Showing 36001 words to 39000 words out of 124686 words
iya cewa ga adadin abin da yake ji a kanta ba.
A ransa ya ce "Ba komai ki yi yadda ki ke so, kin cancanta" A zahiri kuma sai ya sauka daga kan gadon, ya nufi hanyar fita.
A ɗan ruɗe ta sauka daga kan gadon ita ma tana faɗin "Ina zaka je?"
Bai yi magana ba ya ci gaba da tafiya, bayansa ta biyo da sauri tana faɗin "Sayyid ba ka da cikakkiyar lafiya fa, ina za ka je?"
Ya rufa ta a cikin ɗakin, ya tafi. Ta jijjiga ƙofar amma ta ji ƙofar a rufe. Ta koma ta nemi guri ta zauna jikinta a sanyaye tana tunanin, kar wani abin ya same shi.
*****
Tun da ɗan da ke cikin Shukura ya faɗo Duniya, ta fara ganin duhu, saboda wani irin bleeding da ta din ga yi. Matar da ta kawo ta Asibiti, gaba ɗaya a ruɗe take, saboda tun da ta haɗu da ita ba ta yi magana ba. Ga shi ta kawo ta Asibiti har ta haihu ba ta yi magana ba.
Likitan ya ba ta shawarar ta kira jami'an tsaro ta sanar musu, saboda kar a je wani abu ya faru da ita.
*****
Doctor Sharif kuwa tun da ya farfaɗo ya tashi da shanyewar ɓarin jiki, saboda tashin hankalin yadda ya ci karo da gawar 'yarsa cike da tozarci.
Duk da maganarsa ba ta fita sosai, amma ƙoƙari yake yi ya tambayi ina matarsa, ya jikinta. Amma aka ce masa tana samun sauƙi, sai dai abin da bai sani ba shi ne, bayan tafiyarsa gurin 'yan sanda Allah ya yi mata cikawa.
*****
Matawalle ne tare da Sultan suke tattaunawa, fuskar Sultan fal damuwa yake faɗin "Na rasa abin da na yi wa Tafawa a rayuwa, da yake nuna wa jinina wannan ƙiyayyar haka, abin da ba zan taɓa yi masa ba"
Matawalle ya ce "Ai dama ba halinku ɗaya ba sam, ka kwantar da hankalinka mu bi a sannu, in sha Allah zamu samo mafita. Amma kwana biyu yaya ka ke ganin jikin Imam ɗin?"
Ya ce "Jikinsa da sauƙi, ana samun ci gaba, sai dai ba ya magana sam. Jiya da yau nima ban shiga ba, ba na son yawan zarya da nake yi musu, kamar yarinyar a tsorace take da mu. Amma na yi mamakin yadda ta iya sarrafa shi ya dawo hayyacinsa."
Matawalle ya ce "Allah ya baka nasara, ni fa ina jin tsoron a sake samun matsala"
Sultan ya ce "Matsalar me fa?"
"Kar a je wani abu ya faru, kana ganin yadda muke fama, ake tunanin yadda za mu ɓullo da lamarin bayyanawa Duniya ɗan gurin Imam Hammad da bayanin da za mu yi a gamsu. Yanzu kuma mun bar shi ya keɓe da ita idan aka kuma samun matsala fa?"
Sultan ya ɗan yi murmushi ya ce "Sai mu karɓi ƙaddara, mu jira ta sake haihuwa. Amma ba na tunanin wani abu ma zai iya faruwa, tun da ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Kuma mai maganin da aka je ɗaukkowa ne ya ɗan yi balaguro, yana ƙarasa warwarewa za a raba su daga ɗakin, mu ga me ya kamata a yi mata"
Matawalle ya ce "Haka ne, Ubangiji Allah ya ba shi ingantacciyar lafiya.
Sultan ya amsa da "Amin"
Hammad bai sake dawowa ba sai bayan sallar asuba. Da ya shigo ma bai kai ko kalli inda Nana take ba.
"Ina kwana" Nana ta gaishe shi tana satar kallon sa, amma ya yi mata shiru bai amsa ba.
Gaba ɗaya sai ta ji babu daɗi shirun da ya yi mata. Ya je gaban mudubi yana gyara gashinsa, ta ƙarasa gaban mudubin ta ce "Kawo na gyara maka?"
