Showing 27001 words to 30000 words out of 124686 words

Chapter 10 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

84

sha ba, haka cacumar Nana da wani irin gigitaccen ƙarfi. Haka nan Nana ta ji jikinta babu ƙwari sosai.
"Habu ku bamu guri" Nana ta furta cikin ƙarfin hali tana ƙoƙarin riƙe hannunsa.

Mahmoudu ya ce "Amma kar ya shaƙe ki fa, ko ya yi miki illa"

Ta ce "Ba zai yi mini ba, zai dawo daidai in sha Allah, idan ma ya shaƙenin zai dawo daidai in sha Allah, amma ku bani guri" Tamkar zai shige cikinta haka yake ƙoƙarin rungume ta.

Gaba ɗaya Sultan ya ruɗe, Mahmoudu ya ce "Ranka ya daɗe, ta ce mu basu guri"

Sardauna ya ce "Tayaya za mu tafi mu bar su, idan ta cutar da shi fa?"

Mahmoudu ya ce "Ba za ta iya cutar da shi ba. Abin tsoron ma kar ya cutar da ita shi" Haka suka fita suka bar shi da Nana.
Su na fita Nana ta sassauta murya ta ce "Sayyid, ka nutsu ka yi addu'a, kar ka yi ihu, ka yi addu'a ka ji" Sai dai sam yanayinsa bai nuna yana cikin hayyacinsa ba.

Ta saka hannunta ta zuge rigarta ta cikin hijjabinta. Sai dai tana yi tana kokawa da shi. A hankali ta ba shi damar ƙanƙame ta kamar yadda yake ƙoƙarin yi. Wani irin nishi ya din ga saukewa mai sauti, jin sanyin jikin Nana. Sai dai sanyin bai kai wanda ya saba ji a jikinta ba.
A hankali ya yi lamo a jikinta, da fari Nana ta fara ƙoƙarin karanta masa Alqur'ani, sai dai ta kasa jurewa ta fashe da kuka. Saboda wani irin gigitaccen zafi ne yake ratsa ta daga jikinsa kamar an kunna musu wuta. Ga shi yadda ya danne ta ba za ta iya matsawa ba, balle ta samu afuwa.
"Ya hayyu ya ƙayyum Allah ka kawo mana ɗauki" Ta furta a lokacin da take jin yana ƙara matseta tamkar zai karya ƙasusuwanta.
Sun ɗauki lokaci a haka, kafin ta ji jikinsa ya saki, ya sassauta riƙon da ya yi mata. Ta ture shi da kyar ta ɗaukko pillow ta tayar masa da kansa da shi. Sai dai idanunsa a lumshe kamar mai bacci, saɓanin da da idanun a buɗe tar sai dai babu ƙwayar idon sai farar.
Ta koma gefe ta jingina da gadon da yake ɗakin, ko rigarta ba ta iya gyarawa ba, ta gyara hijjabinta ta jingina ta lumshe idanunta.
Hawaye ne suka fara bin gefen idonta, wani irin azababben ciwo jikinta yake yi mata, kamar an yi mata dukan tsiya da kulki. Ga raɗaɗin da take ji a kan fatarta.
A tsorace take waige-waige, ganin bugiren da Ƙaisar yake kwnaciya babu kowa. Ta duba gurin zamansa nan ma baya nan. Ta fita da sauri zuwa ɗakin magungunansa, nan ma baya nan ga inda Giyaz ya yi ɓarna ba a gyara ba, tabbacin bai da lafiya bai gyara ba. Ta din ga shiga tana fita a cikin Libraryn tana kiran sunansa amma ta ji shiru.
Wata siririyar hanya ta bi, da haske ya ratso gurin. Ta bi hanyar sannu a hankali tana addu'a a cikin zuciyarta, da fatan Allah ya sanya ba wani abin ne ya samu Ƙaisar ɗin ba.

Bayan Library ɗin ta ɓulla, ta hango shi a cikin tafkin da yake gurin a kwance, ya lumshe idonsa. Da sauri Nana ta ƙarasa tana faɗin "Ƙaisar, wannan ai sai ka tsorata ni, meyasa ka dawo nan ka kwanta, jikin ne dai?"
Ya buɗe idanunsa ya kalle ta ya ce "A'a hutawa kawai nake yi" Nana ta samu guri ta zauna a gefe ta ce "A'a ai na san jikin ne, ba zaka faɗa mini ba ne"

Ya ce "Ya jikin mijinki?"

