Showing 9001 words to 12000 words out of 80390 words

Chapter 4 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

144

saki baki, don ban san dalilin kalamin nata ba. Ta yi dariya ganin kamar na d an firgita ta ce  Eh mana, yanzu yaushe k afafunki su taka gida na? Tun ranar da Ustaz ya je ya d auke Matarsa&  wani irin runtse ido na yi jin abinda ta ce. Sai naga ita ma ta dafa kanta ta furta  Oh Am Sorry Sisi, ni kai na bana son ambaton sunan mutumin can wallahi na tsane shi shi kuma Yayanku ya kafe ba laifinsa ba ne, ko shine a shoe d insa abinda zai aikata kenan, yanzu dai ba wannan ba, yaushe za ki kawo min ziyara? Ajiyar zuciya na saki, don kam ta famo min wani miki a zuciyata. Ranar d aurin aure na da Ustaz ya je gidan Ya. Muhammad da duk abinda ya faru. Na lumshe idona kafin na bu de su na ce  Zan zo duk ranar da Umma ta yarda. Tana dariya ta ce  Ai kuwa yau zan tambayi Umma ta barki ki je, ko kya huta don na ga duk kin rame kamar ba Ayshatu y ar Gaye ba. Ta kira ni da sunan da Brothers d ina suke kira na. Na d an yi murmushi kawai jin abinda ta ce. A zuciyata kuwa addu a nake Allah yasa Umma ta bar ni na je gidan Anty Khadija don macece mai karamci kuma ina sonta sosai.  Idan mun dawo d aga kai lefe kawai sai mu yi tafiyar mu, In sha Allah zuk eken mijinki na hanya wanda zai so ki da dukkan aibunki&  cikin mamaki nake kallonta na ce  Lefen wa za a kai yau d in? Wani kallo take min ta ce  Baki san za a kai lefen Umar da Usman ba yau? Wasu k walla na ji sun zubo min kawai na girgiza mata kai ina sunkuyar da kai na. Jikinta a sanyaye ta dafa ni, sai naga ta kasa magana ta cije leb enta kawai ta shige parlorn Umman. Na runtse idona ina jin sautin zuciyata yana tashi daga normal zuwa wani irin bugu da ya dinga ba ni tsoro. Ba komai nake tsoro ba sai bana son ciwon zuciya ya kama ni. Tunani nake shi ma Ya.Usi ya daina ta tawa kenan shi yasa har aurensa zai zo bai gaya min ba. Tsabar ciwo da kaina yake da rawa da jikina yake da k yar na samu na gama wankin na mik e na shige d akin da nake ina fasa wani irin kuka mai saka k unci da ciwo a zuciya.


Kafin yamma kuwa gidan mu ya cika taf da mutane. Ina daga cikin d aki ina jiyo hayaniyarsu sai dai ko da wasa ban yi gangancin shiga cikinsu ba. Na yi zama na a d aki. Idona a lumshe don ko waya bani da ita tunda abin ya faru Abba ya saka Ya.Muhd ya k wace wayar. Ji na yi an turo k ofar d akin da nake. Anty Khadija ce a tsaye tana kallona tana bin d akin da kallo kuma duk a lokaci guda. Ta ce  Ke ba zaki fito ba ne AYSHA? Ki shirya a tafi ganin lefen da ke, wai ma me ki ke yi a store? Wani malalacin murmushi na saki kafin na ce  Ba store ba ne, yanzu nan ne d aki na Anty Khady. Sai naga ta waro ido ta furta  Ah haba wasa ki ke, sai kace wacce ta yi kisan kai? Ta d an shigo tana sake k arewa d akin kallo. Ina kallon yarda take dakiya tana k ok arin kada k wallar da take idonta ta zubo.  Tashi mu je, dole yau idan mutane suka watse zan yi wa Umma maganar ta bar ki koma gida na. Dama Arfa ta fara isata da saka magana ga shi kwanannan laulayi ya saka ni a gaba. (Arfa yarinyar su ce da suka haifa na manta ban gaya muku ba.) girgiza kaina na yi na ce  Ku je kawai Anty ba inda za ni bana son shiga mutane. Tana shirin sake magana aka turo k ofar d akin. Zinatu da Zaituna suna tafe suna wata irin shewa. Ina ganin su na mik e zumbur daga tabarmar da nake kwance. Idanun su cikin nawa ba su yi magana ba har sai da suka gaishe da Anty Khady ta fice daga d akin tukunna sannan suka juyo waje na. Zannira y ar Umma Dije k anwar Abba da yake bin sa. Ita kuma Zinatu y ar k anwar Umma ce Umma Sa a. Da yake na gaya muku Abba da Umma first cousins ne auren zumunci aka musu. Sarai na san Zinatu da Zaituna basu da mutunci k warai da gaske kuma a kansu Abba yake fa da da iyayensu don kamar yarda ba su da kunya suma iyayensu ba kunyar ce da su ba. Inna ta sha fa da min an sha fama da iyayensu suna y an mata har sai da aka aurar da su ba shiri, sai ga shi sun haifo kwafinsu tsaf ko a ce wanda suka fi su. Ba sa wani zuwa gidan mu amma lokacin bikina suka zo suka tare a gidan sun doshi kwana goma da su aka yi komai a bikin. Duk da ban wani saba da su ba, Abba ya k i bari na na saba da su don baya sake musu fuska.