Ya harare ta, ya share ta ya ci gaba da taje gashinsa.
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, ya ajiye comb ɗin, ya kalli Nana ta je ta ɗaukki hijjabinta ta saka. Ya ƙarasa ya buɗe ƙofar.
Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci.
Ya gaida Hammad, ya ɗaga masa hannu. Nana ta gaishe shi ya ce "Ni yakamata na din ga gaishe ki, uwar gijiyarmu. Ya mai jiki?"
Nana ta ce "Asma'un dai. Mai jiki da sauƙi Alhamdillah ina Nene?"
"Tana nan ƙalau, ga saƙon ki nan in ji ta, ina ta lallaɓata ta dawo Agadez, na ajiye ta a gidana amma ta ƙi" Ya yi maganar yana nuna wa Nana flask.
Nana ta ce "Dan Allah idan ka koma idan za a bari na ganta, ka ce dan Allah ta taimaka ta zo na ganta, Kodayake da an sallame ni daga nan, gurinta zan je ta ce za ta raka ni gid.. sai dai sauran maganar ba ta fito ba saboda harar da Sayyid ya yi mata.
Mahmoudu ma ya kawar da maganar, ya koma yi wa Hammad magana da yarensu. Hammad ya yi shiru yana saurarensa. Ba ta san me suke tattaunawa ba, amma da alama abin da suke tattaunawar ya ɓata masa rai. Ya tashi ya ɗaukko biro da takarda ya fara rubutu.
Sai gaban Nana ya faɗi, zuciyarta ta fara raya mata ko takardar saki yake rubuta mata. Ya gama rubutunsa ya miƙa wa Mahmoudu, suka fita tare.
Ta yi ajiyar zuciya ta buɗe flask ɗin da Nene ta bayar a kawo mata. Nana ta yi murmushi ganin naman kaza cikin flask ɗin, ta ce "Nene so take sai na fashe saboda girma"
Ba ta sake ganin Hammad ba, sai da daddare, da yaje ya yi wanka, ya canza kaya ya nufi hanyar fita. Nana ta ce "Sayyid wai yau ma nikaɗai zan kwana a ɗakin nan? Amma ka san ɗakin nan tsorata ni ake yi"
Ya ce "Me zan zauna na yi miki, zan iya ɓata miki rai idan na ci gaba da zama a ɗakin nan, gurin matata zan tafi" Ya yi mata maganar a gadarance. Ƙifta ido kawai ta yi idanunta suka yi jawur. Sai a lokacin ya yi dana sanin abin da ya gaya mata, biyo bayan tuna matsanancin kishi da take da shi.
Ji yayi kamar ya bata haƙuri, ya koma ya zauna, amma ya yi jarumta ya fice. Sai dai tun da ya fita abin duniya ya dame shi. Tausayin Nana ya mamaye shi, ya sa dole ta yi kishinda Asal kuma ta ji haushin sa, mussaman yadda Asal ɗin ta din ga yi mata isa da iko, da nuna mata ita ba komai ba ce ba.
Tun da ya fita Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, wani abu mai raɗaɗin gaske, ya soke mata a ƙirjinta zuwa wuyanta. Duk da ta saba ganinsu guri ɗaya, tana kishin hakan amma na yau ya yi mata ciwo nesa ba kusa ba.
Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ta, sai dai wannan mummunan mafarkin, na halittun nan, suka din ga bin ta, gaba ɗaya baccin ya gaza yi mata daɗi.
Kafin Asuba ta farka da wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon da kai.
A inda ta yi salla ta kifa kanta ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa, ga jikinta babu daɗi.
Ji ta yi an danne ta, ta buɗe idonta ta ga Muhsin ya ƙanƙame ta. Tashi ta yi zaune a rikice tana faɗin "Muhsin ɗina"
Ya ƙanƙameta, ita ma ta rungume shi tana wani irin murmushi tamkar ta mayar da shi cikinta.
Ta ɗaga kai ta ga Hammad a gefe, yana karyawa. Muhsin ya tashi daga jikinta, ya je gaban Imam ya ɗaukko dabino, ya dawo ya saka mata a baki, ya sake komawa ya ɗaukko ya kawo mata. Ta saka hannu ta karɓa tana jin wani irin tasirin alaƙa ta tsakanin uwa da ɗa.
