Showing 114001 words to 117000 words out of 124686 words

Chapter 39 - BUZU BOOK3 COMPLETE

23 Feb 2026

69

san Jamila zata faɗa ba zan yadda mu zo tare ba. Ki yi haƙuri ba zan ce sai kin yafe ba, amma kar ki ɗaga masa hankali, tashin hankalinki yake gudu ya sanya ya ɓoye miki. Kina kallo ya rasa ɗansa dalilin yar uwassa, abokinsa ya cutar da shi da mugun baƙin sihiri, kar ki ce za ki huce a kansa dan Allah"

Ayshercool
08081012143
Littafin kuɗi ne, a biya 1k via 0069685771 Aisha Adam stanbic

103

Fadila ta saki rigar Alhaji Fatuhu, ta koma da baya tana zubar da hawaye cikin matsanancin tashin hankali da damuwa.
Nana ta din ga yi mata nasiha mai shiga jiki tare da ba ta misali da kan kanta, irin faɗi tashin da ta din ga yi bayan auren ta.
A hankali kuma sai Fadila ta din ga samun nutsuwa, tana jin damuwar ta ta, ta ragu ta kaɗu sosai da sosai da jin irin iftila'i da Nana ta din ga faɗawa ita ma.
Alhaji Fatuhu ya ce "Sannu Nana"
Nana ta yi murmushi ta ce "Yanzu ga shi komai ya wuce, amma soyayyar da nake yi wa marigayi Muhsin, ta sanya bayan na haihu na sanya wa yarona Muhammad Muhsin, shi ma sunan shi Muhsin, zai yi sa'an wannan Muhsin ɗin" Ta yi maganar tana kallon Muhsin da ya kwanta a jikin Alhaji Fatuhu.
Fadila ta ce "Yanzu har sunan Muhsin ki ka saka wa yaronki?"
Nana ta ce "Ƙwarai kuwa, Allah shaida ne na so Muhsin yaron nan ya shiga raina nesa ba kusa ba. Bayan shi sai Haidar ɗin Shukura jikan Alhaji Zailani, gaba ɗaya zuciyata ta tsinke ina tsoron a ce shi ma wani abin ya faru da shi"

Alhaji Fatuhu ya ce "A'a yana nan cikin ƙoshin lafiya shi"

Nana ta sake cewa "Dan Allah Maman Muhsin ina sake baki haƙuri, kar ki ga laifin 'yar uwata tun da har ta nemi yafiyarki ta bayyana duk abin da ya faru ba tare da tsoron abin da zai biyo baya. Yadda aka bi aka saka ta a ƙungiyar asiri ba da saninta ba, kuma a garin ta ceci wannan Muhsin ɗin, ɗan Hajiya Sa'a ya rasa ransa kuma ita ma haryanzu fama take yi da rashin lafiya"

Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, dukkaninmu nan bamu wuce jarrabawa ba. Sai dai mun gode Allah, muna fatan ya zama kaffara a gare mu, domin ni jinya na sha, da sai da na din ga wari da raina, na yanke tsammani da rayuwa na rasa komai. Na ƙi yarda a yi mini maganin addini, ina tunanin ko na Asibiti ne. Wataƙila ma da Muhsin na amince an yi masa na addini da ko zai mutu zai samu afuwa.
Ni kaina mafarki na din ga yi da ke kina ce mini sihiri aka yi mini, na nemi magani na yi mafarkin nan ya fi a ƙirga sannan na yarda na fara neman maganin addini. Wallahi rasa ɗana Muhsin bai yi mini zafin yadda nake tausaya wa Shukura da Zailani ya salwantar da rayuwarsa domin wai ya ga bayana ba. Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Yayi maganar yana fashewa da kuka, saboda dauriya kawai yake yi, amma abin yana mugun cin sa. Ya kasa sakin jiki ko Allah ya isa ya yi wa Zailani da 'yar uwassa gani yake iya bala'i da masifar da suka jefa kansi ma, ta ishe su a wajen Allah ba sai ya ƙara musu da Allah ya isa ba.
Sai azahar su Nana suka bar gidan, sun yi hira sosai da Alhaji Fatuhu jin sa take yi kamar uba. Yake tsokanarta da zai din ga aika mata da kaya Niger tana sayarwa.
Daga gidan Alhaji Fatuhu gidan Ummi suka wuce, jikin Nana duk a matuƙar sanyaye, sai abu ya faru ta yi ta tunanin a ina ta san abin, a ina ta taɓa gani, sai ta nutsu sai ta tuna Ƙaisar ne ya nuna mata.
Ummi ta din ga yi wa su Nana masifar dan me za su zo da rana haka, bayan tun safe take saka ran ganinsu. Cikin jimami da damuwa, Nana ta kwashe komai ta gaya wa Ummi.
Ummi ta kaɗu ta tsure da jin labarin da Nana ta bata, sai dai sam bata bayyana mata, wai Jamila har ƙungiyar asiri ta shiga ba, ita ma Ummin bata nuna mata Baba ya gaya mata ba.
Ummi ta ce 'Ina ta saka ran ki zo mu sha hira, amma kin zo mini da abin tashin hankali.
Suka watsar da wannan hirar, suka shiga wata. Hira tayi hira har take ba wa Nana labarin Saleh yana gidan yari, saboda sayen kayan sata da suka yi na gwangwan an kulle shi a Lagos.
Ta tambaye ta su Barira, ta gaya mata auren Barira ya mutu, Sajida kuma tashi suka yi daga unguwar gaba ɗaya.
Ta gaya wa Nana cewar sau biyu Hammad yana aiko mata da kuɗi masu tsoka, ya ce ta ɗauki nata ta tura wa Uwani sauran.
Nana ta ce "Ni bai taɓa gaya mini ba ma, ha tsaraba kuma ya sake bani na kawo miki"
Ummi ta ce "Allah sarki, Nana kin sha wahala ashe dai Allah ya yi kina da rabon jin daɗi a duniya"
Nana ta ce "Ke dai bari, irin wanda ban taɓa tsammani ba. Amma wahalar da na sha sai da na yanke tsammani da samun afuwa. Sai kuma a hankali na lura da wani tsananin da na din ga shiga, shi ya din ga sadani da hanyoyin warwarewar matsalolin nawa. Na koma na din ga istigfari saboda na yi wa Ubangiji halin namu ɗan Adam, raki da kuma gaggawa Allah dai ya ƙara datar da mu" Jamila sai koma wa tayi gefe ta yi shiru, ba ta iya cewa komai.
Da suka koma gida bayan magariba, Baba ya yi ta faɗan Nana ga ga da aure, amma taje ta yi dare a waje.
Ta idar da sallar isha'i, tana ƙare wa ɗakinsu kallo, ɗakin da ta din ga shan azabar a Ƙaisar a cikin sa. Kawai ta tuna lokacin da ta ga bararoji na shan jinin Suwaiba. Ta kalli inda Suwaiban take, ta koma kamar wata mai shan inna, duk ta bushe ko abincin kirki ba ta ci, ƙwaƙwalwarta ta taɓu sosai da sosai.
Ba shiri ta tashi ta aika Nasiru, ya nemo mata tazargade.
Da kanta ta ɗauki Alqur'ani ta din ga karantawa tana busa wa a ruwa.
Ta idar ta ba wa Suwaiba, ta shashashfa mata ruwan a jikinta, ta rungume ta tana ci gaba da yi mata karatun Alqur'ani ƙasan zuciyarta ta din ga yi mata addu'a da fatan Allah ya yaye mata wannan ciwon.
Kullum sai Sayyid sun yi waya da Nana, aka fara processing yi mata passport, da kuma visa a Nigeria.
Kwanan Nana uku, sai ga Suwaiba na iya cin abinci, Jamila ma tana cewa yanzu tana iya bacci sosai, ba tare da ana tsorata ta ba. Nana ta yi mata nasiha sosai da sosai a kan kula da ibada da kuma yin addu'a.
Yaya Atine da kanta ta wanko ƙafa ta zo gidan, tana bala'in Nana ba ta je ta gidanta ba.
Da ta ga Nana ba ta kula ta ba, sai kuma ta hau kame-kame tana faɗin "Haba ta gidana, a ce kin zo takanas bayan tsawon shekaru ba kya nan a ce, kuma ba ki taka kin je inda nake ba? Babu faɗa me ya kawo gaba Nana?"
"To Yaya Atine kwata-kwata yaushe na zo garin, sai a hankali ai nake zagayawa amma kin zo kina ta faɗa"
Nasiru ya ce "Ke ma dai Yaya Atine da fitina ki ke, ya za a yi ki zo ki rufe basarakiya da faɗa haka, kin ma ci sa'a da ta kula ki. Nanan yanzu fa ba wadda ki ka sani da ba ce"
"Aikuwa na ga alama, maganar ma da kyar take yi, aishikenan"
Nana duk gidansu ta rasa wanda ya ke da lambar Sarkin baka, kowa sai ya ce mata ba shi da ita.
Nana ta kira lambar Sagir, kamar yadda ta karɓa a gurin Alhaji Fatuhu.
Bayan sun gaisa ta ce masa kwatancen gidansa take nema, za ta zo gurin Shukura. Ya kwatanta mata ta yi masa godiya ta kashe wayar.
Tana katse kiran, kiran Sayyid ya shigo wayarta.
Ta yi murmushi ta ɗaga ta ce "Masoyi"

