Showing 111001 words to 114000 words out of 124686 words
da wasu daga cikin abokansa, ciki har da Malam Gambo, ya sanya jami'an tsaro kama su.
*****
Sayyid a gurin Asal yake, amma yaje yana damunta. Sai da ya fara shirin tafiya, ta ce masa ya jira tana da baƙi su gaisa.
"Suwaye baƙin kai a Agadez? Umma ce? (Da yake haka yake kiran Nene, kamar yadda Mahmoudu yake kiran ta)"
"Ba ita ba ce"
"To suwaye?"
"Baƙi masu muhimmancin gaske ne, za ka gani"
Ya ce "To bari na je masallaci, kafin su zo" Ya yi alwala ya fita falo, ya ga Nene tare da wata mata da namiji da alamu suka nuna mata da miji ne. Su na ganinsa suka ƙara nutsuwa, domin sukan ji zancensa a bakin Nene. Cikin girmamawa suka risuna su na gaishe shi. Ya amsa yana mamakin dalilin shigo masa da ƙato haka har cikin falo. Ya dake ya ce "Umma dama ke ce baƙuwar, ta dage kar na fita sai kin zo?"
Ta yi murmushi ta ce "Ba ma nice baƙuwar ba, ga baƙin nata nan" Ta yi maganar tana nuna masa mata da mijin. Ya yi shiru yana kallonsu, ba su yi kama da 'yan Nigeria ba, sun fi kama da hausawan Niger, mussaman daga yanayin hausar su.
Nana ce ta buɗe ƙofa ta fito, da gudu ta nufi Hajara ta rungume ta, Muhsin ya biyo bayanta ya ja ya tsaya a kusa da mahaifinsa.
"Hajara, dama zan sake ganinki?"
"Gani kuwa shugabata" Hajara ta yi maganar cikin girmamawa.
Nana har ƙasa ta durƙusa ta gaida Auwwal, takaici ya kama Hammad, haryanzu Nana ta kasa gane mene ne matsayinta. Banda haka ya za a yi ta durƙusa har ƙasa tana gaida mutumin da shi kansa ya girme shi, da ma dattijo ne da sauƙi.
Nene ta ce "Nana ba girmanki ba ne, ai shi yakamata ya gaishe ki"
Shi ma a tsorace ya ce "Wallahi kuwa"
"Kash, Nene ba ni da wani girma, ni na kasa jin girman nan. Meyasa ba zan girmama mutane mafiya karamci a gare ni ba?" Ta taso tana kallon Sayyid fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Wannan gidan su ne je, lokacin da na baro Agadez na nemi Nene na rasa, a can gidansu aka ɗaukko ni. Sayyid lokacin da na zo Niger na sauka a Maraɗi, ba ni da kowa sai Allah, Allah ya dubi zuciyata ya ji ƙaina ya haɗa ni da mutane masu karamci. Wannan su ne sanadin haɗuwa ta da Nene." Nan ta kwashe komai ta gaya masa. Sannan ta ɗora da cewa "Ina tambayar Nene su, ta ce mini sun tafi ci rani can ƙasar Mali. Sai yau Neme ta kira ni ta ce mini sun zo Niger, su na Agadez za ta kawo su mu gaisa. Ni na so mu je har inda suke amma ta hana" Kukan da Nana take yi kawai ya tabattar masa da ba ƙaramin karamci suka yi mata ba.
Ya taka ya ƙarasa gaban Auwall da kansa yake ƙasa, ya miƙa masa hannu su yi musabaha. Da kyar ya iya miƙo masa hannu.
Suka gaisa Hammad ya dafa kafaɗarsa ya ce "Na gode sosai da sosai. Mutane a zamanin nan abin tsoro ne, amma ka zama mutum na farko gurin bawa matar da baka sani ba taimako.
Na gode sosai da sosai, dama Umma uwata ce, kai ne dai ban sani ba, tabbas tana bani labarinku. In sha Allah ba zaka sake zuwa Mali ci rani ba, da yardar Allah na gode sosai da sosai Allah ya biya ka"
Ya kalli matarsa ita ma ya yi mata godiya sosai.
Tare suka je Salla da Auwwal, Hajara ta yi nufin ɗaukar Muhsin, amma ya ƙi saboda ƙyuya.
