Showing 51001 words to 54000 words out of 80390 words

Chapter 18 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

137

bu de baki suna kallonmu. Ina kallon yarda Umma take Zare ido kamar yarda Mammy da Abba ma suka shiga shock. Ita kuwa Aysha sai nuna ni take da yatsa sai dai ta kasa furta komai. Fuskarta ce dai d auke da tsananin mamakin da ya kasa b uya a idonta. Sai k ikkifta kyawawan idonta take.

Mai shari a dai tsabar ru dani ajiye biron ya yi, yana jijjiga kansa ya ce  Hukumullahi laaa ajaban.. wannan lamari to ya abin yake ne? Bayan tsawon mintoci da samun hayaniya a parlorn. Alk ali ya mayar da glass d insa ya kuma dakatar da hayaniyar ta hanyar amfani da guduma ya buga table d in da ke gabansa& nan take kowa ya nutsu aka kuma kasa kunne don cigaba da sauraran shari ar. Kowa ba son jin yanke hukunci yake ba, so yake yaji ya aka yi aka samu wannan matsananciyar kamar da muke da juna. A idanunsu na gano hakan. Ni dai ina tsaye sai mayar da ajiyar zuciya nake ina sake ware idona ina kallon SHANY da take tsaye tana ta fisgar leb enta da alama yanayin ya zame mata jiki. Idanunta kuwa kamar ma a buge take tsabar yarda suke lumshewa da kansu. Maganar da Alk ali ya yi ne yasa na d auke hankalina a kanta na gyara tsayuwata ina sauraran abinda ya ce.  Baiwar Allah ko bayin Allah, da gaske ne ku kuka yiwa Minuster D an Audu sata bayan kun same shi a hotel kun shak a masa abin Maye kuka yi amfani da wannan damar ku ka d au hotonsa kuka ya da a social media kuna nuna tsiraicinsa& ko da yake kafin nan zan so sanin sunayenku da na iyayenku garin da kuka fito da komai ma ina son sani&  Ya fa da yana duban su. Gaba d aya suka shiga kallon juna d aya bayan d ayansu suka shiga nuna mai kama da ni. Da alama itace shugabarsu ita kuma zata wakilcesu. Ba tare da shakkar komai ba ta gyara tsayuwarta tana cigaba da juya idonta exactly irin na y an Maye ta ce  Sunana SHANY, haka na taso na ji ana kira na a gidan da na rayu. Na ji ana kirana da SHANY. Aisha shine cikakken sunana. Sunan Uba ko wakili kuwa ba ni da ko d aya, ban kuma San su ba& .


Gaba d aya naga y an gidanmu Sun zaro ido. Musamman Umma da Abba. Mami kuwa k asa Naga ta yi da kanta. Shi kuwa Ustaz Ware idonsa ya yi sosai sai ya kalleni sai ya kalleta. A raina na dinga nanata sunanta wato itace wacce aka zata ni ce a jikin wancan hoton na farko Har Ustaz y a sake ni saboda shi&

Cikin fuskar mamaki Alk ali y a zuba mata ido kafin ya furta ban gane baki san iyayenki ba? Shi mahaifin naki mutuwa ya yi ko kuwa sallmaki ya yi kika shiga rayuwar bariki? Muryar ta a shak e ta furzar da huci ta ce  Na ce maka ban san su ba. Hakan yana nuni da amsar kai tsaye bani da su. Alk ali ya girgiza kai ya ce  Mahaifiya fa? Sai naga ta saki malalacin murmushi tana juya kai ta furta  Babu! Ni y ar tsintuwa ce, kamar yarda wad annan da kake gani suma duk y an tsintuwar ne, kai gaba d aya k ungiyarmu ma y an tsintuwar ne mun tashi a k ark ashin kulawar wata mata&  Ido kawai naga an zuba mata nima
Kallonta nake cikin matsanancin mamaki. Alk ali ya ce  Ikon Allah! Ita matar kuma bata San iyayenku ba take rainonku? Ina kallo SHANY ta d an yamutsa baki kafin ta girgiza kai da alama ta gaji da question d in Alk alin.

