Showing 63001 words to 66000 words out of 80390 words

Chapter 22 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

133

ce  Mhmn, Umma dama maganar Ustaz ne na amince zan koma gidan sa a bar maganar aurensa da Humaira. Wani irin kallo na ga Umma tana min bakinta a sake da alama mamaki ne fal a zuciyarta ta ce  AYSHA wace irin magana nake ji, Mara da din ji haka? Me yasa kike son mayar damu k ananan mutane? Da kanki fa kika ce ba kya sonsa sai yanzu da Har ya kawo lefen y ar uwarki da saka ranar aurensa sai kuma ki ce shi kike so. To wannan maganar ta tsaya tsakanin ni da ke kawai bana son ko a zuciyarki ki sake maimaita ta. Ahmad shi ya dace da auren y ar uwarki ko ba kya son ya zama silar gyaruwar dukkan laifikanta. Kada ki zama mai son kanki mana Ayshatu. Ta dafa hannuna ta ce  Ki yi hak uri kina gama idda ke ma zaki samu mijinki ki tuna ita zata yi wuyar samun miji musamman irin rayuwar da tayi a baya, tunda yanzu kuwa Allah yasa babban Malami irin Ahmad zai aureta ai sai mu godewa Allah ke kuwa na San zaki iya samun kwatankwacinsa ko Wanda ya fi shi In sha Allah, tunda ke baki da wani aibu&  Zufa ce kawai take fita daga jikina. Na dinga kallon Umma ina mamakin kalamanta. Anya kuwa Umma na so na? Ko dai Har soyayyar uwa ta tattara ta barwa Mami ni. Idona suka ka da suka yi jajur ina jin yarda jijiyar kaina take harbawa da k arfin gaske na runtse ido na ina ji Umma ta d an rungumeni ta hau bubbuga kaya na. A hankali ta ce  Ki zama mai son y ar uwarki fiye da kanki AYSHA, ke kin taso da gatanki ita kuwa fa? Kinga dole yanzu tana buk atar kulawar mu da dukkan soyayyarmu. Ban amsa mata ba. Kukan ma kuwa ya k i zuwa sai zugin zuciya da tsananin b acin rai. Na janye jikina na mik e kawai ina harha da hanya na bar d akin. Kashe wayata na yi gaba d aya na daina kula kowa a gidan kullum cikin shiru nake hakan kuma bai saka Sun fasa shirye shiryen biki ba. Wanda zai zama daidai lokacin da na gama Idda.


Ranar da naga period d ina na k arshe hankalina ba k aramin tashi ya yi ba. Don na San ni da Ustaz kuma sai gani sai hange daga nesa. Hakan ya tashi hankalina sai dai na tattara na mik a lamari na ga Allah. Na tabbata tawa k addarar ce haka. Mami na ma ban sake nemanta da zancen ba. A ranar da zan yi wankan tsarki na gama period kasa yin wankan na yi saboda matsananciyar fargaba da b acin rai. Na yi wata irin rama da ko lokacin da abubuwan can suka faru ban yi ta ba. Fuskata baka ganin komai sai idanuwa. Na kasa samun nutsuwa Har sai da na danna kiran Mami na. Bugu guda kuwa ta d auka tana furta  A in Mami ya aka yi? Na fashe ina gaya mata na gama idda yau. Shiru ta yi kafin ta saki ajiyar zuciya ta ce  Ustaz ya san kin gama ko zaki gama a yau? Cikin kasala da mutuwar jiki na ce  Na san ya sani don kwanakin period d ina a kansa suke kamar yarda duk zan fara period shi yake gaya min yau Madam fa sai a hankali bak o zai zo. Mami ta yi shiru kafin ta ce  AYSHA, yanzu ba abinda ya rage mana sai ki fito musu ta yarda suke so, da zarar sun Miki maganar fito da miji ki ce kawai kin bawa Abbanki wuk a da nama na San zai gane kina son komawa auren Mijinki ne, shikkenan sai ki a mayar da aurenku. Na saki ajiyar zuciya ina jin shawarar Mami accepted har cikin rai na.


Da sassafe kuwa da kaina na shiryawa Abba favorit food d insa Masa da miyar taushe. Duk ba na komai bane sai na cin hanci. Na dama masa kunun gya da ha dadden ba abinda yake sai k anshin gya dar gashi fari tas kamar yoghurt. Har a Sallahr walaha sai da na rok i Allah yasa Abba ya amince da abinda zan je masa da shi. Ina kallo Su Humaira kallona kawai suke yi, sai dai ba su min magana ba don yanzu na zame musu horror komai suka yi masifa nake musu. Da kaina na kinkimi kwandon Abincin Abba na shiga da shi parlorn a raina ina furta  Yairinya kwalelenki, mijina yafi k arfinki ko ta halin k ak a sai na k wato abu na.


