Showing 42001 words to 45000 words out of 124686 words
yake ba wa Nana, yadda ake ɗakuna a lunguna da saƙo na gidan, kamar marasa gaskiya, inda ba ka yi zato ba ma, sai ka ga ɗaki ne.
Da Asal ta yi tozali a ɗakin, idanunta jawur, tana ganin Nana ta sake tsuke fuska, kamar ta tashi ta kashe ta ta huta. Suka je gaban Sultan suka gaishe shi, Nana ta basar ko kallon inda Asal take ba ta yi ba.
Sultan ya ce "Asal, na saka an kira ki ne, saboda a yi komai a gaban idonki, a ji me mai maganin zai ce, saboda kina da hakki ki sani kar ki ga ana ci gaba da rufe ki a kan abubuwa, tun da mijinki ne" Ta yi shiru, saboda shi kansa Sultan ɗin haushin sa take ji.
Sallamar da aka yi ne ya sanya Sultan yin shiru, Nana kuma ta miƙe tana faɗin "Kaii Sarki, dama ka na nan?"
Ya yi dariya ya ce "Tuba nake uwar gijiyata, tuba nake uwar ɗakina"
Bakin Nana ya ƙi rufuwa, tamkar ta ga wani ɗan uwanta na jini.
Cikin murmushi ta sake cewa "Sarki mai baka mai aska, kai ne mai maganin da zaka duba Sayyid?"
Ya ce "Ni ne uwar gijiyata, an yi mini lamuni, ko kuwa na koma ba a bani dama ba?.
Ayshercool 08081012143
88
1K NE VIA 0069685771
AISHA ADAM STANBIC IBTC BANK 08081012143
Nana ta kalli Sarkin baka ta yi murmushi ta ce "Wane mutum! Dama zan sake ganinka?"
Ya yi murmushi, hadimin da ya rako Sarkin baka, ya ankarar da shi Sultan. Cikin girmamawa Sarkin baka ya risuna ya kwashi gaisuwa a gaban Sultan.
Sultan ya ce "Na ga kamar ka santa ko?"
Ya jinjina kai ya ce "Ƙwarai uwar gijiyata ce" Sai kuma ya sauke idanunsa a kan Sayyid, ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Kamar ba ka gane ni ba ko?"
Mahmoudu ya ce "Ina dai yi maka kallon sani"
Ya matsa gaban Hammad, ya zuba masa ido ya ce "Ka tuna ni?"
Hammad ya yi shiru sannan daga bisani ya ce "Na tuna ka"
"Waye ni?"
"Ba zan iya cewa ga waye kai ba, amma mun je gurinka a Nigeria"
Sarkin baka ya yi murmushi ya ce "Yanzu tunaninka kaf na zamanka a Nigeria ya dawo kana tuna komai?" Ya jinjina masa kai alamar eh.
Ya dubi Nana ya ce "Kin ga batutuwan duk da na gaya miki sun dawo ko? Kin yarda ko haryanzu kina da ja?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ta sauya zani ba, ina nan a kan bakana"
Ya ce "Babu laifi, amma an bani dama ko kuma na bar lamarin tun da na manya ne?"
Matawalle ya ce "Bawan Allah, ina ganin ka yi abin da aka kawo ka ka yi mana. Idan ma wani abu ne a tsakaninku, kwa tattauna daga baya. Nan ba gurin wasa ba ne"
Sarkin Baka ya tsuke fuska ya kalli Matawalle ya ce "Duk cikin aikina ne, kai ka san wacece wannan kuwa? Ku na da maganin matsalarku a tare da ku, amma ba ku sani ba" Gaba ɗaya suka kalli Nana, ita ma ta yi sororo cikin mamaki.
Sarkin baka ya ce "Allah ne ya taƙaita masa, ba domin tana tare da shi ba, da sai ya zare ko ya mutu" Sultan da Mahmoudu suka haɗa ido.
Sarkin Baka ya ce "Ni yanzu abu ɗaya zuwa biyu zan ce, sauran magana ce tsakanina da ni da shi da Nana Asma'u Uwar ɗakina ba Allah ya taya miki" Ya yi maganar cikin girmamawa da jinjina wa Nana. Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi.