 Shegu ne mu, haka uwar gijiyar mu Atine harka take gaya mana bamu da wasu dangi bayan ita, ita ta rainemu ta kula da mu har muka kawo yanzu bayan iyayenmu Sun cillar da mu& . Alk ali ya yi rubutunsa kafin ya d ago ya zuba mata ido ya ce  Ina son sanin tarihinki& 

Ta sake turo bakinta cikin yanayin tsiwa ta ce  Atine y ar harka shine sunan wacce take kula da mu tun da muka tashi ita muke gani ita kuma muka sani. Tun muna yara tare muka taso da wa dannan, su na sani a matsayin y an uwana. Sune dama sa annina a gidan Babu wani mai cikkaken asali a cikin
Mu. Takurawar da Uwar rik onmu take mana yasa muka tashi da k untutaccuyar zuciya mai zafin gaske da k unci. Wahalar da mu take tamkar bayi. K alilan daga cikinmu take warewa ta saka a makarantar boko Wanda kyansu ya kai kyau, hakan yasa ta saka ni a makarantar nima don ta sha fa da ni jarinta ce, kuma wacce ta bata amanar kula da ni a kullum tana jik ata da naira.

Na yi makarantar private school tun daga nursery Har Secondary school, yanzu ma Ina jami a. Tana bani abinci mai kyau sutura mai kyau ba don komai ba sai don na yaudari k usoshin gwamnati hakan yasa bata gajiya da siya mana sutturu masu alfarma da supplement na gyaran jiki.

Yaudarar maza muke ta hanyar nuna shigar banza don tun yarinya tana shekaru sha hu du dama zata fara koya mata duk wata hanya da ta San zata mallaki namiji da dukiyarsa. A duk inda masu ku di suke muna zuwa mu zak ulosu mu kuma yaudaresu bayan sun saki jiki da mu sai mu saka musu abin Maye a abin sha mu yashe dukiyarsu mu d auki hoton tsiraicinsu mu ce da zarar sun fa da sai mun ya da a social media. Har zuwa yanzu da muka yaudari Minister d an Audu! Daga haka ta ja d an mitsilin bakinta ta tsuke tana cigaba da ka da jikinta. Da alama sam ba abinda yake damunta balle ta shiga cikin fargaba sai far far take da idonta da ya sha eyeliner.


Alk ali ya jinjina kai yana sake kallonta ya ce  Yanzu ina uwar d akin taku take? D an rausayar da kanta ta yi kafin ta furta ta ce  Tana Abuja ta ce kada ma mu nuna min santa mu je mu yi ta kanmu, wannan ne dalilin da yasa na d au alwashin sai na tona mata asiri& ta ce d an Audu bai da mutunci da dai wani ne tana da hanyar fito da mu. Alk ali ya sake jinjina kai ya ce  Ikon Allah! To ina kuke kai ku dad en da kuke yin fashi? Ko damfara zan ce? Alk ali ya jinjina kai ya ce  Ku bada address d in inda za a sameta. Kafin nan zaku zauna a hannun hukuma Har zuwa lokacin da zata zo mu tabbatar da abinda kuka gaya mana gaskiya ne& . Da wannan nake cewa Kotu ta wanke Aisha daga zargin da ake mata& muna kuma rok on ta yiwa jama a afuwa akan kuskuren da aka samu& Za a dawo shar ai sha bakwai ga watan nan da muke ciki& daga haka ya buga gudumar kotu d aukacin jama ar da suke wajen suka furta  Kotuuuuuuu! Wanda ya yi daidai da isowar duka zuri ar gidanmu wajen har Ustaz da bakinsa ya kasa rufuwa. Na dinga kallonsu da wani irin yanayi da ni kaina na kasa tabbatar da abinda nake ji. Haushinsu da haushin rashin yarda da ni da suka yi ya nanna de duk farin ciki na. Na dinga jin wani irin zafi a zuciyata. Idona ya sauka kan Mami da take zaune kanta a k asa na lura tun d azun bayan bayyanar SHANY a yanayin da take ciki kenan& ..




5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA& .49.


NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.


