Showing 45001 words to 48000 words out of 124686 words
sake jan wani numfashin ba. Gaba ɗaya sai ta kasa gane me ma ake son a yi mata bayani. Wace ce ma kukun? Take tambayar kanta.
Tafawa ma sak ya yi, yana murza yatsun hannunsa, ya tsare su da idanu ɗaya bayan ɗaya, sannan ya numfasa ya ce "Ku na nufin Imam Hammad ya auri wata wadda ba ƙabilarmu ba, daga Nigeria har ta haifa masa wannan yaron da na gani?"
Sardauna ya ce "Haka ne"
Ya sake rausayar da kai ya ce "To ina fatan a wannan karon, za ku yi adalci dokar masarauta ta yi aiki a kansa, a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata."
Sardauna ya ce "Tukuna dai, sai mun ga abin da hali ya yi, saboda yanzu hankalinmu na kan samun lafiyarsa"
"Lafiya, wace irin rashin lafiya kenan yake fama da ita? Kuma me ya kai shi Nigeria? Kuma a kan me ya karya dokar masarauta?"
Matawalle ya ce "Wannan duk abu ne da za ka ji daga baya, amma yanzu a kan wannan gaɓar muke, zuwa gaba kaɗan za mu duba abin da ya dace a yi"
Wani irin kuka Asal ta fashe da shi ta ce "Hammad, abin da za ka yi mini kenan, ka munafunce ni? Ka cutar da ni, ka ajiye ni hoto ban haihu ba ka je ka haihu da wata. Saboda ka tozarta ni ba ma ka auri Buzuwa daidai ni ba sai wannan ƙazama mummunar yarinyar?"
Tafawa ya ce "Rufe mini baki, mutuniyar banza uban waye ya ce ki je ki kawo ta gidan sarauta, a matsayin kukun mijinki, alhalin kin san ba haka dokar masarauta take ba?"
Hammad ya kalli Asal ya ce "Ki yi haƙuri, na san na yi miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki haƙuri yadda al'amuran suka kasance ba wai da gangan na yi ba. Kin san babu yadda za a yi ina zaune haka kurum na ɗau jiki na tafi Nigeria na...
"Ka yi mini shiru, babu wata magana da zaka faɗa na yarda da kai, maƙaryaci...
"Hattara!" Matawalle ya yi mata tsawa.
"Ko me ya yi miki, dole ki ambace shi da girmamawa kar ki kuskura ki faɗi wani abu mummuna a kansa, ko me ya yi kuwa. Dan haka ki kiyaye harshenki"
Cikin kuka take cewa "Wallahi sai ka sake ni, ba zan zauna da kai ba, kuma na bar ka da Allah sai ka sake ni"
Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Yarinyar kirki, na san za ki ji abin wani iri, amma babu abin da zai raba aurenki da Imam. Haryanzu mu na kan tattauna matakin da za mu ɗauka amma sai kin bamu cikakken haɗin kai kin nutsu. Haryanzu ke ce halattacciyar matar Imam da kowa ya san da zamanta."
A fusace Tafawa ya tashi ya kalli Asal, da gaba ɗaya ta rikice take kuka ya ce "Ke tashi mu tafi" Ta yinƙura ta tashi ta yanke jiki ta faɗi.
Hammad ya taso da sauri ya nufo ta, amma Tafawa ya ce "Kar ka kuskura ka taɓa mini 'ya" Ya kalli Asadullah ya ce "Zo ka ɗauke ta mu tafi"
Hammad ya ce "Ba zai yiwu ba, ba zai ɗauke ta ba. Kar ya fara taɓa mini mata"
"Ni ka ke gayawa kar ya fara taɓa maka mata?"
"Ni nake da hurumin ɗaukarta, ko na taɓa ta ban yarda ya taɓa mini mata ba" Ya yi maganar yana tsare Tafawa da ido.
Sardauna ya ce "Tafawa ko da an samu rashin fahimta, bai kamata a ce ka hana shi taɓa matarsa ba, sai ka gama wannan ɓaɓatun ita kuma ta baka kunya, ai ba a shiga tsakanin mata da miji. Bari a kira barori mata su zo su ɗauke ta, a kai ta ɓangaren Gimbiya Bilkisu"
Ya ce "Babu wanda ya isa, ba wanda zai taɓa mini 'ya"
Sultan ya ce "Umarni ne, a kaita sashen Gimbiya Bilkisu, idan ta farfaɗo ta ɗan nutsu sai a kai ta gida" Tafawa ya tsaya cak yana kallon Sultan cikin ƙunar rai. Ƙaninsa yana ba shi umarni kuma dole ya bi.