Mahmoudu ya ce "Bawan Allah, nan fa a gaban Sarki ka ke, in yi maka da yaren da zaka fi ganewa"
Sarkin Baka ya ce "Nima Sarki ne, dan haka a bari ni na gudanar da aikina. Kai ka manta Garba ga Baka ga Aska da ku ka kai mini wannan ɗan uwan naku can Nigeria" Mahmoudu ya yi sak ya ce "To ai na ga kamaninka sun canza?"
"Eh, ba kamannina ne suka canza ba, dan baka ganni cikin kayan aikina ba ne ba."
Sultan ya ce "Asal tashi ki je, duk abin da aka tattauna za a gaya miki"
Asal ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah ina roƙon alfarma, a yi komai a gabana, ina son sanin halin da yake ciki nima".
Sardauna ya ce "Ke Asal! Ki nutsu ki saurara tukuna, ki tsaya mu ji kan rashin lafiyar tasa, sannan a yi miki bayani daga baya"
Asal ta tashi jiki a sanyaye, tana kallon inda Nana take da kuma Hammad ta fice.
Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Nana Asma'u, mene ne labari? Meyafaru bayan tafiyarki ne? Kuma yaya aka yi na ganki a birnin Agadez?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Komai ma ya faru Sarki, amma dogon labari ne, mai tsayin gaske"
Ya murmusa, ya ƙare wa mutanen gurin kallo, sannan ya sake kallon Nana ya ce "Uwar ɗakina, me ya kawo ki Agadez ne?"
Nana ta nuna masa Sayyid. Mahmoudu ya yi murmushi ganin abin da Nana ta yi.
Ya ce "Uwar gijiyata, kina nan me yasa aka neme ni, kin karɓi aikin gurin uban duƙusa ne?".
Nana ta girgiza kai. Ya ce "To bani labari meyafaru?"
Sultan ya ce "Bawan Allah, ban fahimta ba me yake faruwa ne?"
"Allah ya baka yawan rai, duk cikin aikina ne. Idan babu damuwa ina son na san matsayin kowa a nan"
Mahmoudu ya ce "Ga Sultan kana gabansa, shi ne mahaifin Imam Hammad, sarkin Agadez, ga Matawalle da Sardauna, su ma iyaye ne a gare shi, kuma manya ne a Agadez. Sai Gimbiya Asal matarsa da ta fita. Sai kuma" Sai ya yi shiru yana bin su da kallo yana tsoron ya faɗi matsayin Nana ya yi laifi.
Sarkin baka ya ce "Ba ka gaya mini matsayin uwar gijiyata ba"
Sayyid ya ce "Matata ce"
Sarkin baka ya sake yin murmushi ya ce "Na san a rina, an saci zanin mahaukaciya jikina ya bani tun a lokacin da na ganku. Allah ya baka yawan rai, in dai yana tare da Nana Asma'u zai samu sassaucin matsalarsa. Tana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya yake zaune lafiya a Agadez, bai sake ɓallewa ya bar ƙasar nan ba"
Sarkin baka ya sake maimaita musu, Nana tana da alaƙa da maganin Hammad.
Matawalle ya ce "Me ka ke nufi? Ko dai wani haɗin bakin ne, ku ke son ku yi mana" Sardauna ya yi maganar yana kallon Sarkin baka.
Sarkin baka ya ce "Ɗan tsahirta mini tukuna, a kan aikina nake"
Ya sake kallon Mahmoudu, ya ce "Ɗan uwana ko za ka iya tuna abin da na gaya muku, lokacin da ku ka je gurina?"
Mahmoudu ya jinjina kai ya ce "Ka ce mana asiri aka yi masa, da baƙin aljani, ya manta duk abin da ya shafe shi, ya bar garinsu ba zai iya zama a garinsu ba. Kai kuma ba zaka iya ba shi magani ba, saboda ba aljani ne da za a iya sasantawa da shi ba, sai dai a je a karya asirin da aka yi masa. Na tambaye ka ko zaka iya karya asirin? Ka ce a'a shiga al'amuran aljanin nan akwai matsala, mu koma ƙasarmu a bincika inda aka yi masa sihiri a warware shi a can"
Ya ce "Madalla"
"Uwar gijiyata, ranar da aka kawo ki gidana neman magani, Meyafaru?"
Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ka ce a je a kira buzayen da suka tafi. Aka ce maka sun tafi. Ka ce da an same su, wataƙila ga maganin nasa ciwon ko nawa"
Sarkin baka ya ce "To Alhamdillah, an zo gaɓar da nake so a zo"
"Allah ya baka nasara. Wannan ita ce rabin maganin abin da yake damunsa"
Matawalle ya ce "Kai kalle mu da kyau, kar ka kuskura ka zo nan ku na gaya mana maganar banza. Idan ma haɗa kai ku ka yi, ku ka haɗa baki domin ku raina mana hankali, wallahi muka kama ka da rashin gaskiya, sai mun yi maka mummunan hukunci"
Sarkin baka ya ce "Na san dai duk azabar da zaka yi mini ba zaka saka ni a jahannama ba ko? To bayan wuta da Ubangiji zai saka ni a ciki, azaba in dai ta Duniya ce babu wadda ban sha ba, duk wadda za ta biyo baya ɗazu ce. Ban sanku ba ban taɓa ganinku ba, dan me zan yi muku ƙarya? Wani abu ne ya faru da tun a baya, na yi hasashen faruwarsa. Zan yi wani bayani amma a gaban mara lafiya da shaƙiƙansa da ya yarda da su. Idan na faɗa ban ce lallai sai kun yadda ba, amma iya gaskiyata zan gaya muku. Wannan baiwar Allah da na nuna na santa, tabbas na santa amma ni babu wanda na haɗa kai da shi domin na zo nan gurin na yi cuta ba. Saboda duk wani abun duniya da nake fatan samu, Allah ya riga ya bani shi. Ranka ya daɗe zaɓi mutum biyu zamu yi magana.
Duk suka yi zuru da ido, suna kallon Imam Hammad.
Hammad ya kalli Sultan, Sarkin baka ya yi caraf ya ce "Ɗayar, na zaɓi uwar gijiyata mutum biyu kenan. Allah ya baka yawan rai, idan babu damuwa ina so mu keɓe tare da ku"
Sultan ya ce "Babu laifi, Matawalle ko za ku bamu guri?"
Sardauna ya ce "Mai girma Sultan, ka yi a hankali kar ka bari su yi maka wasa da hankali, su faɗa maka abin da ba shikenan ba"
Sultan ya ce "Babu wani abu in sha Allah"
Bayan fitarsu gaba ɗaya, Sarkin baka ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba dan ina tsoron hadisin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce Allah yana fushi da ɗan kasuwa mai rantsuwa a kan kasuwancinsa ba, da na yi maka rantsuwa domin nima bayar da magani kasuwancina ne, amma ina baka tabbacin duk abin da zai fito daga bakina gaskiya zan gaya maka. Na san duk alkhairin da zaka yi mini ba zaka yanke mini talauci ba, sai Allah ya yanke mini. Kuma ba zaka talauta ni ba sai Allah ya talauta ni. Babu ƙarya ko haɗin baki ko yaudara a cikin abubuwan da zan yi maka. Wannan bayin Allah biyu babu wanda ba a kawo mini shi gurina neman magani ba. Asma'u ko ba ta bayar da magani ba, tsantsar tauhidinta da yarda da Allah da ta yi, zai iya sanyawa yadda yake tare da ita ya samu lafiya ko dan albarkacin addu'a. Ai Allah shi ya ce a roƙe shi zai amsa. Kafin na ce maka komai, bari na yi maka wasu tambayi m ya ka ji lokacin da ka neme shi ka rasa a ƙasar nan?"
Sultan ya ce "Na shiga tashin hankali, ba na iya cin abinci da cikakken bacci saboda rashin sanin inda yake."
"Alhamdillah, yanzu da ya dawo ya ka ke ji?"
"Murna nake yi mara misaltuwa, da jin cewa zan iya yin komai, dan na ga bai sake yin nesa da ni bax
Sarkin baka ya ce "Alhamdillah, ka yi bayani dai-dai da abin da nake son ka faɗa. Wannan yarinyar da ɗanka ba za su rayu guri daban-daban ba. Idan haka ta kasance kuma ɗaya zai rayu cikin wahala. Saboda alaƙarsu akwai tasirin soyayyar uba da ɗa a tsakaninsu"
Cikin rashin fahimta Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Me ka ke nufi?"
