Showing 96001 words to 99000 words out of 124686 words
nan take faɗa ne haka?"
Mama ta ce "Nima ban sani ba wallahi, ina ga jikin ne ya motsa."
Baba ya ce "Jikinta ya motsa kuma take irin wannan maganganun?"
Ba ta ko saurare su ba, ta ci gaba da surutanta. "Ni ban so shiga kungiyar nan ba, dole ki ka yi mini, ga shi kin sanya ni a bala'i, na rasa mutuncina, kin saka nayi kisan kai, yanzu kuma na kasa samun kwanciyar hankali, sai tsorata ni ake yi, nima ana nema na a kashe ni, kin cuce ni"
Baba ya ce "Jamila, meyafaru ne? Me ki ke faɗa wai?"
"Baba riƙe hannuna, Baba ku taimake ni"
Ya ƙarasa ya riƙe hannun Jamila, cikin kuka ta ce "Baba na shiga uku, na aikata mummunar ɓarna, Baba hakki ne zai yi ajalina"
Baba ya ce "Jamila, ki gaya mini, me ki ka aikata?"
"Ƙungiyar asiri, Baba ƙungiyar asiri aka shigar da ni, saboda na kai jinin Nana"
Kamar ta watsa wa Baba wuta, haka ya fizge hannunsa ya ja da baya, yana kallon Jamila da take ta uban kuka.
Mama ta ce "A'a baban su Jamila, dan Allah kar ka yarda da abin da ta faɗa, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya, wataƙila zafin ciwo ne, amma wace irin magana ce wannan, a ina Jamila za ta ga wata kungiyar asiri ta shiga"
Alhaji Zailani ne a durƙushe a gaban gawar ɗansa Yusuf, bayan an dawo da shi daga makaranta, dama babu rai aka dawo da shi. Ba shi ne abin da ya ɗaga masa hankali ba, sama da ganin busashshen jini a baki da kuma hancin Yusuf. Ba dan ya yi iya ƙoƙarinsa ba, da tuni ya aikata abin da zai fallasa kansa. Wani irin raɗaɗi da zafi ya din ga ji a zuciyarsa ya kasa magana, ya kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi.
Ba a jima ba, gidansa ya cika da jama'a, Hajiya Amina sai kuka take, ga Shukura ta ɓata, ga kuma mutuwar Yusuf.
Ya hau neman lambobin yaransa, da ya sanya su kashe Shukura, a kan kar su kuskura su kashe ta, amma ya kasa samun su. Duk da daɗewar da yayi yana aikata zalunci kala-kala, mutuwar Yusuf ta dake shi, ta tsaya masa. Ya din ga jin tamkar ya yi ta kururuwa yana burgima, ko zai ji daɗi.
Ko da aka yi jana'izar Yusuf, Alhaji Zailani tafiya ya yi ya kulle kansa a ɗaki. Kaf yaransa babu kowa sai Shukura yanzu, Shukuran ma ba a san inda take ba. Kuma ita ma baya tsammanin za ga tsallake sharrin dodon ƙungiya, tun da ya gaza bashi jinin shekara.
Sosai ake ta shirye-shiryen gudanar da bikin auren Imam Hammad, da matarsa 'yar Nigeria. Ita Nana abin har mamaki yake bata.
Tun da Sultan ya amince da auren Nana da Sultan, Nene take sintiri kawo wa Nana kayan gyaran jiki. Ban da matar da ake ware mussaman Nene take zuwa da ita, take yi wa Nana wani irin gyaran jiki na mussaman.
Nana ta ce "Nene duk wannan abin fa ihu ne bayan hari"
Nene ta ce "Ke, gyaran ne ba kya so?"
"To Nene ya riga ya sanni a yadda nake, me kuma zan gyara?"
Nene ta ce "To kar ki gyara, komai yana buƙatar gyara ai"
Aka ajiye wa Nana kayan sakawa, da na ado irin na Buzaye. Nana ta ƙudurce a ranta, bayan ta tare, kayanta na 'yan Nigeria za ta saka Hammad ya ajiye mata, saboda ita ma tana son tata al'adar.
Shi kansa Hammad ya so a ƙyale masa ita a haka, dan shi komai nata ya yi masa. Sai dai gyaran jikin da ake yi matan ba ƙaramin kyau take yi ba.