Hadimai suka gabatar da Abinci, da abubuwan sha daban daban. Sayyid a dole yake ɗaga ƙafa a wasu abubuwan duk da azabar kishin Nana da yake yi. Ya yi iya ƙoƙarinsa a kan kar ya yi wani abu da ran su Auwwal zai sosu ko na Nene, ko dan albarkacin ɗawainiyar da suka yi da Nana.
Har da kyautar kayan wasan Yara, suka kawowa Yarima Muhsin. A hirar ta su suke gaya wa Nana haryanzu Allah bai ba su haihuwa ba. Ta yi ta musu nasiha da basu misalai masu kwantar da hankali.
Sai isha'i suka tashi tafiya, Hammad ya yi musu alkhairi, tare da jaddada musu godiya, ya kuma gaya wa Auwwal lokacin da zai zo Maraɗi, ya ba shi katinsa ya ce idan yaje ya nuna katin za a bari ya gan shi, zai ba shi abin yi.
Bangaren Nana ma, kyaututtuka ta ba wa Hajara sosai, da ta ce ba zata karɓa ba, abin da suka yi wa Nana, dan Allah suka yi mata, Nene ta ce mata ba a mayar wa da masu mulki kyauta.
Sai da Nana ta karɓi lambar wayar Hajara, ta din ga yi musu godiya kamar ta tsuguna musu. Hammad ya ɗauki Muhsin ya ce da kansa zai mayar da su har gidan da Nene take, kasancewar a gurinta suka sauka a Agadez. Daga can ya so wucewa gurin Asal da Muhsin dan yana kyautata zaton bata taɓa ganinsa ba, amma Nana ba ta sani ba, tsaf za su iya yin faɗa a kan hakan. Kuma da gaskiyar Nana kome nene Asal ce ta janyo, kuma duk abin da Nana za ta yi domin ta ba wa ɗanta kariya. Bugu da ƙari kuma ba ya son duk wani abu da zai kawo musu matsala, saboda wata irin kwanciyar hankali ya tsinci kansa a ciki. Ga taraiya da soyayya da yake samu daga gurinta. Duk da haryanzu Giyaz yana taɓa shi. Amma idan yana tare da ita, da ya gaya mata alamomin da yake ji, take yi masa addu'a ko ma muraran ta ga Giyaz ɗin tare da shi.
Ya tattara hankalinsa a kan Nana da ta nufo shi, ta sanya doguwar riga ta cika ta, rigar ta zauna a jikinta.
Ta ce "Wannan kallon sai ka saka na faɗi tukuna?" Yayi murmushi ya ce "Sai na riƙo ki kafin ki faɗin.
Ta yi murmushi ta zauna a kusa da shi, ta kai kofin hannunta bakinsa ya buɗe baki yana sha. Ta ce "Amma ka yi sauri fa"
"Eh, ina kai su na juyo ne, in sha Allah idan muka haɗu a Maraɗi, zan sama masa aikin yi"
"Gaskiya ka kyauta, Allah ya saka maka da alkhairi" Ta ci gaba da ba shi labarin irin taimakon da suka yi mata.
Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Lokacin mu na Nigeria, ba wuya kin samu rabo, Allah ya sa Niger ma haka ne, Allah ya sanya ƙani ko ƙanwar Muhsin sun samu a cikin nan"
Nana ta tura baki ta ce "Sai Yarima ya shekara biyar"
"Wace shekara biyar kuma? Kowa so yake sai ya karɓe shi, Zahradeen nata masifa, ga Sultan ya ce gobe na kai masa shi, amma idan Allah ya sa ki ka haihu, ko an ƙwace shi mu na da wani ko?" Kawai ta yi shiru tana murmushi, dan ji take gara ta haifi wasu a ƙwace da a ƙwace mata Muhsin.
Su na hira ta ɗauki wayarta, za ta nuna masa abu, sai dai tana buɗe data videon Alhaji Zailani ta fara cin karo da shi a dandalin sada zumunta.
