Showing 75001 words to 78000 words out of 124686 words
ne, an sallamo shi daga can"
Ɗayan ya ce "Ke ƙarya ki ke yi, mene ne sunanki?"
Yusra ta ce "Ban gane mene ne sunana ba, suwaye ku tukuna me kuma ku ke nema a gurina ni ban sanku ba"
Ɗayan ya dubi hoton cikin wayarsa, ya kalli Yusra ya ga sam babu haɗi.
Ya tunkaro Yusra ya ce "Ki gaya mana mene ne sunanki?"
"Yusra, sai kuma me?"
"Na ke ce wata mata ta tsinto, ta kawo Asibitin nan ba?"
"A ka tsinto kuma kamar wata kuɗi? Ni ban san zancen ba, mijina tare muka je na ɗaukko jaririna. Yanzun nan yayata kuma za ta dawo da take zaune tare da ni. Amma mene ne dalilinku na zuwa ku ritsa ni kuna tuhuma ta." Ta yi maganar cikin dakiya tana tsare mutumin da ido. Ƙasam zuciyarta fata take yi, Ubangiji Allah ya sa kar Shukura ta ce za ta fito ta tona musu asiri.
Ɗayan ya ce "Ba fa ita ba ce ba, mu koma mu gaya masa ba ta Asibitin nan, ba a ba shi bayanin daidai ba" Suka ƙara ƙare wa Yusra kallo sannan suka fice.
Abin da ya faru kuwa, Shukura babu yadda ba ta yi da Yusra ta tafi ba, amma ta ce babu inda za ta je ƙafarta ƙafarta, ba za ta tafi ta bar ta ba. Ga shi ta uzzura mata da tambayoyin yaya aka yi ta ɓata aka neme ta aka rasa. Alamu ya nuna mata haryanzu Yusra da saura kan babu daɗi dan haka ta ce mata sace ta aka yi, ta kuɓuta da ƙyar shi ne wata mata ta tsinto ta ta kawo ta Asibiti.
Yusra ta ce "Lallai kin auna arziki tashi mu tafi to"
Shukura ta ce "Ai ba a sallame ni ba, ba zai yiwu mu tafi ba, ba ni da cikakkiyar lafiya fa"
"To ba sai mu koma Asibiti a can cikin gari ba, kin ga yadda mamanki ma hankalinta yake a tashe, idan muka je da Baban Haidar ta yi ta kuka"
Wata Nurse ce ta yi sallama, suka gaisa da su Shukura, ta yi wa Shukura allurai. Wata ce ta sake shigowa da sauri, ta kalli Shukura ta ce "Ke ce Shukura ko?"
Ta jinjina kai.
"Wasu mutane ne suka zo, wai 'yar uwassu ce ke dubiya suka zo, amma yanayinsu kamar marasa gaskiya, mun ce babu mai wannan sunan, saboda mun san case ɗinki, amma ga shi can ana ta faɗa da su sun ce sai sun caje Asibitin nan, 'yar uwassu ce ke dole su ganki"
Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskar Shukura.
Nurse ɗin ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai an kore su ma, kar ki damu" Bayan sun fita a rikice ta kalli Yusra ta ce "Ina ga wanda suka sace ni ne suka biyo ni nan, dan Allah ki tashi mu tafi "
Yusra ta ce "Ai da tuni mun tafi ki ka dage, yanzu bamu san suwaye ba, idan muka fita ai sai a samu matsala. Dole mu jira zuwa anjima sannan mu saci jiki mu gudu."
Da ƙyar Shukura ta amince sai dai da aka jima suna tsaka da shirin guduwa, suka ji muryar mutanen a waje, Shukura ta rikice, Yusra ta yi dabarar janta su ɓuya.
*****
Bin su da kallo Nana take yi , Asal ta ƙaraso gaban Nana cikin huci da zafin rai, tana kallonta kamar ta kai mata duka.
