Showing 72001 words to 75000 words out of 124686 words
tayi shiru sannan ta ce "Sayyid ba ka nuna mini mene ne a cikin ɗakin can ba" Ya kalli ɗakin ya ce "Hanyar tsohuwar prison ce, inda daga baya ake aikin sarrafa gold a ciki, amma yanzu babu abin da ake yi da gurin"
"Ina son ganin mene ne a ciki" Ya ce "To shikenan" Ya ja hannunta zuwa ƙofar gurin, amma suka tarar da ƙaton kwaɗo a jikin ƙofar. Ya ce "To ai gurin a rufe yake ma"
"Ya aka yi sauran ƙofofin ba a saka mukulli ba sai wannan? A tambayi mai tsaron gidan ya buɗe mini zan gani"
Hammad ya ce "To ai lokacin salla ya yi"
Ta ce "Na sani gani kawai zan yi mu tafi"
Ya tsaya yana kallon Nana da rikicin tsiya, ya ce "Zo mu je sai mu yi wa mai gadin magana, ya zo ya buɗe mana" ta bi shi a hankali jikinta cike da kasala ga kuma bacci da take ji.
Ko da Hammad ya tambayi tsohon nan mai tsaron ƙofar, sai cewa ya yi "Allah ya taimake ka, ban san wanda ya rufe ɗakin nan ba, ya kwana biyu a rufe"
Hammad ya ce "Wataƙila ko masu yawon buɗe ido su na ɓarna a gurin, shiyasa aka rufe"
Nana ta ce "Waye yake da alhakin rufewar?".
"Ma vie, wai lafiya kuwa?"
"Hammd sai an buɗe gurin nan kafin na bar Agadez"
"Shikenan na ji, za a buɗe amma muje mu yi salla tukuna" Da kyar ya lallaɓa ta suka bar gurin, saboda yadda take nema ta burkice masa gaba ɗaya.
*****
Shukura na zaune a kan gadon Asibiti, ta zuba ido tana kallon ɗan jaririnta, ƙato da shi mai matuƙar kama da Sagir, ta din ga tuno da jaririnta da aka ce ya mutu da haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da hakan. Ji ta yi an turo ƙofar ɗakin ta ɗago da sauri, gabanta ne ya faɗi ta yi turus tana kallon mai shigowar.
Ayshercool
08081012143
94
LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAFIN KI KARANTA.
0069685771
AISHA ADAM STANBIC
Yusra ce ta shigo ɗakin, Shukura ta yi tsuru da ido tana kallonta.
Yusra ta ƙarasa gaban gadon Shukura cikin damuwa ta ce "Meyasa ki ka taho nan, ki ka saka ake ta neman ki, duk hankalin mutane ya tashi?"
Maimakon Shukura ta bata amsa sai cewa ta yi "Ke kaɗai, ki ka yi driving ki ka zo nan? Ina Baban Haidar ɗin?"
"Wayarsa ce lalace, ya saka layin a wayata, yana can gurin meeting, kafin ya dawo kawai na ce bari na zo na ɗauke ki. Wannan ɗan da ki ka haifa ne?" Ta yi maganar tana karɓar jaririn hannun Shukura. Shukura ta jinjina kai jiki a sanyaye.
Yausra ta ƙura wa jaririn ido tana kallonsa, tana ɗan murmushi ta mayar da hankali kan Shukura ta ce "Wai meyasa ki ka zo nan gurin ki ka zauna?"
"Ba komai"
"A'a da komai, kowa kin saka hankalinsa ya tashi sosai, ga ki da tsohon ciki, ki tashi mu tafi gida idan ya dawo kawai sai dai ya ganki. Abbanki har yana cewa zai ɗaure shi, shi ne ya saka ki ka ɓata, ai ba dan ya dawo da ni ki ka tafi ba ko?" Ta yi maganar jikinta a sanyaye tana kallon Shukura.
Da mamaki Shukura ta ce "Daddyn ne ya ce zai ɗaure Sagir saboda ɓata na?"
Yusra ta jinjina kai ta ce "Wallahi haka ya ce"
Ta yi shiru tana zunzurutun ɓarna da zaluncin da ya gaya mata ya aikata. Ta numfasa ta ce "Amma ina fatan ba ki gaya wa kowa ina nan ba?"
