Showing 3001 words to 6000 words out of 80390 words

Chapter 2 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

151

yafe miki ba, Allah ya isa! Cikin duhun idanu na na dinga kallon yarda Mami take runtse ido tana taune leb enta ta furta  Ya isheka Imamu! Na gaya maka ya isheka! Ya za a yi ka dinga tuhumata da laifin da ba nawa ba? A gidan Uban wa nace AYSHA ta lallace ko na san tana lalatarta a b oye? Ta ya zan san abinda take aikatawa a b oye. Ka saurara min ko don an ga bana haihuwa shine kuke tunanin zan lallata y ar kishiya? Ta fa da muryarta na sark afewa da wani irin kuka mai k arfin gaske. Tsaki Abba ya ja ya furta  Idan ma ta tabbata ke ce, to wallahi ki tabbata kin tattara kin bar min gida kafin na san hukuncin da zan yanke a kanki.  Saki nake so Imamu idan ka tashi sakin nawa ka min saki Uku, haka kawai zaku jingina min laifi&  Umma dai na gefe tana runtse idonta fuskarta ta bayyana tashin hankalin da take ciki. Ya.Muhd ne ya kalli Abba idanunsa na zubar da hawaye ya ce  Abba ka bari mu ji ta bakin wannan munafukar yarinyar? Uban waye wannan d in? Don da alama sun da de da shi don ga kayan shaye shaye nan Suna sha, daga ganin wannan madarar abin maye ne a ciki, ji fa idanunsu&  Madara? Ita na ji ta zo kai na, na bu de kumburarrun idanuwana da bana son sake ganin abinda suke cikin hoton, amma hango cup d in madarar sai na tuna da madarar da Mami ta dinga d ibga min kafin tariyar bikina. Ya.Muhd ya kai min wani duka ya furta  Don Ubanki ba magana ake miki ba? Na ce Uban waye wannan d in? Sannan har shaye shaye kike ko? Da sauri na girgiza kai na na ce  Ni bana shan komai wallahi, ni ban san komai ba na san dai daf da zuwan bikina Mami tana bani wata madara kullum da daddare da take saka ni barci bayan wannan wallahi ban san komai ba!

Wani irin shiru naji parlorn ya yi. Kowa idonsa a kan Mami da kawai yake kallonsu tana waro ido. Ta kasa furta komai sai kallona take bakinta a bu de Abba ya wani irin yunk orowa ya isa inda take.  Fateemah gaya min madarar Uban me kike bawa AYSHA duk dare? Gaya min kafin na datse igiyar aure na da take kan ki&  Ya fa da yana janta da k arfin gaske. Ta mik e tsaye itama a zafafe tana kallon cikin idonsa kafin naga ta saki wani murmushi ta wafce jikinta tana furta  Madarar da zata bugar da ita ta saka ta karuwanci na bata Imamu kuma burina ya cika yau AYSHA ta zama karuwa, ban yi haka don komai ba sai don aurenta da Ustaz ya mutu kuma na samu riba akan hakan& & 