"Munafuka, muguwa, na jawo ki jikina ashe haɗa baki aka yi da ke a cuce ni? Kin auri mijina kin haihu da shi ban sani ba, kuma da yake ke munafuka ce, ba ki taɓa gaya mini saboda ba kya tsoron Allah. Wallahi idan ba ki rabu da shi ba, sai na kashe ki, na kashe ɗan naki dole ki koma inda ki ka fito a yau ba sai gobe ba, 'yar matsaiyata ƙasƙantacciyar halitta"
Nana ta dubi Asal ta ce "Subhanallah, ai Allah kaɗai ya san ƙasƙantaciyar halitta ba ke abar halitta ba. Kuma ɗan ja da baya, numfashinki yana takura mini a fuskata, sai na baki amsar maganganun"
Asal ta rikice ta kalli Gimbiya Bilkisu ta kalli Nana, ita kanta Gimbiya ganin Nana da ta yi ta ɗauka sokuwa ce ba ta magana. Nana ba ta jira me za su yanke ba ta matsa daga gaban Asal ta ce "Wannan abubuwan da ki ke faɗa, duk ba ni za ki gaya wa ba, Sayyid za ki gaya wa domin igiyar aurena a hannunsa take. Sai ki ji amsar da zai baki. Kuma ni Allah ya bani haƙuri da na zauna ina kallonki da mijina ban nuna miki komai ba, na biki a yadda ki ke so zuwa lokacin da ya dawo hayyacinsa ya gane ni.
Dan haka yanzu da ki ka san komai, ni ba baiwarki ba ce, kuma ba kukun mijinki ba ce, matarsa ce wato kishiyarki"
Asal cikin ƙaraji ta hankaɗa Nana ta ce "Wallahi na fi ƙarfin na yi kishi da ke 'yar matsiyata ƙazama, baƙa mummuna. Wallahi sai na kashe ki na kashe abin da ki ka haifa." Gimbiya Bilkisu na ƙoƙarin riƙe ta, amma sai fizge-fizge take yi tana ihu.
"To Bismillah Asal, ki kashe ni idan har hakan zai sanya ki huce. Ba za ki taɓa canzawa tuwo suna ba, Hammad mijina ne, wanda na fiki ƙaunarsa"
"Ke ya ishe ki malama, dan kin ga na yi shiru saboda ba ki da kunya da mutunci sai ki tsaya kina gaya mata maganganun banza? To bari ki ji na gaya miki, sai kin bar gidan nan a yau ba sai gobe ba. Sai kin bar gidan nan buzayen jinin sarauta ba sa raɓar talaka, balle su aure su su rayu da su. Sai kin bar gidan a wulaƙance cikin ƙasƙanci kuma sai an hukunta Hammad kan laifn da ya aikata"
Nana ta ƙare wa Gimbiya Bilkisu kallo ta ce "Haba Mama, ke da ba da ke nake kishin ba? Nifa kamata ya yi a sara mini akan haƙurin da na yi. Kuma ko ba komai, dole sunan 'yar matsiyata ya shiga kundin tarihin Agadez, mace ta farko da ta karya tarihi bayan ɗaruruwan shekaru. Ku daina zagina dan ban yi muku komai ba, abin da na sani kawai na fi Asal son Hammad har Duniya ta naɗe, haka zalika ba ni da tsara a zuciyarsa ki yi haƙuri"
"Ƙarya ki ke yi, yadda na yi amfani da kuɗi na mallake ki ta ƙarfin tsiya, haka zan yi amfani da su na yi maganinki mummunan a bar ƙyanƙyami"
Nana ta ji zafin maganganun Asal, amma ta yi murmushi ta ce "Ke kin ga alamar muni a tare da ni, kalli da kyau Gimbiya Asal. Kodayake ba wannan ba ma; kar ki manta kina magana da matar da ki kai gidan da ki ke kwana kina shaye-shaye da kaɗe-kaɗe da ƙawaye a lokacin da ba ta san halin da mijinta yake ciki ba, kar kuma ki manta matar da ki ke bawa magani ta zuba a shayin Imam Hammad, haka zalika matar da ta san kina ajiye masa takarda mai hoton ƙwarangwal da yake ci da wuta, wanda shi ne yake burkita masa hankali da lafiyar jiki; wannan matar ita ce matar mijinki kuma baƙa mummunar da ki ke ta kushewa ki ke iƙirarin kashewa"
Dummm ƙirjin Asal ya buga da ƙarfi, ta ƙwalalo ido tana kallon Nana.
