Showing 48001 words to 51000 words out of 124686 words
duk magautansa, yana da tarin mabiya. Azhar yana cikin manyan kwamandojin yaƙin sarkin wancan lokacin. Kakansa ya taɓa zama Sultan, aka yi masa juyin mulki aka rufe shi a kurkuku. Aka kame 'ya'yansa aka mayar da su fursinoni ciki har da mahaifinsa lokacin shi Azhar yana ƙarami Nono yake sha. Bayan da ya tasa bai fi shekara sha biyu ba, aka kame shi, aka sanya shi cikin sojojin yaƙi. Duk zuriyarsu aka mayar da su bayi, ya tashi da wannan ciwon a ransa, ya zama gawurtaccen Sadauki da ake ji da shi, saboda ƙarfinsa. Ashe yaƙin sunƙuru yake shiryawa Sultan ɗin lokacin ya shammace shi ya kifar da shi, ya ɗare karagar mulkin. Ya kame 'ya'yansa ya kashe su, ya kashe matan Sarkin, har ma da sauran 'yan uwansa da yake tunanin za su iya tasowa su nemi su karɓi sarauta.
Ya din ga yaƙar sauran ƙasashen da ke kusa da Agadez, yana mayar da su ƙarƙashin ikonsa, ya kame baƙaƙen buzaye ya mayar da su bayi. waɗanda suka rage a 'yan uwansa wanda su ma sun tasa, yake ganin za su iya kawo masa tarnaƙi ya sanya aka gina wata irin kurku a ƙarƙashin ƙasa, duk aka zuba su a ciki.
Wannan cikin dutsen da suke ciki, Bayin zamanin Sarki Azhar ne suka rarake shi, suka gina katafariyar fadarsa, kuma a cikinta aka gina kurkun da ya zuba 'yan uwansa.
A cikin kurkukun nan, idan ka mutu a ciki zaka ruɓe ka lalace, a cikin rayayyu za ka gama ruɓewa babu mai fita da gawarka. Babu kalar azabar da ba a ganawa fursinoni a wannan kurkuku. Bayi kuma su na aikin ƙarfi gurin haƙo zinare, da aikinsa a kai wa Sarki Azhar a sarrafa a yi kayan more rayuwa ko a sayar ga maƙwabtan ƙasashen, ko kuma a yi musayarsu da wani abu mai muhimmanci.
Ya kame bokayen ƙasar gaba ɗaya, aka haƙa rami aka cinna musu wuta, a cikin wannan fadar tasa.
Boka ɗaya ya bari, wanda shi ne ya tallafa masa ya zama Sultan, wanda shi ma iyayensa na cikin amintattun kakan Azhar da ya yi sarauta, kan a yi juyin mulki a kashe su. Bokan nan ya mallaka wa Azhar gangan manyan Aljanu da suke taimaka masa gurin tafiyar da mulkinsa.
Duk wata kafa da zai iya bari da za a iya amfani da ita gurin kawo ƙarshen mulkinsa ya toshe ta. Sai da ya fara manyanta, sannan ya auri wata kyakykywar matashiyar budurwa. Ta fara haifa masa 'ya'ya maza. Allah ya ɗora masa tsananin ƙaunar yaran nan kamar ransa. Sanin a kowani lokaci, ana iya amfani da wata dama a cutar da su, ya sanya ya killace su. Ya sanya bokansa sadaukar musu da wasu Aljanu da za su din ga yi musu hidima.
Ya sanya doka a kan ko bayan ransa, babu wani wanda zai yi sarauta idan ba a cikin yaran nan ba. Duk dokar da ya kafa, babu mai iya yi masa musu. Babban abin da yake bawa al'ummarsa mamaki bai wuce yadda duk wanda ya fara ƙoƙarin ƙulla wani abu a kan ya kawar da sarkin nan ba, sai dai a wayi gari ya zama gawa.
Sultan Azhar ya shimfiɗa mulki da dokoki yadda yake so, ya tara dukiya da haraji, da kuma arzikin zinarin da Agadez take da shi. Duk da haka ya kamanta kawo ci gaba a lokacin, a wani abin talakawa sun samu sassauci, an samu ci gaba a fannin cinikayya a lokacin, sai dai laifi ƙalilan sai a kai ka kurkukun Sultan Azhar wanda har abada babu wanda zai sake ganinka, idan kuma ya so sai a gadar wa zuriyarku da wata hidima ga fada da kai da iyalinka har abada.