*****
Wata kyakykywar matashiya ce ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune tana bawa jaririn Nono. A rikice ta ƙarasa da sauri tana faɗin "Sister kin farfaɗo Alhamdillah, Alhamdillah, Alhamdillah ala kulli halin. Barka da arziki sannu" Ta ƙarasa gaban gadon tana rungume Shukura.
Shukura ma ta rungume ta, tana faɗin "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"
Ta kalli Shukura ta ce "Babu komai, ni dai na gode wa Allah da ya sanya ki ka farfaɗo ki ka tashi. Sannu 'yar uwa" Ta sake maganar cikin iyayi da kulawa.
Ta kalli likktar da ta take ta ɗawainiya da Shukura, ta ce "Sannu da ƙoƙari doctor, Allah ya biya ki kema"
Doctor ta ce "Ba komai, yi wa kai ne."
"Yanzu kawo lambar wani a kira miki"
Shukura ta ɗan yi shiru sannan ta ce "To" Ta bayar da lambar Sagir, aka saka a wayar aka danna kiran wayar"
Shukura ta miƙa hannu, ta karɓi wayar.
Muryar Yusra ce ta yi mata sallama, ta tsuke fuska ta ce "Ina Baban Haidar"
Wata irin rikicewa Yusra ta yi, ta ce "Shukura ke ce? Ina ki ka tafi muke ta neman bamu ganki ba? Kina ina?"
Sai Shukura ta ɗan yi saroro, jin yadda Yusra ta rikice da murna.
"Ina nan, idan yana kusa ba shi wayar"
A rikice Yusra ta sake cewa "Baya nan, ki gaya mini kina ina na zo na ɗaukko ki?"
"A'a ina nan lafiya kalau, idan ya dawo ki haɗa ni da shi"
Yusra ta ce "Baya nan, layinsa ya saka a wayata, ni ban san lokacin da zai dawo ba, ki gaya mini kina ina?"
Kamar Shukura ta share ta katse wayar, sai kuma ta gaya mata. Tana can wani Asibitin kuɗi, a can wata local government a wajen Kano. Sannan ta ɗora da cewa "Amma kar ki gaya wa kowa mun yi waya da ke"
Yusra ta ce "Har mamanki? Tana can hankalinta a tashe fa ita ma"
"Eh har ita, kar ki gaya wa kowa, idan ya dawo ki haɗa ni da shi, ina Haidar? Yana lafiya?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido, cike da fargabar ko shi ma ya salwanta.
"Yana makaranta, to kina lafiya cikinki ma yana nan lafiya?"
Shukura ta ce "Eh, lafiya kalau"
"To dan Allah kar ki je ko ina daga nan gurin"
"Tom" Ta faɗa a taƙaice.
Matar ta kalli Shukura ta ce " 'Yar uwakki ce?"
Ta girgiza kai ta ce "Abokiyar zamana ce"
"Allah sarki, gaskiya daga ji tana sonki sosai ji yadda ta rikice" Shukura ta yi murmushi kawai. Sai dai ta tafi tunanin ta yadda za ta fuskanci Duniya ta sanar da cewa mahaifinta shi ke da alhakin sace ta, da salwantar mata da ɗa, da kuma mummunan zaluncin da ya yi wa mahaifiyarta da wadda yake tare da ita yanzu. Ita gaba ɗaya ma ba ta san ta ina zata fara bayanin miyagun ayyukansa a idon duniya ba a matsayinsa na mahaifinta.
****
Nana tana son ta ga Sarkin Baka, akwai maganganu da dama a bakinta, amma ƙiri-ƙiri Sayyid ya hana. Ga shi ba ta da damar fita idan ba umarnin hakan a ka ba ta ba, tana son sake ganin Nene ma amma babu halin fita.
Zaman Nana a guri ɗaya, ba fita daga ci sai sha da kwanciya, ya sanya ta ƙara yin kyau, ga lafiyayyen Abinci. Sai dai haryanzu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya ne ba ta da shi.
Tana zaune tana zancen zuci, har bacci ya fara sace ta, ta ji an taɓa ta. Ta tashi da sauri tana kallonsa.