Ta ɗan yi shiru ta ce "Yana can Giyaz na ci gaba da azabtar da shi. Na rasa me ma zan yi gaba ɗaya, ni kaina a jikina nake jin na ƙone"

Ƙaisar ya tashi zaune sosai a cikin ruwan ya ce "Ba Giyaz ba ne kawai, akwai tasirin asirin nan da ake yi masa da wuta. Sannan kuma ga Giyaz, shi Giyaz yana wasa da ƙwaƙwalwarsa ne, ya sanya ya tuna wannan ya manta wancan. Sai kuma ya kan shafe shi sai ya yi wannan suman. Amma wannan ƙonewar yana da alaƙa da wutar da ake hurawa wadda aka yi masa asirin da ita"

Cikin damuwa Nana ta ce "To dan Allah waye ya yi masa asirin, kuma a ina aka yi masa?"

Ya girgiza kai ya ce "Ki yi haƙuri, ba na shiga duk abin da bai shafe ni ba, saboda ni har kullum zaman lafiya nake fata. Sai dai na ga uwargijiyarki a dalilinki ta tuna gadon nasu gidan, da ke ki ka guji naki. Babu lallai sihiri ya yi tasiri mai ƙarfi a jikinki. Zai iya yiwuwa kina daf da inda aka yi masa sihirin. A wannan karon ne za ki yi faɗan ƙarshe, kar ki yi da wasa ki yi da gasken gaske. Ki buɗe idanunki, kibiyoyin da ki ka gani ana harbinsa da su mahaifinsa na karewa, yanzu ke za ki tare su.
Ya fito daga cikin ruwan jikinsa yana ɗigar da ruwa, yana takawa da kyar, jikinsa duk wasu irin ramuka duk ya yi baƙi. Ya gyara zaman rigarsa ya rufe jikinsa sosai.

Ya sake duban Nana ya ce "Kar ki yadda ki komawa iyayenki gida, babu wani kyakykywan sakamako. Za ki sake komawa farko dan sunanki zai ɓaci. Kar kuma ki yarda a raba ki da ɗanki, kar ki aminta da duk wani murmushi da za ki gani a fuskokin mutane, kuma kar ki sakankance da ƙiyayyar da za ki gani. Kowanne na iya taimaka miki ki samu haske.
Kai da fata ki dage, duk rintsi kar ki kuskura a ci moriyar ganga a yada ke a gefe, saboda kin gama yi musu amfani. Ki kula sosai da sosai. Allah ya ba da sa'a"

Cikin damuwa Matawalle ya ce "Shirun nan fa ya yi yawa. Anya ba za mu je mu sake dubawa ba"

Sardauna ya ce "Abin da nake tunani kenan, kar abin da ba a so ya faru. Kai Mahmoudu tashi ka wuce gaba ka duba, idan lafiya mu shigo. Ni na kasa samun nutsuwa tun da na ji tana wai mu bata guri."

Mahmoudu ne ya fara yin gaba, ya tura ƙofar ɗakin a hankali ya hango Nana a jingine shi kuma yana kwance a kusa da ita a kan fulo.

Ya ƙarasa da sauri yana kiran sunan Nana, amma ba ta motsa ba, sai hawaye da yake ta fita daga idanunta da ta lumshe.

Ƙarasowa suka yi su ma, suka rufu a kan Hammad. Sai suka ga jikinsa ya saki, idanunsa a rufe wannan jijiyoyin duk sun koma yadda suke.

Sardauna ya ce "Ya aka yi ya koma daidai? Me ta yi masa?"

Mahmoudu ya ce "Ban san me ta yi masa ba, Nana" Ya yi maganar yana kallonta.
Sai dai shiru ba ta amsa ba.

Sultan ya taɓa Hammd yana kiran sunansa, amma shi ma bai motsa ba.

Kawai su ka ga Nana ta fara jijjiga, duk su ka ɗan ja da baya a tsorace su na kallonta. Mahmoudu ya rasa me zai yi. Sai bin su da kallo. A hankali kuma ta daina ta nemi guri ta kwanta a ƙasa.

Matawalle ya ce "Wai ni na kasa fahimtar wannan abin, me ya same su haka?"