Sultan Azhar bai bar mulki ya mutu ba, sai da ya tsufa sosai da sosai, yaransa sun tasa sun zama matasa. Bayan ya mutu aka naɗa babban ɗansa a kan karagar mulki. Shi ma ya ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya, kuma shi bai samu tangarɗa da 'yan uwansa ba, saboda ya janyo su cikin harkar mulki.
Sai dai mahaifiyarsu ce ta je ta samu bokan mijinta, ta gaya masa kokenta a kan ba ta son kan yaranta ya rarrabu, a kan mulki, ko wani ya kashe wani.
Ya ba ta tabbacin hakan, ta hanyar yi mata surkulle daban-daban a kan yaran nata.
Kasancewar komai nufin Allah ne, da wanda ya yi addu'a, da wanda ya bi hanyar da ba daidai ba ma, yana iya amsa wa kowa idan ya so, Allah ya taimake ta ba su kashe junansu a kan Mulki ba. Shi ma ya yi tsawon rai a kan karagar mulki, sai dai Aljanun nan sun ci gaba da bibiyar zuriyar 'ya'yan sarakunan, su na ba su kariya. Bayan mutuwar wannan Sarkin da aka zo naɗa sabon Sarki, a nan aka samu dambarwa, sai da aka yi hatsaniya aka so yin ƙaramin yaƙi daga bisani aka ɗora ɗaya daga jikokin Azhar a kan Mulki wato Sultan Sadam. Har a lokacin matar Azhar tana raye haka Bokansa. Ba ta da wani abokin shawara da ya wuce wannan boka. Ta fuskanci kalubale sosai da sosai, saboda yadda magauta suka sako ta da 'ya'yanta gaba da son tarwatsa mata iyali, dan a banƙara Sarautar ta bar gidansu.
Bayan hawan jikanta karagar mulki, a lokacin Bokan nan ya mutu, ɗansa ya gaje shi. Shi ma ya samu kyakykywan kusanci da Sultan Sadam a lokacin. Bokan ya ba shi shawarar mallakawa 'yan'yansa Aljanu, domin su ƙara samun tsaro daga duk wani farmaki.
Sarki ya yi shawara da bokan, a kan yana son duk yadda za a yi, ya zamana kar sarauta ta bar gidansu, kar wani daga cikin 'yan'yan 'yan uwansa ko 'yan uwansa su yi sarauta.
Sai ya fara da kafa dokar, duk wanda ya haura shekara talatin da biyar, babu shi babu sarauta a Agadez, sai dai ka na kan mulki ka kai wannan shekarun. Kamar yadda ya zo a tarihi da kakansa, da Sultan ɗin da ya gabace shi, duk ba su kai shekaru talatin da biyar ba suka hau kan karagar mulki.
Bokan nan ya ƙera masa zobuna da azurfa kowanne yana da mallakin Aljani a jikinsa, da wannan zoben za su iya sarrafa aljanun nan yadda suke so.
Tafi a hankali bayan shuɗewar zamaninsa, abubuwa suka ci gaba da juyawa, kowane Sarkin da zamaninsa da kuma yadda yake nasa mulkin.
Sai dai Mallakar zoben nan ya zama sabon tashin hankali, dan daga bisani sai ya zamana wanda yake da zoben nan, shi ne kaɗai zai iya zama Sarki. Sai faɗa ya koma kan kowa na son ya mallaki zobe cikin 'ya'yan Sarakuna. Dan sai Zobunan suka zama gado na kowane gida, daga cikin 'ya'yan Sultan ɗin da ya sanya aka ba shi zobe.
A hankali ya zama doka, duk wanda zai zama Sultan, sai ya zamana bai kai shekaru talatin da biyar ba, kuma sai ya zamana ya mallaki wannan zoben.
Duk wanda ya mallaki zoben, yana da damar sarrafa aljanin da aka ɗora wa alhakin ɗawainiya da mamallakin wannan zobe, da dole sai ya zamana jinin zuriyar Sultan Azhar sannan zai yi masa hidima."
Hammad ya numfasa ya fara nuna mata hotunan nan da bayaninsu ya ce "Kamar yadda yake a babban kundin adana tarihin masarautar Agadez, wannan shi ne Kakan Sarki Azhar, ga mahaifinsa, shi ma ga hotonsa, ga 'ya'yansa ga waɗanda suka yi sarauta a cikin 'ya'yansa.
