Showing 12001 words to 15000 words out of 124686 words

Chapter 5 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

87

ke kwanciya a nan gurin"

"Lafiyata ƙalau. Na ɗauka zan gan ki cikin murna da farin ciki, tun da mijinki ya dawo hayyacinsa ya gane ki, sai kuma na gan ki cikin damuwa?"
Ta nemi guri ta zaune a gefen Ƙaisar ta ce "Ni fa ba na ƙaunar mutumin nan, fatana kawai ya bani ɗa na, na koma Nigeria Ubangiji Allah ya sanya su Baba su yafe mini, ina kyautata zaton alhakinsu ne ya kama ni"

Ƙaisar ya ce "Waye ba kya ƙaunar yanzu?"

"Sayyid"

"Ƙarya ki ke yi" ta ce "Ƙarya kuma?"

"Da dai ban san halinki ba ne"

Cikin sanyin jiki ta ce "Da gaske nake, ba wasa nake yi maka ba. Ba na ko ƙaunar jin sunansa, ya yaudare ni, sun cutar da ni. Gaba ɗaya kimarsa da son da nake yi masa sun zube a idanuna"

Ƙaisar ya yinƙura ya tashi zaune, yana ƙara rufe jikinsa ya ce "Tun da ya ce ki saurare shi, ki tsaya ki ji mai zai ce miki mana. Kar zuciyar da ki ka yi ta sanya ki yanke hukuncin da ba zai ɓulle muku ba"

"Ni fa babu abin da zan ji daga bakinsa, ba na buƙatar sa a rayuwata gaba ɗaya" Ƙaisar ya yi murmushi yana gyara zamansa a hankali. Idon Nana ya sauka a kan Jakar Sarkin baka da ke gefen gadon da yake.
"Ƙaisar, me ka ke yi da jakar Sarkin baka?" Ya yi mata shiru kamar bai ji ta ba.
Miƙewa ta yi da sauri ta ce "Wani abu ya faru tsakaninka da Giyaz ko?"

"A'a aron jakar na yi, wani aiki na yi da ita".

Nana ta saka hannu ta ɗan ja mayafin da ya rufe jikinsa da shi, wani irin haske ne ya haske mata ido, daga bisani hasken ya ragu a hankali.
Jikinsa ya yi wani irin kore-kore, wani gurin kuma ya yi baƙi ƙirin tamkar an ƙona shi.
Nana ta ce "Meyafaru? Me ya same ka haka? Giyaz ya yi maka wani abu ne?"

"Babu abin da ya faru, zan dawo miki da jakar ki kuma, ki je sai na sake neman ki" Nana ta farka daga baccin da take yi, fuskarta duk hawaye.
Gaba ɗaya jikinta a sanyaye ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili, sannan ta gabatar da sallar asuba.
Har gari ya yi haske, tana zaune a ƙasa. Shiru ta yi tana tuna yadda ta ga jikin Ƙaisar, sai ta ji abin ya dame ta sosai da sosai.

"Mene ne makomar wannan sakankancewar da nake yi da Ƙaisar yanzu? Me yasa kuma yake taimakona a wasu guraren? Anya ba wani tarkon na yaudara ya yi mini ba, yake son na afka ya yi amfani da damar ba? Ko ma dai yaya ne, Ubangiji Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abin ƙi." Sosai take son mantawa da tunanin Ƙaisar, ta koma tunanin Muhsin, da wannan balahirar ta gabanta, amma abu ya ci tura, a jikinta take jin Ƙaisar, take jin ta damu da halin da ta gan shi a ciki.

Sallamarsa ce ta katse mata tunani, ta amsa masa ciki-ciki. Ya je gabanta ya ajiye tray. Ya ɗan tsura mata ido ya ce "Barka da safiya Rayuwata" Wani mugun kallo ta yi masa, haɗi da uwar harara.

Ya yi murmushi ya ce "Ga abin karyawa nan, kar ki manta sakin jikinki, da cin abincinki ne zai sanya ki ga ɗana"

"Ka daina danganta mini ɗana da kanka, ba shi wata alaƙa da kai" Ta yi maganar cikin tsiwa.