Da murmushi na tare su, sai dai ga mamaki na sai naga sun wani zuba min harara suna min kallon banza. Zannira ta turo baki tana furta  Oh! Ikon Allah sai kuma ga karuwa a gidan Ashsheikh Imamu, waliyyin Allah! Da sauri na waro ido ina kallon su, jin wulak ancin da suka shirya yi min. Suka tuntsire da dariya Zinatu ta ce  Gane min hanya Zannira, yanzu kuma ban san ya zai yi ba? Mutum duk ya bi ya takura mana akan d an shan Mintin da muke da samari, sai ga shi y arsa tana abinda ya ci Uwar na mu, zigidir a kan cinyar saurayi da kayan maye, kai wannan abu ya yi min sugar na so na ga Idon Shehi Imamu ranar& . Wani irin kukan kura na yi na maku reta da k arfin gaske ina haki ina huci idona duk sun ka da sun yi jajur, tun Zinnira na ganin kamar zata iya k waceta ba tare da kowa ya ji ba har taga abin ya gagareta da sauri ta fita tana ihun a kawo d auki jama a AYSHA zata kashe Zinatu. Duk wasu jama j da suke gidan suka yi yo dandazo zuwa d aki na. Sai dai na k i sakin Zinatu, ranar kam kamar an k ara min k arfi. A mak ure nake da ita ina mata wani irin kallo. Anty Khadija na ji ta ja ni jikinta hakan yasa na kwanta lamo a jikin nata ina sakin wani irin kuka cikin kukan na bata labarin abinda ya faru& na kuma lumshe idona na ce  Anty a yanzu bayan Mami su ne mutane na biyu da nake zargi akan wancan vedion, ai ba k arya na ne kowa yana fa da ina kama da Zannira sosai da sosai jikin mu farcen mu duka iri guda ne, fuskar ce dai nake tunanin tawa suka saka a gangar jikin Zanniran! Tsit na ji mutanen d akin sun yi idanu kuma suka koma kan Zannira da cikin wani irin razani take ware ido tana pointing d ina da yatsunta& .




JIKAR NASHE&
'?
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA 30..


NAZEEFAH SABO NASHE&
'?



Ki tashi mu tafi na ce miki Aysha! Ya.Usman ya fa da cikin muryar da ke bayyana fushinsa. Girgiza kaina nayi na ce  Ya Usman ka bar shi ba zasu fahimceka ba suma a potiskum d in, ka bar shi na yarda da k addara zan Jure, zan auri Tanimu.  Ba zaki jure ba AYSHA, hauka ake za ki auri Tanimu, ki tashi mu tafi na ce. Hawaye ne suka zubo min na ce  Ya.Usman, Umma fa? Baka ganin ranta zai b aci kuma zata yi fa da. Fuskarsa a tsuke sosai ya finciki hannuna da kansa ya zura min Hijabin ya ja hannuna muka fice da sauri. Motar gidan mu da Driver yake ja ita Yaya Usman ya tura ni a ciki. Ya tayar da ita da sauri muka bar gidan cikin wani irin mugun speed. Ni dai lumshe idona kawai na yi saboda sam raina babu da di.


