Showing 30001 words to 33000 words out of 124686 words
yi shahada"
Jamila ta ce "Mama ba ki san tarin zunuban da suke kaina ba, tuban da na yi sai Allah ya karɓi shahadata." Takaici ya sanya Mama fara rafka wa Jamila maficin hannunta ta ko ina. Jamila ta tashi da sauri, amma ta bi bayanta tana ci gaba da raɗa mata.
Baba ya kawo kai cikin ɗaga murya ya ce "Rabi, wannan wane irin rashin imani ne haka? Yaya yarinya ba ta da cikakkiyar lafiya za ki biyo ta kina duka, me ta yi miki?" Mama ta tsaya tana mayar da numfashi cike da baƙin ciki da takaici.
Suwaiba kuwa da take gefe, ta din ga tuntsura wata irin dariya mara daɗin ji, wadda ke bayyanar da rashin cikakken hankali ga mai yin ta.
Mama ta rasa ihu za ta zunduma ta ji daɗi, ko kuma me yakamata yi ta ji sanyi. Hutu da fatan arzikin da take da shi a kan 'ya'yanta duk ba ta samu ba, ga mahaukaciya ga karuwa Nasiru shi ma ya fara 'yan ɗauke-ɗauke, dan sau biyu 'yan vigilant na kama shi, da laifin satar tukwanen mutane da kayan ƙarafa ya sayar da sunan gwangwan. Dan tun da Jamila ta cire tallafin da take ba su, ta daina zuwa gurin Hajiya Sa'a, suka koma ruwa.
Baba ya ci gaba da yi mata faɗa a kan dukan da ta yi wa Jamila, ba tare da ya tsaya ya ji cikakken abin da Jamilar ta yi ba. Ji ta yi tamkar ta kama shi shima ta jibge shi, ko ta huce. Dan duk wannan masifar shi ne sila da ya tsaya ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da wataƙila ba su shiga wannan halin ba.
Babban abin da ya ƙara ɓata mata rai, shi ne rashin zuwan Hajiya Sa'a ta duba Jamila, duk da taga kwana biyu ba ta zuwa maimakon ta neme su ta ji ko lafiya amma ba ta yi hakan ba. Ga Maman Khairat ta tashi daga unguwar da ta so zuwa a rakata gidan Hajiya Sa'a ta ji ko wani laifin Jamila ta yi wa Hajiya Sa'a haka?.
Hajiya Sa'a kuwa tana can tana fama da kanta, dan tun mutuwar Abba ta shiga wani mawuyacin hali, duk lokacin da ta zauna babu abin da take yi sai tunanin ko yaya Abba ya ji da dodon ƙungiya ya zuƙi jininsa har ya mutu? Ta daina bibiyar duk wani abu da ya shafi kungiyar. Kasuwancin ma ta tattara ta ajiye a gefe ta koma guri ɗaya kawai. Daga kuka sai kwanciya da dana sani. Ga shi da ta fara tunanin wani irin mummunan ciwon kai yake yi mata dirar mikiya, har sai ta daina gani sosai. Wasu lokutan haka zata kulle kanta a ɗaki ta wuni, sai dai mai aikinta ta yi ta sabgoginta itakaɗai. Ta ce ko mutanenta sun zo, kar a bar kowa ya shiga inda take, kaɗaici kawai take so.
****
Mahmoudu ya dawo, ya kai wa Nana shayi da kayan marmarin da ta ce . Sai kuma kayansu da Alƙur'ani. Ya haɗu da Sultan a hanyar da suke bi su shiga gurin. Domin wani sashi ne a can cikin sashensa da ba kowa ma ya san da shi ba. Hatta iyalansa sai da izninsa suke zuwa gurin. Wasu lokutan ya kan sanar da ya yi tafiya, ya tafi cikin gurin ya kulle kansa ya samu hutu da nutsuwa.
Mahmoudu ya ƙarasa gabansa cikin girmamawa.
Ya ce "Abincin ka kawo musu?"