"Ba shi da alaƙa da ni, sai da Ƙaisar?" Ya yi maganar ya kallonta yana murmushi. Bai ba ta damar ba shi amsa ba ya ce "Yau zan koma gida, zan je na ji yadda za mu yi da su Sultan, amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki dan Allah"

"Ba ni da wata nutsuwa ko kwanciyar hankali, idan ba ɗa na na gani ya zo hannuna ba".
Ya yi shiru yana tsare ta da idanunsa.
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ji gabanta ya faɗi, ta rasa gane wane irin kallo ne yake yi mata haka.
Ta sunkuyar da kanta tana haɗe rai.
Ta sake ɗaga ido ta suka haɗa ido, ya yi mata murmushi, ya ce "Ma vie, ban san daga ina nake jin ƙaunarki ba a rayuwata, kar ki hukunta ni da abin da ki ka gani kawai a zahiri. Ina sake roƙonki, ki bani dama ki ji ta bakina"

"Ni babu abin da zan ji, na ce maka ɗana kawai nake buƙata"

Ya shafi sajensa ya ce "Muhsin ai nawa ne ni da Asal. Idan ki ka haihu kuma nawa ni da ke, shi ma idan ba kya so sai ki bani abina"

Wata irin ɗagowa ta yi, cike da takaici, ya shammace ta ya rungume ta ya haɗe bakinsu.
Nana ta tattara nutsuwarta, da duk wata jarumta dan ganin ba ta biye wa Sayyid. Ta din ga ture shi iya ƙarfinta tana kai masa duka, amma tamkar dutse ba jikin ɗan Adam take duka ba. Sai da ta gaji ta ƙyale shi. A hankali ya zare bakinsa daga nata ya ɗago fuskarta yana kallonta.

Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taɓa samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina ƙaunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar.
"Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a ɗakin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar ɗakin, ta bi bayansa da harara.

Nene ce rungume da Muhsin, ya sha ado cikin kayan buzaye, kayansa iri ɗaya da na jikin babansa, sai ƙoƙarin cire mayafin da aka rufe masa gashinsa da shi yake yi, sai ƙamshin turare yake yi.
Hammad ya saka hannu ya karɓe shi fuskarsa ɗauke da murmushi har da wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.

Hammad ya ce "Mu je ko?"

Nene jiki a sanyaye ta ce "Ina mai neman afuwarka, ni tsoron zuwa gidan nan nake yi. Kuma a wane hali Nana take ciki yanzu, na kasa nutsuwa gaba ɗaya, ina jin ban kyauta ba gaba ɗaya"

"Ki kwantar da hankalinki, Nana tana tare da ni, kuma babu wanda zai yi miki komai a cikin gidan, ki taimaka mini dan Allah"

AREWABOOKS

Nene ta numfasa ta ce "Alfamarka ce kawai za ta sanya na yi maka abin da ka nema, dan na yi alƙawarin babu abin da zai sake haɗa ni da wannan gidan naku, saboda mummunan tabon da yake binne a zuciyata. Kuma da ko me za ka yi mini ba zan ba da ɗan nan ba, saboda ya saɓa alƙawarin da muka yi da Nana, ban kyauta mata ba za ta yi mini kallon mutuniyar banza mara alƙawari. Amma kai ma ɗa ne a gurina, ban da dalilin haka gaskiya ba zan iya ba"

"Na sani, kuma na gode sosai da sosai, da wannan alfarma da ki ka yi mini"

Ta risunar da kanta cikin girmamawa. Ya miƙa mata Muhsin ta karɓe shi, suka shiga mota.

*****
A tsanake Tafawa ya kalli Asad ya ce "Asad, wai waye ka ce ya karɓi ayabar nan ya ci?"

"Wata yarinya ce, ni ban santa ma a gidan nan ba gaba ɗaya"

"Dole a nemo ko wacece, saboda an tabattar mini, da cin ayabar da ta yi, da gayya ta karɓa ta ci, dan aikin da aka yi ya ɓaci ya lalace."

