissafi, ya yi abu da ita a zahiri amma ta din ga ganin kamar a mafarki ne. Haka zalika Giyaz da yake taka rawa gurin addaba musu, tare da cutar da su, da abubuwa na ban tsoro. Ƙarfin ibadar Nana ne ya sanya suke samun sassauci a wasu abubuwan. Nana ba ta taɓa sanin amfanin zoben nan na hannunsa ba. Ya ɗauki zoben ya ba wa Nana kyautarsa, saboda abin da yake ji a zuciyarsa game da ita. Saboda a jikinsa yake jin zoben na da muhimmancin gaske, dan haka ya ɗauka ya bata.
Ƙaisar ya yi ta gargaɗin Nana a kan Sayyid, saboda yana jiye mata tsoron Giyaz, da kuma kar Aljanun da yake ta'amalli da su, su cutar da ita.
Duk da yadda Ƙaisar yake jin haushin Sayyid, da yadda Nana ta saki jiki da shi suke rayuwa, amma ya taka muhimmiyar rawa gurin ƙara jirkita hankalin Nana, da sauƙaƙawa Sayyid ɗin wasu abubuwan. A sakamakon yarjejeniya da suka yi da hadiman jikin zoben Sayyid, a kan za su ba shi wasu labarurruka da suka faru a wasu zamani da suka shuɗe, tun kafin a haife shi a cikin Duniya, bisa yarjejeniyar idan suka cutar da Nana ba za su taɓa zama lafiya ba.
Duk da tsamin alaƙar da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar, amma yana jin daɗin ganin ɗan nasa, bayan shafe shekaru masu yawa bai gan shi ba. Ya na tsananta cutar da Nana da Sayyid, saboda ya muzgunawa Ƙaisar.
Ko lokacin da ya bi Nana, har ya duba Baba, a zahiri ya ga ƙullin da Ƙaisar ya yi a ƙafar Baban, kuma da aljanun jikin zobensa, ya warware ƙullin.
Rayuwarsa da Nana yana saka shi jin wata nutsuwa a tattare da shi, ga alaƙar Giyaz da ta Ƙaisar da ta shafi rayuwarsa da Nana. Sau ɗaya ya yi mafarkin Sultan, ya gan shi cikin damuwa da tashin hankali, ya farka a rikice da sunansa a bakinsa amma bai iya tuna ko waye shi ba.
Can Agadez kuwa, bayan ɓatan Hammad, aka ankara da ɓacewar Mahmoudu, hakan ya sanya Sultan cewa duk inda Hammad yake yana tare da Mahmoudu. Sultan ba ya iya cin abinci, ba ya isasshen bacci saboda tashin hankalin rashin sanin inda Hammad yake. Ga shi ɓoyewa suke ta yi, duk da yadda Tafawa da muƙarrabansa ke ta ƙoƙarin bin diddigin gano abin da Sultan yake ɓoyewa.
Lambar Mahmoudu da ta ƙi shiga, sai aka yi ta tracking lambar Mahmoudu, aka gano last inda ya yi amfani da ita a Nigeria ne. Aka din ga bin diddigi har gidan Alhaji Zailani, aka tafi da motoci gaba ɗaya aka kwaso Buzayen layin kaf. Sai da aka zo Agadez, sannan aka tantance su bayan da aka fahimci su ba su san komai ba, hasali ma wanda ake maganar a kansa ba su san waye shi ba. Aka ɗauke Mahmoudu daga cikinsu, aka din ga tuhumar sa, ina Hammad yake, amma ya ƙi magana saboda yana jin tsoron gargaɗin da aka din ga yi masa, a kan muddin Hammad ya dawo Agadez mutuwa zai yi.
Mahmoudu ya sha azaba kala-kala, tamkar ba zai yi rai ba, sai da ya ji azaba sannan ya gaya musu cewar Hammad yana Nigeria. Aka saka shi a gaba zuwa Nigeria, aka taho da Hammad. Sai dai tunda aka taho da shi, sai ƙwaƙwalwar ta sak burkicewa, tunaninsa ya rikice.
Bai gama tantance waye shi ba, hankalinsa ya dawo ba, sai da aka fitar da shi Faransa. Dama ƙwaƙwalwar a hargitse take, baya tantance komai, sai dai sannu a hankali tunaninsa na rayuwar da ya yi a Nigeria, ya shafe gaba ɗaya.
Sai ainihin tunaninsa na waye shi ya dawo masa. Ganin ya dawo hayyacinsa ya daina iface-ifacen da yake yi, ya nuna ya gane Sultan da Matawalle, suka yi farin ciki sosai, suka tambaye shi ko ya tuna abin da ya faru da yaje Nigeria, sai ya rikice yake tambayar me ya kai shi Nigeria. Daga nan kawai sai suka ɓoye masa, suka ce jinya kawai ya yi mai tsawo a faransa. Likitoci suka din ga ba shi kulawa a kan matsalar zuciya da yake fama.
Can a Agadez kuma, aka ci gaba da azabtar da Mahmoud a kan lallai sai ya faɗi dalilin da ya sanya, ya sace Hammad ya tafi da shi Nigeria.
Ga Tafawa ya matsa a kan lallai sai an faɗi inda Hammad yake, tun da an doshi shekara biyu, babu wanda ya gan shi, ko kuma a ba su dama su je su duba shi, su gan shi ido da ido su tabattar yana raye babu wani abu da ya same shi.
Sai dai Hammad ya kasa yarda da cewa, tsawon wannan lokacin, jinya yake yi. Tiryan-tiryan abin da ya faru na ƙarshe daga gidansa, zuwa gidan tarihi daga nan kuma sai ya rikice ya kasa tuna komai.
Ya ce wa Sultan lallai a kawo masa Mahmoudu, Matawalle ya ce "Ko ka tuna wani abu ne? Me Mahmoudun zai yi maka?"