Har k asa na kai na gaida Abba da yake ta kallo na yana furta  Yau A in Mami ta tuna da Abbanta kenan, Har gashi an min delicious.
Na yi k asa da kaina ina murmushi ganin fuskar Abban fal nisha di da alama hak ata zata cimma ruwa. Abba ya ce  Ko an samo min surikin ne? K in ga shikkenan sai a ha da da na y an uwanki don na San yanzu dai k in gama idda. Na girgiza kai na ina murmushi na ce  dama akan maganar na zo Abba. Ya gyara zama yana furta  Alhamdulilah, addu a ta ta amsu kenan, yaushe suka ce zasu turo?
Idona ya kawo ruwa sosai kafin na d an girgiza kaina cikin k arfin hali na ce  Abba, na baka zab i ka zab a min duk Wanda ya maka ni kuma zan aure shi. Abba ya saki murmushin jin da di ya ce  Kin tabbata AYSHA? Ko wa na baki zaki amince ki aure shi? Na d aga kai da sauri. Sai na ji ya ce  Alhamdulillah da y a ta gari, ina alfahari da zamowar ayshatu cikin zuri ata, Allah ya Miki albarka ki shirya yau da daddare zaki yi bak o. Duka k irji na yake yi sosai na mik e a kasalance na mik e na fita. Sam ba haka na so na ji Abba ya ce ba, so na yi ya ce shikkenan AYSHA za a mayar Miki da aurenki da mijinki. Duk da haka nan cire rai ba, ban sani ba ko akwai wani suprise da Abba yake min, may be da daddaren Ustazu na zan gani a zuwan Wanda ya zab a min. Don haka har dare na kasa samun nutsuwa duk da haka na fece kwalliya sai zabga k amshi nake sabuwar atamfa na saka mai masifar kyau na yafa babban mayafi da niyyar ina shiga wajen Ahmad zan cire mayafin tunda Naga yanzu hankalinsa na kan wayayyun mata. Kaina dama ko d ankwali babu gashi na ne na gyara shi sosai ya kwanta abaya na.


Ai kuwa Maryam na zuwa ta ce min ina da bak o na mik e. Kitchen na shiga na d au tray d in da na ha da masa delicious a ciki. Na saka kai na a parlorn. Zuciyata ta yi wani irin bugawa ganin Wanda yake zaune ban san sanda na saki tray d in ba, kayan ciki suka tarwatse a k asa gaba d aya& ..





5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA& .60.


NAZEEFAH SABO NASHE&
'?



08033748387.


Don haka bana so na sake Jin kin furta kina son Ahmad, balle wani ya ji a yi da mu. Ki rungumi Mijinki ki so shi, sai ki ga watarana kin yi alfahari da aurensa balle yana son ki kuma shima yana da rufin asiri fiye da Ahmad ma. Wasu hawaye kawai na ji Sun ziraro min na kasa furta kalmar komai sai ajiyar zuciya nake saki. Umma ta ce  Ke ai gaba ta kai ki, irin wa dannan mutanen da suke ninka ka a shekaru Sun fi iya lallab a mace da nuna mata tattali, don Allah Ausha ki so Abin ki ki bashi dukkan kulawa&  zaro ido nake kawai, ina tunanin ta ina zan fara son wannan abin? Ta ina zan bashi kulawar? Da wani rungumemen cikin za a sha soyayyar. Ni AYSHA mai mafarkin auren Miji d an gayu sai na b ige a Mamuda mai tumbin ku di. Na San su Asma zasu sha dariya don na sha alwashin ba zan auri mummunan mutum ba ko mai ku dinsa kuwa gara na auri kyakykyawan da bashi da ko sisi. Umma bata sake bi ta kaina ba ta dai dafa kaina ta d an shafa alamar rarrashi ta fice daga d akin. Ni kuwa bin bayanta na yi da kallo ina tunanin yarda Umma ta zamo uwa a gareni Amma bata damu da ni ba, bata son farin ciki na. Ban sani ba ko sanda ta bawa Mami ne Har duk wani so da tausayi irin na uwa da take min ta tattara ta barwa Mami. Za a sha drama don ba zan yarda da auren Mamuda ba.