"Aljanin da aka yi wa ɗanka asiri da shi, ɗansa ne a kanta yake ta ɗawainiya da ita saboda ta yarda ta yi masa wani aiki. Ya ɗauki tsawon shekaru ba sa tare, kwatsam da aka ba shi aiki a kan ɗanka, ya yo Nigeria da shi, suka haɗu da ita. Dan haka duk abin da zai faru, duk rashin jituwar da ke tsakaninsu, uban ba zai bari ɗansa ya ƙara nesa da shi ba. Saboda shi ne ɗa mafi soyuwa a gare shi"
Sultan ya yi shiru cike da mamaki, yana bin Nana da Hammad da kallo.
Ya ce "To yanzu babu yadda za ayi, a karya sihirin?"
"Ni ba na ƙarya dan a so ni, ban san waye ya yi masa asiri ba, ban kuma san a daidai ina aka yi ba, balle na ce kai tsaye ga gurin a je a tona ba. Kuma ba zan yi karambani ba saboda aljanin shu'umi ne zai iya halaka ni. Amma ita tun da ɗansa yana tare da ita, ban sani ba ko ya samu sassauci ko makarin abin a dalilnta ba"
Sultan ya yi shiru yana kallon su, lallai biri ya yi kama da mutum, duba da yadda lokaci guda take iya sarrafa shi, idan ciwon nan ya tashi.
Sultan ya ce "Yanzu mene ne abin yi?"
"Abin yi ɗaya, a ci gaba da addu'a, kuma ku ƙara taka tsantsan, sannan ban sani ba ko uwar gijiyata za ta nema mana alfarmar shugaba, ko akwai abin da zai iya yi a kan lamarin"
Nana ta ɗan tsuke fuska tana mazewa.
"Wa za ta roƙa mana " Sultan ya yi maganar cikin damuwa.
"Ɗan nasa mana, ai hadiminta ne, kuma babu abin da za ta saka shi, ya kasa yi mata"
Sultan ya kalli Nana ya ce "To ko za ki roƙa mana ɗin, duba da mawuyacin halin da yake shiga idan ciwon ya tashi" Nana ta yi shiru ta sunkuyar da kanta.
Sarkin baka ya ce "Kar a yi gaggwa, a bi ta a sannu tukuna, ta yanke hukunci da kanta"
Sultan ya ce "Shikenan, a mayar da kai masauki, kafin na kuma nemanka"
Nana ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah zan yi magana da shi, idan babu matsala a hakan" Sultan ya ce "Babu damuwa"
Hammad ya haɗe rai, amma Nana ta tashi ta bi shi waje.
Ta ce "Sarkin baka, dama kana raye? Ƙaisar ya ce mini kashe ka zai yi"
"Nana Asma'u, uban duƙusa bai kashe ni ba, sai dai na ji jiki kamar ba zan rayu ba. Shi ya kawo mini magani ma, sannan ya ƙara yi mini kashedi sosai a kanki. Daga nan ma har wasu magungunan ya sanar da ni"
Ta ce "Ikon Allah, sarki ya magunguna ya marasa lafiya? Ina Salamatu da wannan aljanar taka"
Ya yi dariya ya ce "Duk su na nan ƙalau"
"To ya aka yi ka san cewa asiri aka yi wa Sayyid?"
Ya harare ta ya ce "Halinki dai yana nan uwar ɗakina. Mutum mai hankali zai yi abin da mijinki yake yi ne? Abin da nake so da ke, ki ƙara addu'a kar ki yarda da kowa, kunnuwanki da idanunki su zama a buɗe komai na iya faruwa idan Allah ya taimake ki wataƙila ya samu lafiya ta hannunki"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ƙaisar ya nuna mini abubuwa da dama, sai dai ba na son gazgatawa ne, na shiga ruɗani, amma har yadda asirin yake na gani, to amma idan ya rabu da Giyaz iya samun lafiya duka?"
