Showing 60001 words to 63000 words out of 80390 words

Chapter 21 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

131

ni kuma ban shirya zubar da aji na ba. Don haka na wuce fuskata a d aure na fa da gidan su Asma. Ina jin zuciyata kamar ta fito don tsananin zafin kishi tabbas na yarda da gaske kishi masifa ne, don haka na sake damk e wa a raina ba ni ba gidan Ustaz Har abada. Da na koma gida Umma bata ce min komai ba ganin kaya na da gaske a hannu na.


Bayan kwana biyu. Sai ga Abba ya shigo gida a yammacin ranar hannunsa d auke da takarda ya same ni da Umma a kitchen ya mik a mata ta dubesa da sauri ta ce  Na menene?  Result d in genotype ne ya fito&  Hannun Umma na rawa ta fara bu de takardar& ..



5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA& .57.


NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.


Akwai a arewabooks masu nema dafa farko.

Wata irin fa duwar gaba ce ta same ni, fa duwar gabar da ta saka ni jin matsanancin ciwon kai. Na kasa gane a wani mahalli zan saka abinda Abba ya ce. Tashin hankalina bai sake yawaita ba sai da Naga Ustaz ya zato jotter da biro da alama cika umarnin Abb? zai yi. Tsaf na daina fahimtar abinda ake cewa Amma miskilancina ya kasa bari na na  d ago na ce wa Abba na janye buk ata ta. Ina kallon Ustaz kuma ya yi rubutun fuskarsa d auke da wani yanayi da na rasa mahallin da zan ajiye shi farin ciki ko bak in ciki. Ya mik awa Abba takardar yana furta  Ku taya ni murna y an uwa da karamcin Abba ba abinda zan sakawa da Abba da shi sai addu a. Abinda ya yi AYSHA Ai shi ya yi Humaira kamanninsu guda ba wani banbanci na gode sosai. Abba ya ce  Bakomai Ahmadu, ka cancanci fiye da haka, sam ba zan so na rasa ka cikin zuri ata ba. Allah ya yi muku albarka.


Tamkar wani magana disu haka idanuna suka game da idon Ustaz kawai sai naga ya d aga min hannu ya saki murmushinsa mai kyau. Da alama manufarsa sai wata rana. Zuciyata ta buga da k arfin gaske wannan shi ake kira da yiwa kai Me na janyowa Kaina Ni AYSHA? Ina miskilanci na ya kai ni yau?


Jikina a salub e na mik e Har jiri nake ji na shige gida zuciyata na harbawa da saurin gaske. Zuciyata a cunkushe da tunani ina tunanin tabbas wata mak ark ashiya Ustaz ya shirya min. Wato yaga Humaira ta fi ni wayewa ta fini faran fatan shine dalilin juya a kalar soyayyata zuwa tata. Sam bana ganin laifin abinda na aikata ni balle na hango kuskurena. Don kuwa ko sonsa zai kashe ni sai dai ya kasheni don ba zan tab a nuna masa na damu koda hakan zai zama Ajali na tabbas miskilanci bai yi ba. Wani irin yawu na ha diye mai kaurin gaske, sai a sannan hawaye suka shiga suntiri a k uncina. Na fara kamar jin haushin Humaira da tsanarta a zuciyata tamkar laifinta ne, tamkar ita ce ta ce tana son sa. Kowa ma na gidan haushinsa nake ji tuni dama na yarda Umma tafi son Humaira a kaina don yanzu janta da take a jiki na bata ja na. Ni kam ai na yi rashin mai k aunata Mami na. Na zaro waya da sauri don kiran Mamin nawa amma still wayarta not reachable hakan yasa na mayar da alamar kiran nawa zuwa MamanK ta. Ta d aga muka gaisa na tambayeta Mamin nan take sanar da ni ta wuce England karatu kwana biyu da suka shige Amma zata turo min numberr da ake samunta ta can. Jiki na a salub e na kashe wayar ina goge zufar da na ji tana tsatstsafo min a goshi na. Ashe wancan lokacin ban ga komai ba yanzu ne NA GA RAYUWA NI AYSHA. Har dare ban fito ba haka na kwanta da yunwa ruwan tea kawai na sha. Ba Wanda ya nemeni har Umman.


Da Humaira da Khadija da Maryam muke kwana d aki d aya wani lokacin Humaira ta gudu d akin Umma. Su kuma sauran biyar d in suna d akinsu da yake b angaren Mami.