Haka aka shiga gudanar da shagulgulan biki, ni dai nawa ido don bani da wata mafita kuma banda Allah. Har Anty Khadija da take fama da jeho bata zauna ba a bikin nan sai kai da komowa take tun tana bani hak uri Har itama ta gaji ta tattara ta zuba min ido. Gyaran jiki kuwa haka na hak ura ina ji ina gani aka gurji jiki na. Bana fita ko ina abinci ya zama bak ona ruwan shayi kawai nake sha shima sai na runtse ido. Yaya Usman tun yana bani hak uri har ya tattara ni y a watsar. Y an matan Umma kam an sha kyau na ban mamaki ina kallo aka kawo lefen Humaira daga gidan su Ustaz akwati na sha biyu.


Ranar da ya kama za a kai amare. A ranar na ji labari wajen Anty Khadija wai nima zan bi Mijina Abu Dhabi a ranar da daddare. Wani irin k ululu ne y a tsaya min a mak ogaro na kasa furta komai sai binta nake da ido. Har sai da ta gaji da kallon ta bushe min ido tana furta  AYSHA lafiya? Kika shiga irin wannan shock haka? Na saki ajiyar zuciya mai k arfin gaske kafin na fashe da kuka na ce  Abu dhabi fa kika ce Anty Khadi? Wallahi bana son mutumin nan kuma duk da haka ba zai barni cikin y an uwana ba sai ya cilla ni wata uwa duniya. Anty Khadi ta dafa cinyata ta ce  Ki saka a ranki wannan k addarar ki ce, shi a can yake kasuwancin sa, baya ga haka kuma ya amince za ki karatun da kike so a can, ba shikkenan ba burinki da na Maminki ya cika kun samu Wanda zia barki ki yi karatu. Kuka nake sosai a jikinta na ce  Ni na hak ura da karatun har abada in dai don haka aka d aura min aure da shi. Aunty Khadi ta ce  Aa fa AYSHA, yanzu ai lokaci ai ya k ure ko so kike a fara k irga Miki aure? Dukkan wasu shirye shirye sun kankama yau za ki bi mijinki. Daga haka ta mik e rik e da d an jaririnta sunan Abba muna ce masa Jawad ta fice. Kifewa na yi akan gado. Kukan ma da nake yi y a d auke d if ba abinda nake ji a zuciyata sai wani irin matsanancin b acin rai da tashin hankali Mara misali. Ban san wainar da ake toyawa a cikin gidan ba, don ban tashi ba sai daf da magriba, cikin matsanancin b acin rai da na k uncin zuciya. Na ma manta da zancen wai yau Mijina zai tafi da ni Abu Dhabi. Wanka kawai na shiga ko na ji sanyi a raina. Ina fitowa d aure da towel a jikina na ga gari ya yi duhu. Sai ji na yi an turo k ofa an shigo ina d aga kai na ga Anty Khadija rik e da wani k aramin akwati a hannunta tana kallo na da alamun rashin wasa a fuskarta ta ajiye Box d in ta ce  Ashe ma kin yi wanka, don har ya fara waya jirginku k arfe goma zai tashi kada a yi delay. Ki samu ki shirya ga can k anne ki suna jira ku yi sallama kafin a kai su d akin mazajensu. Wani irin rawa jikina yake ina kallon Anty Khadija da sam abinda take fa da baya damunta naga itama yau har da kishiya za a kai mata amma sam bata damu ba, mace ce mai wata irin zuciya Mara misali. Ta fita sai gata ta sake dawowa wannan karan kaskon turaren wuta ne a hannunta sai zabga k amshi yake ta ajiye daf da ni. Sannan ta mik a min Humar da kwalacca tana danna wayarta ta k ara min a kunne  Maminki zata Miki magana, saura ki mata kuka ki d aga mata hankali. Ai kuwa ban ji kashedin Anty Khadija ba ina karb a na fasa mata kukan sosai. Kamar ba zata yi magana ba, sai can ta saki ajiyar zuciya ta ce  Yi shiru Babyn Mami, ki kwantar da hankalinki zan Miki wani alk awari muddin kika yarda kika yi zaman aure da kyau cikin soyayya da kulawa ni kuma zan share Miki hawayenki zan kuma dawo gidanku. Na bu de ido na da sauri Har ban san sanda murmushi ya sub uce min ba na furta  Da gaske Mami? Sautin murmushi ta na ji tana furta  Am serious Baby, buri na kawai ki bawa Mara d a kunya. Haka ta min nasiha sosai sannan ta ce  A cikin akwatin da na aiko Miki da kayan da zaki saka yau, akwai magunguna a ciki kada ki yi wasa da su masu kyau ne na gaske na saka matar ta rubuta Miki duk bayanin yarda zaki amfani da su. Allah ya miki albarka ya yiwa rayuwar aurenku albarka ki dage da biyayya AYSHA ko kya rabauta duniya da lahira. Daga haka ta yanke kiran ina ta fa din Hello Hello Mami na, amma ban ji ta ba. Hakan yasa na sauke wayar daga kunnena cikin mutuwar jiki da ta zuciya wasu hawaye masu zafin gaske suka shiga zubo min. Wa zan yiwa soyayyar? Wa zan nunawa kulawar? Wa zan wa biyayyar? Wata zuciyar ta amsa min da MAMUDA MAI KATON CIKI. Sai kawai na lumshe ido na ina sake hasasho shi a cikin duhun idona hankalina y a sake tashi, gani nake ko da wasa ma ba zan iya d aukar nauyin wannan mutumin ba. Anty Khadi na tsaye tana kallona Har ta gaji ta mik a min kwalaccar haka kawai sai naji k arfin zuciya yazo min don zuciyar ce ta bani shawarar na je gidan Mamudan Amma zallar rashin kirki da zan dinga nuna masa sai ya gaji ya sake ni, kuma ba zan tab a yarda ya kusanceni ba, sai me don an k irga min aure ai ba kaina farau ba.