Ga shi tare da Muhsin suke kwana da Nene, hakan ya ƙara sanya ta farin ciki.
Hammad ya ce ta fita ta ɗan zagaya, amma ta sanya takunkumi ta rufe fuskarta.
Har mamaki Nana take yi, yadda idan Muhsin ya ga raƙuma ko shayi, kamar zai tashi sama saboda murna. Sarkin baka ta hango, suka nufe inda yake.
Cikin jinjina ya ce "Barka da tattaki uwar gijiyata" Nana ta yi dariya ta ce "Dan Allah ka daina kunya ka ke bani"
Shi ma yana murmushin ya ɗago ya kalli Nene, ya ce "Ni kuwa dama ina ta son na yi miki magana, Allah bai yi ba"
Nene ta ce "Ni ɗin ko? Ka sanni ne?"
Ya ce "Eh, ai duk inda muka ga juna, muna gane kanmu"
Ta yi dariya ta ce "Na ji, ai ban yi zaton haryanzu akawai abin da tattare da ni ba"
Sarkin baka ya ce "Ni na ji na gane ai. Kuma ni ɗalibin marigayi Sa'adu Aska ne"
Nene ta waro ido ta ce "Kana nufin Babana?"
Sarkin baka ya ce "Ƙwarai da gaske, ya sanar da ni magunguna, sai muka kwana casa'in tare da shi, a mabanbantan dazuzzuka, daga bisani muka rabu, ban sake ganinsa ba. Mahaifinki mutumin kirki ne, ba zan manta da shi ba har abada"
Nene ta ce "Ikon Allah"
Nana ta ce "Sarki kai komai ma ka sani ne? Kuma kowa ya sa ka"
Yayi murmushi ya ce "Na san dai abin da Allah ya sanar da ni, kowa ya sanni kuma na sha yawon duniya ne" Yayi maganar yana ɗaukar Muhsin.
Nana ta ce "Sarki ka ga Nene ta daina harkar bayar da magani, kaima ina fatan zaka daina?"
Ya ce "Meyasa zan daina? Ba a daɗe ba ni ba, ke kanki ki ka bayar da magani zan ce, ko ba ke ki ka tono inda aka yi wa mijinki asiri, meyasa Allah ya zaɓe ki ya nuna miki, duk yawan jama'ar da ke ƙasar nan. Abin da ki ke ta gudun sai da ya faru"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ba ina nufin ka daina bayar da magani ba, ka daina aiki da aljanu, shi ne ɓarnar. Sannan ka yi ilimi na zamani, cikakke domin ka inganta harkar maganin naka. Ya zamana maganunnanka da awo kar ka bayar da abin da zai cutar maimakon a samu lafiya"
Yayi dariya, Nene ma ta yi, Ya ce "Yaro yaro ne. Nana a dalilinki wallahi na daina surkullen haɗa ayoyin Alkur'ani da wasu abubuwan na yi sihiri. Saboda uban gidana ma, Allah ya ja zamaninsa uban duƙusa ko in ce Ƙaisar, shi ma ya ce na daina wannan, na kuma daina. Na daina surkulle da sihiri na tuba, amma ba zan iya daina aiki da aljanu ba"
Nana ta ce "Amma saboda me?"
"Saboda ɗebo mini magani, wasu ayyukan kuma dole su ne nake aikawa su yi wani aikin."
"Sarki, ta'amalli da aljanu da ka ke yi ba shi da wani alkhairi shirka ne, dan Allah ka daina. Kana cikin mutanen da nake son mu tsira Duniya da lahira."
"Ni ba ni na nemi aljanu na fara aiki da su ba, aljanu su suka takura ni, kamar dai ke da kuma wannan baiwar Allah.