Har asuba ranar ban yi wani barcin kirki ba, ina salloli. Shi yasa da barcin ya d auke ni y a d aukeni da k arfin gaske. Hayaniyar su ce ta farkar da ni daga nauyayyan barci kaina na ji ya sar? ganin yarda suke ta hayaniya suna shiryawa. A tsawace na ce  Malamai kun dameni fa, kun hanani barci.

Humaira da tsallenta ta dir? saman gadon tana jan bargon. Cikin masifa na ce mata  Ke meye haka? Langab r kai ta yi. Kafin ta furta  Sissy, kin manta da batun zuwa potiskum d in, ki shirya kada Su Yaya su tafi su barki ni a motar Ustazu na zan tafi. Wani kallo nake mata ina jin kamar na k unduma mata zagi wato da iskanci ma da sunan da nake kiransa take kiransa. Sai dai na ha diye ina jan tsaki na ce  ku je kawai, ni ba zan je ba. Bata ce komai ba ta fice daga d akin. Tsawon lokaci sai gata Sun dawo da Umma. Umma ta kira suna na ni kuwa na yi shiru kamar mai barci. Sai na ji ta ce  Humaira mu je barcin ne a kanta. Sa zauna da masu aiki. Na bi bayan Umma da suke ficewa daga d akin da kallo. Wato abinda na lura da shi sam Umma bata damu da ni ba balle ta tambayeni damuwata. Na datse leb ena ina jin raunin zuciyata na sake rub anya.


Na mik e a hankali na shiga toilet wanka na yi sosai kafin na fito na hau shafe shafe a jikina. Abinda ban cika yi ba yau nice har da kwalliya ba don komai ba sai don na burge Ustaz, don ban ban sani ba ko kwalliyar SHANY tana daga abinda yake janye hankalin Ustaz d in.

Na shirya cikin black abaya mai masifar kyau kalar kuma ta amsheni sosai kalar light pink da adon black stones a jikinta. Ni kaina na San na yi kyau ba d an ka dan ba. Fuskata kuwa sanye nake da wani black shade da ya sake fito da kwalliyar tawa. Ni kaina sai da na sake duban kaina a mudubi kafin na saki murmushi don na San ba Ustaz ba duk Wanda ya ganni sai ya yi mamakin kwalliyar da na zauna na rincab a.



Ina fita kuwa suka zuba min ido suna furta Wow Ma sha Allah. Na d an d aiuke kaina bakina nake d an motsawa ina tauna chewingum d in da yake cikinsa.



Motar Ya.Usman na bi, don ko da wasa nan nufi motar Ustaz ba. Jan aji da shan k amshi na ba zai bar ni na aikata hakan ba. Shima ina kallo sau  d aya ya kalleni bai sake ba, Ya tattara dukkan nutsuwarsa ya mayar kan Humaira da take ta masa surutu da dariya shima kuma ina kallon yana mayar mata da murmushin kamar dama jira yake.


Na shiga Motar Ya Usman zuciyata na min wani irin nauyi, don har sai da na sauke ajiyar zuciya a hankali. Yaya Usman ya juyo yana kallona bayan ya tada motar ya ce  Yaya dai AYSHA? Na girgiza kai na ce bakomai. Ina bayan motarsa matarsa kuma a gaba haka muka yi tafiyar. Ina ji jefi jefi suna hirarsu wani zubin su sako ni. Sai dai bana tofa musu na yi shiru kawai saboda tunanin da y a cika min zuciyata ba zai bar ni na yi walwalar da zan amsa musu ba.


Har muka isa potiskum ban sani ba ni dai ina zaune jigum cikin mota duka tunani na yana kan motar Ustaz da duk sanda muka zo wuce su sai na hango fuskarsa da ta Humaira fal farin ciki da walwala. Bayan motarsa kuwa Yaya Muhammad ne da Anty Khadija da ta kafe sai tazo duk da tsohon cikin da take da shi. Mune farkon isa potiskum d in don haka Hajiya da murna da karsashi ta tare mu. Ta dafa ni ta ce  Kaga Baiwar Allah, tun d azu nake zuba idon ganinku ina y ar Uwar taki? Kafin ta rufe baki Humaira da su Umma suka shigo. Hajiya ta bu de baki cike da mamaki tana furta  Hukumullahi La ajabun& . Ikon rabbi ya shige misali wannan kam ko a hanya na ha du da ita zan k walla mata kira da sunan Ayshatu. Ki ga kama ba banbanci ko ka dan&  Umma tana dariya ta ce  Aa fa Yakumbo akwai banbanci na  dabi a a tattare da su, Humaira akwai d an banzan rawar kai, da yawan surutu Aysha kuwa miskila ce ta bugawa a jarida. Ina ji duka wajen suka shiga furta tabbas. Na d ago ina kallon Ustaz da sam bai tofa ba yana ta danna wayarsa. Ya Muhammad ya ce  Wallahi gaskiyarki Umma, Humaira akwai sakewa da jama a Aysha kuwa akwai nurk ifanci. Na turo baki na cikin jin haushi ina kallon Abba da yake murmushi shima ya ce  Humaira kam ba dama surutu fa kamar aku. Ai kuwa Humaira ta fara turo baki tana shirin saka kuka, Yaya Faruk y a kama hannunta yana furta  Common my friend, kada kiyi asarar hawayenki a banza, ai gwanda mai irin halinki Sun fi da din zama. Me za a yi da mutum mai k unbiya k unbiya. Na kuwa zuba masa harara don na San wannan maganar kansa tsaye da ni yake.


