Showing 69001 words to 72000 words out of 124686 words

Chapter 24 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

90

gazgatawa zai yi ko ƙaryatawa, idan ya yi duba da wasu abubuwan sai ya ga yakamata ya gazgata batun, dan Mahmoudu ba zai masa ƙarya ba.
Amma ya din ga jin sa kamar ba mutum ba, ko kuma a wata Duniyar yake ta daban.
Da daddare yana tare da Asal, tana danna waya, Nana ta kawo Abincin dare. Kamar ya yi mata magana ya fasa, sai dai ƙasan zuciyarsa ya din ga fatan Allah ya sanya gaske ne, Nana matarsa ce, ta kowacce fuska ta yi masa. Tun kan ya ji kan wannan burkitaccen labarin yake jin wani abu na sukan zuciyarsa a game da ita. Babban abin da yake ƙara burge shi da ita, sanin mutuncin kanta da ba ta yadda Asal ta taka ta ba. Saɓanin waɗanda suke kwantar da kai Asal ɗin ta taka su saboda abin Duniya. Ya gaza manta rungumar da ta yi masa a turakarsa.
Ta ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, amma bai sauke idanunsa ba ya ci gaba da kallon ta. A ɗan diririce ta ce "Na gama zan iya tafiya. Bai amsa mata ba ya tuna yadda take ba shi Nonon raƙumi da habbatussauda, ga abinciccikan da yake matuƙar da take gwangwaje shi da su.
Asal ta ce "Za ki iya tafiya" Sai da Nana ta je tsakiyar falon sanan ya ce yana buƙatar lemon kankana da shayin citta da kanumfari kawai, ba zai sha na kimba ba.
Nana ta yi shiru ta ci gaba da tafiya, Asal ta ce "Kin ji ai"

A hankali Nana ta ce "Na ce miki ba ni da kunne ne, da ba zaki iya tsinana wa mijinki uban komai ba"

"Ke ba magana nake yi miki ba" Nana ta waiwaya ta ce "Ai na amsa na ce to"

Shi kuwa ya yi haka ne, dan ta sake dawowa ya ci gaba da kallon ta ko Allah zai sanya ya iya tuna wani abin.
Amma har ta kawo masa shayin tayi tafiyarta bai tuna komai ba.

Sosai faɗa ya ɓarke a tsakanin Giyaz da Ƙaisar a kan Nana, Giyaz ya din ga ɗaga Ƙaisar yana bu ga shi da ƙasa. Karfin Ƙaisar da na Giyaz ba ɗaya ba ne ba, duk da Giyaz ya kwana biyu a duniya amma yana da matuƙar ƙarfi.
Ƙaisar ya baje a gurin, bayan buga shi da jikin dutsen gidan tarihin Agadez,da Giyaz ya yi, ga ƙona shi da ya din ga yi da wuta. Sai dai ganin Ƙaisar ya baje ko motsi ba ya yi, ya sanya ya nufe shi da sauri yana kiran sunansa, ya ɗago Ƙaisar, amma ya shammaci Giyaz, ya fito da jakar gurin Sarkin Baka daga cikin rigarsa, ya naɗe masa wuya da hannun jakar. Wata irin kururuwa Giyaz ya din ga yi, yana tumami a gurin yana burgima. Ihun nasa sai da ya razana da yawa daga cikin halittun da suke cikin gidan tarihin.
Ƙaisar ya miƙe da kyar ya tunkari wani ɗaki, aljanun da suke ƙofar ɗakin su ka dare suka ba shi guri. Ya zura hannunsa a ya ɗaukko kwalbar da Giyaz ya ce tunanin Imam Hammad ne a cikinta. Ya ajiye ta a nesa kaɗan ya ja da baya ya din ga hura iskar bakinsa a jikin kwalbar. A take kwalbar ta yi wata irin ƙara ta tarwatse, a take ɗan hayaƙin da yake cikin kwalbar yana zagayawa a cikin wani ruwa ya bar cikin ta. Ƙaisar ya koma kan Giyaz da ya suma a gurin, ya ɗauke jakar da ya shaƙe shi da hannunta, ya ɓace daga gurin.

