Showing 78001 words to 81000 words out of 124686 words
alaƙa da shi, na yarda zan zame masa uwa na zame masa uba.."
"Babu inda za ki je mini da ɗa, kuma kema babu inda za ki je" Ya katse Nana yana maganar cikin ɗaga murya.
Cikin kuka Nana ta ce "Sayyid babu abin da ya fi ahali daɗi da muhimmanci, sai da na baro nawa na fito nemanka na gane hakan, ni na baro nawa ahalin kai ga ka cikin gata, sun baibaye ka da soyayya da ƙauna. Dama gudun rasa ahalin ga Muhsin ne ya sanya na fito nemanka da tsohon cikinsa." Ta saka hannu a hijjabinta ta ciro zoben da ya bata ta ce "Wannan zoben ina kyautata zaton shi ne zoben da ake ta magana a kansa, tun mu na Nigeria Sayyid ya bani shi kyauta, domin jaddada soyayyarsa a gare ni. Muhsin kai wa Abbanka zobensa, kuma ina fatan ba za a ƙwace kujerarsa ta shugabanci ba, sanyin halinsa zai zamo ƙwarin gwiwa ga talakawan da ba su da ƙarfi. Na gode matuƙa da kulawa amma kar ku raba ni da ɗana dan Allah" Kuka Nana take yi sosai da sosai.
Imam Zahradeen ya dubi Nana ya ce "Ɗauki yaronki ki koma, za a neme ki" Nana ta durƙusa ta ɗauki Hammad da ya riƙe zoben da Nana ta ba shi yana zura wa a baki. Ta karɓi zoben za ta ajiyewa Hammad shi, amma ya haɗa ya karɓe Muhsin.
Asal kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka take jin yadda a gaban mutane ya nuna wa duniya ita zai iya rabuwa da ita, Nana ce ba zai rabu da ita ba.
Tafawa bai yi shiru ba ya ci gaba da zazzaga bala'i kamar zai ari baki. Har sai da ran Sultan ya ɓaci. Ya yi wa Hammad umarnin ya tashi ya tafi kawai. Yana rumgume da Hammad ya ji muryar Asal a bayansa.
Ya tsaya ya waiwaya yana kallonta, tamkar mahaukaciya sabon kamu ta ce "Hammad yau nika tozarta a gaban jama'a ka zaɓi bare baƙuwar haure a kaina, ka ƙasƙanta ni a gaban mutane, Hammad ni?"
Ya girgiza kai ya ce "Asal ban ƙasƙanta ki ba, kuma har abada ba zan yi ba. Kamar yadda Nana ta faɗa daga ni har ke mu na cikin ahalinmu, muna da cikakkiyar ahali ita kuma fa? Sannan kuma harshenka alƙalinka Asal. Da raina da lafiyata da ƙuruciyata ki ka kalli tsabar idona ki ka din ga jifa na da kalaman ba kya sona ba kya ƙaunata. Duk da na yi miki uzurin ƙuruciya da yarinta a wancan lokacin, amma haryanzu ina ganin wani abu a cikin idaunki da ban tantance so ne ko ƙiyayya ba. Nana ta so ni a bata san waye ni ba, ta so ni a mutum mara asali da makoma auren shahada da kasada, ta rayu da ni da na ɓacewa duniyarta ta ci gaba da bulayin nema na, ba dan tana sanya ran na saka mata ba. Ki duba ratar za ke tsakanin misalan da na baki" Ya wuce rungume da yaronsa ya tafi.
A ƙarshe dai Imam Zahradeen ne ya mayar da Sultan turakarsa sai jiri yake yi saboda ɓacin rai. Ya ɗebo ruwa ya ba shi ya karɓa ya sha yana mayar da numfashi.
Sultan ya ce "Zahradeen"
Ya amsa da "Na'am Abbie".
"Na rasa ta ina zan ɓullowa lamarin nan gaba ɗaya"
Zahradeen ya numfasa ya ce "Allah ya taimake ka, da Tafawa ne a matsayin da ka ke, komai za a yi ba zai taɓa ƙin goya wa ɗansa baya ba, dan ya faranta muku ba. Ka rintse idanunka ko toshe kunnenka. Ka kamanta yarinyar nan a matsayin 'yar cikin ka. Ana maganar shekara biyu zuwa ta uku rabonta da gidansu. Ka ga dai yadda yake zare idon nan, bai ƙi ya aikata duk wani abin kunya da zai zubar da mutuncin Agadez ba.