Kwana guda muka yi a potiskum muka yi sallama da Hajiya da niyyar ana fara shirye shiryen biki zata taho.


Kwana biyu da dawowarmu kuwa aka fara hada hadar saka rana. Wani abu da Abba ya yi ya burgeni ha da su Yaya Muhammad su biyar da biyar daga cikin y an matan nan. Masu mata ya k ara musu d ai daya marasa mata kuma ta basu auren d aid aya daga cikinsu. Yaya Ali ne kawai aka ce ya yi k ank anta da aure don haka sauran biyun Malaman mu suka nemi aurensu Abba kuma ya amince da su ya basu auren don haka duka yau za a saka ranar biki ciki kuwa har da na Humaira da Ahmad Ustazu na.


Ranar kam Allah ne ka dai ya san yanayin da zuciyata take ciki. Duk da k wayar idanuna ta kasa b oye nakasar da zuciyata take ciki.

Y an saka ranar da suka zo Har da y an gidansu Ahmad su Khadija da Aunty Doctor Khadija ta saka ni a d aki tana tuhumata me yasa na k i amincewa komawa gidan Ahmad? Suka ji labarin da k anwata kuma za a yi auren. Na bita da kallo ina sakin ajiyar zuciya kafin na ce  K addara ce! Duk abinda ta ce kuma na kasa bata amsa Har ta gaji ta yi shiru.


Zo kuga lefen Humaira, akwatina goma sha biyu har da na saka rana. Akwatina ne manya kuma masu masifar kyau. Kaya ne damk ar a cikinsu masu masifar kyau da tsada. Kai daga gani ka San dukiya ta yi kuka. Wata uku aka saka cif. Humaira sai rawar kai take ita ko kunyata bata ji. Wannan iyayi da take shine abinda yake sake dugunzuma zuciyata. Hakan yasa na shige d aki na fasa kuka mai tsima zuciya. A wannan daren kam cire duk wani girman kai da miskilanci na na yi na d au waya na danna numberr Ustaz, yarda wayar take bugu haka k irjina yake bugu sosai na tashin hankali tsawon lokaci kafin ta d aga wayar& & . Cikin k arfin hali na furta  Hello Ustazu na& .





5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA& ..58.



NAZEEFAH SABO NASHE&
'?

08033748387.







Na fa da a hankali cikin muryar nutsuwa. Shiru ya yi kafin daga can gefen ya ce  Humaira me yasa kika d aukar wa AYSHA waya? Wani takaici ne da zafin k irji na ji yana shirin babbaka zuciyata wato ya zata Humaira ce. Na cije leb ena kafin na yi k asa da wayar jin yana cewa  Maza Humy mayar mata da wayarta zan shigo da safe na ji damuwarki yanzu Am with my wife&  k it na kashe wayar tafarfasa kawai zuciya ta take yi. Ban san me yasa na kasa hak ura da Ustaz ba, alhali yanzu ta bayyana k arara ba so na yake ba. Hankalinsa da tunaninsa kacokam yana kan Humaira. Ranar kam da ky ar na samu na yi barci.


Da safe kuwa ban fita daga d akin ba. Maryama ta shigo tana kallona ta ce  Sis AYSHA Abba yana kira. Kai kawai na d aga mata kafin na mik e na zira hijab d ina na fice zuwa amsa kiran Abba.

Ina saka kai gaba na na wani irin bugawa da k arfin gaske ganin Abba ne da kafatalin y an uwansa da alama wannan meeting d in duk nawa ne. Kai Ni AYSHA na ga rayuwa. Cikin rawar murya da kasalar jiki da na zuciya na shiga babban parlorn kai na a k asa. Fuskarsu sam ba annuri suke kallo na. A takure nake sosai musamman irin kallon da suke min mai sanya rashin nutsuwa ko ka dan.

