Showing 87001 words to 90000 words out of 124686 words
yi?"
"Na san sai Sultan ya gaya maka, amma dan Allah ka yafe mata"
Hammad ya ce "Ki na tunanin ban san komai ba ne? Lokaci ya yi da yakamata na huta"
Nana ta ce "Wataƙila akwai abin da baka sani ba, dan Allah ko ka sani ka yi haƙuri ka yafe mata"
Ya yi shiru ya sake kwanciya a jikin Nana, ta ƙara ƙanƙame shi, cikin matsanancin tausayawa.
*****
Sultan na kashingiɗe, yana sauraren Tafawa, da sauran 'yan majalissa, sun kafe kai da fata a kan lallai a san matakin da za a ɗauka a kan Hammad, saboda yadda ya karya musu Al'adar masarauta.
Sultan ya ɗago ya numfasa cikin ƙasaita, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Amm kamar yadda kowa ya sani, Agadez ta gaji Al'adu da ƙa'idoji daban-daban, wanda wasu an samar da su ne, tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci, ina ga lokaci ya yi da yakamata mu kama addininmu, mu yi watsi da duk al'adun da muke ganin su na kawo mana koma baya.
Saboda haka a matsayina na Sultan mai ci na wannan lokaci, na soke wannan Al'ada a ƙasar Agadez. Baƙaƙen buzaye za su samu 'yanci, farin buzu ko buzuwa na da cikakken 'yancin auren duk wata ƙabila ko kalar fatar da yake son aure. Matar da Imam Hammad ya aura, bincikenmu ya tabattar da halattaccen aure suka yi, kuma mun karɓe ta. Hakazalika za mu bayyanawa duniya ɗan da ya haifa tare da matarsa ta Nigeria.
97
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
Gaba ɗaya 'yan majalisar suka waiwayo suna kallon Sultan.
Tafawa ya ce "Jalaludeen wannan wace irin maganar banza ce, dan me zamu bar gadon al'adun da muka gada daga iyaye da kakanninmu saboda son zuciyarka da ƙoƙarin bawa ɗanka kariya? Babu wanda zai lalata mana dokokinmu da al'adunmu. Dole a hukunta Hammad dai-dai da abin da ya aikata"
"Mutanen farko ma, gadon iyaye da kakanni ne ya halakar da su. Daga lokacin da muka gaji al'adun, zuwa yanzu me al'adar ta haifar mana bayan tarin ɓarna kashi-kashi? Kuma ina bayar da wannan umarni ne a matsayina na Sultan, shugaba a Agadez ba magana nake yi ba a matsayin ɗan uwanku ko abokinku ba, duk wanda ya ɗaga murya ko kawo abin da ba shikenan ba, zan hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata"
Matawalle ya ce "Amma Allah ya baka yawan rai, yanke wannan hukuncin haka kai tsaye, baka tunanin zai sanya wa talakawanka wasi-wasi da kawo tashin tashina a tsakanin masarauta da kuma jama'ar gari"
Sultan ya numfasa ya ce "Lokuta da dama, gyara baya buƙatar lallai sai ka yi wa wani daidai, ko kuma sai kowa ya soka, ya yarda da kai mai gaskiya ne ko me kirki ne.
Haka zalika zan sauke wasu daga cikin Imam Imam na ƙasar nan, zan yi wa dokokin Agadez garambawul da gudunmuwar dokokin ƙasar Niger, domin kowane ɗan Agadez ya samu cikakken 'yanci kamar sauran ɗan ƙasa ba tare da al'ada ta tauye wasu daga cikin 'yancin da suke da shi ba a ƙasar nan.
Sai dai na san da yawa ba zai yi muku daɗi ba, za a ga kamar na yi rashin adalci saboda Hammad ɗana ne, amma kafin ku ce haka, bari mu yi komai a buɗe tare da ku". Ya kalli wani dogarinsa, ya ce "Ina da baƙo a mararrabar fada da hanyar cikin gida, ka ce ya iso"
Duk suka yi tsuru-tsuru su na jira.
Ba a jima ba, dogarin ya dawo tare da Sarkin baka sai kuma wannan mai gadi a ɗaɗɗaure da igiya tamau kamar ɓarawo.