"Babu wanda na gayawa, ai kin ce kar na faɗa, ga abinci can ma na ɗaukko a mota, da 'yansanda zan gayawa amma na fasa"
Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa gara da ba ki faɗa ba"
Yusra ta ce "To ki taso mu tafi"
"A'a ai sai an sallame ni tukuna, kuma yakamata ki koma gida saboda ki sanar masa inda nake"
"Babu inda zan koma, salon in tafi ki sake guduwa" Ta yi maganar tana ƙara lulluɓe jaririn Shukura da yake hannunta.
*****
Cikin damuwa Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, yadda take zubar da yawu tana wani irin ihu, da gurnani duk ta yi najasa a jikinta.
Ga ƙafafuwanta sun shanye, ba ta gane kowa sai wannan gurnanin da take yi. Likitoci sai dai su ta mata allurar bacci. Ranar da Fadila ta je duba ta, duk da ba ta magana amma tana ganinta tare da Muhsin ta din ga ihu tana tsine masa tana faɗin "Da tuni wannan shegen ɗan ne zai mutu ba Abbana ba, Allah ya isa ba zan yafe ba" Alhaji Fatuhu yana gurin, ya yi mamakin jin irin wannan maganganun da take yi, amma sai ya bar hakan a sakamakon taɓuwa da aka ce ƙwaƙwalwarta ta yi.
Likitan da ya kammala rubutu a kan takarda, ya miƙa wa Alhaji Fatuhu. Alhaji Fatuhu ya karɓa tare da kallon Likitan ya ce "Doctor haryanzu ba a gano takamaiman abin da yake damunta ba?"
"To, duk wani abu da yakamata mu duba mun duba, jininta lafiya kalau ba ta da hawan jini. Babu alamar strock a tare da ita. Sai dai idan sakamakon gwaje-gwajenta ya kammala bamu ga komai ba, zamu tura ku ɓangaren ƙwaƙwalwa dama mu nan mun riƙe ta ne domin mu gano maƙasudin shanyewar limbs ɗinta, to haryanzu ba a gano komai ba, zuwa ranar Litinin zamu fara tura ku physiotherapy ko Allah zai sanya a dace"
Alhaji Fatuhu ya jinjina kai cike da karaya, tabbas da lokacin da yake da kuɗinsa ne, da kansa zai fitar da ita waje a duba ta. Ko a yanzu ba ya jin daɗin yadda da kuɗinta ake nema mata magani.
Haka ya tafi gida jikina a sanyaye. Alhamdillah jikinsa ya yi kyau sosai, duk da haryanzu da sanda yake yawo bai gama warewa ba, amma yana iya fita shikaɗai.
'yarsa Rauda ya samu a gida yake ta yi wa faɗan rashin zuwa duba Hajiya Sa'a da ba son yi. "A ƙa'ida kamata ya yi a ce ke ce a gurinta Raudah, kina kallo lokacin da nake kwance kullum tana tafe"
Rauda ta ce "Daddy ni wallahi tsoron ganinta nake yi, kuma duk lokacin da muka je da Maman Muhsin, sai ta yi ta ihu tana tsine masa tana da tuni shi ya mutu ba ɗanta ba, ta yi ta ihu tsoro take bani"
"To Raudah ai larura ce, ni da Allah ya jarabbe ni, ba har wari na din ga yi lokacin da nake kan fama da larura ba. Jarrabwa ce Allah ya jarabce mu, kuma ku da ku ke kusa da mu, ku ne zaku ƙarfafa mana gwiwa. Ku din ga haƙuri". Ta jinjina masa kai kawai ta ce "To"
****
Nana bayan sun idar da sallar asuba, ta ɓungire ta hau bacci, saboda yadda suka kwana jiya babu bacci. Ya zauna a gabanta ya zuba mata idanunsa, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya din ga jinta a cikin jikinsa. Me zai yi wa wannan halitta domin nuna mata ɗumbin godiyarsa da farincikin kasancewa da ita. Ƙarshe ya ɓuge da sumbatarta yana shafa fuskarta, daga bisani ya tashi ya fita.