"Eh ranka ya daɗe"
Sultan ya numfasa ya ce "Shikenan, amma ina fatan babu wata matsala barinsa tare da yarinyar nan, duk da na fuskanci tana da hankali akwai abubuwan da take ɓoyewa. Ni kaina ba komai nake son kowa ya sani ba"
"In sha Allah Sultan, kare martaba, mutunci da kuma sirrikan Imam Hammad abu ne da ya zama wajibi a gare mu. Kuma tabbaci nake da shi ba yaƙini nake da shi, ba za ta taɓa aikata wani abu da zai cutar da shi ba"
Ya jinjina kai ya ce "Na ga alamun haka, duk da na ga wasu abubuwa na ban mamaki a tattare da ita. Dama Hammad ya gaya mini sai mun neme ta, amma ban ɗauki zancen nasa da wani muhimmanci ba. Akwai wasu abubuwa da ya gaya mini da ban gama gane ma'anarsu ba, amma bari mu jira mu gani ya samu sauƙi"
Mahmoudu ya risuna ya ce "Godiya muke ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana" Ya ɗaga wa Mahmoudu hannu.
Nana na ganin Mahmoudu ta yi ajiyar zuciya, domin shi take ta jira ya kawo abin da za ta ba wa Hammad ya saka a cikinsa. Yana kwance a kan cinyarta tana shafa gashin kansa.
Ya ajijiye mata kayan, Nana ta ce "Sannu da ƙoƙari, Ubangiji Allah ya biya ku da kai da mahaifiyarka, na fuskanci kirki da karamci a jininku yake, gado ka yi Nene akwai kirki"
Ya ce "Allah ya taimake ki, ai kin ƙwace mini ita" Nana ita abin dariya yake bata, idan ta ji su na girmamata.
Ta ce "Sayyid, ga abinci an kawo tashi ka ci" Mahmoudu ya taimaka mata, ta zaunar da shi. Ta zuba shayin a kofi, ta fara ba shi a hankali da cokali.
Duk da wata irin yunwa da yake ji, tamkar ya haɗa da Nanan ya cinye, amma haka ya daure ya din ga karɓa a hankali.
Ta ce wa Mahmoudu "Ka je ka samu ka huta, amma dan Allah ka zo da wuri, ka san ni da kai na saba, kuma kai kaɗai nake jin zan iya sakin jiki da kai. Sannan dan Allah abincinsa kar a bari ya biyo ta hannun kowa, ta gurinka kawai"
Ya ce "In sha Allah, zan yi yadda ki ka ce, sai da safe"
Sosai ya din ga cin kayan marmarin nan, yana sake shan shayin girfae da Habu ya kawo. Sai da Nana ta lura jikinsa ya daina rawa. Ya ɗan huta sannan ta tashi tsaye ta ce masa "Sayyid yinƙura a hankali ka tashi mu gani"
Ya dafa gadon, ya tashi a hankali amma ya ji kamar kayan cikinsa zai zubo. Ta riƙe hannunsa yana durƙushe yana tafiya a hankali.
Ƙofar banɗakin suka je, ta tsaya ta kalle shi ta ce "Mun yi wanka a Nigeria, yau za mu yi a Agadez ko?"
Murmushi ya yi mata sai da haƙoransa suka bayyana. Suka shiga banɗakin. Sai dai wata irin kunyarsa da ba ta san daga ina ba, ta bujiro mata. Za ta iya cewa yau jiƙa-jiƙa kawai ta yi masa, saboda yadda ya ƙara yi mata kwarjini take ganin kamar wani aka canza mata. Babban abin da ya ƙara takura ta, shi ne kallon da yake ta bin ta da shi, kamar zai lashe ta. Da kanta ta yi masa brush, hakan ya din ga tuna mata da rayuwarsu ta Nigeria.
Ta saka ya yi alwala, suka dawo ɗakin ta saka masa doguwar rigar jallabiya. Ta ce "To an ce kwananka takwas baka hayyacinka, yanzu zaka lissafa sallolin da suke kanka. Ka yi wanda zaka iya yanzu sauran sai ka ci gaba ko gobe in Allah ya kaimu ne"
Ya jinjina kai, ya kalli gabas daga zauna ya tayar da salla, saboda ba zai iya tsayuwa ba. Nana ta din ga tunani ko ta roƙi alfarmar su nuna mata ɗanta ta gan shi, tun da nasu ɗan ya farfaɗo, amma wata zuciyar ta hana ta hakan, duk da tarin kewar Muhsin da take yi. Ta shiga banɗakin ita ma, ta yi wanka ta gama ta sako hijjabinta ta fito.