Ya yi murmushi ya ce "Bayan kin tafi kin bar ni, kewa duk ta dame ni. Jina nake yi kamar maraya. Tabbas Nana ke rayuwata ce, ina roƙon Allah ya bamu jinkirin rayuwa mai amfani tare da ni da ke masoyiyya"

"Amin ya hayyu ya ƙayyum. Ni kaina duk da ina farincikin ganin yan uwana, amma ina kewarka kai da Yarimana"

Hammad ya kalli gefensa da larabci ya ce wa Muhsin "Zo ga Ammi, zo ka gaishe ta"

Muhsin ya matsa kusa da Hammad ya kalli screen ɗin wayar, ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce "Ammi ki dawo"

Jikinta ya yi sanyi ta ce "Haba yarimana, kar ka yi kuka ka ji, da wuri zan dawo ba zan iya jure ganin ka yi kuka ba" Ya jinjina mata kai.
"Wai zuwa ka yi ka ɗaukko shi?"

"Eh mana, karɓo shi na yi aro, muka taho gida, tun jiya ma yana gurina"

Kamar ta yi magana sai ta fasa. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki, ban kai mata ɗanki ba, amma dole zan kai shi ta gan shi, ko da kuwa ba ta ƙaunarsa, amma zan yi hakan ne idan ki na nan. Ki zama cikin shiri daga kowane lokaci wataƙila ta nan Nigeria za ki tafi Egypt mu haɗu a can"
"To ai saura kwana uku na taho"

"Eh, za a jinkirta tahowar ne, gara ki tafi ta Nigeria."

Nana ta ɗan langaɓar da kai ta ce "To ai ni ban san ya ake abubuwan ba, kuma idan na zo ina zan yi?"

Yayi dariya ya ce "Idan kin je ba ɓata za ki yi ba, ni zan je na taho da ke"

Sun daɗe su na waya, sannan ta ajiye ta shirya. Tun da Nana ta zo gidan nan abinci mai rai da lafiya ake ci sau ukun nan, kuma duk abin da aka girka har maƙwabta ake kaiwa. Mama ga shi tana cin arzikin nata amma baƙin ciki kamar ya yi ajalinta, da ba 'ya'yanta ne a wannan daular ba.
Gaddafi ma da yake ta shirin aure, shi ne yake kai komo gurin shirin tafiyar Nana Egypt.

Ta gama shirinta, suka fita da Jamila, Baba har mamaki yake yi yadda Nana ta shiga cikin su take rayuwarta, domin shi Jamila tsoro ma take ba shi. Ita kuwa Nana abubuwan tashin hankalin da ta gani a rayuwarta, ba ta ɗauki wata ƙungiyar asiri da Jamila ta shiga da Muhammad ba.
Su na ta sallama a falo babu kowa, can ƙasa-ƙasa suka ji an amsa. Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ya san muryar.
Yusra ce ta fito tana amsa sallamar. Tana ganin Nana ta ruɗe ta tafi ta rungume ta, "Ƙawata kece? Ina ki ka tafi ban sake ganinki ba, kowa na yi wa maganar ki, sai a ga kamar shirme nake faɗa".

Cikin mamaki Nana ta ce "Ƙawata me ki ke yi a gidan nan kuma?"