"Har kin fara bacci ba ki jira ni ba?"
"Eh, na zata a gurinta zaka kwana ai"
"Idan ma na kwana a can ɗin, ai ke ki ka ja, kin daina damuwa da ni, ko tausayina ba kya ji"
Ta kwaɓe baki ta ce "Garin tausayinka, na kwashi wani cikin na haihu ku kaɗa ni Nigeria"
Ya ɗan marairaice murya ya ce "Haba Ma vie, Sayyid ɗinki ne fa, ke ba kya kewar ɗumin jikina ne"
Nana ta kalle shi ta ce "Wane ɗumin, ai yanzu jikinka ba wani ɗumi idan ba azaba ba"
Ya rausayar da kai ya ce "Da ɗin ma akwai, kuma kina jurewa"
Ta girgiza kai ta ce "Amma bai kai na nan ba"
"To ni ki bani Sanyin dan Allah"
Ta tsuke fuska ta ce "Sayyid ka daina taɓa ni dan Allah, ni ba ƙin ka nake yi ba, amma ka tausaya mini inga yadda al'amuran za su kaya tukuna, ka san dambarwar da ake ta yi haryanzu ni tsoro nake ji kar a yi mini yadda aka yi wa Nene"
Ya kwanta a gefenta ya numfasa ya ce "Ta baki labari kenan?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"In sha Allah a kanmu wannan muguwar al'adar za ta zama tarihi, dan ba zan yarda na rabu da rayuwata ba"
Nana ta zumɓura baki tana kallonsa, ya ce "Da gaske nake Ma vie" Ya yi maganar sumbatar hannunta.
Ta ɗan lumshe ido tana kallonsa. Ya ce "Tashi mu je"
"Ina?"
"Zo mu je ki gani mana, ko zan cinye ki ne" Ya yi maganar daga kwnace yana ci gaba da kallonta.
Ta tashi zaune tana faɗin "Na sani, ko cinye nin zaka yi. To ka tashi mana kuma ka kwanta"
Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga yana yi mata wannan kallon yana shafa bayanta.
Ta ce "Yane? Ko in kwanciyata ne?"
Ya ce "Allah sarki Hammad bawan Allah, kowa baya so na" Ya yi maganar yana tashi zaune.
Nana ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa gashinsa ta ce "To dama wa zai so rigimamme"
"Allah sarki, Ina kewar Ma vie ɗina ta da, mai so na da tausayina, ko motsi na yi hankalinta yana kai na, Allah sarki Asmyna ta Nigeria, soyayyarta ta daban ce a cikin zuciyata"
Nana ta ce "Allah sarki Sayyid ɗina na Nigeria, da baya ganin kowa a duniyarsa sai Asmynsa kaɗai. Mai kallona da idon tausayi, wanda nake iya gano ƙaunata da tausayina a idanunsa, mai yaba duk wani motsina da ƙoƙarina. Ina kewar Sayyid ɗina na Nigeria"
Ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Wannan Imam ɗin na Agadez fa?"
Ta kalle shi ta ce "To ga shi nan dai, ban ma san inda ya dosa ba" Ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki.
Ya yi dariya ya ce "Haka za ki ce ko? Ni ɗin ko? Sayyid ɗinki ne fa"
"Sayyid nawa, Hammad na Asal"
Ya ce "Wow, sake faɗar sunan na ji?" Ta noƙe masa kafaɗa.
Ya ce "Shikenan ma, dama Asal ta fiki iya faɗar sunan" Ta harare shi, tare da sauka daga kan gadon. Shi ma saukkowar ya yi, ya wuce gaba ta bi shi a baya. Daga bisani ya jira ta, suka tafi tare. Ƙofar nan da suke bi su fita hanyar saharar nan, suka shiga, sai dai wannan karon canza akalar hanya, zuwa wata matattakala. Tsoro ya fara kama Nana, amma ta kasa magana, sai rarraba ido kawai da take yi.
Wata ƙofa suka iso, ya ce "Kin san ina ne nan muka ɓullo?"
Ta ce "A'a"
"Gidan tarihi ne na masarautar Agadez"
Nana ta ce"Wannan dutsen da nake hangowa?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh nan ne"
Wani takurarren tsoho suka tarar a bakin ƙofar shiga gurin, yanayin ƙofar ya bayyanar da tsufan da ta yi a Duniya.