Bana ta'amalli da aljanu, na bayar da kuɗi, ko na yi wa wasu sihiri, ko wani abu makamancin haka, ai kin je gurin maganin nawa kin gani"
Nana ta ce "Sarki, kar mu shiga wani bugire da bai kamata mu shiga ba, mu kalli gaskiya kai tsaye kar mu yi mata wata kwaskwarima saboda son zuciyarmu"
"Asma'u babu kwaskwarima domin ba wa ƙarya kariya a maganganuna. Su turawan da ku ke taƙama da su, su na amfani da ku, da daƙile magungunnku ne, saboda gina nasu kasuwancin. Kuma Nana magunguna na da awo nake bahar da su. Ban ƙi ba akwai masu bayar da magani, saboda neman abinci. Amma wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba, bai sani ba kawai. Kuma banda abin ki tun a zamanin baya magungunan 8su na da awo, wani a ce ka auna da ɓawon gyaɗa,ko farce, wani a ce ka sha safe da yamma, duk sharri ne wasu abubuwan da ake faɗa, da ƙoƙarin kashe mana magungunanmu. Sai a ce ku daina shan magungunan gargajiya saboda ɗaci, hanta ba ta son ɗaci, amma Allah ya halicci maɗaciya a tsakiyar hanta. Idan hanta ba ta son ɗaci, Allah ba zai sanya matsarmama a cikin hanta ba. Kuma su magungunan baturen, ba ɗaci ne a cikin su ba. Ba zan kushe wa kowa ba, amma kar a kuskura a kushe mini nawa. Yakamata mu daina wannan musun haka,kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai "
Nana ta ɗan yi jimm tana tunani, daga bisani ta ce "Wasu maganganun naka na kan dai-dai, amma kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai!"
"To ki daina takura mini a kan lallai sai na yarda da abin da ki ke kai"
99
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
Har Nana za ta sake magana, Nene ta riƙo hannunta, ta ce "Nana mu koma ciki, ai kin ɗan tattaka, kin san baya son a ganki, ko a gane ki a yanzu. Ɗan uwa idan muka kuma haɗuwa zamu tattauna sosai mu gaisa.
Sosai shirye-shirye suka yi nisa, hankalin Sultan gaba ɗaya ya koma kan shirin zuwa Nigeria da bikin da za a gudanar. Sai dai yana ta fuskantar ƙalubalanta a kan hukuncin da ya zartar.
Gimbiya Bilkisu ta rasa inda zata sanya kanta, ta tuntuɓi Tafawa ta sanar masa da matakin da Sultan ya ɗauka a kanta, amma ya ce mata shi ma ta kansa yake yi, hankalinsa a tashe yake.
Duk yadda ta kai ga ƙoƙarin yin dabarun da Sultan zai saurare ta, fafur ya ƙi ko kallo ba ta ishe shi ba.
Ranar ƙarshe ma da ta je ɗakinsa kamar zai dake ta ya ce "Bilkisu bana ƙaunarki bana ƙaunar ganinki, tun da har za ki yinƙurin sabauta mini rayuwar ɗa, idan ki ka sake zuwa inda nake, sai na yi miki abin da baki taɓa tsammani ba, fice ki bar mini ɗaki kafin na yi miki illa" Abin ya ɗaure mata kai, bata taɓa tunanin zai yi irin wannan fushin har haka ba.
Jamila ta koma gata nan gata nan, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, kuma ita ba mara lafiya ba. Shi Baba gaba ɗaya ma yanzu tsoro suke ba shi. Ya riƙe istigfari ba dare babu rana, gaba ɗaya yaransa sun watse babu wani na kamawa.
Gaddafi ya zo gida, ya tarar da gidan nasu duk wani iri. Yayi mamakin ganin yadda Jamila ta wani rakwakwkwaɓe, jiki babu ƙwari, ta yi wata irin muguwar rama ta fita daga hayyacinta kamar ba ita ba.
Sun dawo daga sallar Asuba, tare da Baba, Baba ya numfasa ya ce "Gaddafi ka ga yadda Allah ya yi da gidanmu ko? Gaba ɗaya babu wani mai ɗan dama-dama"
Gaddafi ya ce "Na gani Baba, ina son na yi magana dai na fasa, na ga Suwaiba ta daina magana gaba ɗaya, har da dalalen yawu take yi. Jamila kuma na kasa gane abin da yake damunta"
Baba bai ɓoye masa komai ba, jikin Gaddafi ya din ga tsuma, ya dubi Baba ya ce "Baba, Jamila ta yi ciki, kuma tana maganar ƙungiyar asiri? Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Cikin matsananciyar damuwa Bab ya ce "Babarta ta ce zafin ciwo ne, amma na kasa yarda nima" Ya yi maganar yana zubar da hawaye.
