Showing 105001 words to 108000 words out of 124686 words
tsaye a falo. Ya ce "Hajiya Amina lafiya kuwa? Shukura ta kira ni a waya ta ce lallai na zo"
Hajiya Amina ta ce "Wallahi nima ban san abin da yake faruwa ba, shi ma na ji yana zancen za a tona masa asiri na kasa ganewa"
Ya kalli Shukura ya ce "Shukura, mene ne ki yi mana bayani"
Shukura ta yi shiru tana kallon Alhaji Zailani, amma ta kasa magana, kawai ta fashe da kuka.
Yusra ta ce "Ina gida wayar Baban Haidar ta lalace, ya saka layinsa a wayata, Shukura ta kira ta ce tana wani Asibiti a can wata ƙaramar hukuma a Kano. Wai garkuwa aka da ita ta kuɓuta, wata mata ta tsince ta, ta kaita Asibiti. Na ce ba zan tafi ba sai tare da ita, da magariba wasu suka zo Asibitin su na nemanta za su kashe ta. Shi ne na tafi da jaririn, ni ban ma san yadda aka yi ba na ganni a gidanmu na Abuja daga Asibitin. Amma babanta ne ya saka a sace ta"
Gaba ɗaya suka kalli Yusra cike da mamaki.
Alhaji Fatuhu ya ce "Kin san me ki ke faɗa kuwa?"
Yusra ta ce "Na sani mana, ba fa ƙarya nake yi ba. Ai ita da kunya ta ce ga abin da ya yi, amma ni dai ku yi haƙuri na faɗa"
Alhaji Fatuhu ya ce "Amma kamar an ce ai ba ta da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, wataƙila...
Shukura cikin kuka ta ce "Yusra ba ƙarya take yi ba, Daddy ne ya sanya a sace ni, saboda ina bin diddigin yadda aka ce jaririna ya mutu, kuma saboda ya bayar da jaririna a matsayin sadaukarwarsa ta shekara a ƙungiyar asiri. Na so rufa masa asiri na yi shiru, amma ba zan iya ba, mussaman idan ina kallon mutanen da ya zalunta, da yadda yake ganin bayan rayuwarsu. Ni Yusuf ma ina kyautata zaton shi ne ya bayar da shi a kungiyar"
Cikin tsawa Alhaji Fatuhu ya ce "Shut up Shukura, mahaifinki ne fa, ki ke yi masa wannan tonon sililin a gaban mutane. Kuma tayaya za ki haɗa kai da abokiyar zaman ki, ku yi masa wannan ƙazafin?"
Shukura ta ce "Ko zan yi wa kowa ƙazafi yaya za a yi na yi masa? Bana jin komai ko a gaban waye zan tona masa asiri, iyaka dai a yi mini gori wataran hakan ba zai dame ni ba. Ɗana ya ɗauka ya bayar aka yi tsafi da shi aka yi maka asirin da ka rasa komai ka yi rashin lafiyar nan. Suka haɗa baki da Doctor Sharif aka yi mini tiyata aka ba su jaririna.
Tayaya zan iya rufa wa mutumin da ya yi mini wannan zaluncin asiri?. Nan Shukura ta din ga faɗar miyagun ayyukan da Alhaji Zailani ya gaya mata ya yi da bakinsa.
Wani irin bugu zuciyar Hajiya Amina ta yi, take ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, tamkar an zare mata lakar jikinta. Wani irin gumi ya fara tsatsafo mata ko ta ina.
Alhaji Fatuhu bakinsa na rawa ya ce "Zailani, abin da yarinyar nan ta faɗa haka ne, ko kuma ɗimuwa ta shiga ne?" Yayi shiru bai yi magana ba, sai tsare su da idanu da ya yi.
Sagir ya ɗan daddana wayarsa, mutumin nan da suka zo tare da Shukura ne ya shigo, tare da wasu ƙarti majiya ƙarfi su uku.
Bayan ya yi musu sallama, ya yi musu bayanin shi jami'in tsaro ne, kuma Likita, shi ne ya haɗu da Shukura a lokacin da nutanen da Alhaji Zailani ya tura, suka gano ta, suka yi yinƙurin kashe ta, ya yi amfani da ƙwarewar aiki, ya kama mutum biyu daga ciki. Kuma sun tabattar da Alhaji Zailani ne ya saka su wannan aiki.