Yaya Usman yana dariya ya bar wajen. Ni kuwa harara na bi bayansa da ita ina kiciniyar k wace kaina da ga wajen Ustaz da ya manna ni da jikinsa kamar zai mayar da mu Abu guda. Idanunsa a lumshe suke sosai yana k ok arin aika sak on da yake so ya aika ta hanyar manna min zazzafan kiss da na ji shi har tsakiyar kwanya ta. Cikin kunnena ya min magana.  Ki shiga ki musu sallama mu tafi gida K alb, jikina na wani irin missing d inki. Na yi k arfin halin tureshi daga jikina ina sakin tsaki na ce  Wallahi ba zan koma gidanka ba Ustaz ko me zai faru sai dai ya faru& . Murmushi ya saki ya ce  Ko? Ki ce Ashe Abba zai shirya samar mana d aki a nan shikkenan Nima sai na dawo nan, kin ga ko aiki ba zaki dinga yi ba sai dai mu wuni muna raya sunna&  na zuba masa harara na ce  Ka d auka wasa nake? To bari ka ji na maka ta yara billahillazee na gama aurenka& Allah ya kiyaye na zauna da mai mata, ka je can ka jagwalgwalata Nima kazo ka jagwalgwalani na bar maka Hameeda Amma ni wallahi a yanzu dai kam saurayi gal nake so&  Shiru ya yi yana kallo na. Kafin Naga idonsa ya ka da ya yi jajur ya janyo ni jikinsa muka tsaya daf da juna da sauri na runtse idona don ba zan juri ha da ido da shi ba, don idon nasa a rikice suke. Cikin dasashshiyar murya ya ce  Open your Eyes and look at me& ki fa da min ba kya so na Mara kunya&  Ya fa da yana zagaye fuskata da yatsun hannunsa  Oya talk mana, madam parrot. Da sauri na runtse idona jin yarda ya zura harshensa a kunnena bayan ya saka hannunsa cikin rigata. Na ji ya saki wata ajiyar zuciya da ta saka ni Jin kamar na saki fitsari. Tsawon lokaci ina jikinsa na kasa Zare jikin nawa sai can na ji ya sake ni ya kwanta flat a saman gado idonsa a lumshe..  Ke da kanki kin yi missing d ina amma kafiya da taurin kai sun hana ki ki gane, sai yaushe zaki daina wahalar min da zuciya ne? Ya fa da yana zagaye ni da kasalallen idon sa da suka jirkita zuwa wani launi da duk Wanda ya ganshi zai gane. Na mik e tsaye cike da tsiwa da masifa na ce  Sai sanda ka sakeni. Malam idan sonka zai kasheni sai fa ka sake ni, idan ma ina son naka kenan. Daga haka na juya da sauri na fice daga d akin haushina guda yanda k amshin mayataccen turarensa ya mak ale a kaya na. Gashi ba dama na canja Kayan da Zarar na canja kowa zai yiwa abin mummunar fahimta. Tilas na zauna da Kayan da duk inda na motsa sai naji k amshin turaren da yake jefe ni a wani yanayi. Ina son Ustaz son da ya sabbaba min zafin kishinsa nake jin Sam ba zan iya ha da shi da wata ba. Ga zafin mahaifiyarsa da nake ji a raina don haka dole zan hak ura na bar mata d anta.


Da daddare& ..


Kamar kowane lokaci da aka Saba a lokutan baya UMMA ta shirya abinci. Abin haushi sai ga Ustaz ya zo don Naci a Daren ma. Kyan da ya yi yau har ya zarce misali. Sam bai ji kunya ba ya zauna a cikinmu duk inda na yi kuma idanunsa suna zube a kaina. Cin abincin ake ba mai magana sai dai ni da Ustaz da y a taku rawa na lura shima ba abincin yake ci ba. Sai da aka gama sannan Abba ya yi godiya ga Allah ya yi addu a mai tsawo sannan ya dubi UMMA ya ce  Ina tsammanin wani al amari game da yarinyar nan mai kama da Aysha. Ina hasashen ko daga tsatsanmu take musamman masu kamar A isha a dangin nan suna da yawa kasancewar da Mahaifiyar Alhaji suke kama don haka na ce lawyoyi su tsaurara bincike har sai an gano marik iyarta da yarda aka yi ta tsinceta saboda kamannin Sun yi yawa. Banda a gaba na aka fito da ita lokacin da kika haifeta tabbas da na ce y an biyu kika haifa. Umma ta ja ajiyar zuciya ta ce  Ashe ba ni ka dai abin nan ya tsayawa a rai ba, kamaninn ga sun b aci kamar irin y an biyun nan da ake kira Identical twins fa Wanda ba a gane su sai da shaida. Amma kuma ai ba Wanda ya tab a rasa y arsa a dangin nan& Abba ya ja ajiyar numfashi ya ce  Gaskiya, ba Wanda ya tab a rasa y arsa a kaf danginmu daga na nan jihar har ba potiskum, Amma ina Jin lamarin yarinyar nan a zuciyata kamar jini na, kuma na tausaya mata da ita da y an uwanta da aka raina cikin irin wannan bak ar rayuwar, koda an bincike ba a dangi take ba, ni zan d auketa da sauran y an uwan nata da ba a samu danginsu ba In sha Allah. Umma ta ce  Gaskiya hakan ya kamata ka yi, Ubangiji Allah ya tayaka rik o, Allah yasa ma tana d aya daga cikin ahalin wannan zuri a tamu. Sam zancen su bai wani burgeni ba a zuciyata haushi ma na ji saboda me za a d au mutanen da suka yi silar afkawa ta cikin bala i? Na dai bi su da ido kawai. A ranar kam k emadagas na k i na je wajen Ustaz duk da lallab a ni da suka dinga yi na yi burus da su na shige d aki, Abba ya ce a k yale ni na huta.