Miƙewa ta yi tsaye jikinta na wata irin tsuma, kamar za ta zare. Ya karɓi wayar hannunta ya kalli videon. Ya ajiye wayar ya ce "Shiyasa wasu lokutan shafukan sada zumuntar nan duk ba su da wani amfani"
"Sayyid ba ka gane waye ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Ni ban san shi ba"
"Ba ka tuna Alhaji Zailani ba?" Ya yi shiru ya tafi tunanin, kamar ya san sunan, can kuma ya ce "Na tuna, mutumin da muka fara gadi a gidansa da su Mahmoudu. To Allah ya kyauta ke mene ne naki na shiga tashin hankali haka?"
"Dan Allah Sayyid ina son zuwa Nigeria" Ta yi maganar cikin tsoro da tashin hankali.
"Sati uku da gama hidimar nan ki ce za ki Nigeria, a ƙalla nan da wata biyu nake son mu je tare"
Sai ta rikice masa gaba ɗaya a kan ita fa dole Nigeria take son zuwa. Abu kamar wasa ya ɗauka da wasa take yi, sai da ya ga ta yanke jiki ta faɗi, jikinta ya yi sanyi ƙalau. A hankali ya ɗaga kai ya kalli tsuntsun da yake shawagi a saman ɗakin, da hakan ya tabattar masa da Ƙaisar ne ya zo mata.
A ransa ya ƙudurce lallai a shirya tafiya Egypt ɗin nan, kafin su zo su ci gaba da samun matsala, su sake hana su zaman aure cikin kwanciyar hankali.
Sai dai idan ya ce a yi mata passport a Niger, zai ɗan ɗauki lokaci, dan haka ya yanke shawarar za su je Nigeria a yi mata, sai su tafi. Har wajen ƙarfe goma na dare yana tare da Nana, sai dai ba ta dawo hayyacinta ba. Ya kira Asal ya gaya mata Nana babu lafiya, dan haka ta yi haƙuri ba zai samu damar dawowa a ranar ba.
Asal kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, gani take kawai faɗa yayi, dan ya zauna ya kwana a gurin Nana, amma babu yadda ta iya. Shi kansa sai da ya raya za ta yi tunanin hakan, amma babu yadda za a yi ya tafi ya bar Nana a wannan yanayin.
Duk yadda su Sagir suke yi wa Shukura ɓoye-ɓoye, sai da ta san Allah ya yi wa mahaifinta rasuwa.
Hajiya Suwaiba ce ta fara ganin Videon nan, sai ba ta yi wa Alhaji Fatuhu magana ba, ta je gurin Fadila. Fadila ta ɗan yi mamakin ganin Hajiya Suwaiba a falon ta.
Bayan sun gaisa ta ce "Fadila, ko Daddy ya gaya miki abin da yake damun sa?"
Fadila ta ce "Wallahi bai gaya mini ba, na yi na yi ya ƙi ya gaya mini"
"Kin ga wani video"
Fadila ta karɓi videon tana kallo, jikinta ne ya hau karkarwa ta ce "Wannan ai Alhaji Zailani ne? Wai yana nufin Alhajinmu ya yi wa abin da yake faɗar nan?"
"Nima abin da ya ɗaure mini kai kenan"
Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama, ya ga duk sun zubo masa ido, kamar marasa gaskiya.
"Lafiya kuwa?"
Hajiya Suwaiba ce ta yi kokarin cewa "Daddy wani abu muka gani, shi ne dama abin da ka ke ɓoye mana?"
"Me na ɓoye mukun?"
Ta miƙa masa wayarta, yana kalla ya ajiya, ya zauna cikin damuwa, ya ce "Koma mene ne ya faru, ya riga ya faru, dan Allah a bar maganar nan ta wuce"
Hajiya Suwaiba ta ce "Amma ya batun maganganun da ya din ga faɗa, yana cewa shi ya yi maka sihiri?"
"Suwaiba a bar maganar nan dan Allah"
"Amma ya zaka ce a bar ta, mutumin da ya tsugunar da mu, ya saka mu a wahala, to wallahi ni dai ban yafe ba."
Fadila ta sha mamakin abubuwan da ta ji a videon nan, kuma ta tsorata imani ya ƙara shigarta, sai dai tun da ta ji Alhaji Fatuhu bai musa ba, to tabbas an yi hakan.
*****
Nana Bakinta ya ƙi rufuwa, wani irin farinciki take ci, ganin sun kama hanyar Nigeria.