Sashen Gimbiya Bilkisu ya wuce, ya tarar ba ta fito ba, ya wuce ɗakin da yake kyautata zaton Asal tana ciki. Aikuwa tana ciki ɗin fuskarta ta kumbura suntum ta yi jawur, idanunta sun yi wani irin kumburi mai ban tsoro. Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ta kawar da kanta gefe ta yi shiru, ji take kamar ta shaƙe shi ya mutu ta huta.
"Asal" Ya kira sunanta. Ta ɗago ta kalle shi a ƙule.
"Ina roƙon ki da kar ki ɗauki damuwa da tashin hankalin lamarin nan ki saka a cikin ranki. Duk abin da ya faru a cikin rayuwarmu abu ne da Allah ya riga ya ƙaddara"
"Hammad ba na son jin komai daga gare ka, ka tashi ka tafi ka bani guri. Macuci ma ci amana, ba ka ji daɗin halinka ba"
Ya ce "Na ji na kuma yadda, duk abin da za ki kira ni da shi na karɓa, na san kina cikin fushi ne, amma ina mai roƙonki kar wani ya ziga ki ko ya tayar miki da hankali aurenmu ya samu matsala"
"Ka riga ka haifar da matsala a cikin aurenmu da kanka, matsalar da ba ta da magani. Har ka yi aure ka haihu ko Hammad, ba ruwanka da matsala ta kanka kawai ka sani. Ka tashi ta fita ka bani guri. Kuma wallahi ina mai yi mka rantsuwa da Allah, sai na yi mata mummunar illar da ba zata moru ba, sannan in saka a hallakata sai ta san ta jangwalo rigima mafi girman da ba zata iya tare ta ba a rayuwarta. Wallahi Hammad kai nawa ne nikaɗai ni Asal ba zan yi tarayya da ƙasƙantaciyar mace a koma mene ne ba"
Ya yi murmushi ya ce "Ni dai ina roƙonki ki kwantar da hankalinki, kar ki biye wa zuciyarki dan kaf cika da batsewar Agadez ke Niger gaba ɗaya babu mahalukin da zai raba ni da matata da ɗana. Dan gara na bar muku Agadez ɗin da mulkinku na bi farin ciki da kwanciyar hankalina. Ba zan taɓa wulaƙantaki ko na yarda a wulaƙantaki ba, saboda matata ce ke kuma 'yar uwata. Amma wallahil azim duk abin da ya samu Asma'u ba zan ɗaga wa kowane mahaluki ƙafa ba, a kanta komai kusancina da shi kuwa, dan Asma'u rayuwata ce, dole kuwa na bawa rayuwata dukkan wata kariya dan babu gangar jikin da take fatan rabuwa da ruhi"
Wani irin kukan kura ta yi, ta din ga kai masa duka ko ta ina, tana gaya masa maganganu masu zafi, amma ko gezau kawai ya tsaya yana kallonta. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo da gudu tana tambayar ko lafiya saboda jin ihun Asal da ta yi.
Ta ƙaraso ta rirriƙe Asal ta ce "Imam me ka yi mata?"
Ya ce "Babu abin da na yi mata"
Asal cikin gunjin kuka ta ce "Ammi ya cuce ni, ya bar gida tsawon lokaci ya je ya yi aurensa a ɓoye ya haihu ban sani ba, sai dai na ji zance sama taka, kuma yarinyar da na kawo a matsayin kukunsa. Wataƙila ma shirya komai suka yi, an cuce ni am zalunce ni, wallahi Ammi ba zan zauna da wata ba. Ya aka yi na fara son shi na bari son Hammad ya yi mini illa. Ni yake gaya wa kaf Agadez babu mai raba shi da waccan ƙasƙantaciyar halittar wallahi sai na kashe ta"
Gimbiya Bilkisu ta rungume Asal ta ce "Yi shiru ki daina magana, ki daina faɗar wannan maganar. Ki kwantar da hankalinki"
"Ammi zuciyata ciwo take yi mini, ko ganinsa ba na son yi, ya tashi ya tafi ya bani guri"
Gimbiya Bilkisu ta numfasa ta ce "Imam, ina ga kamar yadda ta buƙata ka tashi ka tafi kawai, ka bata lokaci ta samu nutsuwa. Domin magna ta domin Allah ba ka kyautawa Asal ba, dole ta shiga damuwa da tashin hankali"
Hammad ya ce "Allah ya taimake ki, kar ki zaɓi Asal saboda 'ya take a gurinki, a zamana da ita har zuwa abin da ya faru ban zalunce ta ba.