Cikin zaƙuwa ta ce "Ai Sagir ya dawo da ni tuntuni"

"Ma sha Allah, Alhamdillah ya gida ina Hajiya da Siyama?"
"Su na Abuja"

"Ƙawata kin canza kamanni, kin yi kyau kin ƙara ƙiba tubarkallah, ina mijinki buzun nan?"

"Yana Agadez. Ni gidan wata Shukura aka kwatanta mini kuma na zo na ganki"

"To ai ita ma gidanta ne, ba Maman Haidar ba? Mijinmu ɗaya bari na kirawo miki ita, ba ta da lafiya ne ma"

Ta juya ta nufi wata ƙofa, Nana ta din ga mamaki.

Jamila ta ce "Ita wannan ɗin a ina ki ka santa?"

"Gidan da muka yi gadi, a gidan suke"

Mintuna kusan goma sha biyar, sannan Yusra ta fito, rungume da jariri a hannunta, ga Haidar ya zama saurayi Sagir kuma ya riƙo Shukura tana takowa a hankali.

Nana ta miƙe tsaye, ganin Shukura ta rame sosai ta yi duhu, tana ganin Nana ta fashe da kuka. Cikin sanyin jiki Nana ta nufe ta tana "Faɗin Subhanallah"

"Nana kin gani ko? Ki ka ce mini mafarki ba gaskiya ba ne ba, ni ga shi ya zama gaske Daddy ne ya yi amfani da ɗana ya yi tsafi, Mummyna ta mutu, ya kashe Yusuf ya kashe mahaifiyarmu da babban yayanmu. Nana ban yi dacen uba ba"

Sagir ya ce "Shukura meye haka wai? Wannan ba sirrinki bane da yakamata ki ɓoye ba?"

"Babu abin da zan ɓoye, Nana ta riga ta san komai"

Nana ta rungume Shukura tana kuka ta ce "Kina nufin Yusuf da Hajiya Amina sun mutu? Tayaya mafarki ya zama gaske? Waye ya gaya miki da gaske ya bayar da jaririnki, ba gaskiya ba ne"

Tamkar za ta shiɗe ta ce "Wallahi gaskiya ne, shi ya gaya mini da bakins, bayan ya saka an sace ni, da niyyar ya sake kashe mini jaririna"

Jikin Nana ya yi wani irin sanyi, ta tuna Ƙaisar ya ce mata aljanu na iya nuna wa  mutum abu a mafarki saboda su haɗa faɗa. Sai dai ga shi abin ya tabatta. Ta rasa tausayin wa za ta fi ji ne? Fadila ko Shukura?
Haka nan ma ta din ga rarrashinta tana ba ta haƙuri, tana tuna yadda ita ma Alhaji Zailani ya sako ta a gaba. Yanzu duk daɗewarsa a duniya, duk tara kuɗin da burin tara arzikin ya tara ya tafi ya bar shi a banza, ga tonon asiri da mummunan ƙarshe, waɗanda ya bari da za su iya yi masa addu'a duk ya bar musu mummunan tabo a zukatansu, da babu lallai su iya yafe masa balle ya samu addu'a.

Ta kalli Haidar ta ce "Ka gane ni Haidar?"

Ya yi murmushi ya ce "Eh Anty Nana ce"

Sagir ya ce "Amma baka gaishe ta ba?"

Ajiyar zuciya da Shukura ta yi, ya sanya Nana mayar da hankalinta kanta, Nana ina ji a jikina nan kusa zan mutu nima, nauyin da ƙirjina yake yi mini da numfashi da nake yi da kyar, na san nima nawa ajalin ya zo. Ki zama shaida idan na mutu kar a ba wa kowa ɗana sai Yusra. Da fari na ɗauki mugun kishi na saka a raina, amma daga bisani abin da Yusra ta yi mini na alkhairi na tabattar da ba kowace kishiya ce kishiya ba, Yusra tana da kyawun zuciya"


AREWABOOKS



Cikin tashin hankali Yusra ta ce "Ka ga zata ci gaba ko?"

Sagir ya ce "Dan Allah Shukura ki daina maganar nan, kina ganin ba ta da cikakkiyar lafiya, tun da ba ta so ki daina dan Allah"

Nana ta matsa kusa da Yusra da tuni manyan idanunta suka tara hawaye, ta kalli jaririn hannunta, ta ce "Wannan naki ne?"