Sayyid ya ɗauki Muhsin, ya ajiye shi a kusa da shi, yana ba shi Abincin. Ya waiwaya ya kalli Nana ya ce "Naaa" ya din ga nuna mata kusa da shi, wai ta zo ta zauna ta ci.
Sam Hammad bai nuna ya san tana gurin ba. Amma duk da haka yanayin ya yi mata daɗi mara misatuwa, yau ga mijinta ga ɗanta a guri ɗaya. Kuma alamu suka nuna mata, a zaman da Muhsin ya yi da su, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu. Dan duk ƙyuyar Muhsin ba ta ga alamar yana yi masa ba.
Ƙarshe ta yi shiru tana kallonsu, ya shirya cikin jallabiya fara ƙal, ya shirya Muhsin da kansa, sai dai ga mamakinta ba ta ga ya naɗa rawani ba, ya saɓa ɗansa a kafaɗarsa ya yi waje. Ƙasan zuciyarsa kuwa raya masa ya din ga yi ya rungume ta, ya ji damuwarta, yana da abubuwan gaya mata da yawa, amma ya daure ya share ta.
Sultan yana zaune, yana saka hannu a wasu takardu, tare da Tafawa da Sardauna. Aka shigo aka nema wa Tafawa iso. Gaba ɗaya suka shiga mamakin me ya kawo shi a daidai wannan lokacin.
Bayan sun gaisa ya ce "Na samu takardar kiran da ka yi mini ne, shi ne na amsa kiran.
Cikin mamaki Sultan ɗin ya ce "Ni ɗin kuma?"
Tafawa ya ce "Amma saƙonna samu har gida aka kai mini takarda"
Sultan ya ce "Ai ni ba zan aika maka da takarda dan ina neman ka ba, amma da mamaki"
Tafawa ya ce "Ikon Allah, to waye ya aikata hakan?"
"Ni ne" Imam Hammad ya amsa ya na ƙarasa shigowa gurin.
Ayshercool
87
LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAN KI KARANTA 08081012143
Ƙwalalo manyan idanunsa Tafawa ya yi, ganin Imam Hammad ya fito gashinsa a buɗe, saboda hakan abu ne mai girman gaske, mussaman ga shugaba kamarsa,hakan kuskure ne.
Ba wannan ya fi kaɗa shi ba ma ɗan ƙaramin yaron da yake hannunsa ne ya fi tafiya da tunaninsa. Ya girgiza matuƙa gaya da ganin yaron.
Su Sultan ma sak suka yi, su na mamakin yaushe ya Hammad ya samu sauƙi har haka, har bakinsa ya yi wannan buɗewar? Ga uwa uba wautar da ya yi na zuwa da Muhsin ba tare da an gama shirya yadda za a kare hakan ba.
Imam Hammad ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa ya gaishe su, bai damu da jiran su amsa ba. Ya dubi Tafawa ya ce "Mai girma Tafawa, ina fatan ban yi laifi ba, kasancewar a ƙarshen wasiƙata, ban sanar da cewa ni nake nemanka ba, ba Sultan ba. Na zaɓi saka gurin haɗuwar ya zama nan ne, saboda sai ya fi dacewa da abubuwan da suke bakina.
Kun aika da takarda Majalisar Sultan, sannan an aika da wata majalissar Imams. Duk da kwana biyu ba na samun sukunin zaman majalisar. Na gayyace ka nan ne domin warware maka duk wani abu da ka ke son sani, ba kai ba duk sauran wanda suke son sani ma. Ba sai mun ci gaba da wahalar da shari'a ba. Kamar yadda na gaya maka wannan shi ne ɗa na Muhsin, ina da ɗa, kamar yadda na din ga jaddada maka, ka din ga ganin kamar shaci faɗi ne, wanda nan gaba kaɗan zan bayyana wacece mahaifiyarsa ba na son mu zurfafa a kan wannan bangaren dan abu ne da ya shafe ni. Abu na gaba kuma ana cewa ba ni da cikakkiyar lafiya ba zan ci gaba da gudanar da shugabanci ba. Haka ne, yakamata na matsa gefe na samu cikakken hutu da nutsuwa kamar yadda ku ka buƙata. Sannan kuma babu zobena na tambari a hannuna. Ina mai farincikin sanar da kai cewa daga yau, na sauka daga kan muƙamina na shugabancin majalisar Imam. Ba iya wannan ba ina san a cire ni daga cikin Imam da ake sanya ran a cikinmu ne za mu gaji sarautar Sultan shi ya sanya na fito maka haka babu rawani. Ka na damar maye gurbina na Imam ko ma shugabancin majalisar Imam ɗin baki ɗaya, ko kuma ka ɗora Imam Asadullah na muddin hakan zai sama maka farinciki da kwanciyar hankali. Ka bar mu mu huta da ni da mahaifina. A ƙarshe ina ƙara gabatar maka da ma petit Hammad wato Imam Muhammad H.J Agadez wato Muhsin" Ya yi maganar yana murmushi tare da shafa kan Muhsin.