Gaddafi ya ce "Shiyasa Baba na din ga maganar kuɗin da ta din ga ta'amalli da su, amma mahaifiyarta ta nuna ba ta so, ta nuna baƙin ciki nake yi, da ci gaban Jamila ka ga irin abin ko? Shikenan sun lalata mana gida"
Baba ya yi kuka ya ce "Ina kyautata zaton hakkin yaran nan ne, su Nana, dan sai daga bayan nan, nake duba wasu abubuwan da na aikata musu na ga sam babu adalci a cikinsa. Amma wasu mutane sun zo wai daga Agadez sun ce mini tana gurinsu" Nana Baba ya gaya wa Gaddafi abin da su Mahmoudu suka zo masa da shi.
Gaddafi ya rikice ya ce "Baba kuma baka karɓi lambar wayarsu ba ko ka bi su ba?"
Baba ya girgiza kai ya ce "Ban karɓa ba, ni tsoro ma na ji, ji nake kamar ƙarya suke yi. Na bar wa Allah ikonsa"
"Amma Baba akwai mamaki a cikin abubuwan da suka faɗa, masu sarƙaƙiyar gaske"
Baba ya ce "To ai shiyasa ban ma gazgata ba, sai abin da hali yayi"
Gaddafi ya ce "Ba wani abu, in sha Allah mu tsammaci alkhairi"
Baba ya jinjina kai cike da gamsuwa.
****
Nana ce a tsaye, tana kallon Ƙaisar, yana zuba wa wata tsuntsuwa abinci a cikin keji.
Nana ta kalli tsuntuwar ta ce "Ƙaisar ita kuma wannan fa, a ina ka samo ta?"
Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce tsinto ta na yi a daji, za ta mutu, ban zaci ma zata rayu ba, sai kuma na ga ta farfaɗo yanzu ta ware ma"
Nana ta ƙarasa gaban kejin ta zauna, sannan ta ce "To kuma tsuntsuwa ce ita, ko kuma aljana ce?"
Ya kalli Nana ya ce "Dama akwai tsuntsu mutum da aljan ne?"
Nana ta ɗan yi shiru tana kallon tsuntsuwar.
Ya ce "Mutum jinsinsa daban, aljani daban, haka ma tsuntsu daban. Babu Aljani tsuntsu sai dai Aljani ya shiga jikin tsuntsun, ina fatan kin gane?"
Ta gyaɗa kai, ta ce "Haka ne, wai ni kuwa Ƙaisar ina Haulat? Ka fara son nata?"
"Ban sani ba" Ya yi maganar yana hararta.
Nana ta yi murmushi ta ce "To shikenan kai ba zaka yi aure ba kenan? To sonta ne baka yi ko kuma me ta yi maka?"
Yayi mata shiru, yana rufe kejin tsuntsuwar nan.
Nana ta numfasa ta ce "Ƙaisar ina kewar gida fiye da tunani, zuciyata kuma ta cika da fargabar rashin sanin abin da zan je na tarar. Ina jin kunyarsu ban san da wani idon zan kalle su ba. Duk da Imrana ya haɗa ni da Mama, ta yi mini Addu'a ta ce na kwantar da hankalina, amma kunyarsu nake ji ban kyauta ba abubuwan da na yi"
Ya ce "Za ki tarar da alkhari in sha Allah, da abun da zai yi miki daɗi da wanda ba zai yi miki ba. Ni na din ga shagaltar da ke daga tunaninsu, da tunaninsu ya yi tasiri a zuciyarki, da ba ki cimma wannan nasarar ba, da kin rushe komai, dan idan ki ka koma gidan babu abin da zai canza"
Cikin mamaki Nana ta kalle shi ta ce "Ban gane ba, kai ne ka sanya na daina jin damuwar da na din ga ji a baya, da son komawa gida?"
"Sosai, saboda ruhi ne mu, mu na iya shiga ko ina a jikin ku, kuma muna iya hargitsa tunani da sanya muku rashin nutsuwa"
Ta yi shiru tana nazari, ta sake cewa "Ƙaisar ka sanya ni a fargaba, abin da zan tarar a gida da gaske mara daɗi ne? Kodayake ko ka gaya mini ma idan na tashi na san mantawa zan yi sai abin da na je na tarar kawai"
"Kin yi zaton da mugunta kawai nake nuna miki abu na mantar da ke ko?" Nana ta jinjina kai.
