Showing 51001 words to 54000 words out of 124686 words

Chapter 18 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

71

su sani ba shi ne, tun Sultan Ansar yana kan karagar mulki, suke tsara komai da shi da babban amininsa Matawallen Agadez, wanda shi ma duk zuriyar Azhar ne, sun haɗa kakanni.
Aka yi ginin ta ƙarƙashin ƙasa, daga sabon gidan Saruta, zuwa tsohon gidan Sarauta, da aka mayar da shi gurin adana kayan tarihi na Agadez. An narka dukiya mai yawan gaske, gurin gina sabon gidan nan, saboda yanayin ƙasar sahara. Da haka ya saka aka ɗaukko masa Imam Jalaludeen, aka biyo da shi ta ƙarƙashin ƙasa, zuwa gidan tarihi, a gidan tarihin ma, cikin kurkukun ƙarƙashin ƙasa, a nan aka ba shi wannan kambun.

Cikin kuka Sultan Jalaludeen ya ce "Yaya za a yi ina cikin jimami da alhinin rashin mahaifina, amma ku ta naɗin sarauta ku ke yi, ni ba zan iya karɓar wannan kayan ba"

"Dole ka karɓa, ya kai Sultan Jalaludeen Ansar, wannan wasiyyar mahaifinka ce, da ya nemi muddin mu na numfashi a cika masa ita, tun kan a binne shi ya nemi a naɗa ka Sultan a Agadez. Ka zuba ido wayewar gari da an binne mahafinka, yaƙi zai nemi ya ɓarke a Agadez, abin da ba a son faruwarsa a zuriyarku. Dan haka muddin ka na son masaruta ta ci gaba da tsayawa da ƙafafuwanta dole ne ka yi haƙuri, sai dai a wayi gari da sabon Sultan."
Haka su ka din ga tausar sa, da ba shi baki har ya yi haƙuri. Sannan suka ba shi wata ƙaramar jakar fata, wadda ta ɗara laya girma, amma ba ta kai girman a kirata jaka ba. Suka sanar masa tun Sultan yana raye, ya sanya bokansa ya yi masa ita, domin tsari da kariya daga miyagu. Kuma a matsayinsa na Sultan, zai iya amfani da ita, gurin sarrafa aljanun gidan Sarauta. Can gidansa kuwa tuni har an kame wasu daga cikin 'ya'yansa, ana ta nemansa ruwa a jallo, an tattare matansa an kame. Sai dai ko sama ko ƙasa aka neme shi a ka rasa. Washegari da sassafe tun kan a binne mahaifinsa aka wayi gari a kan ganshi an kan karagar Mulkin Agadez da duk wani abu da yake nuna shaidar shi ne Sultan a Agadez.

Ayshercool
08081012143

90
1K NE A BIYA KUƊIN KARATU KAFIN A KARANTA.
0069685771
Aisha Adam stanbic bank
08081012143
Mutane sun sha mamakin abin da ya faru. Babu wanda ya isa ya ce dan me? Aka kame waɗanda suka yi yinƙurin nemansa su kashe shi. A ka yi jana'izar Sultan Ansar. Gaba ɗaya Jalaludeen baya murna, saboda raɗaɗin mutuwar mahaifinsu, ga kuma wannan nauyi da ya hau kansa da ƙanan shekaru da ba su wuce Ashirin da takwas ba.
Sai dai duk zigar da Saifudden ya din ga yi wa Imam da 'yan uwansa, zamewa ya yi ya bar su, aka kama su sukaɗai.
Mahaifiyar Jalaludeen ta yi masa nasiha sosai da sosai, a kan gudanar da sha'anin mulki.
Duk da ya san tarin ƙiyayyar da Saifudden yake yi masa, da wasu daga cikin 'yan uwansa, amma haka ya janyo su a jikinsa, ya basu sarautu domin ya rage musu raɗaɗin abin da suke ji, kuma ya ƙara musu zaman lafiya da fahimtar juna. Ya yi wa Saifudeen Tafawan Agadez, wanda yana cikin manyan 'yan majalisar Sultan, da suke faɗa a ji. Ya yi wa ɗan uwansa Turakin Agadez, ɗan wan babansa ya yi masa Sardaunan Agadez. Bayan mutuwar Matawallen Agadez ya naɗa ɗansa Matawallen Agadez. Ya saka aka saki Imam Imam ɗin da suka yi zamani tare da su, suka yi yinƙurin halaka shi, sai dai gaba ɗaya ya sauke su daga kan muƙamin ya kuma yi amfani da ƙarfin mulki gurin ƙwace duk zobunansu, ya ce daga lokacin duk wanda zai zama Imam sai ya tantance shi, kuma sai da sahalewar sa. Aka yo caaa a kansa kamar za a cinye shi, su na ganin zai canza musu tsarin Al'ada.
Duk gidajen da suke da gadon, suka bayar da wanda suka zaɓo. Hankalin Tafawa ya ƙara dugunzuma bayan da ya san cewa ba shi da makoma, ya san ba zai taɓa mulki a Agadez ba, haka 'ya'yansa, saboda rashin zoben, dan ya san Jalaludeen 'ya'yansa zai bawa.
Wata rana Sultan Jalaludeen ya aika aka kira masa ɗan uwansa, ya zo ya same shi ya dube shi ya ce "Ya kai ɗan uwana, na san kai ne gaba da ni,  kuma ka so ka yi mulkin Agadez sosai da sosai, amma Allah bai nufa ba, ina mai sanar da kai cewa zobe ɗaya da aka neme shi aka rasa ya ɓace a tsakanin zuriyarmu, yana nan bai ɓata ba. Dan haka zan damƙa shi a gare ka, ka duba wanda ya dace a cikin 'ya'yanka ka bawa. Wataƙila a bayana a iya samun wani ya yi mulki daga gidanka"