Cikin ƙaraji Asal ta ce "Ammi kin ji ko? Kina jin abin da yake faɗa"
"Imam ka tashi ka je kawai" Ya miƙe tsam ya fice daga ɗakin, Asal kuma ta ci gaba da kuka.
Fita ya yi, ya nufi wani sashi na gidan, ya yi umarnin a je a zo masa da Sarkin baka.
Yana nan zaune hadimai biyu suka shigo, tare da Sarkin baka, ya tarar da Hammad fuskar nan a ɗaure tamau babu annuri.
Sarki ya ce "Barka da wannan lokaci"
Hammad ya amsa da yauwwa barka.
Ya ɗora da cewa "Ammm duk da zan iya cewa baƙon Sultan ne kai, amma saboda ni aka kawo ka gurin nan, kuma ina tunanin ina da damar yin magana da yanke wa kaina hukunci"
Sarkin baka ya ce "Wannan gaskiya ne"
"Ina ganin tun da babu wani abu da ya yi saura, ka ce ba zaka iya yi mini magani ba, yakamata ka yi magana da Sultan a sallame ka ka tafi"
"Saboda ba ka son na kula matarka ko?" Hammad ya yi shiru yana kallon Sarkin baka.
Sarki ya yi murmushi ya ce "Ai duk taka tsantsan ɗinka ina da yaƙinin Nana ta fika, kuma ko da take yi mini kallon ba a kan daidai nake ba, ta san ni ba mutumin banza ba ne. Wannan gidan naku ba zan taɓa tafiya na bar Nana a cikinsa ba saboda balahirar da na gani a gidan"
Ya kalli Sarkin baka ya ce "A matsayinka na wa?"
"A matsayina na ɗan uwanta, ba ka san ina da alaƙa da ita ba? Duk da na san zaka kalli alaƙar ba wata ta kusa ba, amma a yadda ba ta da kowa a cikinku daga ahalinta ina ga zan wakilci ahalinta a nan. Ina da dangantaka ta kakannin kakannin da ita. Ka kwantar da hankalinka ni ba zan cutar da kowa ba, ko na shiga tsakaninku ba amma dole zata buƙace ni, idan kuma ka bari na tafi wallahi ba zan dawo ba bar abada kuma hakan ka iya zame muku matsala. Kuma ya zama dole ka bata duk wata dama ta ganawa da ni a duk lokacin da ta buƙaci hakan, ta nan ne za a iya samun warwarar abubuwan da suka baibaye ka. Ba na son a ji daga bakina ne, kuma ina son ta fahimci akwai abin da idan yana cikin ƙaddararka ba ya nufin ka saɓa wa Allah, amma Allah na iya amfani da kai ya kawo wa wani bawan nasa mafita" Hammad ya yi shiru yana jujjuya maganganun Sarkin baka, duk da ba komai ya gane ba. Amma ya numfasa ya ce a mayar da Sarkin baka masaukinsa.
Ya tashi ya fita, ya ɗauki mota ya bar gidan. Ya yi tafiya mai nisa aƙalla ta awa guda sannan ya iso wani makeken katafaren gida. Bayan ya shiga da motar ya ajiye, sai gaishe shi hadiman suke yi yana amsa musu cikin girmamawa.
Ya shiga cikin gidan ya bi wata hanya ya hau kan bene.
Ya ƙwanƙwasa wata ƙofa, sannan ya saka kansa ya shiga da sallama.
Yana zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana cin inibi tare da wasu ƙanan yara su uku, jikin bangon ɗakin kuma ƙatuwar TV ce take yi, ana shirin cartoon.
Cikin nishaɗi yaran ke ta cin inibin su na zubarwa, ɗaya daga cikinsu kuma yana jikin mutumin yana tana jagwalgwala nasa inibin cikin nutsuwa.
Sallamar da ya yi ne ya sanya su waiwayawa, Muhsin ya jefar da inibin hannunsa, ya nufi Mahafinsa da gudu. Hammad ya ɗaga shi yana murmushi ya ƙarasa shiga cikin falon sauran yaran maza su ma suka nufi Hammad.
Ya rungume su yana murmushi ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Kai ne ka ke wasan da su da sassafen nan?"