Abie shin ba ka tunanin wata aya ce Ubangiji Allah ya saukar mana, domin ya nuna mana fari da baƙi halittarsa ce kuma duk yana kishi da son abin sa? Ka lissafa Allah ya hana shi haihuwa duk da ya yi aure da ƙanan shekaru, aka hana shi ƙara aure. Lokaci ɗaya Allah ya jarabce shi da ciwon da sai da ya keta ya bar Niger ya tafi Nigeria rabon wannan ɗan ya kai shi har can. Kuma duk da haka Allah ya jarabce shi da ciwon da sai tana kusa da shi yake samun afuwa. Yanzu idan muka rintse idanu daga hukuncin da Allah ya zartar dan mutunta al'ada muka tozarta baiwarsa kana tunanin Allah zai barmu? Ka duba ɗan jaririn yaron nan da yake kai komo a tsakanin su cikin farin ciki idan aka raba su, duk gatan da za a nuna masa bai kai ya tashi a tsakanin iyayensa ba. Abie Mai girma Tafawa ɗan uwanka ne, kuma ɗan uwan mahaifiyata ne, amma ina mai tabbatar maka ba zai taɓa ƙaunarka ba, har gara ni yana yi mini kara saboda ɗan 'yar uwassa ne, amma ba zai taɓa son Hammad ba. Kai kuma Hammad ɗanka ne komai za a yi ka banƙara shi ma ya samu abin da yake so"
Sultan ya yi shiru cikin nazari, ya numfasa ya kalli Imam Zahradeen ya ce "To yanzu kai me ka ke tunani, kuma meyasa ba ka yi mini duk wannan bayanin tuntuni ba?"
Zahradeen ya ƙara nutsuwa ya ce "Ina tsoron shiga lamarin ne a baya, amma Hammad da kansa ya same ni da maganar, kuma ya nuna mini yarda ta hanyar ajiye ɗansa a gidana. Yanzu ka bar wani batun Tafawa da wata majalissa kai ne Sultan, idan ka yi doka dole a bi ta. Ka bar Imam Hammad da matarsa, kuma ka soke wannan al'adar da aka ba wa wannan ƙarfin, ka yi musu fatan alkhairi"
Sultan ya girgiza kai cikin jimami ya ce "Ba abu ne da zai yiwu cikin sauƙi ba"
"Ka duba dai Abie, ka duba makomarsu baki ɗaya"
"Shikenan, ka je zan yi tunanin abin yi"
Imam Zahradeen ya ce "To shikenan Abie, amma dan Allah kar ka jira sai ka yi shawara da wani a cikin 'yan majalisarka"
Sultan ya ce "To shikenan"
Imam Zahradeen ya miƙe tsaye, ya ce "Bari na ƙarasa gurinsu, zan karɓi Muhsin na tafi da shi"
Sultan ya jinjina kai kawai.
Hammad ya shiga ɗakin da Nana take, cike da takaicin yadda ta ce, ita ta haƙura da shi, a bata ɗanta ta koma Nigeria, sai dai ya tarar da ita tana kuka.
Ya kwantar da Muhsin da ya yi bacci, ya ƙarasa gabanta ya ce "Meyafaru kuma ki ke kuka?" Ta yi shiru ta ci gaba da kukan.
"Mene ne?" Ya sake tambayarta.
"Sayyid" Ta kira sunan shi a raunane. Ya zauna a kusa da ita ya ce "Mene ne?" Ya yi maganar yana ɗago ta cikin damuwa.
Ta ƙanƙame shi tana kuka ta ce "Sayyid na faɗi haka ne dan su daina yi maka faɗa, amma ina sonka wallahi Sayyid, dan Allah kar su raba ni da kai" Ta yi maganar tana sheshsheƙar kuka.
Shi ma rungumota ya yi sosai da sosai a jikinsa, yana wata irin ajiyar zuciya.
