Showing 18001 words to 21000 words out of 124686 words

Chapter 7 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

55

wane irin yanayi ma take ji.

Ya kalli Nana ya ce "Ki nutsu mana, kar ki ji tsoro, dan Allah kar ki yi wani abu da zai rusa mana rayuwa, kar haushina da ki ke ji, ya sanya ki makance, ki yanke mana hukuncin da zai cutar da rayuwarmu" Nana dai ta gaza ko ƙwaƙƙwaran motsi.

Ya ja hannun Nana, suka ƙarasa tsakiyar ɗakin suka zauna. Duk suka zubo musu ido.

Sardauna ya yi wa Nana alama da ta cire niƙabinta. Ta saka hannu ta cire tana sunkuyar da kai.

Abdou matawalle ya ce "Wannan kamar na taɓa ganinki ko?" Nana ta sunkuyar da kai.

Sardauna ya dube ta ya ce "Ya sunanki?"

"Nana Asma'u" Ta yi maganar kanta a sunkuye.

"Daga ina ki ke?"

Ta ce "Nigeria"

"Kin san wannan?" Ya yi maganar yana nuna mata Imam,Nana ta ɗaga kai ta kalli Imam, ta kalli Sardauna, ta sunkuyar da kai.

Matawalle ya ce "Ki yi magana mana, kin san shi?"

AREWABOOKS

Nana ta kalle shi, ya kalle ta, ya tsare ta da idanunsa, yana jiran ya ji me za ta ce.

Abdou matawalle ya ce "Mu za ki kalla ki yi wa bayani. Ke ba ke muka gani cikin waɗanda suka kawo abinci ranar da aka yi taro ba?"
Ta jinjina kai alamar eh.

"To kin san shi ne dama?" Ya sake jefo mata tambayar.

Ta jinjina kai. Sardauna ya ce "Ki buɗe baki ki yi magana mana, ki daina amsa mana da kai".

"Eh na san shi"

"Waye shi a gurinki?"

Ta yi shiru tana nazarin amsar da za ta bayar, kar ta zama ta kwafsa su hana ta ɗan ta. Cike da karaya ya sake kallon Nana ya ce "Ma viee, talk ki yi magana mana"

"Ni sai na ga Muhsin zan yi magana, dan Allah ka fara nuna mini ɗa na"

Ya ce "To shikenan"

Ya ce "Ina neman alfarma, zan saka a kawo mata Muhsin, za ta yi magana"

Matawalle ya ce "Wane irin abu ne wannan? Ta san a gaban su wa take kuwa?"

Sardaunan Agadez ya ce "Bari Matawalle, a saka a kawo shi, mu ji me za ta ce"

Sardauna ya ciro wayarsa yana ɗan taɓawa, yana satar kallon Nana.

Sultan kuwa rasa abin yi ya yi, ya tuna fuskarta a gurin taron cin abinci da aka yi, ya so ya bibiyi me ya kawo baƙuwa wannan gurin, amma abubuwa suka sha kansa.
Wani irin gumi ne yake tsatstsafo masa bayan tuna irin taɓargazar da Hammad ya aikata, ka iya janyowa. Babban abin da ya ƙara sanya masa fargaba, shi ne abin da yake iya gani daga idanun Hammad a kan yarinyar. Ko a yanzu ya tattara hankalinsa a kanta, ta sunkuyar da kai sai zubar da hawaye take, da alama ma tamkar ya manta da zamansu a gurin.

Wata hadima ce ta shigo, hannunta ɗauke da Muhsin. Yana ganin Nana, ya yi wani irin zillo daga jikin hadimar, yana wata irin ƙara yana cewa "Naaa" kamar yadda yake kiranta, Nene  kuma ya ce mata umma"

Nana ta yi wata irin zabura ta nufe shi da gudu ta ɗauke shi, ta ƙanƙame shi a jikinta, tana zubar da hawaye cikin damuwa da kewar tilon ɗan nata. Shi na Muhsin ɗin, ƙanƙameta ya yi ya fashe da kuka.

Jikin Sayyid ya yi sanyi sosai, ya din ga jin abin da ya aikata bai kyauta ba, kamar ya shiga hakkinsu da yawa, amma babu yadda ya iya ne, hakan ne kawai masalaha a garesu baki ɗaya.