Bakin Hajiya Amina na rawa, da kyar ta ce "Me na yi maka haka Zailani?" Daga nan ba ta sake cewa komai ba, ta silale ta faɗi ƙasa.
Alhaji Fatuhu shi ma kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi ya yi, ji yayi tamkar numfashinsa zai ɗauke. Sai yanzu wasu abubuwan da suka faru suke dawo masa, amma bai taɓa zaton Alhaji Zailani zai iya aikata masa wannan mugun abun ba.
Kafin a bar gidan da shi, ya tsaya ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Kar ka yi mamakin abin da ya faru, domin ban taɓa sonka ba, duba da yadda ka fini ta ko ina, kuma ban yi nadamar abin da na aikata maka ba. Duk abubuwan nan da na yi babu wata cikakkiyar shaida da za a iya kama ni da laifi da ita, balle a hukunta ni. Sai shaidar sace 'yata da na yi, wannan ma na san yadda zan fitar da kaina.
Sai dai dole mu yi mutuwar kasko, domin ba ni kaɗai ba ne a ƙungiyar asirin, har da yayarka, da ta sadaukar naka da ɗanka da ya mutu, dan haka ko wani mataki zaka ɗauka a kaina, sai ka haɗa da ni da ita, gara ni abokinka ne kawai, ita kuma 'yar uwakka ce!".
*****
Nana ta so sanya kayanta na Nigeria, a gurin bikin nan, Hammad ya ce shigar buzaye za a yi mata. Ta sha gyara ta yi kyau. Agadez ta ɗinke da tarin jama'a.
Tun daga kan gashin kanta, lungu da saƙo na jikinta, babu inda bai ga gyara ba.
Sai da ta tuna da lokacin bikinsu na farko, yadda aka kawo mata shadda ta alfarma. Yanzun ma haka ne, rigar ta sha aiki ita kanta shaddar ƙamshi take yi na musamman.
Babu babban abin da ya razana Nana, irin sarƙar da aka saka mata ta gold da ta sauka har cikinta. Ta kalli mai kwalliyar ta ce "Ni gaskiya a cire mini wannan sarƙar ba zan iya saka wa ba, fariyar ta yi yawa"
Matar ta ce "Ba fariya ba ce shugabata, ado ne na mutanen ƙasar nan, dan Allah kar ki ji wani abu, ai ana kammalawa dole za ki cire ne" Sai da aka yi ta fama da Nana sannan ta haƙura, gani take yi kamar ba ta hanyar da ya dace ta yi wa Allah godiya ba kenan, da wannan fariyar.
Ta din ga istigfari, da fatan Allah ya sanya kar hakan ya sanya ta ji wani abu na girman kai ko tinƙaho.
Ƙaton ɗakin taro ne, ta kowane ɓangare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan mutane gurinsu daban, ɓangaren danginta daban, abin har ya fara bata tsoro ta ji kanta yana juyawa. Ba iya wannan ba, shi kansa Muhsin da kusan kwana biyar rabon ta da shi, an yi masa ado, kayansa iri ɗaya da na mahaifinsa.
Aka buɗe taro da addu'a, da karanto jadawalin abin da za a gudanar a gurin.
Aka fara da sake tabattar da rushe majalisar Imam, da zimmar duk wani ɗan sarki Imam ne, amma babu majalisarsu, da kuma cewar lallai su za su gaji sarauta.
Aka sanar da sauke wasu daga manyan makusantan Sultan, ba tare da faɗar cikakken dalili ba, sai cewa saboda za a yi gyare-gyare ne a masarautar Agadez.
Aka gabatar da roƙo ga gwamnatin tarayya, a kan ta bayar da tallafi su haɗu da masarautar Agadez, a gyara gidan tarihin nan, a faɗaɗa shi a ƙawata shi, ya zamana gurin buɗe idanu sosai ga baƙi. A kuma gina Hotel a ciki ko wajen gidan, saboda samar da masauki ga baƙin da za su din ga zuwa yawon buɗe ido.
Daga nan aka sake jaddada dokar, halattawa ƙabilar buzaye auren duk matar da suke so, daga kowace ƙasa.
Aka yi ta kaɗe-kaɗe ana shiga ana fita da abinci kala-kala.