Hammad ya ce "Babu komai, ni ba na jin daɗin zama nikaɗai ne, na saba duk inda nake mu na tare, ni dai a kawo mini shi"

Matawalle ya ce "Ka yi haƙuri, Likitoci sun ce ba a buƙatar kowa ya zo inda ka ke ne"

Ya yi shiru yana tunanin, ina Asal da ko sau ɗaya ba ta zo ba ita ma. Sai dai a jikinsa ya din ga jin kewar wani abu mai muhimmanci a tare da shi, kamar yana jin matsananciyar ƙishirwa.

Sultan kuwa ya sanar da Asal batun ganin Hammad, amma ya ce mata rashin lafiya ce ta kama shi a Niemey, aka kai shi wani Asibiti a can, daga baya a ka kai shi faransa. Duk da ta yi mamakin yadda za a ce rashin lafiya ta kama mutum, a kai shi Asibiti amma ba a nemi ahalinsa an sanar da su ba tsawon shekaru.
Sai dai hakan ma sai da ta gaya wa Tafawa. Ya ruɗe ya rikice dan ya so a ce wani mummunan abin ne ya samu Hammad.
Tun da Asal ta ji labarin Hammad zai iya dawowa a kowane lokaci, take shirin karɓar sa, dan ba ƙaramin kewarsa ta yi ba. Dan ta shiga damuwa da tashin hankalin da sai da suka samun matsala da Tafawa bayan ɓacewar Hammad.
Tun da Sultan ya ce a kowane lokaci zai iya dawowa, ta sanya aka yi gyaran gidan sosai. Sannan ta fara lissafin canza kuyangin da za su din ga yi masa hidima. Ga Tafawa ya yi mata alwashin idan ba za ta ci gaba da ba shi haɗin kai ba, zai nemi wani ya yi masa, ko da kuwa ta kama a salwantar da ran Hammad ɗin ne baki ɗaya.
Sai dai duk da tunaninsa na Agadez ya dawo, bai fasa fama da wannan matsanancin zafin jikin ba, da yake jin tamkar ana ƙona shi ba. Sai dai ya rage tashi a kai a kai.
Haɗuwar Asal da Nana, ya zame wa Asal tamkar tsintar dami a kala, ta ga idan ta kawo Nana gidan sauratar Agdez, kanta a tukunya yake game da sha'anin sarauta, ga girki ta iya, saboda Hammad na son daddaɗan Abinci, ga kuma Nana baƙa ce 'yar Nigeria, babu yadda za a yi ta ɗauki hankalin Hammad, saboda baƙar mace ta haramta a gare su, bisa ga Al'adar Agadez. Sai dai abin da Asal ba ta sani ba shi ne; a rashin sani kaza ta kwana a kan dami.

AREWABOOKS

Tun da Hammad ya sauka a filin tashi da sauukar jirage, gabansaa yake faɗuwa, ya kuma rasa dalilin hakan. Jin sa yake yi tamkar yana daf da maganin ƙishirwar da ta addabe shi.
Bayan Nana ta yi amfani da ƙarfi, gurin tursasa wa Nana zuwa Agadez, ta sanya Nana cikin jerin waɗanda za su yi girkin karɓar Imam Hammad.
Gabba ɗaya gida ya ɗauka Hammad zai dawo, bayan shafe dogon lokaci yana jinya. Su kansu wasu daga cikin Imam Imam ɗin, ba haka su ka so ba duk da abin jita-jita ake ta yi, Sultan bai tabattar da hakan ba, kuma a daren za a yi babban taro tare da 'yan majalisar Sarki, da kuma su Imam na shekara da ake gabatarwa.
Sai dai babu tsammani, su ka ga Hammad ya bayyana a gurin. Tun da ya shiga gurin, ya ji wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, da kowace irin AC aka kunna, sanyin baya wadatar da shi har cikin ƙashinsa ya ji ya gamsar da shi.
Ya ji wani irin jiri na neman ya ɗebe shi, amm ya daidaita nutsuwarsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa ya rabe ya je ya zauna.
Bai ɗago kansa ba, ya ji Matawalle na tambayar me ya kawo wannan nan gurin. Aka sanar masa tana cikin masu girki ne.
Bai dai ɗago ba sai murmushi da yake yi, saboda barka da zuwa da ake ta yi masa.
Sai dai ƙirjinsa ya tsananta bugawa, da aka ce ta zo ta ɗanɗana Abincin, ta nufo inda suke. Ya kasa jurewa ya ɗaga kansa, sai ya ji kamar sanyin da yake ji yana ƙaruwa. Wani abu ya ji mara daɗi a ƙirjinsa ganin yadda ta ɗaura rigar girki a kan kayanta, ana ganin shape ɗin kyakykyawar surar da Allah ya yi mata ta bayyana. Kalar fatarta ya ɗauki hanklinsa, tsohon muradinsa na son baƙar mace ya motsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login