Ta din ga tuna lokacin da ta yi balaguro, daga Nigeria zuwa Niger tsawon shekaru, ta tafi zuciya a cunkushe cike da rashin sanin makoma, sai dai kyakykywan yaƙini da dogaro ga Allah. Sai ga shi a wannan karon ta nufi zuwa gidan, cike da farinciki da kwanciyar hankali. Ta so tahowa da Muhsin, amma Hammad fafur ya hana, wai sai zo ɗaukarta zai taho da shi.
Sai da suka samu saɓani kafin ta taho, dan cewa ta yi muddin Asal zai kai wa ɗanta gara ta haƙura da tafiyar. Ƙarshe sai da suka kai shi gidan Zahradeen, sannan ta hakura ta taho.
A garin Bauchi ta fara yada zango, duk da nan ma abin da ya faru ba zai taɓa gogewa daga cikin ƙwaƙwalwarta ba. Mama tana ta kiranta a waya ta ji ko ta kusa ƙarasowa.
Ko da Nana suka isa, Iliyasu ta fara gani a ƙofar gida, ya tsaya yana washe baki, ganin Nana ta fito daga danƙareriyar mota da aka kawo ta a ciki.
"Maraba, sannunku da zuwa, sannu da zuwa"
Ita Nana ma abun da yake yi matan, kunya ya din ga bata. Ta tarar da su Adda Maryam da Fati da wasu daga dangin Umman, duk sun cika gidan. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana. Suka din ga yi mata barka da zuwa.
Nana ta sha karramawa, mijin umman sai nan nan yake yi da ita, yana washe mata baki har da yi mata raha.
Baba ya din ga kiran Nana yana tambayarta sai yaushe zata ƙaraso. Ta ce masa ai ta sauka a Bauchi, sai ta kwana biyu za ta zo. Gaba ɗaya bai ji daɗin hakan ba, saboda yadda yake Alla-Alla ta zo ya sake ganinta.
Sai da Nana ta kwana uku a Bauchi, Mama tana a kaita tasha a saka ta a mota, ta ce ai direbanta yana nan a Bauchin bai tafi ba.
Suka sake ɗaukar hanyar Kano, jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fika. Nana ta yi kewar garinta na haihuwa ba kaɗan ba.
Da sallama Nana ta shiga gidansu, Iya suturar jikinta, da yadda ta yi kyau mai ɗaukar ido ya sanya Mama yin saroro da kasa amsa mata sallamar. Nasiru ne ya fito da gudu yana faɗin Oyoyo ga masarautar Agadez da kanta. Masu arzikin zinare, masu kyauta da dama hagu ma ba ta san ana yi ba. Barka da zuwa Garkuwar matan Agadez ke ta Afrika ma gaba ɗaya." Kawai Nana ta tsaya tana murmushi, Jamila ta fito daga ɗakin, ta zo ta rungume Nana, sai Nana ta manta da batun wata Mama, ta hau murnar ganin 'yan uwanta. Nasiru ya je ya ɗaukko mata Akwatinta a mota.
Nana ta dake ta ce "Mama ina wuni?"
A dole bisa yaƙe Maman ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ai kasa gane ki na yi, irin wannan gwala-gwalai haka. Ai na zata ba zaki sake saka su ba, dan kar ki yi almubazzaranci tun da da muka je fama aka yi ta yi da ke, ki ka ce ba kya so"
Nana ta yi murmushi, tana tuna karatun da Ƙaisar ya yi mata, amma ta ce "To Mama yana iya, masu abu da abinsu, an ce mini haka suke adonsu, idan ka je gari ka ga 'yan gari da jela, aka ce kai ma ka nema ka maƙala. Gaba ɗaya Mama ba ta san baƙin cikinta ya fito muraran ba.
Baba ma da ya dawo ya ga Nana, bakin nan a buɗe ya din ga murna yana yi mata maraba. Babu laifi sun yi nata karɓa mai kyau. Ta yi musu tsaraba mai yawa sosai kamar yadda ta yi wa mutanen Bauchi.