Cikin mamaki ya kalle shi ya ce "Amma yaya aka yi ka mallaki zoben da ake tunanin ya ɓace?"

"Mahaifinmu ne ya bani shi, bayan nawa da yake hannuna, ya ce bayan ransa na damƙawa wanda ya cancanta"
A take Saifudeen ya ji ya ƙara tsanar mahaifinsu, saboda irin wariyar launin fata da aka nuna musu, ya fifita ɗa ɗaya a kan su da ya haifa. Wannan abin da Jalaludeen ya yi bai sanya ya rage ƙiyayya da jin haushinsa da yake yi ba.
Sai dai duk da haka majalisar Imam ba ta cika ba, ana ta zuba ido a ga wa Sultan zai bawa sauran zobuna biyun.
A lokacin ya auri mahaifiyar Hammad, buzuwar ƙasar Algeriya da mahaifinta ya ba shi ita, bayan da yaje taron tattaunawa na bunƙasa tattalin arziki. Sai dai cikin ikon Allah, jininsu ya haɗu sosai da sosai ta shiga ransa. Imam Jalaludeen yana da kuyangi, da haihu da su, sai dai Gimbiya Bilkisu ta tsani Gimbiya 'yar Algeria Gimbiya Aafaf.
Aurota babu daɗewa, ta haifi Hammad, dan watanninta tara cif ta haifo shi. Gimbiya Bilkisu tana da yara huɗu, uku mata sai guda ɗaya namiji Zahradeen, sai kuma 'ya'yan kuyanginsa mata guda biyu. Ba ta taɓa farga Gimbiya Aaafaf tana da juna biyu ba, saboda doguwar mace ce sosai, kuma su kan kwana biyu ba su haɗu ba, babu wanda yake shiga harkar wani.
Haihuwar Hammad gaba ɗaya ya gigita Gimbiya Bilkisu, domin ta gama sakankankancewa ɗanta zai iya zama Sultan wataran kasancewar shikaɗai ne namiji. Sai dai ta shiga ɗar-ɗar da tunanin abin da ka iya zuwa ya dawo.
Sultan Jalaludeen Amira yake kiran Aafaf da shi saboda ƙauna, ga wani irin so da yake yi Hammad, tamkar shikaɗai ne ɗansa. Sai dai ba Bilkisu ce kawai ta shiga ɗar-ɗar ba, har da sauran waɗanda suke sanya ran 'ya'yansu su zama sarakuna wataran. Bayan haihuwar Hammad, aka ci gaba da zuba ido a ga, ta ina sauran zobunan nan biyu za su ɓullo.
Bilkisu a tsaye take sosai da sosai, gurin nema wa 'ya'yanta kariya mussaman Zahradeen, ba ta da yadda ko kaɗan a kansa abinci ma sai wanda ta tantance ta yarda da shi, sannan zai ci. Ba a daina ta'amalli da bokaye ba har a wannan lokacin.
Hammad kuwa sai dai Sultan ya sanya a yi masa, dan sam Umminsa ba ta iya irin wannan abubuwan ba. Hammad ya tashi da hazaƙa da karsashi, sai dai ba ya son mutane. Kwatsam yana da shekaru shida, ya yi wata irin rashin lafiya da sai da aka fitar da rai da shi, da kyar da siɗin goshi sannan ya warke.
Daga lokacin Sultan ya ƙara tsananta kulawarsa a kan Hammad. Sai dai a lokacin Mamman, mijin Nene, ya san wanda suka ba wa Hammad guba, kasancewar yana cikin manyan hadiman da yake shiri da Gimbiya Bilkisu. Shi yasa da ya aikata wannan laifin, manyan da suke majalisar kusa da Sultan, suka ƙara kambama abin aka yanke masa wannan hukuncin da babu sassauci a cikin sa.