Bayan Sun amsa gaisuwata Usual murya a cunkushe sai kuma Baba Yahya ya gyara zama yana furta  Ke wannan zaman naki ne, saboda wata magana da muka ji wai zaki jingine maganar aure ki tafi wata uwa duniya karatu, haka ne? Na d aga kai a hankali ya gyara zamansa ya ce  To baki isa ba, kin yi ka dan mu dai a zuri armu kaf ba wata mace da zamu bari ta tafi karatu waje. Don haka ki bu de kunne da kyau mu gaya Miki da zarar kin gama idda zaki fitar da miji mu Miki aure tunda ke kin kafe ba zaki koma gidan mijinki ba, har ta kai ga rabuwa an Maye masa gurbin ki da y ar uwarki to hakan ba zai baki lasisin da zaki zauna ki mik e k afa ba. K asa furta komai na yi sai ruwan hawaye da yake ambaliya a fuskata. A haka suka sallame ni na mik e jikina har rawa yake na tafi cikin d aki na. Zuciyata na ke furta na shiga uku, na jawowa kai na masifa me ya kai ni furta bana son Ustaz na San halin su Baba yahya da kafaffiyar zuciya. Tunda suka furta sai na fitar da Miji abu ne mawuyaci su janye furucinsu.


Kaina ya yi dum, sakamakon rasa mafita da na yi, a lokacin kam na San tabbas na yi rashin uwa Mami na da ta nan da na San ba zata bari a k wace min Miji a bawa Humaira ba. Ita kuwa Umma murna ma take don k iri da muzu ina jinta ranar tana gayawa K anwarta ita hankalinta ma zai fi kwanciya Humaira ta auri Ustaz ta San zai kula da ita da tarbiyyarta ma.


Na runtse idona hawaye na zuba kamar da bakin k warya a idona. Numberr Mami na shiga latsawa ta can k asa da Hajiya Mama ta bani. Cikin sa a na samu Mami na, tana d agawa na fashe mata da kuka ina furta  Mami na shiga wani hali, Na ga rayuwa Mami na wai Humaira za a aurawa Ustazu na&   What? Saboda Uban me? Na ji Mami ta furta cikin muryar da ta bayyana tashin hankalinta. Na lumshe ido ina gaya mata duk abinda ya wakana. Sai na ji ta saki ajiyar zuciya ta ce  Ke ma AYSHA kin yi wauta, a wannan zamanin ta ya zaki furta hakan? Ustaz fa maza ne masu tsada da sai mace mai muguwar sa a take samunsu. Ko da da kika ga ina Adawa da aurenki da Ustaz don bani da wani burin da ya wuce naga kin yi karatu ne. Amma na San ta ko ina Ahamad ba shi da makusa. Yanzu wannan nurkufancin naki zaki cire ki samu Umma ki gaya mata kina son mijinki zaki koma gidansa ita sai ta samu Abba ta gaya masa amma idan kika ce zaki shiru kina ji kina gani zaki rasa Ahamad Humairan ta aure shi&  na d aga kai zuciyata ta amince da shawarar Mami na. Na mik e da sauri na nufi d akin umma. Ita da Humaira ne a zaune Humairan sai sangarta take mata. Kayan kitchen ne a gaban su suna ta warewa. ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Jikina a sanyaye na shiga na zauna a gefen gadon, ina nazarin fuskokinsu da suke
cike fal da walwala da alama koma zancen me suke suna cike da nisha di.


Umma ta d an kalle ni tana furta  Ayshatun Mami ya aka yi ne? Akwai matsala? Na d aga kai kawai ina wasa da yatsu na na ce  Ina son magana da ke Umma. Umma ta d an dubeni tana duban d akin kuma sai ta ce  Yi maganar ki mana, ai ba kowa ni da y ar uwarki ne kawai kuma bai kamata ace kina b oye mata abinda ke ranki ba, duk duniya baki da makwafinta. Na d ago ina kallon Humaira da itama take kallona tana sakin murmushi a hankali. Sai kuma Naga ta mik e ta yi pecking d ina a kumatu ta ce  Feel free Sis ki gayawa Umma matsalarki she is ur mother baki da misalinta, bari na baku guri. Bata jira cewar Umma ba ta fice da sauri. Na saki ajiyar zuciya ina kallon Umma da ta kafa min ido.  Ina jin Ki Shatun Mami, me ya faru?
Na yi k asa da kaina cikin rawar murya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login