Showing 120001 words to 123000 words out of 124686 words

Chapter 41 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

62

saka miki cutar da ke da na yi, ba tare da wata halattacciyar hujja a kan shari'a ba."
Nana na kuka ta ce "Ƙaisar na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana gaba ɗaya, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka ya sanya ka cikin salihan bayinsa. Ba zan taɓa mantawa da kai ba har abada"
"Nima ba zan manta da ke ba Asma'u jikar Lanti. Ina fatan za ki yi ilimi mai zurfi ki karanci fannin ilimin magungunan musulunci da na gargajiya "
Nana ta ce "Na yi maka alƙawarin haka. Amma daga nan ina zaka je?"

"Can nesa da Duniyarki, zan nemi ilimi sosai "

"Dan Allah ka tafi da Haula mana, tana matuƙar sonka da ƙaunar ka"

Ya miƙe tsaye yana murmushi, ta ga ya zama wani irin dogo mara misali. Ta ja da baya tana kallonsa. Ta din ga jin muryarsa a sama ya ce "Yi haƙuri, kar na tsorata ki, duk suffar da ki ke ganinmu a cikinta da ni da Giyaz, ba suffofinmu ne na halitta ba, idan muka fito muku a siffofinmu na halitta zaku iya rasa rayukan ku, ko ku zauce. Mu kan suffantu da abubuwa ne da idanunku za su iya kalla. Na gode sosai da sosai uwar gijiyata ina yi miki fatan alkhairi."

"Wayyo Allahana, shikenan ko ziyara ba zaka sake kawo mini ba. Tabbas a kan ka na yarda a sauran halittu akwai bayin Allah na ƙwarai, ba zan taɓa bari a raba ka da rayuwarka ba kai ma. Ina yi maka fatan alkhairi uban ɗakina, kuma ɗan uwana. Na san ba haka kurum Allah ya haɗa ni rayuwa da kai ba, duk da mu na da banbancin jinsi"

Kuka take yi iya ƙarfinta, Hammad yana riƙe da ita gam a jikinsa, sai mimmiƙewa take yi tana ci gaba da kiran Ƙaisar.

"Asmyna, ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" Ta buɗe idanunta a hankali ta kalli Sayyid, ta kalli dattijon malamin nan, ga su Sultan a gefe duk a cikin wani ɗaki. Ta fashe da kuka ta ce "Shi ma an kashe shi ko?"

Ya girgiza mata kai ya ce "A'a yarjejeniya kawai aka yi da shi, ya ce kun riga kun gama magana ma, ya yi miki alƙawarin ya tafi ya rabu da ke har abada"

"Shikenan ba zan sake ganin Ƙaisar ba? Ya cutar da ni, amma... Sai ta kasa magana ta ci gaba da kuka.
"Na sani, na san komai Asmy ki yi haƙuri, mu na da banbancin da ba zai yiwu ki ci gaba da rayuwa da shi" Haka suka din ga rarrashin Nana. Shi kansa malamin ruƙiyyar cewa yayi bai taɓa samun case mai rikitarwa kamar na Nana ba, domin shi kansa Ƙaisar sai da ya yi kuka ba kaɗan ba, kafin ya ƙara tabattar wa malamin ruƙiyyar nan cewar ya bar ta har abada.

