Showing 123001 words to 124686 words out of 124686 words

Chapter 42 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

82

gaba ɗaya ya shirya mini yarana".
Nana ta ƙwanƙwasa ƙofar ta yi sallama, suka amsa, ta shigo da kwanukan Abinci.
Hammad ya ce "Wai gida ki ka je?"

"Eh na je na ɗaukko Abinci ne, mutane na ta son su zo su ga jaririya fa."

"Ki ƙyale su, idan sun koma gida a ganta"

Har ranar suna Nana ba ta san sunanta za a saka wa jaririyar ba, aka shirya gagarumin suna a Agadez. Nana ta yi wa jaririyar nan kaya na alfarma. Kawai ta ji Hammad yana gaya wa Zahradeen wai sunan jaririya Asma'u. Nana ta yi turus ta ce "Sayyid, amma da wasa ka ke yi ko?"

"Kamar yaya wasa? Da gaske nake"

Cikin damuwa ta ce "Dan zatin Allah ka yi haƙuri, wannan ai rigima ce, kawai salon ka ja mini magana a garin nan, shekara da shekaru tana neman abu, ta sha wahala ta haihu kuma a saka sunana?"

"To ai ita ta nemi hakan ba ni ba"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi mata fin ƙarfi dai, Asal ba za ta yarda a saka wa yarinyarta sunana ba. Ni dai dan Allah ka canza"
Kawai ya hau dariya, ya ce "To ni yaya zan yi muku? Idan kin je gurin sunan, ki tambaye ta"

Nana ta ce "A'a ni dai na yafe, dan Allah ka canza mata suna, ya za a yi ka yi mata haka, salon kawai ka saka a ƙara tsana ta"

"To ai ni ina sonki dan a tsane ki ba komai tun da ina sonki"

Da gaske Nana ta fututtuke ta ce bata yarda ba, sai da ya ɗauke ta suka je gidan.

Asal ta ce "Dan na ce a saka wa jaririyar ki sunanki shi ne za ki ce ba kya so? Kina jin haushina kenan tun abubuwan da suka faru tsawon shekaru goma"

Nana ta ce "Wallahi ba haka ba ne ba, ba na son a yi miki fin ƙarfi ne, a takura miki abin da ba kya so"

Asal ta ce "A'a ni na ce a saka mata, babu wanda ya takura mini" Nana ta yi wa Nana bayani kamar yadda ta yi wa Hammad, sannan ta ɗora da cewa "Nana ni da ke mu na da tabon juna, da ba zai taɓa yiwuwa na ce sai mun yi nu'amala da juna ba. Amma ina son yaranmu su tashi da haɗin kai, kamar yadda ki ka kawar da kai ki ka nuna mini yaranki nawa ne. Ba na fatan a sake samun matsala na rabuwar kawuna saboda mulki ko abin Duniya a tsakanin yaranmu. Ina fatan za ki saka mini takwarar ki a cikin su Yarima, ta samu kyakykywar kulawa. Kuma ina godiya da dukkanin wasu abubuwa na alkhairi da ki ka yi mini, da ɗaukar damuwa ta taki, duk da ba jituwa muke yi ba"
Wani irin farinciki ya mamaye ta, ta ce "Tabbas takwarata kin haife ta ne, amma ni ki ka haifawa. Kuma na yi wannan alƙawarin na sanya ta cikin jerin 'ya'yana. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ya kawo biyar a bayan ta"

Asal ta ce "Biyar sun yi yawa ai, yadda shekaruna su ka ja ɗin nan? Ita ɗin ma na gode Allah"

Nana ta ce "Taskar Allah babu abin da babu, ko ba biyar ba Allah ya ƙaro mana wasu, shekara iyanzu a ce an kusa haifo mana wasu. Na gode sosai da sosai da karamcin nan da ki ka yi mini"

Jin sunan da aka saka wa jaririya, ya janyo cecekuce sosai da sosai a garin. Da ganin kamar ba a yi wa Asal adalci.

Kwanan Husna arba'in, Nana ta buɗe cibiyar magungunan musulunci.