Nana ta ci gaba da cewa "Ni ba karabutin mutanen da ki ka saba wulaƙanwatawa ba ne, kasancewar Hammad mijina ya sanya na bar idanuna a buɗe ta kowace kusurwa a kansa, tunda na haihu da shi, har abada ba zan bari wani abu mummuna ya same shi ba"
Asal ta tattaro jarumta ta yi murmushin ƙarfin hali, bayan da mararata ta cika taf da uban fitsarin tsoro.
"Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo ƙarshena a masarautar Agadez, saboda ba ki za hujja a kan wannan soki burutsun da ki ke yi" Ta yi maganar tana tsare Nana da ido.
Nana ta ce "Kwantar da hankalinki, ba na buƙatar wata hujja ko wani abu, dan har gaban Abada ba zan taɓa tona miki asiri ba. Ai Hammad yana sonki kuma ko ba komai 'yar uwassa ce ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, amma daga yau da rana mai kamar irin ta yau, muddin ina tare da Hammad da ke da duk wani abu da yake kawowa rayuwarsa wani tarnaƙi"
Gimbiya Bilkisu ba ta bari Asal ta sake magana ba, ta kama hannunta suka yi waje.
Nana ta ja numfashi tana bin bayansu da kallo, kafin tsunduma tunani.
Gimbiya Bilkisu ta kalli Asal ta ce "Ke, kina wani wawanci har ki ka bari ta san kina wannan abubuwan? Asal kina da hankali kuwa?"
Cikin kuka ta ce "Ammi yaya zan yi, wallahi ban san da wata alaƙa a tsakaninsu ba, ban sani ba. Kuma ban san za ta kawo wani abu ba. Na shiga uku ba zan iya rayuwa babu Hammad ba wallahi Ammi ina son mijina, kuma ba zan iya buɗe ido na gan shi da wata ba ki taimake ni"
"Nutsu ki kwantar da hankalinki, bari na yi wa babanki magana a san abin yi a yau ba sai gobe ba, dole a san yadda za a yi da yarinyar nan ki daina kuka" Da kyar ta din ga rarrashin Asal.
Nana na zaune na zaman jiran dawowar Hammad,furucin Asal ya tsorata ta, ta fuskanci da gaske kowa na iya aikata duk abin da yake so, a wannan gidan domin cimma burinsa.
Ita ba ta kanta take yi ba, ta ɗan jaririn ɗanta da ba ta san inda yake ba ta shi take yi. Ta ƙudurce a ranta, idan Hammad ya dawo, bori za ta yi masa sai ya fitar da ita daga gidansa komai zai faru, amma ƙasan zuciyarta yana ta azalzalarta a kan son a buɗe wannan dakin na gidan tarihin.
Bayan azahar ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata a cikin damuwa yake.
Ya nemi guri ya kwantar da kansa a kan cinyarta. Nana ta shafa kan a hankali ta ce "Lafiya kuwa?" Ya jinjina mata kai kawai.
"Ka ci abinci ne?"
"Na ci" ya amsa a hankali.
"To meyafaru?"
Ya ce "Babu komai"
Nana ta numfasa ta ce "To dan Allah ina son ka dawo mini da Muhsin, kuma nifa na damu na koma gida, Sayyid hankalina a tashe yake wallahi, na san iyayena sun gaji da nema na"
"Asmy kar ki ƙara mini damuwa dan Allah, ina sane da komai, a tsare nake yin komai in sha Allah zai wuce"
Cikin damuwa ta ce "Zai wuce yaushe? Shekera ta uku nake shirin yi a ƙasar nan, nima ina da ahali bai kamata na tare a nan ba" Ya tashi zaune cikin damuwa, ya kalle ta zai yi magana, amma bai yi ba ya ciro wayarsa da take vibrating"
Da to kawai ya amsa ya tashi ya fita. Nana ta koma ta nemi guri ta zauna cikin damuwa.
Da sallama ya shiga ɗakin, ya tarar da Asal ga Sultan, ga Matawalle ga Tafawa da Sardauna sai Gimbiya Bilkisu da take ta ƙoƙarin rarrashin Asal. Gefe ga Imam Asadullahi ga kuma Imam Zahradeen rungume da Muhsin. Asal ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu ganin Muhsin, dan babu abin da ya banbanta shi da Hammad.