Sultan ya kalli Abdou matawalle suka haɗa ido, suka mayar kan Nana da ta durƙushe a gurin tana ta uban kuka.

Matawalle ya yi gyaran murya ya ce "Wannan yaron wane ne shi a gurinki?"

"Ɗa na ne" Ta faɗa cikin kuka.

"Shi kuma wannan fa?" Ya nuna mata Hammad.

"Mijina ne" Ta furta cikin sanyin jiki.

"Waye baban yaron naki?" Ya sake tambayarta. Ta kalli Hammad ta ce "Shine"

"Kin tabattar shi ne mahaifin yaron nan, kuma ke ki ka haifi yaron?"

Ta jinjina kai ta ce "Na tabattar"

"Ya aka yi ku ka haɗu ku ka yi aure?"

Ta numfasa ta ce "A Nigeria muka haɗu, a can muka yi aure"

"Waye shaidarki cewa mijinki ne shi?"

Takaici ya fara kama Nana, wace shaida kuma bayan wannan ɗan wata shaida suke nema?.

"Ni ba ni da wata shaida, Allah ne shaidata sai babana da ya ɗaura mana aure."

Sardauna ya ce "Yaya aka yi mahaifin naki ya aura miki wanda bai san daga inda yake ba, ko ku ƙasarku ba ka bincike ku ke aure?"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ana yi, akwai 'yan uwansa da suke gadi tare, sun san aure muka yi, su Habu"

Matawalle ya ce "Ban gane gadi ba, gadi kamar yaya?"

Hammad ya ce "Ina neman alfarma dan Allah a tsagaita yi mata tambayoyin nan haka, duk a rikice take. Ga wannan wayar akwai video da hotuna a ciki, lokacin da muna rayuwa ne da ni da ita a Nigeria"

Sulta ya ce "Hammad, ya zama dole ka yi mana shiru, a kammala binciken da yakamata, domin tabattar da gaskiyar lamarin nan"

Sardauna ya sake kallon Nana ya ce "Ya aka yi ki ka zo gidan nan yin aiki?"

Ta haɗiye yawu ta ce "Mu na Nigeria lokaci ɗaya na nemi 'yan uwansa na rasa, ya haɗu da larurar zuciya, ina tsaka da jinyarsa na neme shi na rasa. Kawai na yanke shawarar na zo Nijar ko zan haɗu da shi" Mamaki ya kama Hammad, yadda kai da fata taƙi bayanin ainihin ciwon da ya din ga yi bayan hawan jini.

Matawalle ya ce "Ya aka yi da ku ka haɗu ba ki sanar da kowa mijinki ne ba? Kuma me yasa wacan karon da ya kira ki a nan, ki ka ce ba ki san shi ba? Anya akwai ƙamshin gaskiya a maganar nan?"

Imam ya ce "Wancan karon laifina ne, kuma gaba ɗaya a ruɗe take"

"Ba kai ake tambaya ba, ita muke tambaya" Matawalle ya katse Sayyid.

Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ni ba na buƙatar na ci gaba da zama da shi, ku bani ɗa na kawai zan tafi na yi muku alƙawarin ba za ku sake ganina a inda yake ba"

Suka yi tsit suna kallon Nana, daga bisani Sardauna ya ce "Haƙiƙa idan ta tabatta kin auri Imam Hammad, to kun tafka babban kuskure mussaman shi da ya san ƙa'ida da dokar masarauta. Sai dai uzuri ɗaya za a yi muku, shi ne shi ya haɗu da larura, ke kuma ba ki san wannan ƙa'idar ba. Babban mai laifi shi ne Mahmoudu kuma sai ya haɗu da tsatsauran hukunci. Babu buƙatar mu ci gaba da bincike da wani bin diddigi.
Daga nan za a ɗauke ki a kai ki gidan baƙi na musamman, ki huta kwana biyu zamu haɗa miki sha tara ta arziki, za kuma mu sanya a mayar da ke har ƙasarku.
Imam Hammad dole zamu san yadda zamu juya wannan lamarin, mu ɓoye gaskiyarsa, idan haryanzu da aurenka a kanta, zaka sauwwaƙe mata zamu karɓi ɗanmu a mayar da ita Nigeria"