Manyan mutane duk sun halarta, har da 'yan uwan Nana na Nigeria. A daidai lokacin ta kammala rubutun littafinta, da ta yi bincike tsawon shekaru, a kan aljanu, da ilimin ruƙiyya da ladduban yin ta.
A cikin sunayen mutane masu muhimmanci da ta lissafo a cikin littafin, sai da ta sanya sunan Ƙaisar Giyaz.

Ko da aka nemi Asal ta tofa wani abu a gurin taron, Nana ba ta zaci za ta yi magana ba, amma ta karɓa ta taya ta murna, tare da shaidawa duniya, a kanta Nana ta fara gwajin maganin haihuwa kuma Allah ya amsa.
Nene ta taimakawa Nana sosai a ɓangaren magungunan, haka Sarkin baka ya halarci taron, Hammad ne da kansa ya gayyace shi. Ya din ga yi wa Nana dariyar ba a guje wa ƙaddara.
Nana ta yi murmushi ta ce "Na karɓe ta ta hanyar da ta dace ne" Nana ta yi shiru tana kallon gurin nata. A hankali ta furta "Na cika maka alƙawarinka uban ɗakina"
"Nima na cika wanda na yi miki uwar gijiyata, na rubuta tarihinki da alƙalamin zinare a cikin kundi na mussaman da ba zai ɓace ba" Ta ji tamkar muryar Ƙaisar a gurin. Idonta ya sauka a kan award da ta yi da sunansa ta ajiye a gefe guda.

Shukura wannan rashin lafiya da ta yi ta fama, da damuwar da take ciki ne yayi ajalinta, Yusra ta shiga damuwa da tashin hankali sosai, sai dai ta rungumi yaran Shukura da waɗanda ta haifa.
Jamila ta samu wani jami'in ɗan sanda mai mata biyu ta aura, Allah ya taimake ta, ya ware mata gidanta sai dai tana shan azabar kishiyoyin duk da haka. Ta rungumi sana'arta sosai da sosai. Suwaiba kam ƙwaƙwalwa ta riga ta taɓu haka Mama ta ci gaba da wahala da ita.

Allah Al-musawwiru, shekarar Husna ɗaya a duniya, ta sake samun juna biyu, a dole Nana ta ɗauke ta, ta yaye ta. Ta haifi yara biyu mace da namiji.
Nana kuma sai a haihuwa ta ƙarshe, ta haifi 'ya mace, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma kan yaransu a haɗe yake sosai da sosai. Nana tsaye take a kan tarbiyya da kuma ilimin yaran mussaman na addini.

Hatta garin Buda sai da suka amfana da Nana, dan ta sai filin da kukar Lanti take, filin da kukar da aka yi wa Lanti girka, aka buɗe islamiyya. Sannan duk shekara suna samun abin alkhairi na kayan masarufi mussaman da azumi.

Ummanta duk ta aurar da ƙannenta mata, Imrana bayan ya kammala karatunsa, ya yi zamansa a faransa, sai da Nana ta matsa masa da batun aure, sannan ya ce ta samo masa duk wadda ta yi mata zai aura.

Suka rayu cikin kwanciyar hankali, da son juna. Ta samu kulawa da tsantsar soyayya daga miji, yaransu gaba ɗaya suna matuƙar sonta da ƙaunarta. Husna kuwa tamkar babbar 'yar Nana. Yayin da Yarima yake ɗan gurin Asal.
Ta shiga cikin mata da aka sanya sunansu a kundin tarihin Agadez.
Ta rayu cikin aminci da nutsuwa, a rayuwar da sai ta so ta yanke tsammani saboda gwagwarmaya. Sai ɗan sauran ƙalubale da faɗi tashin rayuwa da ba a rasa bawa da shi.