Asad ya yi shiru, ya ce "Gaskiya ban san ko wace ce ba, sai dai ko a tambayi Asal, ko ta santa abinci dai ya kawo mana. Ina kyautata zaton ko kuku ce ko dai makamancin hakan. Ban ma san yadda aka yi ta zo inda muke ba, dan kamar ba buzuwa ba ce gaskiya"

Tafawa ya yi shiru yana nazari, ya ce "Babu yadda za a yi wadda ba buzuwa ba, ta tsallako ta shigo gidan sarautar Agadez, ta yi wannan abin, lallai zuwanta na manufa ne, dole a binciko wace ce."
Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa.

Asal duk ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankali, mussaman da Imam ya kwana uku ba ta san inda ya shiga ba, hakan ya sanya ta fara jin kamar akwai ƙamshin gaskiya a maganar da Tafawa ya gaya mata. Ta kasa jurewa ta je ta samu Sultan, tana yi masa kuka.

Cikin damuwa ya ce "Yarinyar kirki lafiya kuwa?"

"Sultan ji na yi an ce wai Imam yana da ɗa, dama aure ya yi ban sani ba? Kuma tun shekaranjiya ban sake ganinsa ba, kuma ba na samun sa a waya"

Sultan ya ce "Waye ya gaya miki?"

Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. Ya numfasa ya ce "Shikenan na fahimta, amma ki kwantar da hankalinki, na tabattar da Hammad ba zai aikata abin da zai zubar da kima da mutuncin gidan nan ba, dan haka ki yi haƙuri ki bani lokaci, ina kan bincike ne"

"Amma Abie, to ina ya tafi, haryanzu ban san inda yake ba, kuma wayarsa ba ta shiga"

Sultan ya ce "Na sani, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki. Zai dawo in sha Allah" Asal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi, sai dai zuciyarta ta gaza haƙuri da samun nutsuwa.

Washegari, Sultan na tare da Sardauna da kuma Matawalle su na tattaunawa, aka zo neman iso cewar Imam Hammad yana neman izinin shigowa.
Cikin takunsa mai burgewa, ya shiga. Gaba ɗaya suka zuba masa ido suna kallonsa.
Hammad ya nemi guri ya zauna a ƙasa tare da gaishe su. Matawalle ya amasa masa. Sultan kuwa rasa abin cewa ma ya yi sai daga bisani ya numfasa ya ce "Ina ka tafi tsawon kwanaki uku haka, ka kashe wayoyinka ka tayar mana da hankali?"

Hammad ya numfasa ya ce "Ina mai bayar da haƙuri, na laifin da na aikata, na yi hakan ne, domin tabattar muku da abin da na faɗa. Ina cikin hayyacina na faɗi abin da na faɗa, kuma da shaida a kan abin da na faɗa".
Sardauna ya ce "Ka na da hankali kuwa? Ka na nufin da gaske ka haihu da matar da ba mu sani ba?" Ya jinjina kai daidai lokacin da Mahmoudu ya shigo ɗakin shima."

Matawalle ya ce "Ga munafukin nan, ya san komai"

Sardauna ya ce "Ni kun sani a duhu, shi kuma wannan waye ya kawo shi cikin wannan mas'alar?"

Sultan ya ce "Bari mu ji ta bakinsa"

Mahmoudu ya zauna ya gaishe su. Sannan ya numfasa ya ce "Da fari ina neman afuwar mai girma Sultan, da ahalinsa da 'yan majalissar sa, da ma duk wani wanda abin ya shafa. Na san na aikata laifin da na cancanci hukunci, kuma a shirye nake na karɓi hukuncin laifina, na aikata abin da ya saɓa wa dokar masarauta duk da girman matsayin Imam Hammad a ƙasar nan"

Sardauna ya ce "Mu na jin ka, ka yi mana bayani, me ka aikata, kuma me a sani a kan lamarin?"