Jakar kayanta ta buɗe, tana duddubawa, ta ga magungunan da Nene take bata na sha da wanka a ciki.
Kawai ta yi murmushi ta shafa mayukanta, ta duba kaya masu sauƙin nauyi dan ta saka, dan duk da ba shi da lafiya ba za ta kwana shimfiɗa ɗaya da shi ba, da haryanzu ba ta san matsayinta ba, da matsayin kawo ta gurinsa ba, duk da da aka zo ita ta nema. Ga uwa uba rashin tabbacin da gaske tana da juna biyu ko kuwa?.
Ta sakankance da salla yake yi, saboda a bayansa take zaune tana ƙoƙarin canza kaya. Kawai ta ji ya faɗo jikinta, suka faɗi ƙasa a gurin, hasken wutar ɗakin ya ɗauke baki ɗaya duhu ya mamaye ɗakin.
Ayshercool
85
LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. VIA 0069685771
AISHA ADAM STANBIC BANK
08081012143
Nana ta razana ta ce "Sayyid lafiya kuwa?" Ya rirriƙeta jikinsa na rawa.
Nana ta yi shiru cike da damuwa, ga shi yanzu ta fara wahala da riƙon da yake yi mata, dan ya ninka wanda yake yi mata su na Nigeria. Haka ta haƙura ƙyale shi.
Can bayan wani lokaci, hasken ɗakin ya dawo, a lokacin ya samu bacci, Nana ta yi shiru tana tunani daban-daban a kansa. Tabba! Tana da tarin tambayoyi da take buƙatar samun amsarsu, daga gare shi, dan akwai tarin abubuwan da suke faruwa, da suke ɗaure mata kai.
Ta ture shi da kyar, ta tashi ta saka kayanta, ta kwanta a bayansa, tana jin yadda jikinta ya ƙara tsami da ciwo.
Sai dai bayan bacci ya ɗauke ta, ta din ga munanan mafarkai marasa kyau da ban tsoro a cikin baccin. Abubuwan da ta din ga gani a gidan, sun tsorata ta. Har da yaƙe-yaƙen da aka din ga yi, kafin kafuwar masarautar, da irin azabar da bayi suka sha haka ta din ga gani. Ban da miyagun Aljanu masu ɗauke da siffofi daban-daban na ban tsoro a cikin baccin.
Juyi ta din ga yi tana haɗa wani irin gumi, tana sauke numfashi saboda tsoro. Ga shi a baccin da fari a gefe take tana kallon abin da yake faruwa, kafin daga bisani ta ganta tsamo-tsamo a cikin rikicin da ake yi, daga bisani ma miyagun abubuwan suka din ga nufo ta. Cike da tashin hankali ta farka tana waige-waige. Amma ta yi ido huɗu da Hammad a zaune yana kallon ta, da alama ma sallolinsa ya yi.
Mamaki ya kama ta, yaushe ya tashi har ya yi alawala ya zo yana rama sallolin. "Sannu ya jikin naka?" Ya jinjina kai yana kallonta.
Ta sake cewa "Ka gama rama sallolin ne?"
Ya girgiza mata kai, ta ce "To shikenan, bari na ƙara maka kayan marmarin, zuwa da safe sai ka fara gwada cin abinci" ya jinjina kai ta din ga ɓare masa ayaba yana ci, tana ba shi ruwa yana sha. Sai da ya yi mata nuni da ya ƙoshi.
Ta tashi ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta ji mararta ta ƙulle. Ta tsuguna ta yi fitsari kawai ta ga fitsarin haɗe da jini. Ta shi ta yi cikin tsoro, ta gyara jikinta sai dai ta kasa gane jinin Al'ada ne, ko kuma na ɓari? Tun da dai ya ce mata tana da ciki. Ta kintsa jikinta ta fito, tun da ta fito idonsa a kanta, ta ƙaraso tana cewa "Sayyid, ka ce ina da ciki, yanzu kuma na ga jini ya zo mini, period ne ko ɓari?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido, cike da son tabbatar da abin da take zargi.