Ba wanda bai bu de ido yana kallonta ha de da jin mamakin furucinta ba, ta bimu da kallo d aya bayan d aya kafin ta sake jinjina kai ta fice daga d akin. Ina ji dai Abba mutuwar zaune ya yi. Umma kuwa idanunta ko blinking basa yi tsabar tashin hankali. Ni dai na san na lumshe ido amma bayan haka ban sake sanin komai ba, sai farka wa na yi na ganni shimfi de a tsakargida jikina sharkaf da ruwa ba kowa a wajen, sai Yaa Usman da Jummai mai aikinmu suna ta faman yi min sannu. Na mik e zaune ina jin kaina kamar zai rabe biyu ina kallon Ya. Usman na furta  Don Allah Ya.Usman kace min mafarki nake ba gaskiya ba don Allah. Hawayen da naga suna sauka daga idonsa ne ya tabbatar min da ba mafarki nake ba. Hannu ya kama ya damk e cikin nawa ya matsa da k arfi yana furta  Why AYSHA? Me yasa kika zab i waccan rayuwar mai matuk ar muni da ba inda take kai mutum sai tashar nadama? A farko dai mutum yana jin da dinta kafin ta jirkice ta koma saka mutum Nadama! Why AYSHA duk tarbiyyar da aka baki a gidan nan kin hanb areta kin dasa wata daban, me kika rasa? Ci sha ko sutura ko kayan more rayuwa? Kowa burinsa a gidan nan samarwa AYSHA farin ciki ashe ke kina nan kina bin abinda zuciyar ki take so. Idan wannan hoton na baya da ya nuna mana a buge kike, AYSHA wancan Kuma vedion a ras  dinki kike, amma kike zaune akan cinyar namiji& Ga shi nan Kin ja Abba ya yi mummunan fushi da ke, Umma kuwa ta ce kada na shigo da ke d akinta gwara ki mutu ta huta& Abba ya saki Mami&  Duk abinda yake fa da idanuna suna kafe a kansa bana ko k iftawa. Wani irin zafi da tafasa nake jin zuciyata na yi. Ba abinda ke min yawo a kwanya sai furucin Mami ta ji da di da na zama Karuwa! Ashe burin Mami kenan a kaina&  Na dinga jin zuciyata na wani irin bugu. Ganin kamar bana hayyacina hakan yasa Ya.Usy bani ruwa na sha, ya kama hannuna muka nufi d akin Umma, binsa kawai nake kamar rak umi da akala. Umma na gani na ta wani mik e da sauri tana kallon Usman. Marairaice mata ya yi sai naga ta yi murmushi ta d aga masa kai. Hakan yasa ya juya ya fita. Tana ganin ya yi nisa ta  dago tana kallona da wasu firgitattun idanunta ta mik e tana furta  Biyo ni nan munafuka! K irjina ya buga na mik e jikina a sanyaye na bi bayanta. Wani  d aki da muke ajiye shirgi nan ta shigar da ni muna shiga ta mayar da k ofa ta rufe ruf har da murza mukulli. Ta dubeni a tsawace tana furta  Cire kayanki tas! Bana son ganin komai a jikinki sai Brezier da pant&  na bu de ido ina kallonta muryata na rawa na ce  Don Allah Um&   Rufe min baki munafuka! Wani abu zaki b oye a jikin naki? Wanda duniya bata gani ba, zigidir kike kwance jikin namiji bakomai a jikinki sai pant&  Ta fa da a tsawace. Ganin ba alamar wasa tattare da ita yasa na cire kayan nawa. Wata irin waya na gani ya ciro a bayanta ta shiga lafta min a jiki. Tun ina ihu har na saduda na yi shiru, don muryarta ma ta daina fita& Tana gama ta cillar da bulalar duk da magi y ar da su Jummai suke mata bata bu de ba, ta juya tana kallona  Kuma ki bu de kunne da kyau ki ji ni, daga yau duk aikin gidan nan ya dawo kan ki& idan wancan hoton a buge kike d ayan vedion fa ras da k afafunki muryarki garau kina furtawa wani banzan namiji zantukan ba dala, Kun cucemu kin karaya zuciyar mahaifinki munafuka! Daga haka ta fice na runtse idona kukan ma ya k i zuwa sai tafasar zuciya. Ina jin Jummai ta d aura min zani na har hawaye take tana furta  Ya Ilahi wani irin duka ne wannan? Bari Usman yazo ya kai ki asibiti. Tana fita kiran Ya. Usman na mik e ina layi na zura rigata  Ba Zan iya ba guduwa kawai zan yi na ayyana haka a raina. Duk jikina ra da din zafin dukan yake& &
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA 24.

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.