Daga bisani aka yi wa Imam Hammad naɗi aka ba shi sarautar Sardaunan Agadez, yayin da Imam Zahradeen aka ba shi sarautar Tafawa.
Sai kuma abin da ba a taɓa tsammani ba, Sultan ya yi wa Mahmoudu Sarautar Tafeedan Agadez, tare da ba shi auren ɗaya daga cikin 'ya'yansa, wanda za a gudanar a nan take. Gigicewa Mahmoudu ya yi, Nana ma ta waro idanu saboda mamaki. Hammad kuwa ya sani, tare da Sultan suka shirya komai. Kuma ya tabattar ƙanwar tasa ta amince da auren Mahmoudu, ita ma tata mahaifiyar rasuwa ta yi, ita ce 'yar autarsu. Dama ba shi da matsala da Mahmoudu, kuma ya fuskanci su na shiri sosai, shiyasa ya nemi alfarmar Sultan ya yi wannan haɗin.
Aka fito da Muhsin, aka gabatar da shi, a matsayin ɗan Hammad, da Duniya ba ta san da shi ba, kuma a ka yi masa naɗin Imam kuma Yariman Agadez mafi ƙarancin shekaru a tarihin Agadez, haka zalika kuma Imam da mahaifiyarsa ta sauya tarihin Agadez baki ɗaya. Nan manyan mutane suka din ga bajinta, da gwangwaje Muhsin da tsadaddun kyaututtuka na ban mamaki. Har sai da Nana ta kalli abin a matsayin Almubazzaranci.
Daga bisani aka din ga koɗa Nana ana yi mata kirari, ita ma aka gabatar da ita, a matsayin matar sabon Sardaunan Agadez, kuma mahaifiyar Yarima.
Nana gaba ɗaya sai ta rikice, kawai ta fashe da kuka.
Aka bata mic a kan ta yi magana, amma ta kasa ƙarshe kawai ta yi sujudu shukur a gurin, jikinta na tsuma tana wani irin kuka. Hammad ne ya din ga rarrashin ta, yana ankarar da ita ranar farin ciki ce a gare su. Ba a bar uwar Yarima haka ba, sai da ta samu sarautar Garkuwar matan ƙasar Agadez.
Haka matan manyan mutanen nan, suka din ga guɗa, suna yi mata kyaututtuka.
Hammad ya yi godiya ga tarin al'ummar da suka halarci taron, tare da fatan ɗorewar Canjin da aka samu, na halatta auratayya da kuma tabattar da 'yancin kowane kalar fata.
Ya yi godiya ga dangin Nana, tare da jinjina mata, da kamba mata a gaban tarin jama'ar nan. Duk bai fito ya bayyana wa mutanen abin da Nanan ta yi yake ta wasa ta ba, amma ya nuna wa Duniya yana ƙaunar Nana, kuma komai zai yi ba zai taɓa biyanta soyayyar da sadaukarwar da ta yi masa ba.
"Haƙiƙa yau rana ce mai girima, da ɗumbin tarihi a gare ni, da ma al'ummar ƙasar nan, duk da akwai ranar da ta fi ta da ba zan manta da ita ba, ranar da na mallaki Gimbiya Asma'u a matsayin matata. Ba ni da kalaman da zan yi amfani gurin yi mata godiya, da nuna muku girma da matsayinta a rayuwata ba. Ni dai na san halitta ce mai girma, da ta cancanci na wasa ta, na yabe ta, na so ta na kambama ta ko a ina ne. Asma'u ke rayuwata ce" Ya ƙarasa maganar a raunane.
"Allah ya yi miki mafificin tukuici. Haka zalika ba zan manta da ɗan uwana ba, ba sabon Tafawan Agadez ba, dama wannan yayana ne. Ina nufin Tafeedan Agadez. Ba ni da abin da zan iya faɗa, sai dai za ku dauwwama a cikin zuciyata da kuma addu'ata. Sai mai gayya mai aiki uba na gari mai girma Sultan uban ƙasa uban kowa da kowa. Mu na godiya da tarin karamci da dattakunka a gare mu.
Iyayena na Nigeria, kafataninku muna ƙara sake miƙa godiya a gare ku"
Nana kam kasa jurewa ta yi, ta rasa ma kukan me take yi, na murna ne ko kuma na damuwa.