A hankali yake juyi, ya buɗe bakinsa domin ya jarraba yin magana, ya ji ko maganar ta dawo ya ce "Ma vie" sai dai ya ji shiru. Shi ma shirun ya yi yana ji wani raɗaɗi tun daga cikin kansa har idanunsa. Ya yi juyi ya ji taushin abin da yake kai ya banbanta da nasu. Ya buɗe idanun da suke yi masa raɗaɗi da kyar yana kallon ɗakin. Asal ce ta shigo ya kalle ta, ta ce "Amour ta gama abinci, ka taso ka karya" Ya jinjina mata kansa da ya yi masa wani irin nauyi mara misaltuwa.
Tabbas ya san Asal matarsa ce, amma ina Nana. Sai ya yi shiru sannu a hankali ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa yadda aka fita da shi daga gidansu na Buda yana fizge-fizge yana kiran matarsa Nana. Ya rintse idanunsa tare da damƙar gashin kansa yana girgiza kan, saboda yadda ƙwaƙwalwar tasa ta hargiste, tunanin ma ya rasa wanne zai yi.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya din ga maimaitawa babu ƙaƙƙautawa. Asal ta sake shigowa ta ce "Amour wai yane? Baccin ne bai ishe ka ba? Sha biyu saura fa na rana, ba ka ko karya ba"
Ya yi mata nuni da hannunsa alamun yana zuwa.

"Ok, ni zan je gida, Abbu yana jira na" Ya jinjina mata kai"

Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miƙe tsaye a hankali, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga ɗibarsa.
Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saɗara-saɗara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maƙarƙashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?"

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da kwandon kwanukan Abinci.
Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaɗinsa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez.

"Barka da wannan lokaci Sayyid, ga abincinka, na ga na safe ma baka ci ba, ko ba shi ka ke so ba ne?" Hannu kawai ya ɗaga mata, ya lumshe idanunsa, mamaki ya cika ta, ganin ba shi da niyyar magana, ya sanya ta tashi ta fita cike da damuwa.
Tana fita ya haɗe tafukan hannayensa, ya dafe fuskarsa ya fashe da kuka, da wace fuskar zai kalle ta? Me zai ce mata? Ta ina za ta yarda da shi cewar ba yana sane ya ƙi kula ta ba. A hankali ya ci gaba da tuna tsantsar juriya da sadaukarwar da ta yi saboda shi. Ba ta haƙura ba ta taho nemansa, sun haɗu kuma bai gane ta ba.

Ya so fita ya je ya samu Habu, amma ba zai iya ba, saboda ji yake yi tamkar an sauya masa gangar jikinsa.
Wayarsa da ya bari tun daren jiya a falon tana caji, ya ɗauka ya duba ya ga Mahmudu ne yake kiransa.
Ya ɗaga wayar bai yi magana ba, Mahmoudu ya ce "Hammad ina tunanin yaron nan fa ɗan gurin Nana ne, kuma..

"Nana matata ce, ina iya tuna komai yanzu"
Mahmoudu a rikice ya ce "Ina fatan ba ka gaya mata ba?"
"Babu wanda na gayawa"
"Alhamdillah, kar ka ce mata komai, sai mun tabattar da abin da muke bincike, ka zo mu je Maraɗin gurin Umma, na san za ta saurareks fiye da ni. Amma ya aka yi ka tuna komai?"

"Maganar ma da kyar nake yi Mahmoudu, ba zan iya fitowa ba. Mu yi magana anjima" Ya ajiye wayar hawaye na ci gaba da zuba daga idanunsa.