Sultan ya numfasa ya ce "Wato Sardauna mun ɓoye wa mutane abubuwa da dama da suka faru. Magana ta gaskiya Imam Hammad ya samu matsala ya bar ƙasar nan bamu sani ba. Mun yi ta bibiyar inda zamu samo shi. Muka rufe muka ce yana faransa babu lafiya. Da muka rasa shi, aka rasa hadiminsa Mahmoudu, shi ne muka koma binciken Mahmoudu ta ƙarƙashin ƙasa, aka yi nasarar gano su a Nigeria. Sai dai da aka dawo da shi Agadez tamkar ya manta da mu baki ɗaya, baya cikin hayyacinsa. Bamu san haƙiƙanin abin da ya faru a Nigeria ba, sai dai idan sun yi mana bayani yanzu.

Abin ya ɗaurewa Sardauna kai, gaba ɗaya bai san lamarin nan ba sai a yanzu, jin abin yake tamkar almara.

Mahmoudu ya ce "Bayan na tafi da Shugabana Imam Hammad Nigeria, nema masa magani, bayan da na fuskanci ya manta duk wani abu da ya shafe shi. A can muka haɗu da yarinyar a gidan da muka zauna, mahaifinta ya ba shi aurenta. Shi da kansa ya ce a biya sadakin aurensa da ita. Tun da shugabana ne ba ni da 'yancin yi masa musu. Na yi ƙoƙarin tunatar da shi, amma ko na tuna masa, ba zai iya tuna komai da ya shafe shi ba"

Matawalle ya ce "Wai wannan wace irin shiririta ce ku ke karanta mana? Wane irin abu ne haka? Ta yaya mutumin da ya manta komai ya san ya ce a biya masa sadaki ya yi aure?"

Mahmoudu ya ce "Imam waye shi, da duk abin da ya shafi Agadez ya manta, amma duk wani abu na rayuwa na yau da kullum ya sani. Kuma ga shi a tambaye shi, tun da yanzu yana iya tuna abubuwan da suka faru a Nigeria"

Sardauna ya ce "Shi tunanin nasa network ne kenan, ko zamani da idan wannan ya zo wannan zai wuce?"

Kafin Mahmoudu ya bayar da amsa, Matawalle ya ce "Wato Mahmoudu ba ka ji kashedin da na yi maka ba a kan sanar da shi wani abu ba"

Mahmoudu ya ce "Ba laifina ba ne ranka ya daɗe, shugabana ne duk abin da ya umarce ni, dole na yi ba ni da zaɓi"

Hammad ya miƙe ya ce "Ina zuwa"
Ko da Hammad ya fita, Mahmoudu suka ci gaba da yi wa tambayoyi, yana ta ƙoƙarin basu amsa da rufa wasu abubuwan.

Tsit suka yi da suka ga Hammad ya dawo, Nene na bin sa a baya da ɗa a hannunta.

Matawalle ya ce "Imam me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Nene ta yi turus tana haɗe rai ta sunkuyar da kai.
Kafin su ƙara magana, Muhsin ya jefo mayafin kansa ƙasa, tare da waiwayowa yana kallon mutanen gurin.
A sukwane Sultan ya miƙe tsaye. Imam Hammad ya karɓi Muhsin daga hannun Nene, ya nufo Sultan da shi. Jikin Sultan ya hau tsuma, yana kallon yaron da ya jiye tamkar Hammad ɗin sa yana ƙarami.
Shi kuwa Muhsin kallon babansa ya din ga yi yana kallon Sultan, ganinsu iri ɗaya. Ya miƙa hannu ya ɗauki Muhsin yana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah"

Su kan su Sardauna da Matawalle, ƙura wa yaron ido suka yi, duk sharrin mai sharri ƙarya ne ya ce wannan ɗan ba na Hammad ba ne ba.

Matawalle ya ce "Ikon Allah, da gaske dai Hammad yana da ɗa"

Sultan ji yake yi tamkar ya haɗiye Muhsin, da a yake son ya sauke shi ya koma gurin Nene. Ya juya yana miƙawa Hammad hannu ya ɗauke shi.