Wanda ba su san me ake ciki ba, suka yi ƙuri su na jiran jin ba'asi, wanda abin ya shafa kuma cikinsu ya ɗuri ruwa.
Sarkin baka ya risuna ya yi gaisuwa a fada, cikin shigarsa ta hargi ya shigo hakan ya ƙara sanyawa duk aka zuba masa ido.
Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Yi musu bayani"
Sarkin baka ya kalle shi ya ce "Duk da na san, sun sanka amma ka yi musu bayanin waye kai"
Ya sunkuyar da kai ya ce "Mai gadin gidan tarihin Agadez"
Sarkin baka ya ce "Kuma me?"
"Boka da nake yi wa wasu daga cikin manyan Agadez aiki"
"Mene ne dalilinka na yin hakan?"
Ya numfasa ya saci kallon Sultan ya ce "Na haka ne, saboda huce takaicin yadda ake bautar da mu tun daga kan kakana, wannan dalilin ya sanya lokacin boka Riyan, na koyi harkar bokanci a gurinsa"
Sultan ya ce "Ina fatan kun ga ɗaya daga cikin illolin wannan al'adun da muke yi, marasa tsuhe balle makama? Mu na jinka ci gaba"
Sarkin baka ya ce "Ba ka ji ka ci gaba mana"
"An bani wasu ayyuka, duk da ba kowa ya san ina bokanci ba, sai dai akwai wani babba a masarautar nan da shi ya ƙarfafe ni na koyi harkar bokanci.
Ni aka saka na yi wa Imam Hammad Asiri, da aljanin da ya sanya ya bar ƙasar nan, ya manta komai da ya shafe shi, ciki hadda tuna waye shi.
Sannan aka bani aikin yi masa asiri da wani tsohon aljani a cikin gidan tarihin, da yake sanya masa wannan zafin jikin da yake gigita shi".
Sarkin baka ya sake cewa "Yaya ka ke yi?"
"Da fari na haƙa rami a cikin tsohuwar kurkuku, ana kawo mini itace cikin dare, ina tona tsofaffin kabarurruka na cikin gidan, na ɗauki ƙwarangwal ɗin, na saka shi a cikin wuta, da hatimai daban-daban da sunan Imam Hammad, duk lokacin da na babbaka wannan wutar yadda ƙwarangwal ɗin nan yake ƙonewa haka yake jin zafin a jikinsa. Idan ƙwarangwal ɗin ya murmushe saboda zafin wuta, sai na kuma tono wani. Daga baya kuma aka koma kawo mini sababbin gawarwaki na koma yin aikin da su, idan na saka musu wutar nan, haka yake jin wannan zafin a jikinsa"
Gurin ya yi tsit, aka rasa wanda zai yi magana. Jikin Matawalle yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma suwaye haka?"
Sultan ya ce "Ba sai an faɗe su ba, amma sun san kansu, kuma duk wanda yake da ja a kan maganar, yana iya zuwa gidan tarihin da kansa ya tabattar. Dan haka a yau na kawo ƙarshen zaman yau, dan haka zan zo da sauran bayani da abubuwan da zamu caccanza".
Nan aka ci gaba da salallami, aka rasa mai sake cewa komai.
Nana tana kwance tare da Hammad, kamar zai shige cikinta, sai shafa gashin sa take yi sannu a hankali.
Ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru.
Yadda bokan nan ya din ga yi musu bayanin, Imam Omar da mahaifinsa Sardauna, suke zuwa da yadda suka yi masa asirin nan na zafin jiki. Kuma da sanin Tafawa, kowa fafutukarsa ɗansa ya samu mulki. Haka zalika Asal ta yi soyayya da Omar, ita take ajiye wa Hammad takardun nan. Ko da auren Hammad sun yi soyayya tare, kafin daga bisani da ta ga babu amfani soyayyar tasu, ta fara son Hammad ta daina biye masa.
Sai dai ya ci gaba da yi mata barazanar sai ya tona mata asiri, irin hirarrakin da suke yi. Sai dai babu wani abu na saɓon Allah da ya taɓa shiga tsakaninsu, sai dai duk wasu zantuttuka na banza har da wanda bai kamata ba, suna yi. Babu abin da bai sani ba a game da aurenta, da abubuwan da yake faruwa tsakaninta da Hammad ba.