Haka ya wuni ba tare da ya ci komai ba, jikinsa kuma gaba ɗaya babu ƙwari, kamar wanda aka zarewa laka.
Babu abin da yake yi banda tuna rayuwar da suka yi da Nana, da girmama yadda aka yi ya manta da ita, ya kasa tuna ta.
Sai dare sannan ya iya samu ya sha shayi kawai. Sai dai zuciyarsa babu daɗi a cunkushe. Ya lallaɓa jikinsa da yake a mace, ya nufi hanyar ɗakin Nana, sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana lissafin me zai ce mata? A hankali ya ɗago hannayensa, ya kalli yatsunsa, ya tuna yadda ya yi mata kyautar zoben, a lokacin da yake tsakiyar jin shauƙin ƙaunarta. A hankali ya murza tagullar hannunsa, sai ga Arun ya bayyana. Ya ce "Na amsa kira ya shugabana"
"Ka duba mini; me yarinyar cikin ɗakin nan take yi?"

Arun ya risuna ya ce "Tana ninkin kaya ne ya shugabana, amma alamu sun nuna a gajiye take sosai da sosai, kuma akwai damuwa a tare da ita, sai kuma bacci da take ji. Gajiyar da ta yi da damuwar da take ciki ya haifar mata da kasala sosai. Kuma ta yi kuka mai yawa awanni kaɗan da suka gabata".
"Ya isa haka, ina son ta yi bacci yanzun nan"
Arun ya ce "Shiga kanka tsaye mai gidana, an riga an gama."
Hammad ya numfasa ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe. Ɗakin sai ƙamshin turaren wuta yake yi. Tana kwance a ƙasa ga kayan ninkin nata a gefe. Daga ita sai zani da ta ɗaura a ƙirjinta, saboda daga wanka ta fito ta zazzage kayan ta hau ninkewa ko za ta ga wayarta da ta nema ta rasa.
Jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa gabanta, bai yi wata-wata ba ya ɗago ta yana kallon kyakykyawar fuskarta.
Wata irin karaya da matsanancin tausayinta ya ratsa zuciyarsa. Ya ƙanƙameta a jikinsa yana wani irin kuka zuciyarsa na yi masa zafi da ƙuna.