Ya sake kallonsa ya ce "Idan babu sauran magana, za ka iya tafiya, ina muma fatan ka fahimci abubuwan da suka shige maka duhu game da ni"
Tafawa mutuwar zaune ya yi, tare da bin Hammad da ido, jin sun Sardauna yi shiru kuma babu wanda ya musa, ko ƙaryata abin da Hammad ya faɗa ya sanya shi tabattar da abubuwan da Hammad ya faɗa gaskiya ne.
Sultan da tuni gumi ya jiƙe shi ya ce "Ina fatan ka ji daɗi, da ka kai shi bangon da ka sanya ya fito ya tabattar maka da abin da ka ke son tabattarwa? Ina ga shikenan za ka iya tafiya."
Tafawa bai iya furta uffan ba, jikinsa a matuƙar sanyaye, ya tashi yana jan ƙafarsa, da yake jin kamar ba a jikinsa take ba, da kyar ya fice.
Gaba ɗaya suka yo kan Imam Hammad da faɗa kamar za su dake shi. Hammad ya ce "Ina neman afuwarku, a kan abin da na aikata ba tare da izninku ba. Amma har abada ƙarya fure take yi, ba ta 'ya'ya, ba zamu dauwwama ɓoye wa duniya abin da komai daren daɗewa sai ya bayyana ba. Ba zan iya ci gaba da jure kullum lokacinku ya tafi a kan bani kariya ba, duk na san na aikata laifi, zan tsaya a kan laifina na karɓi duk hukuncin da ya dace".
Sardauna ya ce "Kuma saboda shirme sai ka ce ka sauka daga kan kujerar Imam? Dama kai ka ɗora kanka?"
Suka din ga yi masa faɗa, shi kuwa ko a jikinsa, dan gara ya ɓallo duk abin da zai ɓallo a san abin yi, duk abin da za a yi masa a yi masa, ya san yadda zai da matarsa da ɗansa.
*****
Kamar yadda Alhaji Fatuhu ya umarci Fadila,ta shirya tare da babbar 'yarsaJannat, suka tafi duba Hajiya Sa'a. Sai dai Hajiya Suwaiba ba ta je ba, saboda ba ta jin daɗi.
Ko da suka je, ƙin fitowa falo ta yi, sai su ne suka shiga cikin bedroom ɗin ta, suka same ta. Sai dai kamar yadda Alhaji Fatuhu ya ba ta labari, haka ta ga tsufan Hajiya Sa'a ya fito. Kamar ba ita ce 'yar ƙwalisar nan mai ado da kwalliya ba.
Suka gaishe ta, amma sai dai ta sake shiga halin ɗimuwa ta kasa gane su, kawai dai ta amsa musu.
Fadila ta sauke Muhsin da yake bayanta, tana ba shi ruwa saboda daga bacci ya tashi. Hajiya Sa'a ta ƙura masa ido, har sai da ya lafe a jikin mahaifiyarsa yana kawar da kansa daga kallon Hajiya Sa'a.
Hajiya Sa'a ta ce "Da tuni wannan tsinannen ɗan ne zai mutu, amma nawa ɗan ya mutu, Allah ya isa ban yafe ba, kuma shi ma in Allah ya yarda sai ya mutu"
Cikin mamaki da rashin fahimta Fadila da Jannat suke kallonta.