Hatta sirrin shimfiɗar aurensu, babu abin da Omar bai sani ba. Shi ya din ga ziga ta, tun daga lokacin da aka ce za a yi aurenta da Hammad, shi ya din ga ziga ta har bayan auren.
Ya ci gaba da zuwa gurin bokan nan, yana karɓar wannan takardar, yana bawa Asal, wanda da ya yi tozali da takardar yake sake ruɗewa, jikinsa ya rikice ya yi ta jin ihun da alajanin nan yake yi a jikin ƙwarangwal ɗin nan, duk ya fita hayyacinsa.
Babu yadda Omar bai yi da Bokan nan, ya yi masa abin da Asal za ta yarda shi, amma ya ce ba zai yi wannan cin amanar ba saboda Hammad yana yi masa alheri ta wasu ɓangarorin. Gaba ɗaya bokan ya gaya musu labarin, da abin da yake tsakanin Omar da Asal a baya.
Babban abin da ya ɗaga wa Nana hankali, bai wuce yadda bokan ya ce, ko za su kashe shi, zai iya lalata sihirin da ya yi da aljanin jikin ƙwarangwal ɗin da yake amfani da shi, amma ba zai iya raba Hammad da Giyaz ba, saboda Giyaz baya saɓa alƙawari, kuma ga Nana tana tare da Hammad, yana ganin ɗansa a jikinta, idan ba kashe Giyaz za a yi har lahira ba, ba zai rabu da shi ba.
Da ta zo nan a tunaninta, ta lumshe idanunta hawaye na zirarowa a hankali.
Hammad ya yinƙura ya tashi zaune, ta maze ta goge hawayenta. Ya ƙare mata kallo ya yi wani irin tattausan murmushi, ya shafa gashin kansa ya ce "Ba ƙaramin kyau ki ka yi mini ba ma vie, ina kewa, ɗan yi mini waƙar mana abar ƙauna" Yayi maganar yana sumbatar hannunta, tare da matsawa kusa da ita.
Ta ɗan matsa kaɗan ta ce "Ana ta kai ka na ta kaya"
"To ni kayan ne suka fi damuna, fiye da kayan ai. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zan yi miki, kuma ina roƙon Allah kar ya kama ki da laifin guduna da ki ke yi, saboda kin fi ni gaskiya ta kowace fuska.
Amma har abada ni mai ƙaunar ki ne, kuma ba zan taɓa yarda a raba ni da rayuwata ba in sha Allah" Ya yi maganar yana sake rungume ta, wani abu mai sanya nutsuwa na fizagarsa game da ita.
"Ka daina yi mini wannan kallon mana" Ta yi maganar tana hararasa cikin wasa.
"Idan ban kalle ki ba wa zam kalla, kina nan a yadda ki ke ma vie, kamar baki haifi Muhsin ba"
Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Da na canza daina sona za ka yi kenan?"
Yayi murmushi ya ce "Haryanzu ba ki san waye Hammad ba, ke ɗin nake so ne Asmy, babu abin da zai canza a tattare da ke, na ji na daina sonki ko kaɗan. Ina son Husna"
"Sake faɗa" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.
"Sai kin yi mini waƙa tukuna" Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce "Sai ka biya ni tukuna."
Ya ɗan yi shiru ya ce "Ina tuna mutane daban-daban da muka rayu da su a Nigeria, ko ina yayarki ɗin nan, da ta yi ta ɗawainiya da mu? Da 'yan gidanku, da mutumin nan da na tsana, wanda na yi wa gadi da farko. Sai kuma mutanen gidan da muka zauna, da muka yi aure"
Nana ta ce "Gidansu budurwarka ko?"
Ya ce "Eh nan"
"To tashi daga jikina"
Hammad ya ce "Ba zan tashi ba, ai ni ban ce budurwata ba, ke ki ka fara."