Wannan ita ce Gimbiya Saira, ita ce matar Sultan Azhar, da tun da ya mutu zuriyarsa ce kawai suke Mulkin Agadez ba a sake samun wanda ya ƙwaci mulki daga hannun zuriyarsa ba.
Nana ta tsare shi da ido, har sai da ya tsargu ya ce "Lafiya kuwa?"
"Sayyid, kana nufin ka na ta'amalli da Aljanu kenan, ta hanyar yin amfani da wannan zoben?"
"Meyasa za ki yi tsalle ki tafi ƙarshen labarin? Ki jira na kai da kaina mana"
AREWABOOKS
Ta ɗan nutsu tana sunkuyar da kai.
Sai dai ya yi shiru bai ci gaba ba. "Yaya ka yi shiru kuma?"
"Ba na son na ci gaba ki yanke mini hukunci ne haka sama ta ka"
"Ka yi haƙuri ba zan yi haka ba, in sha Allah na yi shiru har ka kammala"
Ya kamo hannunta, suka fito daga cikin wannan ɗakin, ya nuna mata wani ɗakin ya ce "Wannan ɗakin, shi ne inda gawarwakin galibin tsofaffin sarakunan Agadez suke, na kusa da shi kuma ɗakin da a kan binne manyan masu faɗa a ji. Ba zan buɗe miki ba dan za ki iya tsorata.
Ya buɗe wani ɗakin ya ce "Nan ɗakin kuma, shi ne ɗakin da ake sarrafa zinari, a cikin fadar Sultan yake. Duk nacin mutum bai isa ya saci zinare ya fita da shi ba, idan kuwa aka kama mutum a kurkukun nan zai mutu.
Wannan ɗakin kuma, a ciki duk wani tarihin yaƙe-yaƙen da Agadez ta yi yake. A nan ake adana duk wani kayan Sultan muhimmai, irin su takalmi, kayan yaƙi takobi da sauransu. Shi kuma wancan ɗakin, wasu daga cikin sassan ƙashi. jikin manyan masu laifukan da aka kashe ne, da Sarakunan da aka yi wa juyin mulki aka kashe su.
Zamani ya ci gaba da jujjuya, hasken addinin Musulunci ya fara bayyana, duk da nisan da Sarakunan ƙasar suka yi ba sa jin kira, dan hatta turawan mulkin mallaka ba su yadda sun kassara musu sarauta da tattalin arziki ba.
Tasirin addinin musulunci ya sanya aka fara rage aikata wasu abubuwan, amma ba a daina wasu ba. Tsaface-tsaface da ta'amalli da Aljanu ba a daina su ba, ga su mutane masu tsatstsauran ra'ayi a kan al'adunsu, da tsafi. Domin ma'abota sarauta sun yarda da cewa, duk wanda ya zauna zai ga zama, mussaman yadda zuriya daban-daban suke farautar kujerar ko ta halin ƙaƙa duk da tushen ɗaya ne, amma kowa burinsa ya zamana Mulkin a gidansu yake.
Sai dai dokar Sultan Sadam tana nan, ta sai wanda bai kai shekaru talatin da biyar ba ne zai yi mulki, sannan sai wanda yake da zoben nan shi ne zai yi mulki.
Sai dai a baya-baya, aka samu ɓarkewar faɗa a tsakanin zuriyar Azhar, har aka yi ƙaramin yaƙi, suka zubar wa da juna jini, abin da ba a taɓa yi ba a tarihin masarautar. Abin a ya girgiza al'ummar ƙasar mussaman ma'abota sarauta, har suka fara tsoron ko ƙarshen masarautar ne ya zo, aka samu rikicin da ta kai ga 'yan uwan junan da tun zamanin iyaye da kakanni ba su taɓa samun rabuwar kai da ta kai ga amfani da makami ba sai a wannan karon.
