Showing 81001 words to 84000 words out of 124686 words

Chapter 28 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

65

alkhairi ne idan Allah ya tabattar sai kowa ma ya ji. Da za a samu kuɗin sai Umman su Raudha ta raka ka. Amma hakan nan za ka yi haƙuri mu nemo kuɗi ko ta mota ne ku tafi tare. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ka sanya alkhairi ne.
Ya amsa da "Amin."
****
Gaba ɗaya Shukura ta yi saranda da da ba zata tsira ba, daga ita har jaririnta, Yusra ta ce mata duk za ta yi ta nemi guri ta ɓuya, ba za ta iya fitar da ita da jaririn lokaci ɗaya ba, ta fuskanci mutanen nan, su na harabar inda Asibitin yake.
Shukura na kuka ta ce "Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?"
Yusra ta ce "To yaya za mu yi, idan ba haka ba daga ke har jaririn za ku iya rasa ranku, ki bari na fita da jaririn, ki san duk yadda za ki yi ki ɓuya ko ki gudu. Amma Shukura suwaye wannan suke binki haka? Kuma me ki ka yi musu?"
Shukura na kuka ta ce "Dogon zance ne, ke dai tafi da shi, idan ban rayu ba ma dan Allah ki kula mini da shi"
Yausra ta bata mukullin motar da ta zo da ita ta ce "Idan kin samu dama, ki gudu ni zan san yadda zan yi" ta goya jaririn Shukura na kuka, Yusra ta fice daga ɗakin.

****
Imran ya ci gaba da kallon Nana cikin zallar farin ciki da shauƙi, tare da kallon Muhsin dukkaninsu cikin shiga ta alfarma da kamala.
Ya ce "Nana, ashe zan gan ki cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka a rayuwata? Allah na gode maka da ban tursasa ki na kashe miki aure ba, ashe alkhairinki yana tattare da auren.
Kasancewar daga Nana sai shi a ɗakin, ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma an sha gwagwarmaya Imrana, duk da na gode wa Allah da ka bayyana yanzu, ka zo a gaɓar da na fi tsananin buƙatar ka, amma meyasa ka yi fushi da ni baka sake dawowa ba, dama akwai abin da zan yi maka ka yi irin wannan fushin da ni?"
Ya girgiza kai ya ce "Babu shi, abin da za ki yi mini da zai sanya na guje ki. Amma ki yi haƙuri kaɗan za ki ji abin da ya faru. Na yi burin na samu wadata ki huta na gatanta ki Nana, amma Allah ya ƙaddara ke ce zan huta a dalilinki."
"Ban gane ba, me ka ke nufi?"

Imrana ya ce "Za ki gane ne"

"Imrana ina Baba da su Jamila, na san ba zuwa gurin su Mama ka ke yi ba, da gurin su Ummi, ban san da wani idon zan tunkari gida ba, na tafka babban kuskure da bana tunanin za su iya yafe mini"

"To kar Allah ya sa su yafe ɗin mana, ke dai ba kin riga kin yi gaba ba, su zauna da rashin yafiyar"

Nana ta buɗe baki ta ce "Lallai hali zanen dutse, Imrana kar Allah ya sa su yafe, su Baban?"

"Eh ɗin, ai ke yakamata a ce ma sun nemi yafiyarki, idan sun yafe shikenan, idan ma ba su yafe ba za ki ci gaba da rayuwa wataƙila ma babu wanda ya neme ki a cikin su"

Hammad ya dubi Imam Zahradeen bakinsa fal tarin tambayoyi, amma yanayin fuskar Zahradeen ɗin babu alamar zai amsa masa tambayoyin nasa"

Imam Zahradeen ya ce "Ya na ga ka ƙure ni da ido ne?"