Ba Nana ba hatta iyayenta, sai da suka yi kukan murna, Baba bai taɓa tsammanin a zuriyarsa za a samu irin wannan tagomashin ba. Sai dai shi Allah, mai aikata abin da ya so ne a lokacin da ya so, ya kan ɗaga abu a lokacin da ya ga dama, zuwa ƙololuwar matsayin da zato bai taɓa zata ba.
Taro ya watse lafiya, aka tashi cikin farin ciki, duk da zukatan maƙiya ba haka suka so ba.
Ai kamar yadda Hammad ya ce, a ranar za ta tare, babu wani abu da ya yi saura da ake jira.
Batun sabbin naɗe-naɗen da aka yi, ya sake cika gari, wasu suna ganin Sultan ya nuna son kai, gurin cire manyan mutane masu muƙamai, ya bawa 'ya'yansa.
Nana ta so ta huta kafin ta tare, amma Maijidda ta ce a'a, tun da haka mijinta ya ce yana so.
Baba duk abin sa, sai ga shi ga babar su Nana, a gurin bikin Nana. Abin mamaki Imrana ne ya sanya su a gaba ya din ga yi musu nasiha, da nuna musu illar gabar da suka din ga ya haifar musu.
Nene ta riƙe hannun Nana ta ce "Gimbiyarmu, dan Allah a yi mana godiya, tabbas Hammad ya cika jagora, na ji daɗin abin da ya yi wa Mahmoudu, Ubangiji Allah ya saka da mafificin alkhairi"
Gaba ɗaya Nana ta so ta sake sosai a cikin 'yan uwanta.
Hammad yana ta shiri a ɗakinsa, Mahmoudu ya shigo, dan bai samu sukunin haɗuwa da Hammad ba, saboda karɓar baƙi.
Hammad ya kalle shi ya ce "Ango ka sha ƙamshi"
Ya buɗe baki zai yi magana, Hammd ya girgiza masa kai ya ce "Ɗan uwa kai ka ke bi na bashi, dan haka babu buƙatar wani dogon jawabi ko godiya a tsakaninmu, mai girma Tafeeda Allah ya taya riƙo" Ya yi maganar yana fesa masa turaren hannunsa.
"Sardaunanmu, godiya ta zama dole a tsakaninmu ai, godiya dole na...
Hammad ya tsuke fuska ya ce "To jeka waje ka yi godiyar"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Wallahi jin abin nake kamar a mafarki, bawa ya zama saraki ikon Allah, amma kana ganin Hanin ta amince da auren nan, tsakaninmu ba soyayya raha ce dai da girmama junanmu"
Hammad ya ce "Ka na tsoro ne? Hanin na sonka, da amincewarta aka yi komai".
"To kuma tana son baƙar fata"
Hammad ya yi tsaki ya ce "Ka na da abin haushi wallahi. Kaf ƙabilar buzaye, ban taɓa ganin baƙi mai kyanka ba, har fararen ma, idan kuma duk baƙar fata gaba ɗaya matata ta fi kowane baƙar fata kyau" A tare suka yi dariya. Hammad ya ce "Kai mutumin kirki ne, mai nagarta na san na yi wa ƙanwata kyakykywan zaɓi ne, dan haka ba ni da fargaba" Suka ci gaba da tattaunawa cikin raha.
Nana tamkar wadda za ta yi sabon aure, haka aka zaunar da ita aka din ga yi mata nasiha, Mai jidda ta nanata mata batun riƙe addu'a a duk inda take.
Sai da aka kai ta har gurin Sultan nan ma ya yi musu nasiha sosai ita da Hammad.
Daga bisani, Hammad ya ɗauke ta daga can gurin Sultan suka tafi, ya ce akwai walimar cin abincin dare tare da ita da danginta kaɗai, washegari kafin su wuce Nigeria.
Asal kamar za ta mutu, haka take wani irin kuka tana rirriƙe Hasna.
Tafawa ne yake ta bala'i ya ce "Wallahi ko za ki mutu sai ya sake ki, ban ga amfanin ki ci gaba da zama da mutane marasa mutunci ba, babu kunya babu tsoron Allah Jalaludeen ya sauke ni daga kujera ta, ya bawa 'ya'yansa, zai ga matakin da zan ɗauka a kansu."