Wani irin mugun kallo Hammad ya yi wa Sardauna. Nana kuwa zabura ta yi tana ƙanƙame Muhsin ta ce "A'a Sayyid ne ɗanku, Muhsin kuma ɗa na ne, ba zan baku ɗa na ba, da shi zan tafi Nigeria"

Matawalle ya ce "Ba zai yiwu ba, mu zamu karɓi Muhsin ki yi haƙuri. Abu ne da muka daɗe mu na nema daga Hammad. Ki yi haƙuri dole mu kare kimarsa da mutuncinsa a Agadez"

Hammad ya miƙe a rikice, jin matakin da za a ɗauka, amma Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya. Da ido aka yi wa hadimar nan magana, ta nufi Nana gadan-gadan za ta ƙwace Muhsin.
Nana ta ƙara ƙanƙame shi tana kuka cikin ɗaga murya ta ce "Ba zan baku ɗa na ba, ku ƙyale mini ɗa na, baku san baƙar azabar da na sha kan na haife shi ba. Zan bar muku naku ɗan har abada nima ku bar mini nawa" Matar ta fi ƙarfin Nana, Muhsin na zunduma ihu, Nana na kuka ta fizge shi.
Nana ta bita da gudu tana janta "Ki bani ɗa na, wallahi ba zan bar muku shi ba. Ba za a kassara rayuwarsa kamar yadda aka kassara ta Sayyid ba".

Wasu hadiman ne maza suka shigo, za su tasa Nana a gaba su fita da ita. Amma mugun kallon da Imam ya yi musu ya sanya suka tsaya.
Ya ƙarasa inda Nana ta riƙe hadimar, ya saka hannu ya cire hannun Nana daga jikin hadimar da ta riƙe gam.

"Ka ce su bani ɗa na, kuna ina lokacin da nake gantalin nemanka ba ni da ko muhallin zama da tsohon cikinsa? Ka damu da ɗan naka, ka tafi baka sake waiwayata ba? Ka bani ɗa na na tafi na barku"

Idanunsa fal hawaye ya ce "Na sani, ki yi haƙuri Ma viee, ba a son raina ba komai ya faru ki yi haƙuri ki saurare ni"
Sai dai tamkar yana ƙara ziga ta, ta ci gaba da cewa "Na yi dana sanin saninka a rayuwata, soyayya da tausayi ba su amfana wa rayuwata komai ba. Da na san abin da zan tarar kenan da na zauna inda Allah ya ajiye ni ban fito neman ka ba. A kan Muhsin zan iya karɓar Ƙaisar da abin da yake so na aikata sai dai masarautar taku ta tarwatse" muryarta tuni ta fara dashewa, saboda ɗaga murya da kukan da take yi mai tsuma zuciya.

Matawalle ya ce "Imam wannan wace irin yarinya ce, mara ɗa'a da rashin tarbiyya? Kai ku fita da ita"

"Kar wanda ya taɓa mini mata, zan fita da ita da kaina" Ya yi maganar yana ɗaga musu hannu alamar dakatarwa.

Nana kuwa tuni ta silale jikinta ya saki, ya riƙe ta a jikinsa ba ta iya cewa uffan sai sauke numfashi da take yi kawai.

Sultan ya yi shiru, yana ƙara jujjuya lamarin a cikin zuciyarsa.

Imam da kansa ya saka Nana a cikin mota, ya babbake ya hana kowa ya taɓa ta. Ya rufe motar ya zagaya zai buɗe ɗaya ɓangaren ya shiga, amma wasu manyan hadimai suka tsare ƙofar.

Ya kalle su ba tare da ya yi magana ba.
Ɗayan ya ce "Tuba muke yi, umarni ne daga sama, cewar kar a kuskura a bari ka bar gidan nan"

Cikin mamaki ya ce "Daga sama gurin wa?"

"Daga sama gurina, kar wanda ya bar shi ya fita ko ina daga gidan nan, har sai mun bayar da umarnin hakan, ku kaita inda muka yi umarni, za mu sanya a mayar da ita Nigeria. Ina sake jaddada muku, kar wanda ya kuskura ya bar Imam Hammad ya fita daga gidan nan sai mun ba da damar hakan" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni, aka ji motar da Nana take ciki aka fita da ita daga gidan.