Shekarun Hammad bakwai a Duniya, ya haɗu da Mahmoudu, saboda yawan zuwa da Nene take yi da shi, ganin mahaifinsa a kurku, kuma ta kan je gaida Gimbiya Bilkisu. Sai dai sun ƙara shaƙuwa ne lokacin da Raƙuminsa ya taka Mahmoudu.
Gimbiya Bilkisu ta so shiga lamarin Maganar mijin Nene, wato Mamman amma Sultan ya ce "Amira, kin ga ke baƙuwa ce a Agadez, kuma ni kaina na taka dokar ƙasar nan aurenki da na yi, dan dai babu yadda za a yi a hukunta ni ne. Idan na matsa aka saki Mamman matsala na iya faruwa. Dan wasu lokutan a kan al'adu babu abin da ba zai iya faruwa ba. Ina matuƙar gudun abin da ka iya biyo bayan sakin Mamman, duk da na san da girman dokar da na karya.
Har ta rasu, ba ta daina yi masa magiya ba, da roƙonsa.
Sai dai rayuwa ta yi wa Hammad tsanani, bayan rasuwar Umminsa. Al'amuran mulki sun yi wa mahaifinsa yawa, bai fiye samun cikakken lokacin saurarar Hammad ba. Ya ɗauke shi ya ba wa Gimbiya Bilkisu, duk da ya san ba shiri take yi da mahaifiyarsa ba, amma a zatonsa abin ba zai shafi Hammad ba. Mussaman da yake son a ƙara samun haɗin kai a tsakanin iyalinsa, baya son kwaɗayin mulki ya yi silar tarwatsewar kawunansu. Sai dai Gimbiya Bilkisu ta din ga samun shawarari daban-daban a kan Hammad. Ciki har da ta kawar da shi ta huta. Dangin Umminsa sun so a ba su shi, amma Sultan ya ce ko da wasa, kar su ƙara yi masa irin wannan zancen.
Gimbiya Bilkisu kan kori Mahmoudu, ta rufe Hammad a ɗaki, tsawon kwanki a cikin sashinta, idan Sultan baya nan, ta hana shi Abinci ba tare da kowa ya sani ba. Ta san idan namansa za ta din ga sara tana zubarwa, ba zai faɗa ba. Sai ta ji Sultan zai dawo zata sake shi. Sai dai su haɗu su yi ta kuka da shi da Mahmoudu, wasu lokutan ma Mahmoudun ne yake kuka ban da shi.
Wataran aka kira Mahmoudu, aka ba shi wani lemo ƙato jawur wanda ya ba shi ya ce  "Ka ga wannan lemon, ka je ka ba wa Hammad ya sha, idan ya sha, zan saka a saki babanka, ku tafi gida tare. Amma kar ka gaya wa kowa, kuma kar ka ce ni na baka"
Mahmoudu ya karɓa, ya  tafi da murnarsa, ya kai wa Hammad lemon nan. Hammad ba ya tunanin komai idan Mahmoudu ya ba shi abu, ya karɓa ya ɓare har zai kai bakinsa, Mahmoudu ya ƙwace, ya gaya masa abin da ya faru.
Hammad ya ce "In dai za a rabu da Abbanka, ka bani zan sha, amma Mahmoudu ya hana shi, cike da ƙuruciya Mahmoudu ya karɓi lemon ya shanye. Haka ya din ga zubar da jini ta hanci ta baki, har da kafofin jikinsa. Hankalin Sultan ya tashi, saboda ya san kusancin da ke tsakaninsa da ɗansa. Ya ɗauki nauyin maganinsa da ƙoƙarin zurfafa bincike a kan abin da ya faru amma ba a gano komai ba.