"Ki yi haƙuri Asmyna, ki yi haƙuri ki yafe mini, ni kaina ban san abin da ya same ni ba, ban san yaya aka yi na gaza tunawa da ke ba. Ban yi miki adalci ba amma kk yi haƙuri rayuwata" Ya din ga yi mata surutai ba tare da ta san yana yi ba, saboda wani irin nannauyan bacci da take yi.
Duk da yadda burki ya so ƙwace masa, kasancewarsa da Nana a wannan yanayi, da ya din ga tariyo masa irin rayuwar da suka yi ta tsantsar soyayya da ƙauna. Ya yi iya ƙoƙarinsa gurin sarrafa kansa da kyar gurin ganin bai aiwatar da wani abu ba. A ganinsa yin hakan tamkar rashin adalci ne kai tsaye a gare ta.
Kamar wani zai ƙwace ta, haka ya matse ta a jikinsa, yana zubar da hawaye, yana sake jin wani abu na ratsa lungu da saƙo na gangar jiki da kuma ruhinsa a game da ita.
A duniya ba ya jin yana da wani abu da zai iya aikata wa Nana ya yi ko kwatankwacin saka mata a kan abin da ta yi masa.
Har gefin Asuba yana rungume da ita, hawaye kuma bai bar kwarara daga idanunsa ba, lissafi yake yi ko za ta yarda da shi, ta sake ba shi dama ta biyu. Ko kaɗan, tunaninsa da hankalinsa ba sa lissafa masa kalubalen da yake gabansa, na auren wata ƙabila baƙar fata da buzuwa ba.
Da kyar ya iya raba jikinsa da ita, ya ɗan yafa mata zaninta, ya gyara mata kwanciyarta, ya durƙusa ya sumbace ta, ya ci gaba da kallonta, daga bisani ya tashi da kyar ya fice ya bar ɗakin.
Ko da Nana ta farka ta sha mamakin yadda ta ga jikinta, ita dai ta san ta yi mafarkin tana tare da Sayyid, amma da ta farka ta ga alamun kamar an taɓa ta.
Ga shi a iya saninta ninkin kaya take yi, amma ta farka ta ganta rabin tsirara, ta yi tunanin ko Ƙaisar ne, amma cikin hanzari ta kawar da wannan tunanin daga ranta da take jin tamkar saɓo ta aikata, dan ta san Ƙaisar bai taɓa yi mata yawo da hankali a abu makamancin wannan ba.
Ta yi iya ƙoƙarinta ta kawar da tunanin komai daga ranta, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta yi alwala ta dawo ta yi sallar asuba tana ta istigfari saboda yadda ta makara.
Gari yana yin haske, ya shirya ya tafi gidan Mahmoudu, duk da yadda jikinsa yake a mace.
Kallo ɗaya Mahmoudu ya yi masa, ya gane a rikice uban gidan nasa yake.
"Mahmoudu, wallahi na gane ta, na tuna ta Nana ce matata ce, to amma yaya aka yi komai ya shafe a cikin kaina na manta da ita?"
Mahmoudu ya ce "Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, yanzu aiki ne ya ganmu jawur, sai dai ba wannan ba dole mu tsananta bincike a kan abubuwan da suke faruwa da kai."
"Ni kaina abubuwan sun ɗaure mini kai Mahmoudu, ji na nake yi wani iri, kamar an ƙwance wani nannauyan dutse daga kaina. Yanzu ta ina zamu fara, ni fa duk abin da za a yi ko Agadez za ta tashi, ba zan rabu da matata ba"
Mahmoudu ya ce "Ban gane Agdez ta tashi ba, a'a gaskiya sai dai ku ku tashi kai da ita"
Hammad ya ce "Mahmoudu ka daina wasa mana"
"Na daina wasa shugabana, amma yanzu ka tuna su Sule?"
"Na tuna shi, yanzu ina iya tuna komai fa a cikin ƙwaƙwalwata."
"To ma sha Allah, albishirinka"
"Mene ne?"
"Wallahi sai ka saya, ba zan faɗa a sadaka ba"
"Faɗi ko me ka ke so, wallahi zan baka"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Zan yi tunanin me nake so, amm yanzu yi sujudar godiya ga Allah tukuna"
"Zan yi amma fara gaya mini"
"Ta tabatta yaron nan, ɗan Nana ne, kuma a bincikena, da Gimbiya ta zo Niger, a hannun Ummana ta sauka. Al-Husssain ya turo mini komai nata, kamar yadda ka sanya shi bincike. A zahirin gaskiya da naje Maraɗi na gano yaron nan a gurin Ummana, shiyasa na damu da matsa bincike. Na kira Umma mun yi magana ta tabattar mini da ɗan Nana ne, kuma ɗanka ne yana daga dalilin da ya sanya ta turo ta Maraɗi aiki gidan cin abincinku, kuma ta ƙarfafeta ta taho Agadez ɗin"
A rikice ya damƙi hannayen Mahmoudu a gigice ya ce "Dan Allah da gaske ɗana ne? Ina da ɗa? Mahmoudu? Mahmoudu dama zan haihu zan ga ɗana a Duniya. Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil Azim. Allahumma lakal hamdu wa laka shukur. Mahmoudu dan Allah da gaske ka ke?"
Cikin tausayawa Hammad, mussaman sanin irin ƙalubalen da ya fuskanta na rashin haihuwa da jarabtar da Allah ya yi masa na son 'ya'ya, aka hana shi ƙara aure, kuma Tafawa ya din ga ƙalubalantarsa da hakan yana nemana a sauke shi.
Mahmoudu ya dube shi ya ce "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ka san ka na da matsalar zuciya kar ciwonka ya tashi, amma ka san ba zan yi maka ƙarya da abin da ka daɗe kana nema ba. Ina da tabbaci a kan abin da na gaya maka, dan sai da na gama bincike na tabattar sannan na gaya maka.
Hammad ya saki Mahmoudu, ya yi sujuda yana yi wa Allah godiya, sannan ya tashi fuskarsa sharkaf da hawaye ya ce "Yanzu mene ne abin yi? Ko ka zo mu je ka yi mata bayani, ban yi burus da ita ina sane ba"
"A'a kar mu kuskura mu sanar mata komai yanzu, sai mun gama daidaita komai da shirya yadda zamu tunkari jama'ar Agadez da wannan babban al'amari"
Ya share hawayensa ya ce "To tashi mu je Maraɗi na ga yarona"
"Mu bari sai gobe in Allah ya kaimu"
Hammad ya ce "Ba zan iya jira ba, kuma kar wani abu ya same shi, dole na dawo da shi kusa da ni, ko na ajiye su a wani guri keɓantacce, idan yana hannuna sai ta fi tsayawa ta saurare ni. Na san halinta akwai sauƙin kai amma akwai kafiya ba za ta saurare ni ta daɗin rai ba"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "To shikenan, amma ka jira kaɗan Sule ya zo, ku gaisa sai mu je Maraɗin tare da shi"
Haka kuwa aka yi, ba a jima ba Sule ya shigo, ya risuna yana kwasar gaisuwa gurin Hammad. Ya rungume Sule tare da yi masa godiya, a kan ɗawainiya da kuma gudunmuwar da suka ba shi a lokacin yana Nigeria.
Suka shirya suka tafi Maraɗi gidan Nene, ko da Hammad ya ga Muhsin, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rungume shi yana kuka, da gode wa Allah da ya sanya yana da rabon haihuwa a Duniya.
Duk da sun kai ruwa rana da Nene, ta ce ba zata ba su Muhsin ba, dan ba su yi haka da Nana ba. Hammad ya ce ba ɗaukar Muhsin zai yi ba yana son ya nesanta su da gurin da suke na ɗan wani lokaci, kamar yadda Hammad ma ya yi tunani haka ita ma Nene ta tabattar masa da muddin ya jewa Nana kai tsaye babu abin da zai hana Nana zuwa ta ɗauki Muhsin ta gudu, dan ta san halinta dole ya bi komai a hankali.