Da kyar ya tattara nutsuwarsa, ya ce "Ki yi haƙuri Ma vie, Ubangijin da ya haɗa mu ne kaɗai zai raba mu. Ni da ke mutu ka raba in sha Allah"
Zata yi magana suka ji ana bubbuga ƙofar ɗakin, Nana ta motsa za ta tashi, amma ya riƙe ta kuma ya yi umarnin a shigo.
Imam Zahradeen ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, kunya duk ta kama Nana.
Ya ɗan tsaya yana kallonsu ya ce "Kuka ku ke ne?" Nana ta yi saurin tashi tana share hawayenta ta ce "A'a".
Imam Zahradeen ya ce "Ga idonki nan duk hawaye. Wai me ki ke gaya masa ne, ya sanya duk ya rikice haka a kanki"
Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi.
Imam Hammad ya ce "Komai ma gaya mini take yi, shiyasa nake jin tamkar raba ni da ita, raba ni da rayuwata ne"
Zahradeen ya jinjina kai ya ce "Na ga alama ai. Amma dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku ci gaba da addu'a, in Allah ya yarda a dalilinki za a sauya tsarin wasu dokokin na Agadez. Yanzu dai Muhsin zan ɗauka zamu tafi"
Cikin marairaicewa Nana ta ce "Dan Allah ka bar mini shi a nan" Ta yi maganar tana kallon Imam Zahradeen.
Ya girgiza kai ya ce "A'a barinsa a nan babu tsaro, tsawon lokacin nan yana tare da ni a can gidana, gobe in Allah ya kaimu za a kawo masa maman Mahmoudu. Idan kuma ba a yarda da ni ba, na bar ku abinku"
Nana ta ce "A'a amma dan Allah ka tafi da ni, ina son na zauna tare da shi, kuma na ga Nene."
"Wani irin mugun kallo Hammad ya yi mata"
Zahradeen ya ce "Ai ko ba ki ce komai ba, dole za ki bar gidan nan, taso mu tafi"
Hammad ya ce "Ya haka? Ku tafi ku je ina? Kuma yaya zaka tafi da ita Sultan bai sani ba?"
Imam Zahradeen ya ce "Idan zaka biyo mu ne taso"
Nana kuwa ta yinƙura ta tashi ta ɗauki jakar kayanta dama da hijjabi a jikinta.
Hammad ya miƙe ya ce "Wai bin nasa za ki yi?"
"Ni ba na son zama a nan, na gaji" Nana ta furta tana tura baki.
Imam Zahradeen ya ɗauki Muhsin, ya kalli Imam Hammad ya ce "Ɗaukko mata jakarta"
Zahradeen yana fita, Hammad ya riƙe ta ya ce "Dan me zaki ce za ki bi shi? Meye haka ki ke yi ne?"
"Amma Sayyid na ga yayanka ne fa"
"Ko ma wane ne, dan me za ki bi shi?"
Ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye "Ni na gaji da zaman gurin nan? Ni gaba ɗaya ma tsoro nake ji"
Sayyid ya ce "Muje kar ki yi mini kuka" Ya saka Nana a gaba, suka bi ta baya, sai ga su a harabar gidan. Zahradeen har ya kwantar da Muhsin a cikin motar.
Hammad ya buɗe wa Nana bayan motar, sai hararta yake yi, amma ta basar ta shige cikin motar ta kawar da kai. Haka nan take jin kamar ta fito daga kurku sai wani irin farinciki take ji da nishaɗi, a haka ya bar gidan da Nana a cikin motar.
Tafawa kuwa ya ɗauki zafi, ya ci gaba da ziga 'yan majalisar Sultan a kan lallai su sanya ido a hukunta Hamma, sannan ya yi baƙin cikin fito da zoben nan da aka yi.
Matar Imam Zahradeen ita ma haka take kyakykyawar gaske, fara sol da ita, yaransu huɗu, kyawawa su ma. Sai dai Nana ta ga matar ba ta ƙyamace ta ba, ta rungume Nana tana faɗin yau ga Umman Muhsin, baƙar Gimbiya ta farko a kaf faɗin Agadez.
Nana dai ta kasa sakin jiki da matar, dan duk mutanen Agadez ɗin tsoro suke bata, kusan kowa ba abin yarda ba ne.
Ganin Nana ba ta sake da ita ba, ya sanya ta bar ta a ɗakin da aka sauke ta.
Washegari da sassafe Hammad ya tafi gidan Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce ba zai gansu ba sai bayan Azahar, tun da shi ba shi da kara.