Kwana biyu suka ƙara a Egypt, Nana sam ba ta walwala kamar wadda aka raba da mahaifinta, gaba ɗaya memories ɗin abubuwan da suka din ga faruwa a rayuwarta a tsakaninta da Ƙaisar suka din ga dawo mata. Tabbas za ta kasance cikin biladama masu ban mamaki da suka yi rayuwa mai kusancin gaske tsakaninsu da Aljanu.
Sai da suka ƙara kwana biyun.
Haka Hammad ya haƙura ya din ga rarrashinta, saboda yadda duk ta danu, domin yana iya tuna wasu abubuwan da suka din ga faruwa tsakaninsa da Ƙaisar saboda Nana.
Suka koma ta Nigeria, har da Sultan da Matawalle, suka gaisa da iyayen Nana, tare da sake jaddada musu godiyarsu, bisa ga abin da Nana ta yi wa yaransu na kulawa, tare da yi musu bangajiya na zuwa biki da suka yi Agadez.
Tun da suka koma Agadez, hasashen Hammad ya tabatta, domin kuwa laulayi ne sosai ya kada Nana.
Babban abin da yake damun Hammad, bai wuce duk yadda ya so, ya haɗa kan Nana da Asal ba, Nana ta ƙi yarda ta ce masa komai zai yi Asal ta riga ta furta mata ba ta ƙaunarta, kuma duk mutumin da zai nuna baya ƙaunarka ba ta ga abin mu'amala da shi ba. Sai dai ya ci gaba da matsa mata har ya yi fushi.
Ta ce "Sayyid, bari na yi maka gwari-gwari tabbas ina jin zafin ƙiyayyar da Asal ta nuna mini, amma muddin za mu din ga haɗuwa, ko ka ce sai mun haɗa kai, ba zata taɓa sakewa ba, zan zame mata takura kasancewar na san sirrinta, za ta din ga ganina da abin. Bana fatan zame wa kowa matsala a rayuwata, ba na fatan Asal ta rayu a takure saboda ni. Dan haka ka yi haƙuri ka ƙyale ni"
Ya gaji ya gaya wa Sultan halin da yake ciki da Nana, ya ce duk ya kai masa su can gida.
Tun da Asal ta ga Nana, hankalinta ya ƙara tashi, ganin Nana da juna biyu a lokacin ya ɗago sosai, ga kuma Muhsin da tana ganinsa a wallpaper Hammad. Nana ta ƙara cika ta yi kyau sosai da sosai.
Sultan ya yi musu nasiha sosai da sosai, tare da roƙonsu a kan komai ya wuce, idan ba haka ba muddin suka tafi a haka, to irin jahilcin da ya din ga faruwa a baya, na faɗan 'ya'yan sarakuna a baya, to kuma zai iya faruwa naku gidan, dan haka ku yi haƙuri ku tura komai baya. Nana sai da ta ɗan sha jinin jikinta, ko a lokacin yanayin yadda ta ga Asal kamar gaba ɗaya a tsorace take, duk ta kame jikinta babu izzar nan da jin kai da take yi a baya.
Suka yi masa godiya, Nana ta tabattar masa da in Allah ya yarda komai zai canza. Asal ta lura da yadda shi kansa Sultan ta Nana yake yi, yanzu baya nuna mata kulawar da yake ba ta a baya. Ta lura Hammad ne kawai ya yafe mata yake yin ta.
Duk yadda ta so share Muhsin, son da take yi wa Hammad, da kamanin da suke yi da Muhsin ɗin, sai da ya sanya ta tsaya kula shi. Babu inda ya bar Hammad a kamanni.
Nana ba ta fasa jin kewar Ƙaisar ba, ita kanta har ƙoƙarin faɗa take yi wa kanta, amma sabo turken wawa, babu yadda ta iya, idan abin ya ishe ta har kuka take yi.
Jamila ta riƙe istigfari da addu'a, da magungunan da Nana ta bata, cikin ikon Allah ta din ga samun afuwa, a kan lamarin larura da take fama. Lamarin Suwaiba ne dai ba arziki. A hankali tana juya kuɗin da Nana ta bata, idan jarin ya karye ta kira Nana, ta ƙara bata wani, gefe Nana tana lallaɓa Baba har ya haƙura yake shiga sabgar Jamila. Gaddafi ma ya yi aure, ya sha tagomashi daga gurin Nana. Nana ba iya gidansu ba, hatta maƙwabtansu sai da suka shiga rigar arzikinta. Tana samun kuɗi sosai a Agadez, ga allowance ɗin ta na sarautarta, ga na kasamcewarta matar Sardaunan Agadez. Ga shi Hammad yana sakar mata kuɗi sosai da sosai. Ban da tarin kyaututtuka da take samu.