A hankali Hammad ya ɗago Nana daga jikinsa ya ce "Asmy bacci ki ka yi?".

"Idona biyu" Ta ba shi amsa.

"Kin yi shiru, Asmy ba da gangan na ganki na ƙi kula ki ba, kin san muddin ina cikin hayyacina babu yadda za a yi na share ki. A lokacin ina ta shirye-shiryen yadda zamu ɓullowa lamarin, Tafawa kuma ya sanya ni a gaba da da haƙilon ba zan yi mulki ba, ni juya ne, ga rashin lafiya ga hauka ga babu zobe. Ya daɗe yana jifana da kalmar juya, abin yana yi mini zafi da ciwo shiyasa na fallasa komai a lokacin da shirin duk abin da zai faru ya faru."

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yakamata mu tashi, an kira sallar Asuba".

Hammad ya ce "Haka ne, amma ba ki ce komai ba" Ta ce "Zan ce ne, ina jin bacci ne sosai ka ga kwana muka yi ba mu yi bacci ba" Ya ce haka ne. Suka tashi suka koma ɗakin nan zai rufe amma ya tsaya ganin Nana na ƙara kallon ɗakin.
Ya ce "Wannan ɗakin tun zamanin Sultan Azhar yake, duk Sultan ɗin da ya zo a nan ɗakin ne turakarsa. Kowane zamani akwai canji da kuma yadda ake ƙawata ɗakin. Kafin daga bisani a daina amfani da gidan gaba ɗaya."

Nana ta jinjina kai ta ce "Ni yanzu abu ɗaya nake son ka gaya mini, ina da ciki ko ba ni da shi?" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓa tana marairaice fuska. Ya yi murmushi ya ce "A cikin labarin kin ji inda wani abu ya faru ne?"

"Eh mana, tun da kana zuwar mini ɗaki ba tare da sanina ba"

Ya jinjina kai ya ce "Sosai kuwa, dan tun da na gano ke matata ce, kusan kullum tare muke kwana, ya yi maganar yana rufe ɗakin. Ya damƙi hannunta suka yi gaba, ja ta yi ta tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login