Hammad ya tsallake abubuwa daban-daban na haɗari, na cutarwa a rayuwarsa, wani ya tsallake wani kuma ya rufta ya sha baƙar wahala ya warke. Mahmoudu kuma da yake tare da shi, kullum shi ma cikin farmaki yake da ƙoƙarin son a yi amfani da shi a cutar da Hammad. Duk wata makaranta da Hammad yake yi, tare suke yin ta da Mahmoudu. Saboda Sultan yana jin zafin abin da ya faru da mahaifinsa, ya san har abada Mahmoudu ba zai daina ganin baƙinsa ba. Ga gudunmuwar da kakansa, wato Baban Nene ya ba wa masarautar ta ɓangaren magunan da tsaface-tsaface.
Shekarun Hammad sha takwas a duniya, Imam Sultan ya damƙa masa zoben tambari, sai dai ba a son ransa ba, ya kuma damƙawa Zahradeen ɗayan. Sannan ya shugabantar da Imam Hammad a Majalisar, duk da shi ne ƙarami a cikinsu, saboda ko a lokacin ya fisu ilimi sosai da sosai. Nan aka ɗauki surutun ya yi amfani da ƙarfin mulki gurin gwada mugunta, ta hanyar raba wasu gidajen da zobunan tambari, ya ba wa 'ya'yansa da ɗan ɗan uwansa.
Sai dai hakan bai ishi Tafawa ba, musamman da ya ga an naɗa Hammad shugaban majalisar, ya ƙuduri aniyar duk yadda zai yi, ko hakan zai janyo yaƙi a Agadez masarautar ta rushe, sai ya yi duk yadda zai yi Asad ya hau karaga, ba zai bari abin da ya faru da su ya faru a kan 'ya'yansa ba, ya zuba ido Jalaludeen ya ɗora ɗansa a kan karaga ba.
Tafawa ya je ya samu Sultan Jalaludeen, ya ce masa yadda nauyi ya hau kansa kamar haka, bai kamata a ce ba shi da aure ba, dan haka idan ba damuwa ga ƙanwarsa nan Asal ya ba shi ya aura.
Sultan ya ce "Tafawa ai Hammad da Asal duk abu ɗaya ne, kuna duk hukuncin da ka yanke daidai ne. Zan sanar masa, sai dai ina so a bari ya ƙarasa karatunsa"
Tafawa ya ce "A'a jinkirin ka iya kawo wani abu daban, a yi auren daga bisani sai ta tare idan ya kammala karatun"
Bayan kwana biyu, Sultan ya kira Hammad, su na zaune su na shan shayi, Sultan ya sanar masa da abin da Tafawa ya zo da shi. A take annurin fuskar Hammad ya ɗauke, amma bai yi magana ba.
"Na san wataƙila zaɓin bai yi maka ba, amma ka san yadda ake ta sururu a kan abubuwan da na aikata. Ka yi haƙuri ka karɓi auren nan. Hakan shi ne cikar kamala, kuma ka ga 'yar uwakka ce. Sannan na gaya maka, babban burina da fatana, bai wuce ka gaji karagata ba, ina fatan a samu canjin wasu miyagun al'adun a dalilinka" Hammad ya yi shiru, tun da ya zama Imam, ake ba shi kyautar mata duk da ƙarancin shekarunsa, amma Tafawa ya babbake ya hana, yanzu kuma ya zo da wannan maganar. Ya jinjina wa Sultan kai kawai bai ce komai ba. Sai dai da ya je sashensa, kamar ya yi wa Mahmoudu kuka, dan dama shikaɗai ne wanda yake sakin jiki da shi, ya gaya masa duka wata damuwarsa.
Mahmoudu ya ce "To mene ne a ciki? Allah ya sanya albarka ya baku zaman lafiya, ai aure abin so ne"
"Ba na son Asal Mahmoudu"
Mahmoudu ya zaro ido ya ce "Ba ka sonta, 'yar uwakka ce fa"
"Ba na sonta kwata-kwata, mahaifinta ba ya ƙaunata, muraran yake nuna mini, duk da yana ɓoye hakan a gaban Abie".