Mahmoudu ya ce "Kamar akwai wani abu da bamu sani ba, ko za mu ɗan ƙara ba su lokaci?"

Matawalle ya ce "Ni kaina duk ya kulle, ban taɓa ganin abu irin haka ba ai"
Ƙarshe sai sake fita suka yi, suka bar Nana da Imam Hammad.

Can jimawa Nana ta farka, ta yi miƙa tana salati, ta kalli agogon bangon dakin ta ga lokacin sallar magariba ya yi. Ɗakin ba kowa daga ita sai Sayyid da yake bacci.
Ta yinƙura da kyar ta tashi tsaye, ta fara dudduba ɗakin, ta samo banɗak a cikin sa. Ta yo alwala ta ɗebo ruwan a wata container ta zo ta ajiye ta tayar da salla.
Tana idarwa ta koma kansa, ta ɗauki ruwan da ta ɗebo a container ta yi shiru tana kallon ruwan, a hankali suratul Mulk ta zo kanta. Ta karanta Bismillah ta tofa, ta karanta suratul Mulk har ƙarshe.
Wata addu'a ce da Malam Auwwal ya kan yi mata, musamman idan ba ta da lafiya ta faɗo mata, wanda tun da take bata taɓa kwatanta karanta ta ba, ba ma ta taɓa sanin ta iya ba sai yanzu da ta faɗo mata a ka.
Da sauri ta yi Bismillah shashshafa masa ruwan da ta yi tofin. Ta dafa kansa ta fara karanto addu'ar "Bismillahi arƙik, min kulli shai'in yu'dika, wa min sharri kulli nafsin, au ainun hasid, Allahu yashfika, Bismillahi arƙik."
Ta ɗan koma gefe ta yi shiru tana kallonsa, tana fatan Ubangiji Allah ya ba shi lafiya.
Ta tattaɓa shi tana kiran sunansa a hankali "Sayyid ka na ji na?" A hankali ya motsa ya buɗe idanunsa da suka yi jaa ya kalle ta. Ƙara ware idon ya yi sosai domin ya tabattar ita ce ko kuma dai mafarki yake yi. Ya yinƙura gaba ɗaya zai tashi, ya ji wani irin jiri ya kama shi, ga cikinsa a ƙulle.

"Alhamdillah" Ta furta tare da faɗin "Sannu yi a hankali" Ta sassauƙe fululluka, ta jingina su a jikin gadon, sannan ta ɗago shi da kyar, ya yinƙura ya zauna sosai ya jingina.
Sai dai tamkar zai cinye ta, haka yake bin ta da kallo. Ya motsa baki yana son ya yi magana amma bakin ya din ga rawa. Ta girgiza masa kai ta ce "Kar ka yi magana".
Ya yi shiru yana ci gaba da kallonta. Ta ce "Ka sanni ne?" Ya lumshe idanunsa ya buɗe.

Ta yinƙura ta nufi wani jibgegen fridge da yake ɗakin, ta je ta buɗe. Ta ɗaukko ruwan roba ta zo ta zauna a kusa da shi. Ta cire masa rigarsa jikinsa. Ta ƙara shashasha masa ruwan nan. Ta lura da yadda jikinsa yake rawa, yake kallon ruwan hannunta da har raɓa yayi saboda sanyi.
Ta kalli ruwan hannun nata ta kalle shi, kamar yadda ta gan shi a bacci, ya rame sosai fatarsa duk ta bushe saboda rashin ruwa. Leɓensa har tsagewa yayi. Ikon Allah ne kawai ya raya shi zuwa wannan lokaci ba ci ba sha.
Ta ce "Buɗe bakinka" bakin yana rawa ya buɗe. Ta ɗaga jarkar za ta zuba masa ruwan su Matawalle suka sake shigowa.

Sardauna ya ce "Ke, mene ne wannan za ki ba shi?"

Nana ta ce "Ruwa ne, a fridge ɗin can na ɗaukko"

Sultan kuwa sai da ya ɗan rikice ya ce "Matawalle ya tashi"
Nana ta fara zuba masa ruwan a bakinsa, ya kai hannunsa biyu ya danƙe jarkar yana ɗaɗɗakar ruwan. Ƙoƙarin ƙwace ruwan Nana take yi, amma ya shanye. Yana shanyewa kuwa ya yi mata amai a jikinta har ta hancinsa haka ya din ga fitowa.