Sardauna ya miƙe ya ce "Yanzu ina uwar yaron take"
"Tana nan" Imam ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.

Sardauna ya ce "Akwai rikita-rikita a lamarin nan. Dole a san yadda za a yi. Mu na buƙatar ka zo mana da uwar yaron nan, gobe in Allah ya kaimu.
Ku kuma zamu tsare ku har sai komai ya daidaita mun gano komai."

Nene ta ce "Ranka ya daɗe me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da tsare shi da duk abin da za ku yi masa, amma ni ina roƙon alfarma a ƙyale ni na tafi"

Matawalle ya ce "Jayayya za ki yi da abin da muka ce kenan?"

Nene ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Hammad ya ce "Zan cika miki alƙawarin da na ɗauka, babu abin da zai faru in sha Allah, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu zan zo da ita" Nene ta yi shiru cikin sanyin jiki.

Duk yadda Sultan ya so ƙanƙame Muhsin ya ƙi yadda, ya zamo ya sauka daga jikinsa, ya koma jikin Nene ya kwanta, ya saka hannunsa a baki.
Gaba ɗaya Sultan ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda ganin Muhsin, bayan shafe lokaci yana fatan ɗan nasa ya samu haihuwa.

Sardauna ya ce "To ita matar Mamman me ya kawo ta cikin wannan lamarin ne? Na ga kamar yaron ma ya santa?x

Hammad ya ce "Eh, a gurinta yake ne" Haka aka killace Nene da Mahmoudu, aka hana su zuwa ko ina.

*****

Ko da ya shiga sashensa babu kowa, Asal ba ta nan, ya yi mamakin inda ta tafi. Ya tafi kitchen ɗin da Nana take girki, ya shiga ya buɗe fridge ya samu sassanyar madarar raƙuma, ya tsiyaya ya fita.
A ƙalla ya kai awanni biyu a zaune, sai ga Asal ta dawo, babu tsammani ta gan shi a falo a zaune.
Ɗan turus ta yi tana kallon sa. Ya ce "Ƙaraso mana" Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi.

"Ina ki ka je haka?"

"Nemanka na je yi" ta furta jiki babu ƙwari.

"To zan gudu ne? Ai gani na dawo"

"Wancan karon ma ai ka tafi ka bar ni"

Ya yi murmushi ya ce "Wannan na larura ne ai Cherié" Ya yi maganar yana miƙewa, har ya nufi bedroom ta ce "Hammad" tsayawa ya yi cak, jin ta kira shi da gundarin sunansa na yanka.
"Da gaske ka haihu da wata a waje ban sani ba?"

"Waye ya gaya miki?"

Asal ta kalle shi ta ce "Kar ka amsa tambayata da tambaya, ka bani amsa ko na samu nutsuwar zuciya, babu abin da yake yi mini daɗi. An ce ka kira ni da juya, kuma ka ce ka na da ɗa, da gaske haka ne?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.

Sai ya fasa shiga ɗakin, ya nufi inda take zaune, ya tsura mata ido sannan ya ce "Ni da ke na taɓa gaya miki haka? Ta girgiza kai jiki a sanyaye.

"Wanda ya gaya miki ya so cin mutuncinki ne, amma da bakina na taɓa faɗa?" Ta girgiza kai jikinta a sanyaye.

"To ki toshe kunneki daga jin abin da za a zo a gaya miki wai wai, ki jira abin da zai fito daga bakina zuwa kunnuwanki"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, amma ba ka gaya mini inda ka je ba"

"Wani aiki nake yi wa Sultan, ki kwantar da hankalinki" Ya miƙe ya tafi ya bar ta a gurin.
Da magariba ta ga yana ta shiri, ta ce "Amour ina zaka je ne?"
Ya ce "Eh yanzu zan yi miki bayani, zan je wani aiki da Sultan da ya saka ni ne, sai gobe in Allah ya kaimu zan dawo"

"Aiki kuma sai da daddare?"

Ya kalle ta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login