Fadila ta ce "Tsinanne kuma Yaya Sa'a, me ya yi miki? Ba ki gane shi ba ne? Muhsin ne ɗan gurin ƙaninki Alhaji Fatuhu"
A fusace ta ce "Shi ɗin fa, Allah ya tsine masa Albarka, shi ma Fatuhun Allah ya tsine masa Allah ya sa ya mutu. Da tuni Abba yana raye, amma bai sha alawar ba sai Abba ya sha ya mutu. Ke ma Allah ya tsine miki shashasha"
Waro ido suka yi gaba ɗaya, cike da tsoro.
Jannah ta ce "Kin ga Anty, tashi mu tafi na fara jin tsoro, kar ta fara kai mana duka"
Babu shiri suka miƙe, Fadila ta goya ɗanta suka bar gidan, sai tsine musu take yi, tana faɗar wasu abubuwa da ba su gane kan abin da take nufi ba.
*****
Asal ta sha mamaki, ganin mahaifinta a gidanta wanda idan ba da wani dalili ba baya zuwa, sai dai yanayin fuskarsa ya sanya gabanta faɗuwa.
Kan ta yi magana ya ce "Hammad da gaske yake yana da ɗa, domin na ga ɗan nasa yau ido da ido, aurenki da shi bai amfana mini komai ba gurin cikar muradina ba, kaiconki da gaza cika wa mahaifinki burinsa"
A burkice ta ce "Wane Hammad ɗin, yana tsare babu lafiya bai san waye a kansa ba ma?"
Cikin tsawa ya ce "Zan yi miki ƙarya ne? Daga cikin gidan Sultan nake, lafiyarsa ƙalau sai dai idan raina miki hankali suke yi, na yi magana da shi, kuma har ɗan nasa na gani da idanuna"
Hannu Asal ta ɗora a ka, tana lissafa maganganun da mahaifinta yake gaya mata. Da ta rasa mene ne gaskiyarsu.
Imam Hammad kuwa, tun da ya shiga ɗakin, ya hango Nana ta yi ruf da ciki a kan gadon, ga sautin sheshsheƙar kukanta na tashi. Ya rufe ƙofar ya ƙarasa gaban gadon da hanzari.
Ya ɗora hannunsa a bayanta ya ce "Ma vie" Tashi ta yi zaune idanunta jawur, ta ce "Ina Muhsin ɗin?"
"Na mayar da shi inda yake. Ya na ji kamar jikinki da zafi ne? Meyafaru ma ki ke kuka? Wani ya shigo ne, ko an yi miki wani abu ban sani ba?"
"Ni ka mayar da ni gurin Nene, tun da ka samu lafiya"
"Yaushe na samu lafiyar? Ni ban samu lafiya ba tukuna, ba ki san me nake ji a jikin nan nawa ba" Yayi maganar yana ci gaba da shafa ta a hankali.
Cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya rayuwata, jikinki da zafi. Ga shi haushina ki ke ji kin ƙi yadda da ni, balle na ce ko Muhsin ne zai samu ƙani"
Nana ta ci gaba da kuka, da ita kanta ta kasa tantance kukan me take yi. Ya yi murmushi ya ce "Yanzu kishin ne ya saka miki zazzaɓi ma viee?" Ture hannunsa ta yi tana kuka. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "Da wasa nake miki, ban je ko ina ba fa da na bar ɗakin nan, a ƙofar ɗakin nan nake kwana, saboda idan mu na tare guri ɗaya akwai matsala ne. Ba kuma na son ɓata miki rai"
Kwanciya ta yi sosai a jikinsa, ta saka hannu ta zagaye bayansa ita ma, ta yi shiru tana mayar da numfashi. Ya din ga murmushi yana shafa bayanta ya ce "Ki yi haƙuri, ba na ƙaunar na din ga aikata duk wani abu da zai sanya mini ke fushi da damuwa. Je vous aime ina son ki rayuwata".
Nana ta ɗago tana kallon ƙwayar idonsa, idanunta fal hawaye.
Ya jinjina kai ya ce "Da gaske nake Asmy, ina yi miki so mai tsananin gaske. A jinina nake jinki ba iya zuciyata ba"
"Sayyid"
"Na'am rayuwata"
"Kar na sakankance da kai, 'yan uwanka su ce ba zaka zauna da ni ba, ban san ya zan yi ba Sayyid. Ba gudunka nake dan na daina sonka ba, tsoro nake