Asal ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, amma zan koma gidan Hammad, iya rufin asirin da ya yi mini ya isa, na yi maka biyayya iya yi na, amma ƙarshe na faɗa halaka, kuma buƙatar taka bata biya ba"
"Wallahi Asal ki ka koma gidan Hammad babu ni babu ke, na gaya miki sai dai ki canza uba!"
101
Alhaji Sabo ya ce "Ya na ga ka tsaya cak haka?"
Da kyar ya harhaɗo maganganun ya ce "Sabo, ce mini kai fa Amina ta mutu?"
Ya ce "Eh mana, ranar da ta mutun mutane na ta tambayar ina ka ke, aka ce kana Asibiti, likitoci sun hana a zo gurin ka. Yanzu sai ka maze duk wanda ya yi maka gaisuwa ko ya zo dubiya kawai ka amsa. Ita kuma Shukura lallai ka san yadda za ka yi da ita, ka ɗauki mataki a kanta, ko kuma ka gaggauta bayar da jininta ga ƙungiya kawai"
Ya yi shiru bai sake cewa komai ba, har suka isa gidansa, mutane na ganinsa suka din ga zuwa yi masa sannu, suna yi masa gaisuwa.
Bai iya amsawa kowa ba, Alhaji Sabo ya ce su yi haƙuri ba ya iya magana, saboda yanayin jikinsa. Har sashensa Alhaji Sabo ya raka shi, suna zuwa ya tarar da hijjabin Hajiya Amina da sallayarta gurin da ta yi sallar walha, kafin ta fita ta bar ɗakin su Sagir su zo. Ya ɗauki hijjabin ya kalli Alhaji Sabo, ya ce "Kana nufin Amina ta mutu? Kalli hijjabinta fa inda ta yi salla"
Alhaji Sabo ya ce "To shi ne me, kowa ma na haka ne ai. Kana ganin zaka iya zama a gidan nan kai kaɗai, ko a samo maka wanda zai tayaka zama?"
Ya girgiza kai jiki a sanyaye, duk da mutuwar Yusf ta dake shi, amma bai taɓa jin mutuwar da ta daki zuciyarsa kamar mutuwar Hajiya Amina ba. Kan ƙiftawa da Bismillah. Ya ɗauka aljanin da ya bawa mahaifarta shikenan ya tseratar da ita daga ƙungiyar, abin da bai sani ba shi ne, bai isa ya tseratar da ita daga ajalinta ba.
Ya nemi guri a gefen gado ya zauna, kawai ya din ga ganinta tana yi masa gizo. Duk izza da ƙafafa ta matan masu kuɗi, da ta'amalli da 'yan aiki, Hajiya Amina ba ta yadda mai aiki ta dafa masa abinci ba. Duk da son da yake yi mata, baya hana shi ya ci mata mutunci wasu lokutan. Amma ko ta yi fushi na lokacin ne ta ware.
Ya yi mata wani irin so, mai wahalar mantawa.
So yake yi ya samu damar zubar da hawaye, amma abu ya gagara. Vibrating wayarsa ta yi a kan gadon, ita ma yadda ya tafi ya bar ta, haka ya dawo ya tarar da ita. Ya ƙura mata ido daga bisani ya kai hannu ya ɗauka ya duba.
Saƙo aka turo masa da lambar Doctor Sharif, ana sanar da shi Allah ya yi wa mai wayar rasuwar, za a yi jana'izarsa da yammacin ranar.
Ya fito daga cikin saƙon, ya ga saƙon Yusuf na ƙarshe, da yake ce masa Daddy idan ka ga saƙona ka kira ni dan Allah na kasa samun ka a waya.
Ya tuna yadda suka yi waya, Yusuf yana tsara masa yadda zai yi walimarsa na kammala master's da ya yi, suka da daɗe su na waya cikin raha da barkwanci. Ya tuna yanzu duk ba sa Duniya.
"Saura kai, nan da anjima kai ne zaka mutu" Ya ji wata zuciyar ta raya masa. A take zuciyarsa ta tsinke ya buɗe idonsa a razane ya miƙe tsaye yana waige-waige. Wata irin fargaba ta shige shi, wani abu da bai san ko mene ne ba, ya tsirga masa tun daga