Da ya san haka abubuwan nan za su kasance, da babu abin da zai hana ya ɗauki Nana da ɗansa ya bar musu ƙasar gaba ɗaya. Sai dai halin da Sultan zai shiga kawai yake tunani.

Cike da baƙin ciki da takaici, ya koma ya iske Sultan, gabansa ya je ya tsaya cikin tashin hankali ya ce "Me yasa za ka yi haka? Idan ni ne a matsayin da take za ka so a yi mini haka? Ka kalli lamarin nan a matsayinka na uba, ba Sultan ba. Dokar masarauta  ba dokar addini ba ce ba. Me yasa 'yan majalissarka za su ziga ka ka yi haka? Babu wata hujja da ake buƙata domin tabattar da Asma'u matata ce, Mahmoudu su suka ɗaura mini aure. Shi ma kun ce a kulle shi ya yi laifi. Aure muka yi da Nana ga yarona ku na gani me yasa za a raba ta da ɗanta kuma a mayar da ita Nigeria haba Abie"

"Hammad, ni ka zo gabana ka tsaya ka na gaya mini magana a haka saboda mace? Dole ne mu girmama tare da martaba al'adun masarautar nan, mu samu mu binne babban kuskuren da ku ka aikata ko dan tsira da mutuncinka.

Hammad ya girgiza kai ya ce "Sultan, Asma'u ba mace ba ce kawai, ba zan binne laifukana saboda al'ada na je lahira ba ni da abin da zan gaya wa Allah ba. Zan ɗauki matata na bar ƙasar nan gaba ɗaya. Na bar muku sarautar da al'adar. Da na rayu babu su ma babu abin da ya same ni, ka gafarce ni"

Mari Sultan ya kifa masa, ya janyo rigarsa yana kallon sa ya ce "Ko ka fara shan wani abu ne Hammad? Ni ka ke gaya wa ka bar mana sarautar za ka ɗauki wata bare ka bar ƙasar nan?"

Jiki a sanyaye ya ce "Ba bare ba ce ba, matata ce kuma akwai ɗa a tsakaninmu. A halin yanzu a Duniya bayan kai ba na tunanin akwai wani wanda zai iya yi mini abun da ta yi mini. Gaskiyar da ba ka sona faɗa Abie ina tare da baƙin aljani, da yake burkita ni. Nana na iya ganinsa kuma itakaɗai take iya fahimtar halin da nake ci. Abie Nana ba mace ba ce kawai, waliyya ce a cikin mata, har shanyewar ɓarin jiki na yi, lokacin da ku ka gano su Mahmoudu aka ɗauke su, ba ta da wani mataimaki sai Allah kuma ba ta taɓa gajiya da ni ba. Asma'u har najasata ta wanke da hannunta. Da jikinta da lafiyarta da lokacikta da zuciyarta ta rayu da ni cikin kulawa da tausayawa. Idan na bari aka yi amfani da rashin gatanta saboda ni shafaffe da mai ne aka cutar da ita ban yi wa kaina adalci ba. Tsakanina da ita ba alaƙa ce gangar jiki ba kawai, akwai tasirin ruhika, da kuma tasirin alaƙar uba da ɗa. Wannan wani abu ne da ni da ita ne kawai muka sani. Abie ba za ku iya raba ni da Asma'u ba, idan ma ku ka raba mu, sai kun nemo ta da kanku" Ya ƙarasa maganar yana ja da baya ya fice ya bar ɗakin.

Sultan ya dafe gaban goshinsa da yake yi masa wani irin raɗaɗi, ya nemi guri ya zauna. Duk yana jin maganganun Hammad a matsayin soki burutsun neman mafitar yadda zai samu ya zauna da Nana.
Shi ma yana ganin ba a kyauta ba, a ƙwace mata yaro kuma a kore ta.

Asal kuwa tana can ta gigice, bayan da ta samu labari cewar, an ga Hammad da wata mata ya riƙe hannunta sun shiga sashen Sultan. Ta rasa wa zata dosa domin ta ji gaskiyar lamarin.

Tana cikin wannan gigitar, Tafawa ya kira ta, ta ɗaga jikinta yana ta tsuma.