"To ai ba ita ce take yi maka ba, bai kamata laifin mahaifinta ya shafe ta ba"

Hammad ya ce "Amma ka san ba zai ɗauki 'yarsa ya aura mini haka kurum ba ko? Kamar yadda ya aura wa Abie Gimbiya Bilkisu na sha wahala a hannunta, haka zai aura mini Asal, su ci gaba da azabtar da ni, za kuma ka ce na gaya maka"

"A'a kar ka yi wa auren baki mana tun kafin a yi, in sha Allah babu abin da zai faru sai alkhairi"
Fuskar nan babu annuri ya kwanta, dan gani yake wannan auren kawai takura wa rayuwarsa za a yi, sai kuma ya numfasa ya kalli Mahmoudu ya ce "Ka san wani abu?"

"A'a sai ka faɗa"

"Ni wallahi baƙar mace ce take burge ni"

AREWABOOKS

Mahmoudu ya waro ido ya ce "Dan zatin Allah daga nan, kar ka kuma ɗaga maganar nan, ka san dai illar hakan, da abin da zai haifar"

Ya gyaɗa kai ya ce "Ba ina nufin zan auri baƙar ba, amma ni dai su na yi mini kyau sosai da sosai. Da Umma ta yi maka ƙanwa sai na aura"

"Dan Allah ka daina wannan maganar, in dai a Agadez ne, mu ba komai ba ne face masu yi muku hidima"

Hammad ya ce "Babu aya babu hadisi a kan hakan, ina fatan wataran wannan dokar za ta kau, kowa ya auri wanda yake so, kowane kalar fata ya rayu cikin 'yanci ba tare da bauta ba. Har na koma ga Allah ina jin zafin abin da aka yi muku Mahmoudu. Kuma abin da ya faru da ku, yana daga dalilan da ya sanya nake matuƙar son baƙaƙen buzaye, da ma sauran baƙaƙen fata, duk farin nan namu fa, duk sunanmu 'yan Afrika kuma baƙaƙe to mene ne na ƙymar junan"

Mahmoudu ya ce "Ai komai ya wuce ma, dan Allah ka daina wannan maganar kar ma ka sake ɗaga ta dan Allah"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Na so a ce zan iya ce wa Abie ba zan auri yarinyar nan ba, amma ba zan iya ba"

"Dan Allah ko da wasa, kar ka gaya masa haka, ka yi haƙuri dan Allah. Kuma ni gara ka ce ba ka son ta, da dai ka yi waccan kataɓorar da ka faɗa da farko" Hamamd ya gyara kwanciyarsa, ya ce "Da wasa nake yi maka, kawai dai na gaya maka abin da yake raina ne. Fararen matan duk ba ga su nan ba, duk inda na kalla su ne ba. Amma ina son baƙa a ce matata ce, baƙa me kyau tubarkallah ka ga da ka na da ƙanwa, mai kama da Umma, na aure ta baƙaƙen mata su na yi mini kyau ma sha Allah"

"Dan zatin Allah ka daina zancen baƙar nan"

Yayi murmushi ganin yadda Mahmoudu da gaske baya son zancen, ya juya masa baya yana murmushi.

Asal ce zaune a gaban Tafawa, yana zaune daga kan kujera. Ya ce "Ki na ji na ko? Na ba wa ɗan uwanki ke a matsayin matar da zai aura, Imam Hammad dan haka ki shirya a kowane lokaci za a iya ɗaura muku aure".
Zabura Asal ta yi ta ce "Aure, kuma da Hammad?"

"Eh da shi, mene ne?" Ta sunkuyar da kai tana girgizawa cikin matsananciyar damuwa.

"Dan haka ki je zan sanar da mahaifiyarki a yi shiri"

Tana barin turakarsa ta saka kuka, ta shiga sashen mahaifiyarta. Cikin damuwa ta ce "Kyakykywata Lafiya kuwa?"

"Ammi, Abbu ne ya ce wai aure zai yi mini, dan Allah ban yi ƙarama da aure ba? Kuma wai Imam Hammad zai aura mini"
Ta tsuke fuska ta ce "Ban gane ba saboda me? Dama haka ake yi"
Asal ta ce "Dan Allah ni ki roƙe shi ya ƙyale ni, kar ya aura mini shi ba na son shi"

"Ki kwantar da hankalinki, babu wanda zai yi miki auren dole ina raye".

Mahaifiyar Asal ta tashi ta tafi turakar Tafawa, cikin takaici ta ce "Amma meyasa za ka yanke wannan hukuncin ba tare da amincewar yarinyar nan ba, ba ta ƙaunar auren nan fa"

"Saboda 'ya ta ce na isa da ita"

"Amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login