A lokacin zuwan ilimin addini da na zamani, da kuma wannan hatsaniya da ta faru, sai aka yi wa dokokin masarautar Agadez kwaskwarima. Domin samar da zaman lafiya da ƙara ƙarfafa masarautar sai aka ce sai wanda yake da wasu nagarta da wasu abubuwa masu muhimmanci shi ne zai zamana yana riƙe da zoben a kowanne gida da suka gaji zobunan. Sannan aka ƙara yawan zobunan suka zama uku, kowane gida su na da anihin zoben tambari wanda shi ne mai ɗauke da sihiri da aljanu sai kuma sauran biyu, sannan da abin hannun na tagulla. A zamanin Sultan Ansar, aka yi duk wannan sauye-sauyen, ya ƙirƙiro ƙaramar majalisar masu ɗauke da wannan zobunan, yadda za a din ga shigar da su cikin sha'anin mulki, da koya musu yadda mulki yake. Aka yi yarjejeniya a kan iya wannan masu zoben ne za su iya zama Sultan, sannan a cikin su duk wanda ya haura shekara talatin da biyar za a karɓi zoben daga hannunsa a nemi wanda ya cancanta a ba shi.
A lokacin aka ce duk wanda zai mallaki zoben, domin zama ɗaya daga Imam, kamar yadda Sultan Ansar ya yi musu laƙabi da shi, dole ya zamana yana da ilimin addini, ya haddace kaso saba'in na tarihin Agadez, yana jin wasu yarurrukan bayan yaren su na uwa, da kuma hausa. Domin ya zamana mutanen Agadez su na jin Hausa sosai, saboda yanayin cinikayya da ke tsakaninsu.
Sai dai har a lokacin akwai baƙaƙen al'adunsu da ba su canza ba, kuma ba a yi wa kwaskwarima ba, ba a daina azabtar da mutane a kurkukun nan ba. Sannan su na ƙyamar ɓakar fata, ta kowace fuska sun daƙile baƙaƙen buzaye, sun bautar da su, sun hana su motsi, dan kar su yi wani yinƙuri su yi musu juyin mulki. Ko a cikin kuyangi, ba a yarda basarake ya yi amfani da baƙar buzuwa ba, saboda kar su haɗa zuriya da su, su sanya ran za su samu 'yanci wataran. Kuma baƙaƙen bayi sun taka muhimmiyar rawa gurin gina daular Agadez, da haɓaka tattalin arzikinta, saboda juriyarsu da aiki tuƙuru. Sun daga lokacin da suka yi 'yanci, za su iya ajiue aikace-aikacen, kuma su na tsoron su ce za su rama bautar da su da aka yi tun zamanin iyaye da kakanni alhalin kakannin kakanninsu, da su aka kafa Daular kuma sun taɓa mulki.
Hukunci na iya zama na kora, zaman kurkuku koma kisa, ga duk basaraken da aka kama, da aure ko mu'amala da baƙar buzuwa. Haka duk cinikayyar da suke yi da sauran ƙabilu, ba su yadda auratayya ta haɗa su mussaman da baƙar fata, nasu ma ba su aura ba balle na waje. Sannan yana daga sharuɗɗan da bokaye suka kafa musu, muddin suka yi auratayya da baƙaƙe, ana iya kawo ƙarshen mulkinsu, kuma baƙaƙe ka iya yin galaba a kansu, su ƙwace sarautar baki ɗaya.
Zamanin Sultan Ansar bayan tabattar da waɗanann dokoki, shi ma yana da zobuna da abin hannun tagulla na waɗanda za su zama Imam.
Lokacin da aka tabbatar da waɗannan dokokin, aka yi musu kwaskwarima, Sultan Ansar yana da tarin 'ya'ya, yana daga cikin dalilan da ya sanya shi ƙara inganta tare da gyara wasu dokokin saboda yana kwaɗayin ɗansa Jalaludeen ya zama Sultan a bayansa, saboda kusan duk abin da aka lissafo yana da su. Kuma ya lura akwai zalamar son Mulkin sosai a wasu daga cikin 'ya'yansa, mussaman babban ɗansa Saifuddeen.
'Ya'yan suka yi ta zuba ido, domin su ga wa zai ba wa zobunan nan, amma ya ƙi bawa kowa, sai daga bisani ya damƙa wa Jalaludeen, ya nemi sauran gidajen da suke da zobunan, su ba wa waɗanda suka zaɓa, a kafa majalisar Imam. Hankalin Saifuddeen da mahaifiyarsa da sauran 'yan uwansa ya yi mummunan tashi, ganin ya ɗauki zobunan tambari ya ba wa Jalaludeen, duk da ga yayyensa.
Sai dai maimakon a samu Imam shida, sai aka samu biyar aka rasa inda sauran zobunan suke.