Hammad ya ce "Abubuwan da na gani suka ɗaure mini kai nake son ka yi mini bayani"

Ya numfasa ya ce "Bayani ya zama dole Hammad, amma ina fatan zaka yi mini afuwa da duk abin da za ka ji a bayanin nawa"
Imam Hammad ya ce "In sha Allah"
Kamar yadda suka taru a falo ɗazu, haka suka sake taruwa bayan sallar la'asar.
Imam Zahradeen ya ce "Ina yi wa kowa barka da zuwa wannan gida nawa. Wasu sun san da zuwan wasu, wasu ba su zan da zuwan wasu ba. Cikinmu akwai yan gidanmu na sarauta, akwai wanda ba su da alaƙa da gidan namu, amma a yanzu tilas mun zama abu guda, kuma zan warware wani abu da na san wasu za su gan shi wani iri, amma yi haƙuri da yadda komai zai zo, duk wanda yake gurin nan abin ya shafe shi ne.
Imam Hammad, wannan bawan Allah da ku ke gani Sulei yarona ne, zamanku a tare da shi, da duk wani abu da ku ke ciki, wani abu ne na shiri da na yi shi" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon Sule tare da Imam Zahradeen. Bai damu da kallon da suke yi masa ba, ya ci gaba da cewa; wannan matashin saurayin da yake ɗan uwa ga matarka Hammad wato Imran, bayan da ya je ya same ku, ya yi yinƙurin tafiya da ƙanwarsa, hankalinka ya tashi sosai, ka kira Mahmoudu ka gaya masa, shi kuma sun yi maganar da Sulei, shi kuma Sulei ya gaya mini. Gudun kar ya kawo tangarɗa a rayuwar aurenku, ya sanya na saka aka bi diddigi aka nemo shi.
Aka kawo mini shi har Agadez, na yi masa bayanin komai, da ko kai waye, da alfarmar da nake nema ya yi mini na yin shiru da bakinsa ya yi haƙuri ya bari ku rayu da ƙanwarsa, kai mutum ne mai asali da daraja, ƙaddara ce ta faɗa maka.
Sai dai ya fututtuke yana ganin kamar rainin hankali ne kawai, idan kana da asali da daraja dan me zan barka a wulaƙance kana gadi. Da kyar ya fahimci abin da nake son ya fahimta, sai dai duk da haka gudun ya ƙara burkicewa saboda na ga rigimamme ne, na aika shi waje karatu. Sunansa yana cikin jerin waɗanda ka ke bawa tallafin karatu a Agadez, a cikinsu na saka shi aka kuma fitar da kuɗin dan kai ka biya masa ba ni ba.
Fuskar Hammad ta yi wani irin ja, cikin kakkausar murya ya ce "Zahradeen"

"Hammad" Ya miƙe tsaye ya ce "Labarin nan bai cika ba me ka ke ɓoyewa?"

Imam Zahradeen ya yi murmushi ya ce "Wannan rigimar cikin gida ce, ka bar maganar a haka"

"Ba zan bari ba, sai ka yi mini cikakken bayani"

Mahmoudu shi kansa ɗaurewa ya yi, kenan duk wannan abin Sulei, kallon biri yake yi masa yake yi musu na ayaba, ya san komai, ya san waye Imam Hammad, amma ya zauna da su har da yi masa masifar kullum yana ɗawainiya da mutumin da bai san asalinsa ba?"
Gaba ɗaya jikin Hammad ya hau tsuma, yana neman ya fita hayyacinsa.
Hammad ya riƙe rigar Imam Zahradeen yana tsare shi da idanu cikin tuhuma.
Zahradeen ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Ni ne nake tura maka saƙon cewar kar ka dawo da Hammad Agadez, lallai ka tafi Nigeria. Kuma ni na shirya yadda aka haɗa ku da Sule har ku ka yi aikin gadi tare. Sule ni yake yi wa aiki, duk wani abu da yake faruwa, da motsinku Sule yana sanar da ni. Kuma nine nake tura maka kuɗaɗe domin kula da Hammad da iyalin da ya aura, kuma aka sanar da ni kwanciyar hankalin da yake ciki.
Sai dai bayan kame ku gaba ɗaya na kasa sanin halin da yake ciki, na tura Nigeria a bincika mini, aka tabattar mini da kama ku. Na ci gaba da bibiyar inda Nana take, amma binciken nawa bai cim mata ba, tayi ɓatan dabo, ga kuma alƙawarin da na yi wa ɗan uwanta, na zan tabattar da tana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai da Allah ya dubi zuciyata sannu a hankali, komai ya din ga warwarewa, tun kafin ka gane ta, ni na gane ta saboda har hotonta ina da shi. Kuma aka yi sara a kan gaɓa ka zo ka same ni, da maganar cewa ka yi aure a Nigeria.
Sai na bika muka tafi a haka, ban nuna maka komai ba, zuwa lokacin da nake ganin ya dace ka san komai!.
96
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143