Da daddare suna ɗaki suna ta hir da Jamila, take gaya wa Jamila abun da ta gani a waya, Jamila ta ƙara bata cikakken labarin abin da ya faru, da yadda Hajiya Sa'a take bayar da 'ya'yan Alhaji Fatuhu har ma da rashin lafiyar da Alhaji Fatuhun ya yi sai da ta bata labari. Jikin Nana ya din ga tsuma ta shiga tashin hankali, ta ƙudurce a ranta lallai a washegari za ta je gidan Alhaji Fatuhu, za ta je.
Suwaiba ma ta dage ta din ga yi wa Nana hira, duk da galibin hirar tata shirme ce, tayi baƙi ƙirin duk ta bushe kamar wadda aka tsotse wa sinadaran jikinta.
Gaddafi ma sun sha hira sosai da sosai da Nana. Da Safe da ta ce zata fita sai da Baba ya yi ta mitar daga zuwanta za ta fara yawo.
Amma Nana ta nuna masa fitar ta dole ce, gidan Ummi za ta je. Tare da Jamila suka tafi gidan Alhaji Fatuhu.
Sashen Fadila suka je, sai dai har suka gaisa ba ta gane su ba, har gara Jamila tana ta ƙoƙarin tuna ta.
Yaronta Muhsin ne ya fito ya taso daga bacci, kamarsa ɗaya sak da wancan Muhsin ɗin.
Nana na ganinsa ta miƙe tana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah. Banda na zo gaisuwar Muhsin, da cewa zan yi Muhsin ɗina ne nan". Ta yi maganar tana ɗaukar Muhsin tana shafa kansa.
Fadila ta ce "Ya salam, Anty ai sai yanzu na gane ki, malamar Muhsin ko? Ai kin canza kamanni ne gaba ɗaya. Tun da ki ka yi aure bamu sake ganinki ba"
Hawaye ya cika idanun Nana, ta ƙanƙame Muhsin, tana tuna wancan.
Jamila ma cikin kuka ta ce "Na yi dana sanin Hajiya Sa'a, da tuni wannan ma ta bayar da shi kamar yadda ta bayar da wancan"
A razane Fadila ta kalle ta ta ce "Me ki ke nufi?"
Nana ta ce "Babu abin da take nufi"
Fadila ta ce "A'a ga abu nan tana faɗa, kenan da gaske Hajiya Sa'a ita ta bayar mini da Muhsin ɗina? Ya aka yi ki ka sani"
"Fadila na gaya miki wannan zancen ba haka yake ba, meyasa ki ke da gardama ne? Wannan ɗin suwaye su?"
Ya kalli Jamila ya ce "Wannan ba ke ce nake gani a gidan Sa'a ba? Ya aka yi ki ka san wannan zancen?"
Nana ta katse shi, ta hanyar gaishe shi, ya amsa sai dai tana magana ya gane ta.
Ya ce "Nana ke ce?"
Nana ta jinjina masa kai tana murmushi.
"Baiwar Allah kin san tsawon lokacin da na ɗauka ina neman ki? Na din ga mafarkai daban-daban da ke. Jinya na haɗu da ita bayan kin yi aure"
Fadila kasancewar ba wannan maganar take buƙata ba, cikin ɗimuwa ta ce wa Jamila ta gaya mata abin da Hajiya Sa'a ta yi wa ɗanta.
Alhaji Fatuhu ya fara ƙoƙarin karewa ya hana, amma Jamila ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, na haddass muku fitina, amma gara na faɗa dan abu ne da yake ta damuna." Nan ta kwashe komai ta faɗa, har abin da Alhaji Fatuhu bai sani ba, da yadda ta shiga ƙungiyar asiri duk sai da ta faɗa, da yadda Abba ya mutu maimakon Muhsin.
Cikin kiɗimewa Fadila ta riƙe Alhaji Fatuhu tana faɗin "Amma ka zalunce ni, saboda ka kare 'yar uwakka, ka din ga yi mini wasa da hankali ka ƙi yarda da abubuwan da take faɗa. Ɗana gudan jinina aka ba wa matsafa. Ɗana fa ɗan da na sha wahala na haifa."
Nana ce ta sauke Muhsin, ta je ta kamo Fadila ta rungume ta cikin rarrashi ta ce "Yanzu wannan da ki ka haifa kin san Allah zai baki shi? Dan haka ko da ita ko babu ita, Allah ya ƙaddara ba rayayye bane ba. Kuma da na