KASHGARI& ..


Tun da na tashi da safe, na ji zuciyata ba abinda take so irin na ga Mami na. Hakan yasa na shirya tsaf cikin wata tsadaddiyar Abaya ta peach color mai masifar kyau. Ina fita parlor na zube a gaban UMMA ina rok onta ta bar ni na je na ga Mami na. Shiru Umman ta yi kafin ta ja ajiyar zuciya ta ce  Ayshatu y ar gidan Mami, ni ba zan hana ki zuwa ganin Maminki ba Amma na San ko kin je ma bai zama lallai ta saurareki ba. Na marairaice fuska ina cewa  Ni dai UMMA ki bar ni na je. Ta d aga Kai  Ki je Aysha Amma kada ki da de tun da mutane suna zuwa Miki murna. Har na mik e na ji UMMA ta tsayar da ni ta ce  Au, tsaya Aysha kin tambayi Ahmad ne ai ya zama dole ki gaya masa kafin ki fita, tunda da igiyar aurenki a Kansa. Gaba d aya na b ata fuska ta na ce  Umma wane irin na tambayeshi kuma? Ni fa wallahi UMMA ba zan koma gidansa ba, don har yanzu ban manta abinda ya min ba, k arshe shine har da aure ban sani ba, ni wallahi bana son zama da kishiya na je ina wani raba miji da ita&  Baki Umma ta saki tana kallo na kafin ta ce  Cab di, ba shakka, kanki d aya kuwa Aysha? Ba zaki raba miji da wata ba, to kin ci gidanku shin mu nawa kika bu di ido kika gani a wajen Uban ki? Gwara ma ki sahhalaewa kanki tunda kika zo A Nigeria dama a wata k asar ne sai na ce mafarkin ki zai zama zahiri& shin menene ma laifin Ahmad da zaki ce ba zaki koma gidansa ba? Rau rau na yi da idona na ce  Umma baki ji fa irin maganganun da yake gaya min ba, duk Akan laifin da ba nawa ba, sai da yaga ba haka bane sannan yake son kare kansa, ga mahaifiyarsa ba irin tsanar da bata nuna min ba. Allah ya kiyaye na koma wani gidan Ustaz&  Umma kallona kawai take cikin matsanancin mamaki ta ce  Duk na ji, ai mu ma iyayenki mun miki laifin me yasa kika yafe mana? Na girgiza Kai na ina fincikar leb ena na ce  Ku daban, shi daban, bari na yi sauri na tafi. Ban jira UMMA ba na fice da sauri ko driver ban tsaya jira ba na tafi Titi da kaina Neman adaidaita sahu.



Tunda na shiga gidan Mama take jifana da kallon banza, ko amsa gaisuwata ba tayi ba, ta hau ni da fa da cikin b acin rai.  Aysha Fateema ba uwarki ba ce, ku barta ta huta tunda gaskiya ta riga ta bayyana bana son na sake ganin sillan k afafunki a cikin gidan nan kin ji na gaya Miki. Turo mata baki na yi na ce  Da dinta ba wajenki na zo ba, wajen Uwata na zo, kuma wallahi sai na ganta babu Wanda kuma y a isa ya ce Mami ba uwata ba ce, don haka ki bar wani balok ok o kafin ki tada hawan jininki a banza&  na haye sama ina dariya ganin yarda ta zaburo a guje. Sai da na tabbatar na kai inda ba zata iya Cafka ta ba sannan na juya na mata gwalo na ce  Ki biyo ni mana, idan kina da k afa gurguwar tsohuwa kawai. Ina ji ta ce  Ba shakka! Za ki sakko ki same ni ne.

A hankali na tura k ofar d akin Mami na. Wannan karan a zaune na sameta tsaf da ita cikin kwalliya sosai sai zabga k amshi take& . Ta d ago tana kallo na da mamaki ta ce  A isha ke ce da safen nan? Ho ho ho! Aysha Sam ba kya girma, idan banda haka daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login