Zahradeen ya yi murmushi ya ce "To ya na iya, su wannan biyun sun hana mamansu sakat da rigima, shi ma Muhsin sai kuka yake yi yau, yana kiran Umma, duk sun rikitata, shiyasa na kwaso su muka dawo nan"
Hammad ya yi murmushi ya ce "Ina godiya sosai da sosai"
Zahradeen ya tsuke fuska ya ce "Da aka yi me?"
Hammad ya sake yin murmushi ya ce "Tuba nake baban Muhsin"
Imam Zahradeen ya zauna sosai ya ce "Yaya ake ciki ne? Sultan bai kuma ce maka komai ba haryanzu?"
Hammad ya girgiza kai ya ce "Ina dai jiran abin da zai ce, kawai dai yana yawan ce mini, sai abin da aka yanke na shawara"
"Ka ga Imam, ka tsaya ka nutsu da kyau ka duba makomarka da makomar wannan jaririn yaron naka. Yaron nan na buƙatar mahaifiyarsa, kuma ina ganin ka dawo da mahaifiyar Mahmoudu gidan nan, su zauna kafin komai ya daidaita, na ga ya saba da ita sosai. Ka san ba abu ne mai sauƙi su bari ka fito da ita daga gidan nan ba. Saboda ina tsoron shawarwarin da Matawalle da kum Sardauna za su yanke a kan matsalar nan. Ba dan kar na yi musu ƙazafi ba, da na ce sun fi mutunta Al'adar Agadez sama da addininsu."
Hammad ya ce "To ina nan dai ina sauraren su, na ji hukuncin da za su yanke ɗin"
Imam Zahradeen ya ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi"
Imam ya amsa da Amin.
****
Jikin Shukura ne yake tsuma, tana kallon Yusra a inda suke ɓoye, ga ta rungume da jariri da yake ta ƙoƙarin farkawa ya tsala ihu.
Yusra na riƙe da jaririn tana yi wa Shukura alama da ta kwantar da hankalinta.
Ɗaya bayan ɗaya mutanen suka fita daga cikin ɗakin, ɗayan ya kira wayar Alhaji Zailani. Yana ɗagawa ya ce "Yaya kun same ta?"
"Alhaji mun caje Asibitin nan kaf bamu ganta ba, ga shi sun yi mana barazanar kira mana jami'an tsaro kar su kama mu"
"An bani tabbacin ta na cikin Asibitin nan, a yadda binciken nan ya nuna, dole ku nemo ta ba sai na ganta ba ku kashe ta kawai, dan ba za ta tona mini Asiri ba"
Jaririn hannun Yusra ne ya tsala uban ihu, hankalin mutanen ya dawo kan ɗakin, ɗaya daga cikin su ya juya da sauri ya nufi ɗakin.
*****
Nana tana tsaye a gaban mudubi, ta saka riga ta alfarma, gaba ɗaya jin ta take kamar a cikin tarko, ta gaji da zaman guri ɗayan nan, hankalinta na kan a ƙarƙare abin da za a yi, a bata ɗanta ta koma Nigeria.
Gefe guda kuma zuciyarta na ci gaba da wasi-wasi da son lallai sai ta ga mene ne a rufe a wannan ɗakin na gidan tarihin Agadez.
Asal ce ta bankaɗo ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske sai da Nana ta tsorata. Ta kalli Nana cikin doguwar riga mai maɗauri, ko 'yar uwatta mace zata sarawa kyawun dirin da Allah ya bata, balle ɗa namiji.
Wani abu ɗacin gaske ya taso wa Asal, Gimbiya Bilkisu ce ta biyo bayan Asal. Nana dai ta tsaya ƙyam tana kallon su.
AREWABOOKS
Da sauri ya dawo, ya buɗe ɗakin jin kukan jariri, kawai ya tarar da Yusra a zaune a kan gado, tana jijjiga jariri.
Cikin tsawa ya ce "Ke, me ki ke yi a nan wace ce ke?"
Yusra ta ce "Kamar yaya? Nice a ɗakin nan, lafiya suwaye ku?"
"Ya aka yi da muka shigo ɗakin nan bamu ganki ba?"
Yusra ta ce "Ku na tsaye a bakin ƙofa na zo na wuce ku, na je na karɓo jaririna daga ɗakin jarirai