Ta yi murmushi ta ce "Babu abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah, ni dai ina ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke a kanmu"
Ya ce "Alkhairi in sha Allah, ni nama manta, yana nemanmu anjima, ban san me zai ce mana ba. Amma ina tsammanin alkhairi daga bakinsa"
"Allah yasa ina fatan hakan nima, amma dan Allah ka sanya baki, na ga ya yi fushi sosai da sosai da ɗan uwanka, ko zaka saka baki?"
"Ba ruwana" Ya bata amsa kai tsaye.
Nana ta ce "Kar ka ce haka" Ya miƙe tsaye gaba ɗaya, sannan ya ce mata "Zan je na dawo, ki yi mana addu'a Allah ya sanya hukuncin da Sultan zai yanke, ya yi mana daɗi"
Ya ƙarasa maganar yana sumbatar goshinta.
Kamar zata tashi sama, haka Gimbiya Bilkisu ta faɗo turakar Sultan hankalinta a tashe, ko haɗiyar yawu ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi.
A nutse ya juyo ya kalle ta, bayan ya gama warware rawanin kansa.
Sai kuma ta tsaya ta kasa magana.
Can kuma ta ce "Sultan, wai da gaske zaka sauke wasu daga cikin Imam? Meyasa? Kuma ina fatan babu Zahradeen a ciki?"
"Idan da shi me za ki yi?"
"Amma dai ka san bai kamata abin da ka yi, kuma a kan me zaka sauke Zahradeen yana ɗan cikinka? A wancan karon ka naɗa ƙaninsa a matsayin shugabansa, sannan ka zo ka sauke shi ai muzantawar tayi yawa. Zai ma zama abin surutu a Agadez"
Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga Sultan, a kan tona muku asiri da ke da shi da ɗan uwanki Tafawa" Ya ƙarasa maganar cikin hasala. Sak ta yi tana ƙwalalo ido waje tana kallonsa.
"Kar ki kalle ni kamar ba ki san abin da ki ka aikata ba, Bilkisu kin cutar da ni, kuma kin cutar da kanki. Kin yi yinƙurin kashe mini mata sau biyu, saboda gudun tonuwar asirinku, yayanki ya yi uwa ya yi makarɓiya ya sanya muka rufe Mamman, waya sani ko a ƙarshe ma ke dai ki ka yi sanadin rayuwar tata? Sannan tilon ɗan da ta bari a duniya ki ka sako a gaba da jaraba, ke kina yi yayanki yana yi, gaba ɗaya Hammad bai ji daɗin rayuwarsa ba, saboda azaba da masifar sihiri da makircinki. Kuma idan ki ka kuskura ki ka buɗe baki ki ka musa mini, sai na tona miki asiri sannan ki bar mini gida. Allah ne ya tona muku asiri a silar matarsa ta Nigeria da ya aura, kuma bokan naku yana hannunmu, ya tabattar da abin da ya aikata.
Abu ɗaya zan duba na rabu da ke, 'ya'yan da na haifa tare da ke. Amma daga yau na haramtawa kaina ke har abada a matsayin matata, za ki yi zaman 'ya'yanki ne kawai. Kuma kar Zahradeen ya ƙara ayyana ni a matsayin mahaifinsa, kuma kar ya sake zuwa inda nake. Da ke da duk wanda ku ka aikata hakan, na bar ku da Allah. Faɗar abin da ku ka aikata tamkar tona wa zuriyarmu asiri ne"
A rikice ta ce "Dan Allah Jalaludeen ka tsaya ka ji...
"Ba zan ji komai ba, fice ki bani guri kafin na canza shawara" Yayi maganar yana yi mata wata irin gigitacciyar tsawa, babu shiri ta fice tana haɗa hanya.
Tafawa ne ya shigo falon hankali a tashe, ya tarar da Asal tare da Asadullah.
A fusace ya ce "Gidan uban wa ku ka tafi tun safe?"
Da mamaki Asad ya ce "Kai ka kira ni a waya ai, ka ce na zo na kai Asal Asibiti, tun lokacin muna Asibiti, ba ta da lafiya sosai.
Ya sharce gumin goshinsa ya ce "To, dara ta ci gida yau, Asirinmu ya tonu a fada" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suka kalle shi.