Har muka isa garin kuma magana jefi-jefi muke yi, duk da tafiya ce muka yi ta bata wasa ba. A cikin gidan kuwa Inna da fara a ta tare mu, ta saka aka kawo mana abinci da ruwan sha da zob o masu sanyi. Kasancewar daga ni har Yaya Usman ba mu karya ba hakan yasa muka ci abincin sosai. Da alamu Inna ta fahimci rashin nutsuwa a tattare da mu, don haka bata mana magana ba har sai da muka ci abincin muka yi sallah kuma. Sannan ta ja ajiyar zuciya tana kallon Yaya Usman ta ce  D an fodiyo tafiyar lafiya kuwa kuka yi na gan ku ficikai ficikai. Ba nutsuwa sam a tare da ku. Yaya Usman, ya kalleta ransa a b ace ya furta  Ba lafiya ba Inna, haka kawai k alau kin san ba zan yi yo wannan doguwar tafiyar ba. Ta girgiza kai ta ce  k warai kuwa, da dai Muhammadu ne shine bawan Allah mai son zumunci, sai ka gaya min me yake tafe da kai? Ya sake tsuke fuska ya ce  Yanzu Inna abinda ake wa AYSHA ya dace akan laifin da ba a tabbatar ta aikata ba, kada fa nan gaba a zo ana jin kunyar yarinyar nan.. Inna ta  dago kai tana kallonsa  Duk na yi wannan tunanin bayan dawowata Usmanu, kuma ina shirin na koma a wannan satin na ce a je can gidan su Fatiman. Rok eta Allah da annabi a ji da gaske yarinyar nan ta san tana aikata ba dala kamar yarda Kakanku ya ce min, sai kuma ga ku kun zo yanzu me ya faru kuma? Usman ya ce  Wai aure Abba zai mata, auren ma na son k ask anta ta wai da Tanimu Driver&  Inna ta ce  Cabd i jam! To lamarin Imamu kuma sai du ai, ta ina wannan abin yazo masa fisabilillah kamar muna garin mahaukata, to ba da ni zaa yi haka ba tozarcin Ai ya yi yawa. Zata yi aure dai amma ba da Tanimu ba da kai na zan samar mata Mijin aure dama can abin yana raina, na ce ko da yaron nan, Alhaji da kansa ma ya yi sha awar hakan da Miftahu za a ha data aure Jikan Mariya k anwata yana da halinsa kuma zai iya rik eta In sha Allah, na san zai rufa mana asiri.. Yaya Usman ya saki ajiyar zuciya yana furta  Wannan kuwa, In dai Muftahu ne ai sam ba shi da aibu, Allah ya tabbatar mana da alheri, amma don baki ga gallaza war da ake mata a gidna can ba kamar wacce ta yi kisan kai. Inna ta tsuke fuska ta ce  Kayya, amma Kubra akwai ragowar Imani kuwa a tattare da ita? Sai ka ce ba ita ta haifi y ar ba, ai shikkenan sai ta yi zamanta anan har lokacin aurenta ta yi aurenta su tafi can lagos da Miftahun. Yaya Usman ya kalleni sai na sakar masa murmushi don har a zuciyata na amince da auren Miftahun, don ba laifi kyakykyawa ne Fulani Usuli kuma d an gayu ne ya yi bokonsa daidai gwargwado. Shigowar Alhaji kakanmu ce tasa aka yi shiru a d akin. Da mamaki yake kallo na ya ce  Tsohuwa ke ce yau a gidan? Murmushi na saki ina gaishe shi ya yi dariya ya furta  Shikkenan amaryata ta zo bari a bu de miki naki d akin ki shiga.. Jan mu ya dinga yi da wasa har na mance kaso hamsin na b acin raina sai b abbaka dariya nake. Tsaf Inna ta gaya masa duk abinda yake tafe da mu. Sai naga ya yi dariya ya ce  Imamu kenan, wato masifaffiyar zuciyarsa tun ta yarinta har yanzu yana nan yana fama da ita, ban da abinsa wa yake tsallake k addararsa idan ma ta aikata d in ta dawo ta tuba Ai sai a yafe mata, Allah Ai gafururrahimu ne. Dama ko baku zo ba ni na yi niyyar kiran Imamun na gaya masa a k arshen watan nan za a d aura mata aure da Miftahu jikan Mariya, tunda kuwa kun zo sai ka barta anan su fahimci juna da Miftahun kai koma. Usman ya mik e yana duban agogo ya ce  Ai yanzu ma zan juya, don baa san mun taho ba. Suka yi sallama nima na raka shi har mota ina jin kamar na yi hawaye don tafiyar da zai yi. Ya girgiza min kai murya a hankali ya ce Be a good girl AYSHA, In sha Allah k arshen matsalarki ne. Na lumshe idona ina cije leb ena ka dan na d aga masa kai ya saka hannu ya share min hawaye na sannan ya dank a min ku di masu d an yawa a hannuna ya shiga mota yana d aga min hannu. Jikina a salub e na koma gidan. Sai dai yarda Alhaji ya tasa ni a gaba da hira da abubuwan ban dariya yasa na wartsake na shiga amsa masa.