Nana ta ƙyale Hammad yake zuwar wa da Asal Muhsin, sai dai ta tsananta addu'a. Su Tafawa suka zama ba su da wata power ko ƙarfin faɗa a ji, dan hatta dogarai da jami'an tsaron da suke tare da su, sai da aka janye musu, aka yanke albashin da masarauta take biyansu.
Hakazalika duk wani kasuwanci da masarauta ke gudanarwa, ake samun riba da Nana da Muhsin a ciki.
Watan Nana tara da sati biyu cif ta sake haihuwa namiji.
Hammad kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, kasancewar kaf Agadez Nana ba ta da uwar da ta wuce Nene, ita ce tsaye a kanta a kan komai. Nana ta yi mamakin ganin Asal ta zo yi mata barka.
Ahmad aka sanya wa jaririn, ake kiransa da Hamdan. Har da kyaututtuka Asal ta bayar a ba wa jaririn. Sosai take jin tausayin Asal, a zuwa ukun da ta yi ganin jaririn, duk lokacin da ta zo, daga gaisuwa babu abin da yake haɗa su da Nana, amma idan ta karɓi jaririn tana daɗewa sosai da sosai tana kallon yaron.
Iya ƙoƙari Hammad yayi, a kan mantawa da duk wani abu da Asal ta aikata, amma bakin alƙalami ya riga ya bushe, lokuta da dama abubuwan da ta aikata masa su na dawowa zuciyarsa.
Ita kanta a dole, take ƙoƙari take rintse idanunta ta kawar da kanta daga wasu abubuwan da yake aikatawa, Nana ke da miji Nana ne da 'ya'ya, kuma take da goyon bayan uban miji, da masaurauta ma baki ɗaya.
Gimbiya Bilkisu ta din ga ziga ta, a kan lallai ta haƙura da auren nan, amma Asal ta ce ba za ta haƙura ba.
Wataran Mahmoudu ya kawo musu ziyara, tare da matarsa, ana falo suna ta hira, yake bawa Mahmoudu labarin, darun da aka sha da Nana a kan raba ta da Ƙaisar.
Mahmoudu ya hau dariya ya ce "Wasa-wasa fa, Gimbiya akwai daru, banda ita wa yake fatan tarayya da Aljani?"
Hammad ya yi dariya ya ce "Mahmoudu sabo turken wawa, ita idan ka lura da ita ne, gaba ɗaya rayuwarta ba ta da damuwa, kuma tana da matsanancin tausayi amma Aljanin nan ya azabtar da ita, ni kuma ga mahaifinsa na gana mini azaba, wallahi yarinyar nan Allah ne yake kare ta, da wata ce tsaf zata haukace.
Saboda azaba har a zahiri muke ganinsu, na zo da muka koma Buda hannuna na dama ya shanye, bakina ya koma gefe nikaɗai na san azabar da nake sha. Ga laulayi tana yi ga jinyata. Idan na fita daga hankalina na yi yinƙurin kashe ta, sai na dawo hayyacina sai na ga abin kamar a mafarki. Duk yadda zan kwatanta maka azabar da muka sha mutum sai dai ya ji kamar labari. Saboda jarabar Ƙaisar da babansa aka tashe mu daga wani gida da muka zauna aka ce mayya ce. Amma sau ɗaya Asmy ba ta taɓa nuna mini a fuskarta za ta rabu da ni ba, saboda ta yi imanin idan ta rabu da ni wa zai kula da ni. Amma yarinyar nan ina lallaɓata ina tuna mata abubuwan da Ƙaisar ya yi mata na cutarwa sai cewa ta yi ina ruwana, lokacin da na gudu na bar ta na san me ya yi mata? Kuma ai ta yafe masa tun da ya yi mata abin alkhairi. An sha daru kan su rabu. Tana nan tana gaya mini sai ta rubuta littafi guda, a kan Aljanu saboda Ƙaisar. Tun ina kishi da aljanin nan na haƙura da na gane dai duk abu ba jinsinmu ɗaya ba"
Suka din ga dariya, Asal dai ta yi shiru, ita zancen ma tsoro ya hau bata.
Fadila kuwa ta din ga yi masa tambayoyi, a kan yadda aka yi ya zamana Nana ɗauke da ɗa a jikinta shi kuma Uba.
Babban abin da ya bata tsoro da mamaki, cewar da ya yi, har ciwon ɓarin jiki yayi, da irin wahalar jinya da Nana ta yi. Ya din ga misalta musu irin yadda yake ji, idan ciwon nan ya tayar masa yadda yake jin kamar ya kashe kansa saboda azaba.