Ya ce "Asal, wace hadima ce a gidanki, ta kai abinci lokacin da su Asad suka zo?" Sai ta manta me ma ake nufi da hadima, sai da ya yi mata tsawa sannan ta farga ta ce "Wata hadima ce a gidan nan. Ce mini a ka yi an ga Imam Hammad da wata ya riƙo hannunta sun shiga sashen Sultan, ko ka na da labarin wace ce?"

Ya ja tsaki ya ce "Sai me kuma? Ina tambayarki ki na tambayata wani abu daban."

"Abbu dan Allah ka gaya mini idan ka san wani abu, ka ga ka ce mini ya ce yana da ɗa, a tsorace nake"

Tafawa ya ce "Asal, kina nufin kina son Hammad ne?"

Cikin kuka ta ce "Abbu mijina ne fa, ko ba na son sa ina duba makomata nima" Sai dai tana rufe bakinta, Hammad ya banko ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske.
A razane ta saki wayar hannunta, ta waiwaya tana kallon sa.
Da sauri ta tunkare shi tana faɗin "Hammad wace mata a ce an ganku kun shigo tare yau, har kana riƙe da hannunta kun shiga sashen Sultan? Kar dai maganar da aka gaya mini gaskiya ce?" Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan gadonsa ya faɗa kai.

Ta nufe shi a hasale ta ce "Ka tashi ka yi mini bayani, wace matar a ganku tare? Kuma da gaske ka na da ɗa ko ba ka da shi? Yanzu da mutuncinka da kimarka ka zaɓi ka tozarta kanka ka kwanta da wata mace a waje dan ta haifa maka ɗa. Wallahi Hammad baka isa ba, ina yi maka rantsuwa da zatin Allah kowace matar ce sai na sanya an kashe ta, kuma an kashe mini banza dan duk cikin Agadez da kewayenta na san duk wata 'yar gata a bayana take. Ka tashi ka yi mini bayani"

Wuyanta ya damƙa, jikinsa na wata irin tsuma, gani ta yi gaba ɗaya ya canza ya koma kamar wani horo, jikinsa ya koma jajawurr tamkar tumatir. Babu baƙar ƙwayar idanunsa sai farar nan tas, duk wata jijiya da taje jikinsa duk sun kumbura. ya faɗo daga kan gadon yana burgima, saboda yadda yake jin tamkar wuta na ci a ƙasan fatarsa.

Tofa!

Ayshercool
08081012143.

Kar dai ku gaji da ni, ina yi muku tuni da cewar labarin Buzu ya shiga gasa a YouTube channel ɗin limamin tsakar gida, wanda da yawan likes na kashi goman farko za a yi amfani gurin alƙalanci. Ku taimaka ku je ku danna like a kashi goman farko na labarin BUZU na gode.

82
LITTAFIN KUƊI NE, KARKI RAINA GIRMAN HAKKI, 1K NE VIA 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
Hankalin Sultan da muƙarrabansa ya dunguzuma nesa ba kusa ba. Suka gaza gane kan Imam Hammad ta ko ina.
Ga Muhsin shi ma yana ta rikici, ba ya cin abinci sam, sai koke-koke ya ƙi saurar kowa saboda rashin sabo.

Cikin tashin hankali Sultan yake kallon Hammad da yake wance kamar itace, ya dubi Matawalle ya ce "Anya Matawalle ba Asibiti zamu kai shi ba. Ina ga wannan ɓoye-ɓoyen da muke yi, lokaci ne ya yi da asirinmu zai tonu. Sai dai ina jin tsoron a san halin da muke ciki".

Matawalle ya ce "Wannan ba abin da ya shafi Asibiti ba ne, ko ka manta haka ya yi ta yi a lokacin da aka dawo da shi daga Nigeria? Sai da muka fita faransa sannan ya daina wannan abin,har tunaninsa ya dawo?"

Sultan ya ce "Haka ne, amma kamar wannan karon, abin ya ninka wancan da ya yi. Ba ya ci ba ya sha fa" Ya yi maganar cikin damuwa.

Matawalle ya ce "Nima abin da ya tsorata ni gaskiya, amma dole mu nemo masu magani da za su duba shi. Amma ya zama dole mu samo waɗanda ba za su furta komai ba, idan ba haka ba nan ma akwai matsala"
Sultan ya dafe kansa yana kallon Hammad, tamkar ya fashe da kuka.
Asal ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login