"Ba haka ba ne, duk da ta wani fannin haka ɗin ne, muguntar ce da takaicin ƙin yarda da abin da na zo miki da su.
Mafarki ya kasu kashi-kashi, duk da shi ma ina kan bincike a kansa. Akwai mafarkin da yake daga Allah ne, akwai mutanen da akan yi wa ishara a cikin bacci, na kusantowa ko kuma faruwar wani al'amari da bai faru ba kwata-kwata. Wasu kuma a nuna musu makamancin abin, wasu kuma su ga abu a duƙunƙune sai an fassara musu.
Galibi waɗanda aljanu ke nuna wa mutum a mafarki, na haɗin faɗa ne. Abu ne da aka yi shi a bayan idon mutum bai san an yi ba, sai su nuna masa. Kuma ba su fiye nuna abin alkhairi ba sai akasin haka. Wasu idan sun gani su na iya shiru da bakinsu, wasu kuma basa iyawa sai sun faɗa. Sai su sanya a din ga yi wa mutanen wani kallo na daban, wasu a dole dalilin hakan kan sanya su fara bayar da magani.
Ke na biyo miki ne ta hanya mai sauƙi, saboda bana son tilasta miki, na fi son ki amince da kanki. Sai na nuna miki abin da ya faru da baki sani ba, ko kuma wanda yake shirin faruwa, ko wanda nake hasashen abu ne mawuyaci bai faru ba. Akwai abin da idan na ƙyale ki, ki ka tashi da shi a ƙwaƙwalwarki, ba za ki iya yin shiru ba, za ki yi yinƙurin ɗaukar mataki, wanda hakan ka iya haifar da fitina, saboda idan ki ka haifar da matsalar ba ki da maganinta, tun da ba ki amince da bayar da magani ba.
Ɗan Adam kuna da nau'in ciwo na gangar jiki, da kuma na ruhi, amma ba kwa damuwa da ciwon da yake damun ruhinku, kun fi damuwa da na gangar jiki. Mutum zai iya kashe maƙudan kuɗaɗe, a kan lafiyar gangar jikinsa, amma sam wani baya yadda ma ruhinsa yana rashin lafiya."
Nana ta ce "Nima ban gane ba"
Yayi murmushi ya gyara zamansa ya ce "Ruhi shi ne asalin rayuwa, da gangar jiki ta dogara a kai, wanda ba a iya ganinsa, ko taɓa shi, amma wanzuwarsa ce take sanya gangar jiki motsawa. Ruhi yana da alaƙa da hankali domin shi ne, ku 'yan Adam ku ke amfani da shi, gurin sarrafa duniyarku da gangar jiki. Lafiyayyen ruhi da tunani suke samar da nutsatsiyar gangar jiki mai cike da karsashi. Rashin lafiyar ruhi, ta fi ta gangar jiki hatsari. Idan ruhi yana rashin lafiya, yana kashe gangar jiki baki ɗaya.
Sannan warkar da gangar jiki ya fi sauƙi a kan warkewar ruhi. Na san bayan nan nawa sun ɗan yi miki tsauri, amma bari na ɗan sauƙaƙa miki bayanan.
Kamar yadda na ce miki ruhinku yana rashin lafiya, tabbas yana yi ciwukan da ido baya iya gani, sai dai ciwon na sanya hankalinku ya ƙwace, ku aikata abin da ba shi kenan ba. Misali Alhaji Zailani ruhinsa na fama da ciwon Hassada, amma bai taɓa tsayawa ya fahimta ba, saboda hankalinsa ya ƙwace har ya din ga aikata miyagun ayyuka. Wasu lokutan ku kan ji duniya ta yi muku zafi, kun tsani komai babu laifin tsaye babu na zaune, yana daga cikin alamomi na ruhinku na buƙatar kulawa ba shi da lafiya. Dan wasu lokutan shi ne yake taɓuwa sai hankali ya taɓu, nan da nan sai a ce ƙwaƙwalwa babu lafiya, idan ciwon ba shi da alaƙa da irin matsalolin da muke haddasa muku a ruhi. Hassada, ƙyashi, yawan ƙarya baƙin ciki babu dalili, burin gushewar ni'ima ga wani, yawan raya faruwar munan abubuwa. Yanke tsammani daga samun rahama, ko wani abu