Kawai ta ga yana murmushi. Cikin rashin fahimta ta ce "To ka yi mini bayani ko da hannu ne, zan gane. Dan Allah cikin ne da ni da gaske ɓari na yi? Ko kuma ba ni da komai dama?"
Ya ci gaba da murmushi yana ƙanƙance idanunsa yana kallonta, kamar ba mara lafiya ba.
Ji suka yi ana bubbuga ƙofa, ya tsuke fuska kamar ba shi ne yake murmushi ba. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Mamaki ya kama Nana yadda ya iya zuwa da duku-dukun nan.
Ya ƙaraso suka gaisa da Nana, ya kalli Hammad ya ce "Wai ya na ga daga jiya zuwa yau kamar ba kai ba. Ko dama rashin lafiyar ta ta ce?"
Hammad ya ɗauki fulon hannunsa zai kai masa duka, amma ya kauce yana dariya. Sai mamaki ya kama Nana, dama yana wasa da Mahmoudu haka? Kodayake ko da suna Nigeria, su na hira amma ba sosai ba, a nan ma tun da ta fara ganinsu tare, duk maganar da zai yi masa cikin girmamawa yake yi masa. Amma kuma yanzu ta ga yana zolayarsa.
Mahmoudu ya ce "Gimbiya ya jikin nasa, duk da daga haka ma Alhamdillah na ga alamun sauƙi a tattare da shi"
Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Dan Allah ka daina ce mini gimbiyar nan."
"Wallahi dole a ce da mijin Iya Baba Nana, babu wadda ta dace da wannan sunan a kaf Agadez idan ba ke ba. Ya jikin naka?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Imam Hammad.
A sanyaye Nana ta ce "Ai maganar ba ta dawo ba tukuna sai a hankali"
"Ikon Allah, kenan dai da gaske bayan tafiyata ya ci gaba da irin wannan ciwon, ni fa na zata tun da muka tafi bai sake yi ba. Amma Nana yaya abubuwa suka kasance ne bayan tafiyata, na san akwai tarin abubuwa marasa daɗi. Na san zuciyar musulunci ce ta sanya ki ke saurarenmu a yanzu ma, amma ki yi haƙuri. Har Nigeria aka je aka kama mu tare da su Sule. Sannan aka zo aka matsa ni da azabtarwa sai da na faɗi inda yake. Aka je gidan da ku ke gadi, ba kwa nan. Na raka su gidanku ina tsoron ya san yana da mata saboda gudun kar a cutar da ke. Ƙaninki ne ya gaya mini inda ku ke. Lokacin da aka je da ni shikaɗai muka tarar a gidan ba kya nan. Wallahi har aka ɗaukko shi sunanki kawai yake kira, yana ba zai tafi ya bar ki ba. Babu halin na faɗi cewa ya yi aure saboda na san hukuncin hakan a masarautar nan. Ga shi aka rufe ni a kurkuku da zargin ni ne na sace shi na kai shi Nigeria saboda ra'ayin kaina. Amma duk abubuwan da suka faru Nana ba su faru dan ni da Imam mu zalunce ki ba, dan Allah ki yi haƙuri"
Tamkar ya sosowa Nana abin da yake yi mata ƙaiƙayi, da dannewa kawai take yi, ta fara hawaye.
Ba Mahmoudu da ya ɗaukko maganar ba, shi kansa Imam Hammad sai ya rikice gaba ɗaya.
Mahmoudu ya ce "Dan girman Allah ki yi haƙuri, da na san maganar nan, za ta ɓata miki rai da ban ɗaukko ta ba, ki yi haƙuri"
Ta jinjina kai kawai, dan ita kanta ba ta san cikakken dalilin kukan ba, ta san dai tana buƙatar yin kukan ne ta samu afuwa a zuciyarta.
Yau Sultan ne kaɗai ya zo duba Imam, sai dai ya ji daɗin yadda ya gan shi. Ya tarar har ya ci abinci ya yi wanka ya canza kaya, sai dai ba magana.