Asal duk sai ta tsargu, ta kalli fuskarsa ta ga hirarsa kawai yake yi, hankali kwance, ba domin da alamar wata manufa a fuskarsa ba.

10YRS LATER
Muhsin na da shekaru goma sha huɗu a Duniya, Nana ta kammala karatunta, na ilimin magungunan addinin musulunci. Hammad ya taimaka mata, ta gina katafariyar cibiyar koyar da addinin musulunci, wata a Agadez wata a Nigeria.
A lokacin Nana yaranta huɗu duk maza, tana sanye da glass a fuskarta tana rubuce-rubuce, Hammad ya kira ta ya ce mata Asal ce ta kira shi ba ta da lafiya, ko za ta tura mata ko Yarima ne, idan da wani magani da za a bata kuma a bata.
Nana ta ce "Ahh me Yarima zai iya yi, bari na je da kaina".

Ko da ta je gidan kuwa, tuni Muhsin yana can, Nana ta ce "Amma maimakon ku kira ni ku gaya mini, me Muhsin zai iya yi miki?"

Asal dai ta yi shiru, Muhsin yana kusa da ita ya ce "Kawai zuwa na yi nima, na tarar da ita bata da lafiya"

Nana ta ce "Ina ganin kawai mu tafi Asibiti" Nana ta taimaka mata ta canza kaya, suka tafi Asibiti.

Likitoci suka ce tiyata za a yi mata a cire abin da yake cikinta. Nana ta kira Hammad ta ce masa lallai ya dawo, tiyata za a yi wa Asal ana buƙatar a saka hannu.
Ya ce "Ki saka, ba zan iya dawowa a yau ba, sai zuwa gobe in Allah ya kaimu"

Nana ta ce "To ai ba zai yiwu ni na saka ba, ko a kira mahaifinta a waya?"

Da sauri ya ce "A'a bari na kira Sultan, kuma ki tsaya ki bayar da order, kar wani ya zo a ba shi ɗana, idan ba ke ko Sultan ba, babu yadda zan yi na dawo ne"

Haka aka yi, Sultan ya je Asibiti da kansa ba wakilici ba, ya sanya hannu aka ciro wa Asal jaririyarta. Nana aka fara ba wa yarinyar, ta yi wata irin ajiyar zuciya tare da gode wa Allah, sannan ta kai wa Sultan ita.

Ya rungume yarinyar yana kallonta cike da ƙauna, ya ce "Kin ga ikon Allah, bayan shekaru kusan ashirin da aure, sai yanzu Allah ya yi ikonsa"

Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya, Abin da na yi ta gaya wa Sayyid kenan, ba a cire rai da rahamar Allah.
Asal na kwance a post up room, ta buɗe idanunta a hankali, ta kalli Nana da take ta shafa kan jaririyar. Tsawon wannan shekarun, babu wata jituwar arziki a tsakaninsu, sai dai tun kiran da Sultan ya yi musu, ya yi musu nasiha Nana ta daina hana yaranta zuwa inda Asal take.
Aka sanar da haihuwar Asal, amma aka hana kowa zuwa Asibitin da take.
'ya'yan Nana haka suka kewaye Asal da jaririyar nan, wannan ya ɗauka wannan ya ɗauka.
Da kyar suka tafi gida, saboda makaranta. Ƙarfe sha biyu da rabi Hammad ya iso Asibitin. Ya tarar da Nana tana shirya jaririyar a cikin kaya.
Bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa mata hannu ta bashi, Nana ta ce "Ba tukuici babu komai"
"Zan baki idan muka haɗu" Tana murmushi ta miƙa masa jaririyar, ta tashi ta basu guri. Ya ƙarasa kusa da Asal yana murmushi ys rungumota ya sumbaci goshinta. Ya ce "Kin ga ikon Allah ko Cherié?"
Ta yi murmushi ta ce "Na gani, kalli kamar ta ɗaya da Yarima, duk kamar ka suke yi"
Ya yi dariya ya ce "Ba dole su yi kama da ni ba, ni ɗin na wasa ne. Alhamdillah bayan samari da Allah ya bamu ga 'yar budurwa."