Tsohon ya miƙe jikinsa na rawa, ya risuna yana gaida Imam Hammad.
Hammad ya amsa cikin girmamawa. Nana ta ɗan tsaya ta yi shiru, tana nazarin ƙamshin turaren da ta ji a gurin, kamar ta taɓa jin sa a jikin wani, sai dai ba ta ga alamun a jikin wannan tsohon wannan ƙamshin yake tashi ba.
Ya buɗe musu ƙofar, suka shiga. Ya kunna makunni, sai ga hasken fitilun ya haske gurin.
Ya ci sunansa gidan tarihi, Nana ta faɗa a zuciyarta. Wani irin ƙaton guri ne mai kama da falo, da ƙofofi kashi-kashi a gurin.
"Wannan gurin kamar Libraryn Ƙaisar saboda tsufa" Ta ɗaga kai tana kallon tsawon gurin, jikin dutse ne aka rarake aka yi wannan ginin da ƙofofi. Kanta ne ya sara ta yi shiru tana tunanin kamar ta san gurin nan, ta taɓa ganin gurin. A take ta fara jiyo wannan ƙamshin da take ji idan ta gan su a wannan ɗakin tare da Sayyid.
Hammad ya kama hannunta ɗaya, ya buɗe ƙofa suka shiga, a take ta sske rikicewa, jikinta ya hau rawa ta kalle shi ta kalli ɗakin, ta sake kallonsa ta kalli ɗakin.
"Sayyid wannan ɗakin"
"Ɗakin da muke zuwa ko?" Ya yi maganar yana yi mata murmushi.
Ta kalli gadon, da mudubin ɗakin, komai irin na da sosai da sosai, sai dai yanayin kayan ya nuna, wanda suka yi amfani da ɗakin masu faɗa a ji ne. Ta dafe kanta da take jin wata irin ƙara a ciki, ga ƙamshin turaren nan ya cika ilahirin gurin.
"Sayyid wai ya aka yi haka ta faru a zahiri? Kar daga baya ka ce mini mafarki ne, ka fita da ni daga gurin nan kar na haukace Sayyid"
"Ba za ki haukace ba, ki tsaya na yi miki bayani"
Wani irin jiri ne ya din ga ɗibarta, ta din ga ganin wasu irin halittu na shawagi a ɗakin, ga hayaniya da suke yi cikin sauti mara daɗin ji.
Jikin Nana na tsuma ta ce "Ka fita da ni daga gurin nan, wasu abubuwa nake gani ka fita da ni"
"Babu wani abun tsoro fa a gurin nan, ki nutsu zan gaya miki komai daki-daki ciki har da abubuwan da suke shige miki duhu a kaina"
Ayshercool
08081012143
89
LITTAFIN KUƊI NE 1K 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
A hankali Nana take ƙoƙarin buɗe idanunta, zuciyarta cike da matsanancin tsoron, da rabon da ta ji makamancinsa har ta manta, tare da fatan Allah ya sanya ta farka daga wannan mafarkin mara kan gado. A hankali take jin numfashin sa na sauke a fuskarta. Ta buɗe idonta sosai ta sauke a kan fuskarsa da ya tsare ta da idanunsa, sai dai kan ta yi wani yinƙuri, ƙamshin ɗakin ya mamaye mata hanci, hakan ya sake tabattar mata da ba mafarki ba ne ba zahiri ne. Ta zabura da sauri ta gansu a kan gadon tare ita da shi a cikin ɗakin dai.
A gigice ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon cikin matsanancin tsoro, tana zazzaro masa ido. Sayyid ya riƙe ta ya ce "Dan Allah ki daina tsorata kanki, ki nutsu mana. Babu wani abin tsoro a gurin nan"
"Ta yaya zan nutsu, kana caza mini ƙwaƙwalwa, na ma rasa me yake faruwa, kuma sannan ka ce babu abin tsoro a gurin"
Ya ce "Zaki fahimci abin da yake faruwar, amma dole ki nutsu, kuma ki saurare ni" Ya ɗago yatsunsa ya kalli zobunan hannunsa, da space ɗin guda ɗayan sannan ya dubi Nana ya ce "Abubuwan da ki ke gani a tare da ni, su na da alaƙa da wannan zobunan na hannuna. Nana ta kalle shi ta kalli zobunan cikin rashin fahimta.