"Na Maman Haidar ne"

"Ma sha Allah"

Kawai Yausra ta miƙa wa Nana hannu tana murmushi. Nana ta kama hannun nata. A take ta ji jikinta ya yi sanyi.

"Haula" Ta furta a hankali.

"Ina yi miki barka da Gimbiyar Agadez, mai ɗauke da abin al'ajabi"

Nana ta ce "Haryanzu ba ki rabu da ita ba dama?"

"Ke kin sanmu akwai alƙawari, ina yi miki fatan alkhairi" Ta zare hannunta daga na Nana.
Nana ta dubi Sagir ta ce "Kana nema mata magani kuwa? Ko kaima ka fi yarda da ciwon Asibiti ne yake damunta?"

Ya ce "Haka suka ce mini a gidansu, Asibiti muke zuwa ganin likita"

Nana ta ce "Gaskiya yakamata a yi mata na islamic ma"

Nan ma Nana ta daɗe tare da su, sosai Shukura ta ji daɗin zuwan Nana, ita kanta Yusra ta ji daɗin zuwan nasu.
Nana ta yi wa Shukura alkhairi, suka yi musayar lambar waya, ta tashi suka tafi.

Daga gidan su Yusra, kasuwa suka je, Nana ta yi wa su Jamila sayayya sosai da sosai. Su na tafe a hanya Nana ta ce "Jamila, to kuma da gaske kin iya kasuwancin saye da sayarwar da Hajiya Sa'a take yi, ko kuma ba kasuwancin ku ke ba gaba ɗaya?"

Jamila ta ce "A'a tana kasuwancin, na iya"

"To jari nake son baki, ki je ki fara kema, na yi magana da Nasiru ma, da makaranta nake son ya koma, amma ya ce; shi gara na ba shi jari, zai fara sayar da omo da sabulai da ake yi a kasuwa. Dan Allah Jamila idan kin fara Allah ya sanya albarka, ki kula da iyayenmu. Kuma duk abin da ku ke buƙata muddin bai fi ƙarfina ba, ki yi mini waya tun da Alhamdillah inda nake babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Kuma na san ba wayona ko dabara ta ce, ta sanya Allah ya kai ni inda nake ba. Kuma Allah bai tsame ni ya yi mini wannan ni'imar dan ya fi sona ba. Kuma ina fatan a cikinmu Allah ya ƙara ɗaukaka wani, sama da inda nake ni a yanzu" Jamila har da kuka, tare da bawa Nana haƙurin abubuwan da babarsu da su suka yi mata a baya.

"Jamila, idan Allah ya yi wa mutum ni'ima, idan ya yi gaba ba ya waiwayen baya, idan ba alkhairi zai kalla ba, ki manta komai ya wuce kamar ba a yi ba".

Jamila ta yi ta nuna wa Mama kayan da Nana ta saya musu, da batun jarin da za ta bata, amma ta kwaɓe baki. Nana ba ta damu ba, ta yi wa Baba ɗinke-ɗinke.

Gaddafi ya shigo, ya ce "Nana, mun yi waya da mijinki, ya ce bai same ki ba. Ki shirya jibi in Allah ya kaimu, jirgin ƙarfe goma za ki bi, zuwa can Egypt ɗin"

Nana ta ce "Kai da wuri haka, na ɗauka za a kai irin kwanakin nan"

Gaddafi ya ce "To ai abin da yake naku ne manya, kuna da alfarma a ko ina, ga shi nan har an yi an gama"

Baba ne ya kalli yadda Mama ke yamutsa fuska, a hasale ya ce "Wallahi Rabi idan ba ki yi wasa ba, baƙin ciki ne zai kashe ki. Duk da abubuwan da ki ka din ga yi wa yarinyar nan, ga shi kina ta cin arzikinta da ke da 'ya'yanki, ba ta yi muku baƙin ciki ba, amma da ta motsa, ta yi wani abin alkhairi ko wani abin alkhairi ya same ta, sai ki kwaɓe baki ko ki kushe"

"Ni kar ka yi mini sharri, me na yi wa Nanan, Allah na tuba me Nana take da shi, da zan yi mata baƙin ciki?"

Baba ya ce "Eh batabda komai, sai abin da yake tukunyarki ki ke ci kika yatsins fuska saboda baƙin ciki"

Takaici ya ishi Nana, ta tashi ta bar gurin.

****
Nana tamkar idanunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login