"Ba na ce ba, tun da ban san a kan me da me aka ba shi aikin ba. Kuma ba shi da fuskar da zan tambaye shi. Amma ina jakar da na baki?"
Kafin ta amsa, Sayyid ya fizgi hannunta da ƙarfi ya yi gaba da ita.
Bai tsaya da ita ko ina ba, sai da suka je ɗakin da yake jinya. Idanunsa jawur ya ce "Dan wulaƙanci kawai ki je ki tsaya ki na surutun banza da mutumin da ba muharraminki ba"
Ta marairaice ta ce "Haba Shugaba, wa nake da shi a nan daga ƙasarmu, yaushe rabon da na ga wani wanda na sani? Kuma Sarkin baka duk da yana wasu abubuwan da nake tantama a kansu, mutum ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba. Bayan tafiyarka daga gidansa, abubuwa da yawa sun faru, ni a gidan nasa a ka bar ni"
"Ba na son jin koma mene ne ya faru" ya yi maganar yana tsuke fuska.
Ta ce "Haba Shugaba, kar ka manta, maganinsa ya taka muhimmiyar rawa lokacin da ka yi rashin lafiya"
Yayi mata shiru yana huci, tabbas a rayuwarsu da shi a Nigeria ta san shi da azabar kishi.
Ta kwantar da murya, tana shafa bayansa ta ce "Haba Shugaba, dama mutum zai iya fushi da rayuwarsa, tuba nake ɗan manyan mutane, kuma babban mutum" Ɗan guntun murmushi ya saki, ita ma ta yi masa murmushin.
Ya ce "Yauwwa, ki yi mini addu'a, in ajima za a sanar da Asal da iyayenta, matsayinki a gurina.
Nana ta kwaɓe baki ta ce "Na yi maka addu'a, ta mutu mana, nima ban mutu ba da kishiyata ta mayar da ni baiwa saboda tana da kuɗi, ga kuma mijina ina kallonsu tare, amma ban isa na ce komai ba".
Tsam ya miƙe, saboda ya san idan aka ci gaba da jan maganar faɗa za su yi. Ya ce "Ki shirya, idan na dawo yau komai dare, za mu je gurin kayan tarihi na Agadez, kuma zan baki labarin duk abubuwan da suka faru"
Ta yi masa shiru ta cika ta yi fam, kamar za ta fashe.
Ya tausasa murya ya ce "Na san kin yi haƙuri, amma ina sake baki haƙuri, dan Allah ki saki fuskarki"
"Ni ka rabu da ni, ka je ku lallaɓa matar so, da al'adarku ta yarda da ita, ni kuma ka sake ni ku kora ni ƙasarmu" Ta yi maganar har da ƙwallar baƙin ciki.
Ya yi murmushi ya ce "Duk wata matar so a bayanki take Gimbiya Ma vie. Kin ci Agadez kin ci Nigeria" ta murguɗa masa baki, ya shammace ta ya yi kissing ɗin bakinta.
****
Asal ce a gaban Sultan, da Matawalle da Sardauna, ga kuma Tafawa sai Imam Asadullahi, da Imam Hammad sai Mahmoudu.
Matawalle ya ce "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya, muka neme ku a yammacin nan, bayan sallar magariba haka.
Mun san za ku ji abin wani banbarakwai, amma mu ma haka nan ya zo mana. Duk ana kan dambarwar ɗa da Imam Hammad yake da shi, wani abu ya sake faruwa da dole mu yi muku bayani, domin babu yadda muka iya mu ma, sai dai mu na kan tunanin matakin da za mu ɗauka."
Tafawa ya ce "Mai girma Matwalle, wannan kwana-kwanar ta yi yawa, ka yi mana bayani kai tsaye."
"Kamar yadda ka yi ta bin diddigi a baya, tabbas Hammad ya yi rashin lafiya, ya kuma je Nigeria jinya. Asal na san abin da ki ka gani ya ɗaga miki hankali kina ta wasi-wasi. Ɗan da Hammad yake da shi, ba ɗan kowa ba ne face ɗan matar da ki ka kawo a matsayin kukunsa. Wannan kukun tasa matarsa ce"
AREWABOOKS
Wani irin nannauyan numfashi Asal ta ja, tana jin kamar daga shi ba zata