"Eh, yau da bokan da yake yi mana aiki, na gidan tarihi aka zo fada, ya tona komai sunayenmu ne kawai bai kama ba. Kuma na san ya gaya wa Sultan komai, kuma duk a dalilin haukanki da dabbancinki Asal, haka kurum ki ka je ki ka jajubo masifa ki ka kawo ta har cikin gidan sarauta. Binciken da na yi, wannan yarinyar da ki ka kawo a matsayin kuku, ita ce ɗin dai ta yi sanadin tona asirinmu. Dan haka sai ku shirya baki ɗayanku, dan ban san wane irin hukunci za a ɗauka a kanmu ba.
Asal ta ɗora hannu a ka ta ce "Wayyo Allah na shiga uku, Abbu sai da na ce muku mu daina wannan abin, amma kai ka saka ni, Imam Asad ya saka ni, Imam Omar ma ya saka ni da Sardauna, ku ka saka ni a tsakiya wallahi ina son Hammad, idan na rabu da shi ba zan taɓa samun miji kamarsa ba, wallahi ina sonsa"
A fusace Asadullah ya ce "Ke rufe wa mutane baki, ke ta wani shashasha ma ki ke yi?"
"Kai ne shashasha, dan duk saboda gobenka aka lalata tawa, an cuce ni, komai zan yi yanzu Hammad ba zai taɓa yafe mini ba, balle ya saurare ni"
Tafawa ya dubi Asal ya ce "Asal kina da hankali kuwa? Kin san abin da ki ke faɗa kuwa?"
"Abbu na san abin da nake faɗa, shikenan bani da makoma, matarsa ta shiga kundin tarihin baƙar mace ta farko da ta auri Imam a Agadez, ni kuma zan shiga kundin tarihin matar da ta sanya hannun gurin tarwatsa rayuwar mijinta" Miƙewa tayi Tafawa yana kiranta, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, ta fice daga ɗakin.
****
Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falonsa, ga mamaki ya ga Fadila tare da uwargidansa Hajiya Suwaiba, suna zaune abin da bai taɓa gani ba.
Suna ganin shi suka zuba masa ido, Hajiya Suwaiba ta ce "Ka ce sai gobe in Allah ya kaimi zaka dawo?"
Ya ce "Eh, fasawa na yi na taho yau"
Fadila ta ce "Amma Daddy lafiya dai ko, Rauda kawo masa ruwan sanyi"
Suwaiba ta ce "Wai dan Allah Baban Rauda Meyafaru a Lagos ɗin ne?"
Ya ce "Sai kun gaya mini, me ku ke tattaunawa ne, ganinku tare ya sanya ni farinciki"
Hajiya Suwaiba ta ce "Abokin nan naka ne ya zo gidan nan, wanda ya sai gidan nan, shi ne muke tattaunawa mu tattara ɗan abin da ya yi saura, a nemo gida mu tashi, tun da mun ga alamar mutumin nan zai iya ci mana mutunci daga mu har kai."
Ya yi murmushi tare da jinjina kai. Cikin damuwa Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka gaya mana, meyafaru muna fatan dai ba wani abin ne ya kuma kunno kai ba"
Ya saki murmushi ya ce "Da baku ganni a haka ba, Alhamdillah an canza sabon controller na hukumar Coustom na ƙasa. An sakar mini kwantena Arba'i da bakwai a cikin kwantenonina, da na mutane da na haɗa na yo order kaya" A rikice suka buɗe ido, suna jin abin kamar a mafarki. Hajiya Suwaiba baki na rawa ta ce "Daddy, kenan suna sane suka kama ka kayan naka, ba wani laifin ka yi ba, yanzu kana nufin an saki kayan?"
Ya jinjina kai ya ce "An saki wasu daga cikin kayan, Allah ya karɓi addu'a" Gaba ɗaya suka rungume shi tare da yaransa, yana kuka su na kuka, babu abin da bakunansu ke furtawa sai tsantsar yabo da godiya ga Ubangiji Subhanahu wata'ala mai zaɓar wa kowane bawa abin da ya dace da rayuwarsa.
Baban su Nana ji yayi tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu, bayan da likita ya sanar masa abin da yake damun Jamila.
Duk da Mama ta roƙe si a kan su rufa