Ya kalli Nana, ƙasan zuciyarsa yana yaba wa ƙoƙarinta da ƙarfin halinta. Ya ce "Kuma zai yi magana, na ga haryanzu bai ce komai ba"
Nana ta sunkuyar da kai ta ce "Zai yi in sha Allah, sai dai wasu lokutan ya kan jima bai ce komai ba, kafin maganar ta dawo"
Sultan ya jinjina kai cike da gamsuwa, ya ce "Muna godiya sosai da sosai. Ko akwai wani abu da ku ke buƙata?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.
"To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini. An je za a taho da mai magani ya zo ya duba shi, idan kuma abin ba zai yiwu ba zamu kai shi Asibiti" Nana ta jinjina masa kai kawai.
Inda Allah ya taimaki Nana, akwai pad a cikin kayanta, sai dai yanayin gurin babu gurin discarding pad ɗin. Cikin ikon Allah kuma ba ta zubar da jinin sosai.
****
Sultan na zaune a sashensa, ya gama ganin wasu baƙinsa, aka yi wa Asal iso, ta shiga gurinsa.
Bayan sun gaisa ta ce "Abie dama na zo ne ina son duba jikin Imam"
Sultan ya gyara zamansa ya ce "Yarinyar kirki, Imam Hammad yana cikin yanayin da ba zai so a cika kawo masa ziyara ba. Dan haka mu na son ya samu hutu ne, kafin lokacin da za a samo mai maganin da zai duba shi"
Cikin damuwa Asal ta ce "Ko sau ɗaya ne Sultan, jiya kwana na yi ina mafarkinsa, ina cikin damuwa ne"
Ya ce "Na ga alamun hakan a tattare da ke, amma ki yi haƙuri ba za ki samu ganinsa ba, zuwa lokacin da zai samu afuwa sai ki gan shi har ma ku koma gida ma"
Ba dan Asal ta so ba, haka ta haƙura ta tashi ta tafi. Tana kan hanya kiran Tafawa ya shigo wayarta.
"Yaya ake ciki?" Ya tambayeta ba tare da amsa gaisuwar da ta yi masa ba.
Ta ce "Yau ba a bani damar ganinsa ba, Sultan ya ce mini jikinsa ya yi zafi, dan haka ba zan samu ganinsa ba. Dole na jira zuwa lokacin da za a samo mai magani ya duba shi"
"Ya dai tabatta haukan yake yi ko? Lokaci ya yi da zan bankaɗa abin nan, yadda Sultan zai kunyata daga shi har ɗan nasa"
Asal ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ba hauka yake yi ba, rashin lafiya...
"Ke yi mini shiru, abin da na yanke dole haka za a yi, kar ki sake ki sake yi mini musu" Ya katse ta yana yi mata tsawa da dole ta sanya ta yin shiru.
*****
Alhaji Fatuhu ne ya kira wani abokinsa, ya ce ya zo ya kai shi gidan Yayarsa Hajiya Sa'a a motarsa, saboda yadda baya samun ta kwana biyu a waya.
Ko da yaje gidan, mai aikinta ta sanar da shi cewa ta ce ko waye ya zo, kar a sake a dame ta.
Ya kalli mai aikin ya ce "Ko wannan dokar za ta yi aiki a kan kowa, ba za ta yi a kaina ba, dan haka yi mini magana da ita"
Mai aikin ta shiga ta fito, ta ce "Na yi mata magana ba ta kula ni ba"
Ba shi da zaɓin da ya wuce ya shiga ɗakin nata da kansa. Ya tarar da ita a zaune, daga mutuwar Abba zuwa yanzu ta yi wani irin tsufa, jikinta duk ya saki. Fuskarta duk ta yi wani iri kamar ba ita ba.
A hankali ya taka da sandarsa, sai ta ƙura masa ido tama fara tunanin a ina ma ta san shi? Gaba ɗaya sai kanta ya toshe ta kasa tuna waye shi.
Sai da ya ce "Yaya Sa'a, lafiya kuwa?" Yana yin maganar, sai kuma ta tuna shi. Ta yi zuru tana tunanin ya aka yi ya samu lafiya haka har yake