Nana tare da Muhsin suka kwana, kasa baccin kirki ta yi ta rungume shi, cikin farin ciki tana shafa shi. Aka kawo mata lafiyayyen Abinci, matar Imam Zahradeen ta kawo mata kaya masu kyau, ta ce ta saka.
Hammad ya din ga yi wa Imam Zahradeen magiya.
Zahradeen ya ce "Ka ga ba fa magana ake ta kai shugabana ne ba, yanzu muna magana ne a matsayin ya da ƙani, dan haka dole ka jira.
Sai da aka yi azahar ɗin, suka yi salla, sai ga Mahmoudu tare da Nene.
Hammad suka gaisa da Nene cikin girmamawa.
Sai dai shigowar su Nene babu daɗewa, sai ga Sule shi ma ya zo, tare da wani matashin saurayi.
Mamaki ya kama Mahmoudu, ganin Sule ya zo gidan, sai dai ya yi ta yi wa matashin kallon sani.
Imam Zahradeen ya kalli Hammad ya ce "Ka san wannan?" Ya yi maganar yana nuna masa matashin.
Ya yi shiru yana tsare shi da ido, ya ce "Na san shi, amma na manta a ina, na san dai na taɓa ganinsa"
Imam Zahradeen ya kira wayar matarsa, ya ce ta zo da Nana.
Wani irin kyau Nana ta yi, ɗinki ne na buzaye a jikinta, sai ƙamshin turare take yi ta shigo da sallama. Kasa riƙe farincikinta ta yi, ta nufi Nene da sauri. Sai dai ta yi wani irin wawan burki, bayan yin ido huɗu da matashin saurayin, da girma da kamala suka bayyana a tattare da shi bakinta na rawa ta ce "Imrana!!!"
Wata irin sufa Nana ta yi, ta nufi Imrana a gigice, ta rirriƙe rigarsa tana zaro ido, tana son tabattarwa da gaske shi take gani, ko kuma gizo yake yi mata.
Cikin rikicewa ta ce "Imrana, Imrana kai ne? Imrana dan Allah mafarki nake yi ko kuma kai ne?"
Ya yi murmushi ya rungume ta idanunsa na cika da hawaye ya ce "Ni ne Nana, Imrananki ne"
"Imrana ka tafi ba ka sake nema na ba, ka tafi ka bar ni nikaɗai, Imrana" Toshe mata baki ya yi, a hankali jikinta ya saki ya kuma yi sanyi ƙalau.
Ƙaisar ta hango a bakin teku, yana kallon ruwan, ta ƙarasa inda yake da sauri, ta ce "Ƙaisar kai ne? Ya jikin naka? Ka warke?" Ta yi maganar tana riƙo hannunsa, sai dai maimakon ta ji ta kama tsoka sai ta ji tamkar ta taɓa ƙanƙara wani irin sanyi ƙalau.
Ya dube ta ya ce "Ina taya ki murna"
Ta ce "Murnar me?"
Ya miƙe tsaye ya ce "Murnar komai ma, alamu sun nuna Ubangiji yana sonki, tsananin da ki ka din ga shiga, ya zame wa wasu silar alkhairi, kuma sannu a hankali Allah yana warware miki komai"
Ta ɗan yi shiru ta ce "Ban fahimci me ka ke nufi ba"
Ƙaisar ya ce "Ba sai kin fahimta ba. Ina taya ki murnar ganin ɗan uwanki, sai dai haryanzu da ɗan sauran rina a kaba. Shi wannan mijin naki, zuciyarsa da karsashinsa a kanki kawai yake. Amma bai damu da tsayuwa tsayin daka a kan abubuwa ba, ya kan karɓi abu duk yadda ya zo masa, ya tafi a haka komai zafi da raɗaɗin cutarwar da abin yake yi masa.
Kar ki kuskura Sarkin baka ya tafi, baku bankaɗo abin da yake faruwa da shi ba, sannan Giyaz haryanzu yana tare da shi, sai dai a galabaice yake yana jinya. Kin san bamu fiye saɓa alƙawari ba, dan haka abu ne mawuyaci ya rabu da mijinki ta daɗin rai, saboda yarjejeniyar da suka yi da bokan nan.