Asal ta ce "A saka mata Asma'u" da sauri ya waiwayo ya kalle ta, ya ce "Ba na son wasa"

"Da gaske nake, na ga kana sonta da yawa, ko ita ma za ta ci albarkacin son da ka ke yi wa rayuwarta, ka so ta sosai"

Hammad ya ce "Kin ga ni ba na son rigima daga haihuwar ki, ke cewa na yi ba na sonki ne?"

Ta girgiza kai ta ce "Ai ba ƙarya na yi ba, da na ce ka na sonta sosai, kuma ta cancanci ka so ta, na gane hakan bayan da na saurari yadda aka yi ka aure ta, da irin rayuwar da ku ka yi da kunnen basira. Duk a ajiye wannan a gefe, tsawon wannan lokacin na rayu da ci gaba da sanya ran samun haihuwa da kalamanta da suka bani ƙwarin gwiwa. Lokacin da na dawo gidanka, babu daɗewa, cikin dare na tashi fitsari saƙo ya shigo wayarka ƙarfe uku na dare. Na ɗau wayar na duba sai na ga saƙonta ne, ta ce ; Albishirinka yanzu na tashi daga barci, na yi mafarkin Asal ta haihu, ana ta shagali har na tashi ina jin abin a jikina da zuciyata, ko a kusa ko a nesa mafarkin nan zai zama gaske in sha Allah, ka samu maƙubaci ka bayar da nannauyar sadaka, Allah ya tabattar mana. Kuma idan mace ce sunana za ka saka"
Duk da a lokacin da naga saƙon nan, na cire rai da samun haihuwa, amma a duk lokacin da na tuna saƙon nan, sai na ji ina ƙara sanya rai. Tsawon shekara goman nan, wannan saƙon nata yana cikin kaina, ina jin sa ina fatan Allah ya tabattar da shi. Babu wanda na taɓa gayawa sai yanzu da nake gaya maka. Bayan haka sanin sirrina, da abubuwan da na aikata bai taɓa sanyawa ko sau ɗaya ta kalle ni ta yi mini gori, da abubuwan da na aikata ba, banda barazanar da ta yi mini, lokacin da na gano matarka ce ita. Kuma bata taɓa yi mini wani abu, na gadara ko makamancin haka ba, saboda ta haihu da kai ni ban haihu ba. Ko na yi yunkurin sanya wa zuciyata irin wannan tunanin Hasna da Fadila su na ankarar da ni, mussaman da Fadila ta gaya mini Nana tana addu'ar ka da Allah ya sanya mata jin wani abu a ranta, dan ta haihu ni ban haihu ba, balle ta yi wani abu da zai sosa mini rai.
A ƙarshe, na san maganin da ka kawo mini, ita ta sarrafa shi a kaina ta yi gwajin maganin haihuwa, kuma Allah ya amsa.
Babu riba yin adawa da mutane irinta, rayuwarta take yi kai tsaye, ba tare da ƙyashi ko baƙin ciki ba. Kuma kasancewata tare da su Hasna, suna ƙara saita ni, saɓanin da da nake tare da miyagun ƙawaye.
Na san ba zan taɓa kai wa ko rabinta a zuciyarka ba, kuma ba zan yi maka dole ba, iya wannan jihadin na zama da ni ka yi, ya isa a kira ka gwarzo, kuma hakan ne hukuncin da ya dace da ni, kana iya ƙoƙarinka a kaina, amma ni dai ka saka mini sunanta, ba kuma na yi hakan dan na burge ku ba ne, ko a ce tsirfa ba ce, a'a na yi hakan ne saboda jin wani sashin na damuwata da ta yi kamar tata."
Gaba ɗaya jikin Hammad ya yi sanyi sosai da sosai.
Ya rungumo Asal a jiknsa, yana sumbatar goshinta ya ce "Abubuwan da suka faru sun riga sun wuce, ki daina dawo da su. Kuma tun farko abubuwan ku ne na kishi da yake damunku, amma tabbas Nana tana da halaye da ɗabi'u na kirki, ina fatan Ubangiji Allah ya haɗa mini kanku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login