Hankalin Saifudeen ya ƙi kwanciya, ya tashi hankalinsa da shi da mahaifiyarsa da wanda suke ɗaki ɗaya, a kan lallai su san yadda za su yi, ko dai a karɓe zoben nan daga hannun Jalaludeen, ko kuma a kashe shi. Sai dai suka fahimci karɓe zoben nan, ba abu ne da zai yiwu ba, saboda ya riga ya mallaki Aljanun da aka wakilta tasrifi da zoben.
Duk wani Imam da yake Agadez, askin gashin kai ya haramta a gare shi, haka zalika barin gashin kansa ya haramta. Sannan babu su babu baƙaƙen bayi, a matsayin kuyangi. Sannan akwai nau'in abincin da ba za su ci ba.
Bayan majalisar Imam ta kafu, da yawa sauran zuriyar, sun shiga taradaddin ina ɗaya zoben ya shiga?.
A dole Saifudeen ya ɓoye hassadar da yake yi wa ɗan uwan nasa, ya ci gaba da ƙoƙarin ganin bayansa ta ƙarƙashin ƙasa. Ya din ga bin bokaye, har da na wata ƙasar a kan a haukata ɗan uwan nasa, ko ma a kashe shi, saboda shi ne ya fi dacewa da matsayin da yake kai, amma abu ya ci tura.
Wataran Sultan Ansar ya kira Imam Jalaludeen ya ce masa "Ka Imam Jalaludeen, kana daga cikin manyan dilalan da ya sanya, na dage a kan canza wasu daga cikin dokokin Agadez, wanda za su iya taɓuwa. Iyaye da kakanninmu sun tafka kura-kurai, kura-kuran da yakamata a ce mun yi wasu sauye-sauyen da yakamata al'umma su samu sassauci. Sai dai kai nake ganin zaka iya kamantawa wataƙila ko bayan raina. Ragowar zoben da ake nema, yana gurina, idan Allah ya yi ka zama Sultan a Agadez kar ka danƙa shi ga kowa, sai mafi cancanta. Na san da duk farmakin da ake kawo maka saboda damar da ka samu, amma ka yi haƙuri ka daure. Sannan zan ci gaba da sanya wa a yi maka duk wani abu na kariya da yakamata. Zan sanya a ƙara sadaukar maka da wasu daga cikin manyan hadiman aljanuna, domin ka samu cikakkiyar kariya. A lokacin an yi ginin zamani, na gidan Sultan, an baro tsohuwar fada ta cikin dutse da ake gudanar da mulki a cikinta.
A zamanin Sultan Ansar, ya samu zaɓaɓɓu, aka gina ɗakuna-ɗakuna, a cikin sabuwar masarautar, da hanyoyin tserewa daga cikin gidan, idan an samu farmaki.
Saifuddeen dai bai haƙura ba, ya haɗa kai da matarsa, ya aura wa ƙanin nasa ɗaya daga cikin ƙannen matarsa Gimbiya Bilkisu. Saifuddeen ya din ga shiga yana fita, dan kar Jalaludeen ya zama Sultan, ya haɗa kai da wasu daga cikin Imam na majalisar lokacin, da ziga su kan cewar lallai su dage, su yi ƙoƙari su karɓi sauratarsu, mulki ya dawo hannunsu. Masu kwaɗayin mulki suka din ga yadda da zigarsa, wasu kuma suka din ga yi masa kallon ya za a yi ya nemi sarauta ta bar gidansu. Ya din ga ziga su ɗaya bayan ɗaya, ba tare da wani ya san yana ziga wani ba.
Sannan ya koma ya din ga ziga sauran 'yan uwansa, a kan kar su kuskura su yarda su bari, Jalaludeen ya zama Sultan, alhalin duk ga su suna gaba da shi.
A kwana a tashi, Sultan Ansar ya koma ga mahaliccinsa, babu ciwo ba komai, ya yi sallar magariba, ya yanke jiki ya faɗi sai gawa.
An shiga cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, aka yi masa sutura, sai dai manyan 'yan majalisar Sultan na lokacin, ba su bari an wayi gari ba, suka damƙawa Imam Jalaludeen tagullar da kambun Sarautar Agadez, kamar yadda ya bar wasiyya. Sai dai a tsakaninsu ma 'yan majalissar sai da aka so a samu rarrabuwar kai, aka nemi a yi ƙaramin yaƙi a cikin daren.
Babban na kusa da Sultan, ya sanya aka je aka ɗaukko masa Imam Jalaludeen, wanda ya san tun da Sultan ya mutu a kowane lokaci za a iya kashe shi. Abin da ba