Matawalle ya ce "To ko Asibiti za a tafi a kai shi?"

Sultan ya ce "Ɗan jira mu gani"

Yana gama aman ya kifa a kafaɗar Nana. A hankali ta ce "Ka gani, saboda kar ka yi amai ya sanya na so na baka a hankali. Sannu" Ya yi shiru yana ajiyar zuciya.
Ta kalli Mahmoudu ta ce "Taimaka ka kuma ba ni wani ruwan" Da sauri Mahmoudu ya sake ɗaukko ruwa ya kawo mata.

Ta ɗago shi ta ce "Yanzu a hankali za ka sha, kar ka kuma yin aman, za din ga zuba maka kana haɗiya" Haka aka yi, ta din ga zuba masa a hankali yana sha, yana yi yana ƙoƙarin kai hannu ya riƙe robar, tana riƙe hannunsa tamkar ƙaramin yaro.
Nana tana son ta sake da shi, amma idonsu Sultan, ya sanya ta din ga komai a ɗarare gudun kar ta yi wani abu su yi mata wata fassarar ko sharrin. Ya jingina yana ta haki saboda duk ya galabaita.

Mahmoudu ya ce "Kuma ke bai shaƙe kin ba da muka fita?"

Nana ta yi murmushi ta ce "Ramin kura ai sai 'ya'yanta Habu. Ka samo mana ko kayan marmari ne da shayin Buzaye ya sha. Ai za ka sha ko?" Ta yi maganar tana kallonsa.
Ya ci gaba da kallon ƙwayar idon Nana, maganganu ne fal a cikinsa, amma babu halin furta su"
Su na ta jera masa sannu, amma babu wadda ya amsa a ciki.

Matawalle ya ce "Bari na yi magana, a sanya hadimai su kawo kayan marmarin ya ci"

Nana ta ce "A'a ranka ya daɗe, a saka Mahmoudu ya kawo" Duk suka tsaya suna kallon Nana, amma aka rasa mai magana.

Nana ta nuna masa Sultan ta ce "Ka san wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Wannan fa? Ta nuna Mahmoudu nan ma ya jinjina kai.
Ta ce "Ni fa?" Sai ya yi shiru, har ta fara karaya, da tunanin ko memory ɗin nasa ya sake ƙwacewa ya manta da ita.

Kawai hawaye ya fara zirarowa daga idanunsa.

AREWABOOKS
Cikin damuwa Nana ta yi masa murmushi ta girgiza masa kai.

Sultan ya ce "Hammad, me yake damun ka ne? Akwai wata matsala ne?"

Ya yi shiru bai kula Sultan ba, Nana ta yinƙura ta ce "Bari na je na wanke aman da ya yi"

Sardauna ya ce "Kar ki damu, za a kai ki inda za ki kwana, ba ma son kowa ya san kina nan. Za a baki wasu kayan ma sannan za a zo a gyara gurin. Kai kuma idan ka kawo Abincin sai a ba shi"

Nana ta jinjina kai, ta yinƙura da niyyar ta tashi, amma ya damƙe hannunta cikin nasa gam.
Ta dube shi ta ce "Mene ne?" Ya tsare ta da idanu.

Ta ce "Kar ka damu, ba nisa zan yi ba, zan dawo in sha Allah" Ya damƙe hannunta ya ƙi saki, yana murzawa a hankali.

Matawalle ya ce "Ka na ji Imam, zamu je a kai ta masauki ne, inda za ta zauna ta huta, kaima ka ci abinci kafin a san abin yi, an tafi samo mai magani da zai duba ka."

Kamar sassaƙe, haka ya yi shiru ya riƙe hannun Nana.

Sardauna ya ce "Ina ga mu bar ta tare da shi kawai, zuwa da safe sai mu san abin yi"
Haka suka mimmiƙe, ƙiri-ƙiri suna ji suna gani, suka kama hanyar fita, su bar shi da Nana.