"Ina Zoben da na baki, mu na Nigeria?" Ba ta ba shi amsa ba, kawai ta hau ƙoƙarin tashi ta bar gurin.
Ya din ga kokowa da Nana, amma idonta ya rufe, hanya kawai take nema ta gudu ta bar gurin. Dan gani take idan ta ci gaba da zama zaucewa za ta yi.
Sai da ƙyar ya lallaɓa ta ya ce "To shikenan, mu je na mayar da ke mu tafi, tun da ba za ki nutsu ba" Ya riƙo hannunta, sai dai duk a tsorace take, su na fita daga wannan ɗakin ya shiga da ita wani ɗakin.
Gurin duk an yi wearing ɗin fitilu, sai dai da ya kunna fitilun gurin ya yi haske. Ta ƙara razana da ganin gurin. Komai na zamanin da ne sosai da sosai.
Wasu zane-zanen mutane ne a manyan frames a kafe, har zuwa kan wasu hotunan da suke dishi-dishi na Black and white na da, zuwa kan hotunan da ake iya gane mutanen jiki sosai wanda ya nuna na baya-baya ne hotunan sai hoton Sultan da ya fita fes. Ɗaya bangon Hoton Sultan ne shi ma, da hotunan Imam Imam na Agadez a jere.
Sai dai mutanen na jikin zanen da na hiton duk masu kyau ne, kuma yanayinsu ya nuna daga zuriya ɗaya suke.
Sai kuma gefe wasu ƙananan hotunan a wani ɓangare na ɗakin, da suke nuna yaƙe-yaƙe, da yanayi na zamanin bayi.
Hammad ya ce "Wannan hotunan da ki ke gani, tun daga kan na zanen nan, hotunan wasu daga cikin sarakunan da suka yi gwagwarmaya gurin kafa masarautar Agadez ne.
Waɗannan kuma, wasu daga cikin bayi ne, da suka yi wasu laifuka na rashin kyautawa, wanda tun daga zamanin har kawo yanzu, duk wanda aka haifa a zuriyarsu bawa ne, ciki har da wannan dattijon da yake gadin ƙofar gidan tarihi na Agadez. Idan ya mutu dole zuriyarsu za su bayar da wani wanda zai ci gaba da wannan aikin.
SHEKARUN DA SUKA GABATA.
Kamar yadda Nana ta fara karantawa, a cikin littafin Ƙaisar. An sha gwagwarmaya da yaƙe-yaƙe tsakanin 'yan uwa da suke ciki ɗaya domin samun damar ɗarewa karagar mulki. Kowane Sultan da ya zo karaga, akwai kalar mulkin da yake shimfiɗawa, wani al'ummarsa su samu sassauci, wasu kuma su shiga halin matsi. Sai dai hawa kan karagar ba shi ne aiki ba, ci gaba da ɗorewar mulkin, saboda a kowane lokaci ana iya samun masu kawo maka farmaki, a haɗa kai da na kusa da kai, a yi maka juyin mulki. Sannan tsugunno ba ta ƙarewa duk wanda ya zama Sultan ba, domin bayan kare kansa dole ya kare iyalinsa, idan ba haka ba 'ya'yansa tun da ƙuruciya za a yi ta kashe su, ana gwara kansu da kwaɗaita musu kwaɗayin mulki, ta yadda idan ba su kashe junansu ba, za su iya kawar da uban dan su hau karagar mulkin.
Ƙasar Agadez Allah ya albarkace ta zinari, wanda tun a wancan lokacin, shi ne babban dalilin da ya sanya kowa ke kwaɗayin ya hau mulki, aka yi ta yaƙe-yaƙe ana zubar da jini, tun da aka fuskanci zinaren abu ne mai matuƙar daraja a lokacin.
Suka ci gaba da gudanar da yaƙe-yaƙe su na mamayar mutane su kafa Daular su. Ana tafe da wannan mulki, wanda mai ƙarfi ya kan kifar da na kan mulkin ya ƙwata, ya kashe na kan karagar, har aka zo kan mulkin Sultan Azhar.
Zuwan Sulta Azhar ya sauya da yawa daga tarihin Agadez, kowane Sultan yana amfani da wani amintaccen boka, da yake yi masa ta'amalli da Aljanu, domin sanin abin da zai faru da ba shi wata kariya ta mussaman.
Sarki Azhar ya gagari