Hammad bai iya cewa uffan ba, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita. Imam Zahradeen kuma bai motsa daga inda yake ba, ya zuba masa ido. Nana ta tashi a rikice ta ce "Sayyid ina zaka je ne? Kar ka yi fushi, ka tsaya ka saurare shi, kar ka yi wa al'amarin wata mummunar fassara.
Bai tsaya ba kawai ya yi gaba, Mahmoudu ma tashi ya yi ya bi bayansa da sauri.
Wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa.
Ga farincikin ganin Imrana, amma alamu sun nuna Hammad ya ɗauki zafi da abin da Yayansa ya aikata, duk da ta wani fannin taimakonsa ya yi, amma ta wani fannin abin a saka masa ayar tambaya ne.

*****
Sagir kuwa kamar zai haukace, saboda tashin hankali bai fita daga tashin hankalin ɓatan Shukura ba, ga Yusra ma ya neme ta ya rasa, tun safe ana maganar sha biyu saura na dare.
Ga shi layin wayarsa yana cikin wayar Yusra, haka a dole yaje police station ya kai rahoton ɓacewar Yusra. Ya fara tunanin kar a fara zarginsa da ko shi ne yake aikata wani abu, matan nasa suke ɓacewa.
Ƙarfe shida na safiya, suka ji ana bugun gate, bugu na tashin hankali kamar za a ɓall gate ɗin. Afujajan mai gadi ya buɗe gate ɗin, babu tsammani yaga Yusra a tsaye kamar korarriya. Ya zaro ido yana kallon ta cikin matsanancin mamaki. Gaba ɗaya gari ma bai gama waye ba, ya kalli hannunta ya ga jariri, bai yi magana ba ta banke shi ta wuce cikin gidan.
A falo ta tarar da Antynta tare da mai gidanta, saboda bugun ƙofar da suka ji ana yi.
Cikin mamaki Antyn ta ce "Yusra lafiya ki ka zo gidan nan da sassafen nan haka? Daga Kanon ki ka taho Abuja" Yusra ta yi shiru ba ta yi magana ba, kallon falon Yusra ta hau yi, tana tunanin yaya aka yi ma ta zo nan. Ita dai ta san ta ɗaukko jaririn ta fito titi, tama tafiya a hankali tana waige-waige, daga nan bata sake sanin abin da ya faru ba, ta ganta a ƙofar gidan Antynta da ta koma hannunta a Abuja.
Mai gidan ya ƙarasa gaban Yusra, ya karɓi jaririn da ya fara kuka a hannunta. Yusra ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi.
"Yusra dan waye wannan, a ina ki ka samo shi?"
Mai gidanta ya ce "Rabu da ita ta huta, wannan yaron a samo madara a bashi, sannan a kira mijinta mu ji ko da saninsa ta taho, kuma me yake faruwa"
Antyn ta jinjina kai cikin damuwa, da fargabar a ina Yusra ta samo ɗa.

*****
Jamila kuwa ta din ga zubar da jini babu ƙaƙƙautawa, ga azababben ciwon mara da ta din ga yi. Ta kwana ta wuni tana wata irin burgima da kuka mai ban tausayi.
Baba ne ya dawo ya tarar da Jamila a cikin wannan yanayin.
Baba ya ce "Rabi wai me yake damun Jamila haka ne, wannan wane irin ciwo ne tun jiya?"
Mama ta ce "Ba fa wani abin ba ne ba, al'ada ce ta zo mata take shan wahala."
"Haba, wahalar ta isa haka, wane irin ciwo ne haka, anya ba za a kaita Asibiti ba"
Mama ta ce "Ba sai an kai ta ba, na bata magani za ta warke"
Baba dai bai ji ya gamsu ba, amma ya ƙyale su kafin ta hayayyaƙo masa da masifa.