A hankali ya yi ajiyar zuciya, ya kalli matashin da yake zaune yana saurarensa, ya ce "Ka ji labarin Gimbiya Asma'u, to kai ma shigen abin da ya faru da su ne yake shirin faruwa da kai"

Ɗaya matashin ya ce "Allah ya yi mini tsari, idan kuma ni ban taki irin wannan sa'ar da Nana ta taka ba fa? Lallaɓawa zan yi na bi dare na gudu na bar garin nan, sai ta koma bin wani. Haka kurum mahaukaciya ta liƙe mini ta din ga bi na"

Ɗayan ya kwashe da dariya, ya ce "Dan Allah kar ka yi haka. Yau wuni ta yi a ƙofar gidan ku, an bata abinci ta ƙi ci, Yaya kawai take faɗa, dan Allah ka je ka bata Abinci kamar ma ba ta da lafiya"

"Kai wallahi ba zan koma ba hauka ake yi, idan ta gaji ta ƙara gaba ta nemi wands za ta bi"

*Tofa, ko su kuma wannan matasan suwaye? Waye wannan aka ba wa labarin BUZU da Nana, shi kuma wace mahaukaciyar ce take bin sa. Sai mu tara a gaba a cikin jerin littattafan da za su zo muku daga alƙalamina nan kusa ko a gaba*

(Waɗanda suka gaza juriya, a farkon littafin da ganin na matsa rayuwar Nana a farko, ina fatan a ƙarshe kun fahimci abin da nake son ku fahimta. Ba kowace Addu'a Allah yake karɓa a take ba, ya kan jinkirtawa bawa, ya amsa masa lokacin da ya fi dacewa. Annabawan Allah misali ne a kanmu. Har kullum ina fatan zamu din ga kamanta wasu darussan da muke karantawa a littafi, da rayuwarmu ta zahiri, hakan ne zai sanya a ɗauki gyararrakin da yakamata.)


TAMMAT BI HAMDILLAH. KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE. ALLAH YA KAWO MU ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN LAFIYA.
DUKKAN YABO DA GODIYA DA JINJINA DA KIRARI SU TABATTA GA BUWAYIN SARKI GAGARA MISALI DA YA BANI ARON RAI DA LAFIYA, NA KAWO WANNAN LITTAFIN BAYAN SHAFE TSAWON SHEKARU BIYU INA BINCIKE A KANSA. INA ROƘON ALLAH ABIN DA NA YI NA KUSKURE YA YAFE MINI.
GODIYA TA MUSAMMAN GA TEAM ƊIN BRIGHT PENS
Aisha Adam Ayshercool
Zainab shehu kumurya
Na'ima Suleiman
Nazeefa sabo Nashe.

Ƙungiyar YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA.

Godiya ta mussaman taki kekaɗai
Amanar Cool

Sai kuma gaisuwa ta mussaman da godiya, bisa taimakawa bincikena da ku ka yi.
Maryam Muhammad Mum amnash
Dr. Salihu Nura Adam (Salihan nur)
Fatima A abdou Nijar
Da ma kafatanin marubuta baki ɗaya.
Hakazalika ina godiya, ga masu gyara, sharhi da shawara Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi ya fi ni yabawa.

Na gode sosai da sosai, da jimirin bibiyata, ina roƙon Allah duk wanda ya karanta littafin nan, ko ya ƙaru da wani abu, ko bai ƙaru ba Ubangiji Allah ya tabattar da zukatanmu ni da ku a kan Imani.

Ina miƙa godiya sosai da sosai, ga waɗanda suka kasance tare da ni a tafiyar nan, tun daga telegram har AREWABOOKS.
Waɗanda na yi wa kuskure, ina mai baku haƙuri, saboda ɗan Adam ce ni, mai ajizanci.

Wanda ku ka sarrafa mini littafi, ta wasu hanyoyi ba da izinina ba, ba a yafiya ranar lahira.

Wanda kuka karanta mini baku saya ba, ga account number na zan saka, ku bani hakkin wahalata na wata shida, akasin haka ina muku tuni da duk mai son ci gaba a nasa neman, baya yi wa wani mugunta. Kuma hakkin wani komai ƙanƙantarsa na iya kawo maka naƙasu a naka neman. A saka mini hakkina dan Allah, ko na bar mutum da Ubangijin Musa da Harun, ubangina ubangijinku.
0069685771
Aisha Adam stanbic bank.

Sai mun haɗu a littafi na gaba, idan Allah ya bamu aron rai da lafiya.

08081012143
💃💃💃💃









Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login