Nana ta ce "Habu, dan Allah ɗan tsaya ka taimaka mini" Ya ce "To"
Bayan fitar su Nana ta ce "Dan Allah ka kawo mini kayana, sannan ka kawo mini kayansa guda biyu. Ka kawo mini Alkur'ani. Sai kuma Abincin nan dan Allah duk yadda za a yi kai tsaye daga hannunka zai zo, kar ya biyo ta hannun kowa. Sai kuma ina son ka kawo mini habbatussauda da tazargade, da ganyen magarya sai almiski ja"

Ya ce "In sha Allah ranki ya daɗe, yanzu kuwa. Sai dai su abin da ki ka lissafa ɗin nan, sai dai na shigo da su a ɓoye kar su ce wani abin za a yi masa"

Nana ta ce "Idan da matsala ba sai ka kawo su ba, kawo mini Abincin da kayan kawai, kar na saka ka a cikin matsala. Amma lokacin da hakan tana faruwa da shi da muna Nigeria, idan na yi masa amfani da su yana samun sauƙi sosai"

Mahmoudu ya ce "Kina nufin a Nigeria, yana irin haka?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Har ɓarin jikinsa sai da ya shanye, ka kawo mini Abincin da sauri na ba shi"

Ya ce "To" Ya kalli Hammad ya ce "Sannu Imam, Ubangiji Allah ya sanya kaffara"

Sai da Mahmoudu ya fita sannan ta kalle shi ta ce "Cika ni na je na wanke jikina, ka ga ka yi mini amai a jiki" A hankali ya saki hannunta, amma har ta shiga banɗakin nan kallonta yake yi. Ta wawwanke jikinta ta fito ta ƙara goge gurin da ya ɓata da aman.

Matawalle ya ce "Anya abin nan ba shiri ne yaran nan suka yi ba, saboda ya ci gaba da zama da yarinyar nan ba?"

Sardauna ya ce "Nima sai da na yi wannan tunanin"

Sultan ya ce "Bana tunanin shiri ne, babu yadda za a yi ya kwana takwas babu ci babu sha, a kwance a guri ɗaya a ce shiri ne. Kai Matwalle ka manta abin da ya din ga yi, lokacin da aka gano shi a Nigeria aka dawo da shi. Ba magana ba cin abinci a sume kawai kuma aka rasa abin da yake damunsa sai da muka je faransa sannan ya dawo hayyacinsa?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin hana kansa, yi musu cikakken bayanin labarin da Mahmoudu ya ba shi, mussaman cewa da aka yi idan aka dawo da shi Nijar, zai iya haukacewa ko ma ya rasa ransa gaba ɗaya".

Sardauna ya jinjina kai ya ce "To ai ita kanta yarinyar abar tsoro ce, ba ku ga abin da take yi ba? Ni abubuwan sun ɗaure mini kai sosai da sosai fa"

Sultan ya ce "Tabbas lamarin akwai ɗaure kai, da ayar tambaya, dama Hammad ya gaya mini wani abu, amma dai bari mu ga abin da Allah zai yi, sannan mu jira zuwan mai maganin da aka tafi nema"

*****

Mama ce take kallon Jamila cike da baƙin ciki da takaici. Kamar ta danne ta ta yanka ta ce "Jamila, so ki ke sai duniya ta san halin da muke ciki? Kin zaɓi mutuncinmu ya zube a rasa wanda zai aure ki saboda wannan abin kunyar. Tun kafin ya riƙa mu je a cire shi kin ƙi, Jamila kin fi son asirinmu ya tonu ko?" Ta yi maganar muryarta na rawa.

Jamila ta girgiza kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Mama ba zan iya zubar da cikin nan ba wallahi, ni tsoro nake ji, kuma kar zunubin ya yi mini yawa ba ki san adadin tarin zunuban da suke kaina ba. Ki bari na ji da wasu dan Allah, ki ƙyale ni kawai"

"Jamila ni ki ke cewa na ƙyale ki? Kin gwammaci ki durƙusa ki haife mana shege a gida, Duniya ta gani a shaida?"

Mama "Na duniya daga baya ne, Allah ya riga ya shaida ya ga komai, ni yanzu addu'ata Ubangiji Allah ya yafe mini. Wataƙila haifar ɗan nan ne zai sanya na samu nutsuwa ni dai dan Allah ki ƙyale ni"

Cikin takaici ta ce "Jamila kin san haihuwa kuwa? Kin san azabar haihuwar ɗan sunna balle shege, tsaf za ki mutuwa fa"

Jamila ta goge hawayenta ta ce "Idan na mutu gurin haihuwa na yi shahada, wataƙila Allah ya yafe mini tarin kura-kuren da na aikata"

Cikin tsawa ta ce "Uban waye ya ce miki mai cikin shege za ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login