Ina wajen Alhaji ya kira Abba ya fara yi masa fa din kan hukuncin da yaso yankewa ba tare da neman shawara ba. Abba dai shiru ya yi sai da Alhajin ya gama fa da sannan ya ce  ka yi hak uri Alhaji, hankalina ne duk a tashe game da lamarin yarinyar nan ta kai har bana son shiga taro&   To sai me shi d an Adam Ai dama haka yake, ba ya raina abin fa da don haka maganar wani Drivern ka na janyeta, na soketa daga yau yaron nan Miftahu zata aura&  wata ajiyar zuciya na ji Abba ya sauke wadda kana jin sautin fitarta har ta cikin wayar. Ya ce  Alhamdulillah, Allah yasa Midtahun ya amince.. Alhaji ya ce  MIFTAHU yaro ne mai biyayya na san ba zai ja da umarni na ba. Suka yi sallama. Sai sannan na mik e na fita tsakargida don taya Inna aiki.

Da daddare a kan gadon Kakata na kwanta, cikin matuk ar kwanciyar hankali da samun sukunin zuciya. Murna ta cika ni ganin na fita daga k angin bauta zuwa y anci da nake fatan ya  dore har gaban abada. Kamar an ce na kai Sunnah T.V na danna remote na kai, abin mamaki kawai sai ga fuskar Ustaz ta cika allon television d in, fuskarsa da  dan murmushi ka dan yana kallon wanda yake karanto masa tambayoyi yana amsawa kamar yarda ya saba a duk sanda ya gabatar da karatun da yake gabatarwa duk juma a da lahadi. Cak lumfashi na yaso d aukewa sai dai na yi jarumta k warai da gaske wajen ganin ban rasa nutsuwata ba. Hannu na saka zan kashe t.vn sai na ji mai tambayar ya ce  Ustaz Ahmad ita wannan tambayarta guda ce, wai me yasa ka saki matarka a daren da ta tare a gidanka? Shiru Ustaz d in ya yi yana murza goshinsa da d an yatsan hannunsa kafin ya furta  K addara. Ya kuma lumshe idon bai sake magana ba. Da sauri na danna remote na kashe Tvn zuciyata na wani irin tunzira da wani irin b acin rai. Na lumshe nawa idon ina jin kwararar hawaye a saman fuskata. Har cikin dare na kasa barci saboda k unar da zuciyata take ciki ba zai bari na samu na yi barcin ba. Shi yasa da na Yi sallahr asuba Inna ta ce koma ki kwanta ki dai ina jin ki ba wani barcin kirki kika yi ba, wato ba zaki bar sakawa kanki damuwa ba ko? Shiru na yi don bani da amsar da zan bata. Dole na koma barci don idona har yaji yake. Da safe na diga jiyo hayanyia daga parlorn Inna sama sama. Da sauri na mik e don sai na ji kamar fa da ake. Na d an d aga labulai d akin sai na ga Gwaggo Mariya ce k anwar Inna take ta masifa idonta a rufe.  Wallahi ba zai yiyu ba Yaya, ta yaya sai da yarinya ta gama watsewarta za a ce Miftahu ya aureta me yasa sanda take da mutuncin ba a bashi aurenta ba sai yanzu to gaskiya da sake ba dai Miftahu ba& ina shi ina auren Karuwa fisabilillah Miftahun da kowa ya shaida da nagartar halayensa&  D if parlorn ya yi ana saurarar tijarar gwaggo Mariya da ko kunyar furta wasu maganganun bata ji. Ni dai ji na yi kai na yana wani irin sarawa ga duhu ina gani ga wata irin hajijiya ni dai daga nan ban sake sanin me ya faru ba sai gani na yi a kwance a gadon asibiti. Inna a zaune kusa da ni sai Alhaji shi kuma yana zaune kan kujera duka fuskokinsu ba sukuni don Inna ma kamar kuka take.. ido na na sake lumshewa don bana son su fahimci na farka ina ji Alhaji ya ce  Yanzu ba zaki shiru da kukan nan ba&  cikin shashshek a ta fara magana  Bar ni Alhaji, bari na yi kukan nan ko zan samu zuciyata ta yi sanyi, Mariya fa! Mariya tawa ita take gudun ha da jini da ni saboda wata k

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login