Yayi mamakin yaushe aka yi masa wannan gangamin har haka? Bayan bai jima da barin gidan Imam Zahradeen ba ya tsaya a gurin Mahmoudu.
Sardauna ya ce "Ka je ka zo da babar yaron nan" Babu kara ya karɓi ɗansa a hannun Yayansa Imam Zahradeen, ya tafi inda Nana take. Ya kai mintuna sha biyar, sannan suka dawo tare. Nana suka yi ido huɗu da Asal da idonta ya kumbura, Nana ta sakar mata murmushi ta kawar da kanta gefe. Guri ya tsit sai Muhsin da yake ta hawa jikin Nana yana yi mata surutunsa na yara.
Zahradeen ya ce "Imam Muhsin, ka yi shiru"
Sardauna ya yi murmushi ya ce "Har ya zama Imam shi ma?"
Zahradeen ya ce "Eh mana Allah ya taimake ka. Ɗan Imam ai Imam ne" Suka yi murmushi.
Tafawa ya ce "Yakamata mu yi abin da ya tara mu, ba tare da ɓata lokaci ba."
Sardauna ya ce "Haka ne kam, Imam Hammad" Hammad ya ɗaga kai ya kalli Sardauna. "Duk da mun san aurenka da ita wannan 'yar Nigeria, ƙaddara ne daga Allah, Amma ina fatan ka sanar da ita matar taka, sharaɗin ƙasar Agadez na rashin auren bare?".
Gaban Hammad ya faɗi, Nana kuma ta kalle shi suka yi ido huɗu.
Sardauna ya dubi Nana ya ce "Ina fatan ya yi miki bayani?"
Nana cikin girmamawa ta ce "Eh ranka ya daɗe. Ya yi mini na sani"
Sororo ya bi Nana da kallo.
Tafawa ya yi caraf da zancen, ganin ana neman a ɓata masa lokaci.
"Amm dama na nemi a yi wannan zaman ne, domin na san mene ne makomar 'yata, sannan wane hukunci za a ɗauka a kan Hammad, bisa karya dokar Agadez"
Hammad ya numfasa ya ce "Ai ni ba ni da wata matsala da Asal, ban sake ta ban kuma yi wani abu da...
"Kai dalla rufe wa mutane baki, ai na san baka saketan ba, amma mene ne matsayinta? Zaka zauna da ita ne? Ka saki waccan yarinyar ko kuma mene ne?"
Hammad ya tsuke fuska ya yi shiru.
Matawalle ya ce "Amma mai girma Tafawa, bai kamata a je ga wannan maganar ba. Kana neman sanin matsayar Asal ne?"
Tafawa ya ce "Ka bari mu yi magana da shi ka daina saka mini baki"
Hammad ya ce "Makomar aurena da Asal, yana daga gare ta, idan tana son zama da ni, ba wani abu dama ni ban ce ba zan rayu da ita ba. Amma ina mai neman afuwarku ina shirye na ɗauki duk wani hukunci da za ku yi mini, amma sau ɗaya a rayuwata, nima ina neman ku yi mini alfarmar nan, ba zan iya sakin Nana ba, mussaman da rabo ya shiga tsakanina da ita. Ba zan iya sakinta ba".
Sak suka yi su na bin Hammad da kallo.
Sultan ya numfasa ya ce "Hammad, ba kai ka ke da ikon yanke wannan hukuncin ba, sai abin da muka yanke maka. Mai girma Tafawa muna mai baka haƙuri, Hammad ya tabattar da cewa aurensu yana nan daram, dan haka yakamata ta kwantar da hankalinta."
"Babu batun kwanciyar hankali a nan, sai zuwa yaushe zamu san matsayarta, yarinyata tana wuni ta kwana babu bacci. Kuma da haka ku ke shashantar da duk wani laifi da zai aikata ba tare da an hukunta shi ba. A wannan karon dole a bar doka ta yi aiki a kansa, kuma a zartar da duk wani hukunci da yakamata a kansa. Ya saki matar nan a yanzu ya bata ɗanta ta tafi inda ta fito shi kuma a hukunta shi"
Hammad ya girgiza kai ya ce "Zan karɓi kowane irin hukunci, amma ba zan rama sharri da alkhairi ba"
Asal ta rushe da kuka tana rirriƙe Gimbiya Bilkisu.