Haka na shirya sai dai ban saka komai a fuskata ba. Laffayar ma da take ta zuba wani cool k amshi Anty Khadija ce ta na da min. Ta ja hannuna muka fita parlorn gidan inda sauran y an matan Abba da za a kai
Gidajensu suke. Kallonsu
Kawai nake d aya bayan d aya don zuciyata ma ta bushe na kasa kukan sai wani irin tafasa take hakan yasa nake fesar da huci a kai a kai. Hucin da yake bayyana Har a k ofofin hanci na.


Dangin Ustaz ne suka fara zuwa suka tafi da Humaira. Ta zo rungumeni na janye jikina ina jin haushin ta da tsanarta sosai a raina. Ina kallo sauran ma duk aka fice da su. Gidan ya yi tsit daga ni sai Umma sai Aunty Khadii da take zaune a gefena tana sake kwantar min da hankali. Ni dai ido kawai na
Lumshe daidai lokacin Abba ya shigo shima ya k araci nasiharsa ban bu de idon ba. A k arshe ya ce  Allah ya baki ikon sauke nauyin da Allah ya d ora Miki. A raina na ce  K warai kuwa nauyi, ko da kanku kun san ni y ar fucilata da ni wannan mutumin ya min nauyi, ba mamaki daga ranar da yazo karb ar hakkinsa ya ragargaza ni na Mutu kowa ma ya huta. Na tuno first night d in mu da Ustaz yarda na ci bak ar azaba ina ga wannan mai randar cikin ga jajayen ido fici fici daga ganinsa ka ga jarababben mutum. Abba da kansa ya ja hannuna zuwa waje wajen Mamuda da aka ce ya zo. Haka na zama tamkar rak umi da akala na kasa wani motsi zuciyata ta soye idanu na fes nake kallon mutane. Ban damu da barin gidan ba don su kansu mutanen gidan na saka musu alamar tambaya a kan su da k yar idan sun damu da farin ciki na.


Suna gaban motar shi da wancan abokin nasa ni kuma ina bayan Mota ni da Yaya Usman da yake ta faman aikin lallashi na. Sai dai ko gezau kallonsa kawai nake. Mamuda mai tulun na ji ya ce  Ka rabu da ita Usman, nan da gobe zaka ganta warai, ai ba a lallab a bazawara tunda ta riga ta San da din aure ita kanta na San yanzu a matse take mu ka dai ce& . Abu na ji ya sake tokare ni a k irji. Jin yarda yake kalamai kamar yazo daga k auyen k awai na yi shiru ina tunanin izaya iri iri da zan masa har sia ya gwammace bai San wata Aisha ba wallahi. Yaya Usman ya ja hannuna ya rik e sanda za mu yi sallama a airport cikin wata irin murya ya ce  I mish you lil sis ne a good girl please AYSHA! Sai a lokacin kuka yazo min na fa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login