*****
Asal duk ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka, ta yi wata irin muguwar rama.
Tana zaune a ɗakinta, Tafawa ya shigo ɗakin, ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya ce "Dalilin me ne ne ya sanya ba kya cin abinci?" Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba.
"Kar ki saka damuwar abin da yake faruwar nan a cikin zuciyarki, duk yadda zan yi dole sai na tabattar da an hukunta Hammad, ba zai ci bulus ba abin da ya aikata."
Asal ta yi shiru, wani irin baƙin ciki na taso mata a zuciyarta, ta din ga tuna yadda mahaifin nata ya din ga ingizata da tursasa ta aikata Wasu abubuwan. Ya yi wa rayuwarta illa duk a ƙoƙarin sa na ganin ya cimma wani burinsa da abu ne mai wahala ya samu cikarsa.
Yana magana amma ta lula Duniyar tunani, ta tuna lokacin da aka kusa auren, ya kawo mata wani abu a ƙoƙo ya ce ta sha, sai bayan da ta sha sannan ya ce bai aura mata Hammad dan taje ta haihu da shi ba, domin har abada baya fatan ya haihu balle ya sanya ran samun magaji ya ƙara dagula masa lissafi gurin cim ma burinsa.
Wasu irin zafafan hawaye suka zubo wa Asal, ta daɗe da gane rashin haihuwarta na da nasaba da wannan magani da mahaifinta ya bata, duk da a ɓoye ta je ganin likita a kan matsalar rashin haihuwar, aka ce mata hakan yana da alaƙa da ta'amalli da chemicals masu ƙarfi da ta yi. Da fari ta yi tunanin shaye-shaye da take yi, sai dai ko da shaye-shaye ta fi kyautata zaton maganin da Tafawa ya bata ne sila.

Nana ta samu ta sake sosai da sosai da Imran ta din ga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa, wasu guraren sai da ya yi hawaye. Haka kuma ya din ga yi wa Nene addu'a, a kan abin da ta yi wa Nana na taimako.
Nene ta ce "Babu komai, ɗa na kowa ne. Kuma in sha Allah Nana daram zata zauna a ɗakin mijinta"

Nana ta kalli Imrana ta ce "Imrana tsoro nake ji, ban san yaya su Baba za su kalle ni ba, ban san me zan ce musu ba, ga shu kai ma tun da ka tafi ba ka je gidan ba?"

Imrana ya ce "Ba za ki daina wannan zancen ba, ba abin da za su yi miki. Nima ban je ɗin ba"

Nene ta ce "Ai dole mu kafa mu tsare, daga nan Agadez a tashi tawaga, su je har gida a bawa iyayenku haƙuri, kaga yanzu kai ne waliyyinta, a tashi manya daga Agadez su je har Nigeria su ba wa iyayenku haƙuri a kan abin da ya faru, sannan kuma a yi. Sannan ya zama dole a yi wa Nana duk wani abu na dukiyar aure, a yi cikakken biki na 'yar gata duniya ta shaida auren yadda yakamata, dan gudun kar ma a zo a samu wata matsala a nan gaba."
Imarana ya ce "Wannan gaskiya ne, amma kina ganin za su amince da hakan?"
Nene ta ce "Dole za su amince, ko dan son da suke yi wa ɗan su. Tun da ɗansu yana son iyalinsa."