Kamar yadda na sanki, ki ci gaba da addu'a, zan iya cewa kusan komai ya zo ƙarshe, sai dai ban san abin da ka iya faruwa a gaba ba."
"Ma vie" Ya yi maganar yana shafa fuskarta, a hankali ta buɗe ido ta kalli Sayyid, ta sake ɗaga kanta, ta ganta a jikin Imran. Kuka take sosai da sosai, da ita kanta ta kasa tantance ko na mene ne.
Imrana da yake share hawayen ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka"
"Kukan ne yake zuwa" Ta yi maganar wasu hawayen na ci gaba da zubowa.
Ya kalli Muhsin da yake ta guje-guje a ɗakin, ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Wannan ne ɗan nata?"
Ya yi murmushi ya jinjina masa kai.
Nana ta sake cewa "Imrana ya aka yi ka san ina nan?"
Ya yi murmushi ya ce "Bacci na kwanta, kawai na farka na ganni a nan"
Kukan da take yi bai hana ta yin murmushi ba. Ta ce "Nene kin ga yayana, duk duniya shi ne kaɗai wanda muke ciki ɗaya da shi"
Nene ta ce "Allah sarki, ga kammanni nan ku na yi da shi"
Imam Zahradeen ya ce "Yakamata a fara ba wa baƙi"
Nana ta ja jikinta ta zauna, ta ƙure Imrana da ido, gaba ɗaya ya nutsu, babu wannan hauma-haumar tasa.
Shi kansa Imam Hammad kallon Imam Zahradeen yake cike da mamaki yana jiran jin bayani daga bakinsa.
*****
Jamila ce a durƙushe tana wani irin kakari, ji take yi tamkar barin duniyar za ta yi saboda matsananciyar azabar da take ji. Ta ɗaga kai da kyar ta kalli Mama, a galabaice ta ce "Mama, me ki ka bani a cikin kukun nan na sha, Mama zan mutu zan rasa raina"
Mama ya ce "Ai gara ki mutun na huta Jamila, gara ki tafi asirina ya rufu da wannan masifar da ki ka ɗaukko mini. Ba dai ke taurin kan tsiya ba, ai na san yadda zan yi da ke nima. Ƙwayar zubar da ciki na je na sayo a gurin Mariya Likita na zuba miki, dan ba za ki haife mini shege a gida ba".
Jamila ta girgiza kai cikin matsananciyar azaba ta ce "Mama ba ki kyauta mini ba, zan iya rasa rayuwata Mama, kin san azabar da nake ji kuwa?"
"Tun da ki ka iya jure miƙawa maza jikinki, dole ki jure azabar fitar cikin"
"Wayyo Allahna" Ta faɗa a marairaice tana sake durƙushewa cikin azababben ciwo.
*****
Fadila ce ta fito daga banɗain da ta shafe a ƙalla awa ɗaya da rabi a ciki, tana tufaka da warwara, sosai an matsa musu a kan su tashi su bar gidan. Har ta gaji da zuwan da wanda ya sai gidan yake yi yana ɗaga musu hankali kamar ba abokinsa ne ba. Ga shi haryanzu bai gama samun cikakkiyar lafiya ba, lallaɓawa kawai yake yi, shi kansa ya rasa inda zai sanya kansa saboda damuwa, ƙarfin hali kawai yake yi.
Tana fitowa ta tarar da shi a tsaye da waya a hannunsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?"
A sanyaye ya ce "Coustom ne suke nema na a Lagos"
Ta ɗan yi saroro ta ce "Suke neman ka kuma, lafiya dai?"
Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi ban san mene ne ba, ga shi ko kuɗin motar tafiya ba ni da su. Allah ya sa ba wani abin ne mara daɗi ya sake tasowa ba"
Fadila ta ce "Jikina ba ya bani wani mugun abin ne, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ne ya sanya suke neman ka. Bari na kira Umma idan da kuɗi a hannunta ta ara mini"
Ya ce "A'a, kin san ba shi ne da ita ba, ba dan halin da Alhaji Zailani yake ciki na ɓatan 'yarsa ba, ai da shi zan cewa ya biya mana, ya raka ni muje mu ji ko mene ne"
Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Dan Allah Daddy ka daina gayyato mutanen nan haka, mu din ga shiru tukuna idan