95
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
Tafawa a fusace ya ce "Kun gani ko? Abin har ya kai raini ya shiga tsakaninmu ya faɗi duk abin da ya ga dama. Kamar yaya ba za ka rama sharri da alkhairi ba, waye ya yi maka sharrin waye ya yi maka alkhairin?. Ya yi wa dokokinmu karan tsaye. Kuma dolensa ya yi murabus a gaban majalissa, a ba wa wani tun da ga taka mana doka, ga kuma rashin zobensa sannan wannan ɗan da yake tutiya da shi, babu wanda yake da yaƙinin na halal ne tun da babu waliyyinsa ko ɗaya a lokacin da aka ɗaura auren."
"Zan jura komai amma ni ba mutumin banza ba ne ba, kuma kar ka sheganta mini ɗa, ban san da wace kalmar za a yi mana bayanin halin da na shiga har na auri Nana ka yarda ba. Tsawon shekaru ina yi muku biyayya, ko ina so ko ba na so, dokar Agadez ba dokar Allah ba ce ku bari na samu nutsuwar zuciya mana, idan ba so ku ke ku wayi gari ku ga na bar muku duniyar ba. Ta yaya zan yi wa Allah butulci akan abin da nake nema? Yarinyar da ta rayu da ni a lokaci mafi tsananin da babu wanda zai iya zama da ni ina hauka, na haɗu da larurar da hatta najasata ita take gyara mini da hannunta ba tare da ƙyama ta ba. Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, Asal na da zaɓin zama da ni ko ta ƙi na bata wannan damar, amma ba zan saki Nana ba ko zaku rataye ni"
Sultan ya miƙe tsaye a fusace ya ce "Hammad!"
Imam Zahradeen ya miƙe tsaye shi ma, ya dubi Sultan ya ce "Ya kai Abbanmu abin alfaharinmu, a duniya ba na tunanin ka taɓa son wani abu kamar yadda ka ke son Imam Hammad, kuma bana tunanin akwai wani wanda yake yi maka biyayyar da yake yi maka. Tun da ta kai shi ga yin sa in sa da ku, to tabbas ya kai bango. Amma ko sau ɗaya yakamata a ce mai girma Tafawa ya yi maka kara a kan Imam Hammad, amma duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsa da Asal, ƙarara yake goyon bayanta a turasasawa Hammad yin abu dan faranta mata, sau ɗaya ko dan saboda shi yakamata a yi wa dokar Agadez kwaskwarima.
Gimbiya Bilkisu ta ce "Zahradeen kana da hankali kuwa? Waye ya sanya da kai?"
"Ummi ki yi haƙuri, kina duba mafitar ɗan uwanki da 'yarsa, nima ta nawa ɗan uwan nake dubawa."
"Ni ka ke gaya wa haka Zahradeen?"
"Ina neman afuwarki, amma dan Allah kar ki yi mini mummunar fahimta Ummi."
A fusace Sardauna ya ce "Ya isa haka, ya isa, kun manta a gaban wa ku ke ne? Ya za a yi kowa ya din ga magana yadda ya ga dama, babu ɗaa da girmamawa?" Kowa ya yi shiru.
Nana cikin ladabi ta ce "Ina mai neman afuwarku, na san wannan hatsaniyar ta faru ne duk a dalilina. Amma da na san wannan al'amari zai faru, ko haka dokar ƙasar nan take, ba zan yi gangancin auren Sayyid ba. 'yan uwansa ba su yi mini wannan bayanin ba. Haka zalika ban faɗi haka dan a ga laifinsu ba, kamar yadda suka gaya mini shi ya nemi a biya sadakina ya aure ni. Amma kamar yadda wannan shugaban ya faɗa" Ta yi maganar tana kallon Tafawa.
"Na amince zan ɗauki ɗana na koma Nigeria, idan ma kun ce ba ku da