Hammad kuwa gidansa ya koma, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ya din ga juyi yana tunani, tare da tambayar kansa, kenan duk abin da yake faruwa da sanin Zahradeen. Kasa jurewa ya yi ya tashi ya tafi gurin Sultan. Yana zaune Gimbiya Bilkisu ta sanya shi a gaba, tana ta maganganu a kan kar ya nuna son kai akan hukuncin da zai yanke, kuma ya duba Asal ita ma a yi mata adalci.
Babu tsammani sai ga Hammad ya shigo, yanayin yadda fuskarsa ta yi jawur, ya sanya Sultan miƙewa yana tambayarsa ko lafiya? Amma Hammad ya yi shiru bai ce komai ba. Sultan ya kama hannunsa ya shiga da shi cikin ɗakinsa, ya zaunar da shi ya ce "Ka gaya mini mene ne?" Sai gumi da yake ta tsatstsafo masa amma bai yi magana ba.
Mahmoudu kuwa daga fitowar Hammad ya biyo bayansa, ya neme shi ya rasa, yana son su yi magana, ya lallaɓa shi su bi abin a sannu su fahimci Zahradeen, dan ya ga alamar ya ɗau zafi lamarin ya ɗaure masa kai.
Matar Imam Zahradeen ta yi sallama, suka amsa. Ta kalli Nana cikin sakin fuska ta ce "Gimbiyar Imam Hammad, Imam Zahradeen yana kira"
Nana ta yi murmushi ta ce "Nana dai za ki ce"
"Ina, wa ya isa faɗar sunan Gimbiya" Nana ta yinƙura ta tashi ta bi bayanta.
Bayan sun shiga, matar Zahradeen ta koma, Nana ta zauna a ƙasan Carfet.

Ya ce "Kin ga mijinki ya ɗauki zafi, yaƙi tsayawa ya saurare ni, balle ya fahimce ni, amma na ga ke kina cikin nutsuwarki, za ki fi fahimtata. Amma kafin nan kin ga ke ki ka zauna da shi, ko za ki iya gaya mini abin da ki ka sani, bayan haɗuwarku lokacin yana cikin rashin lafiya?"
Ta jinjina masa kai, sannan ta yi masa bayanin, abin da take ganin ya dace ta gaya masa.
Ya ce "Shikenan, Sultan ya kira ni a waya, ya ce yana nema na, na san wataƙila ya gaya masa ne, tare da ke za mu je gobe in Allah ya kaimu da safe"
Nana ta amsa masa da "To"

*****
Hajiya Halima ta kiɗime, tun bayan da Sagir ya kira wayarta yake tambayarta, ko Yusra ta je gidan.
Har ta fara shirin tafiya Kano, Yayar Baban Yusra ta kira ta a waya, ta sanar mata ga Yusra ta zo tun ƙarfe shida na safiya tare da wani jariri da ba su san a ina ta samo shi ba.
A kiɗime Hajiya Halima suka shirya, suka tafi gidan Antyn, su na zuwa suka tarar da ita cikin yanayin ɗimuwa, ba ta magana ga kuma wani ƙosashshen jariri da ba a san inda ta samo shi ba.

Hajiya Halima ta ce "Ai ni mijinta ya kira ni cikin tashin hankali, yake tambayata wai ko Yusra ta zo, ya neme ta ya rasa. Hankalina a tashe na fara shirin tafiya Kano, kin san uwargidanta fa ita ma an neme ta an rasa.

"Mami" Yausra ta faɗa da ƙarfi.
"Na'am Yusra, sannu"
"Ku gaya wa Daddyn Haidar yaje ya ɗaukko Shukura, za su kuma sace ta"
Cikin rashin fahimta ta ce "Suwaye?"
"Nima ban san su ba, amma sace ta za su yi, na baro ta a can"
Duk yadda suka yi da Yusra ta yi musu bayanin yadda za su gane, ta kasa sai kukan aje a ɗaukko Shukura kar a kuma sace ta.
Hajiya Halima ta kira Sagir da lambar da ya kira ta, ta sanar masa ga Yusra a Abuja tare da wani jariri da ba su san a inda a ta samo shi ba. Cikin kiɗima da tashin hankali, ya ɗauki mota ba tare da ya gaya wa kowa ba, ya kama hanyar Abuja.

*****
Bayan su Nana sun hallara a gaban Sultan, ta yi tozali da Giyaz a tsaye da sandarsa a bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya ƙara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login