Ina saka kai tsakargida Ya.Usman shima yana shigowa hankalinsa tashe yake kallo na. Kafin na ga ya kama hannuna da sauri ya ja ni muka koma cikin d akin.  Ina zaki Aysha? Shine tambayar da ya fara jeho min. Madadin na amsa masa wani hawaye ne ya shiga suntiri a kumatuna. Ya zaunar da ni yana kunna fitilar d akin. Wani guntun tsaki ya ja, yana furta  Nan Umman ta kawo ki? Anan d akin shirgin zaki kwana?  Usi ba wannan tambayar ya kamata ka mata ba, ka kamata mu tafi asibiti ji fa jikinta yarda duk ya yi Shatun Bulala. Sai sannan ya kalli jikin nawa da sauri naga ya waro ido yana furta  Ya Ilahi! Tashi AYSHA tashi mu tafi asibiti. Na mik e da k yar ganin ina layi yasa Ya.Usi ya kama ni muka fita zuwa tsakargidan. Turus ya yi Jin Umma ta ce  Gidan Uban wa zaku? Usman ba zaka fita shirgin gallafirin yarinyar nan ba? Fuskarsa a tsuke ya ce  Umma abin ya yi yawa, ji fa jikinta ji yarda kika mata rauni da bulala. A zafafe ta ce  Sai me? Sai me don na raunatata ba gwara na illata jikin da take tak ama da shi wajen jan hankalin mazan ba, ba wani asibiti da zaku wuce ki koma ciki. Kai kuma idan ka sake ka bita ban yafe maka ba.. Ina ji cikin sanyin jiki Ya.Usman ya zame hannunsa daga cikin nawa, ya wuce zuwa part d in su. Wasu zafafan k walla ne suka shiga zubo min, Ina ji Umma ta sake jan tsaki ta koma d akinta. Jummai ce ta ja hannuna idonta fal k walla muka koma cikin d akin da muka fito. D akin ta tsaya tana kallo na san ba mamakin da take sai ta yarda Ni AYSHA y ar gayu zan kwana a d akin nan, da aka tabbatar da ba komai a cikinsa sai shirgin b eraye da muk arebansu.  Ko zamu je zan wajen mu ki kwana AYSHA kafin komai ya lafa. Jummai ta fa da na girgiza mata kai na, na ce  Bar ni kawai Jummai, bar ni na kwana a inda Umma take son na kwana, fata na Allah ya  d au raina a daren nan na huta& . Da sauri Jummai ta saka hannu ta rufe min bakina.  Ki yi shiru AYSHA kowane bawa baya wuce k addararsa, kawai ki yi ta istigafari Allah gafururruhimu ne, duk girman laifin ki matuk ar kika yi tsarkakakken tuba zai yafe miki&  Ido na k ura mata cikin jin mamakin lafazin bakinta, kenan itama Jummai ta yarda ni zan aikata zina. Madadin na bata amsa takaicin da yake cin zuciyata ya hana ni kawai sai na lumshe idona ina zurarar da hawaye. Jummai ta mik e ta fita daga d akin sai gata ta dawo da bargo da zanin gado har da pillow ta mik o min. Karb a na yi na saka a gefena ta min sai da safe ta fita bayan ta bani panadol. Ban bi ta kan maganin ba, don ba buri na waraka ba ni ban k i na mutu a ranar ba. Har jiri nake ji tsabar jigata da rashin cin wadatacen abinci tun bayan afkuwar lamarin. Alwala na samu kai na da fita yi kamar an tuna min a wannan gab ar Ubangiji ne kawai gatan ki Aysha. Na shiga toilet d in masu aiki duk da k yama ta a ranar neman k yamar na yi na rasa na fito na d aura alwala a famfon tsakargidan mu. Na koma d akin da a yanzu ya zama mallaki na. Sallah na tayar na dinga jerata ina kaiwa Allah kuka na a cikin sujjada da son ya agajeni ya tona asirin duk mai hannu a cikin wannan sharrin da aka min. Don dai na san ba ni ba ce, ba zan kuma tab a yarda da ni d in ba ce.


Ban kwanta ba sai k arfe uku da kwata na dare. Kiran sallahr farko kuwa Umma ta banko k ofa ta tashe ni. Da k yar na bu de idona ina kallon yarda take min kallon tsana ta furta.  Fito y ar banza lokacin hutu Ai ya k ure miki, fito maza ki ha da wutar kunun sadaka ki kuma wanke wake na k osan sadaka. Don na gayawa su Jummai wannan aikin daga yau ya dawo kan ki, wanke wanke da shara kawai za su dinga yi. Wani irin kallo nake ma Umma kallo mai cike da mamaki kamar ina tantamar zamowar Umman Mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeni. Bata bi ta kan kallon da nake mata ba ta mik e ta fice. Jikina ciwo yake matuk a da gaske amma hakan bai hana ni tashi na isa inda ta ce na je d in ba. Ba tun yau ake koko da k osan sadaka ba a gidanmu. Don haka na san duk inda su Jummai suke yi musamman kasancewata mace mai son girki. Tukunya na  dora a wuta babbar gaske mai cin kwano goma. Sannan na dinga d ebo ruwa a bokiti in zubawa sai da na zuba bokiti uku na paint. Na ha da wutar da k yar su Jummai dai suna tsaye suna kallo na da Umma ta ja kunnensu akan bata amince su taya ni ba. Sannan na koma kan wake kwano biyar na  debo don ma a surfe yake shi yasa ban sha wahala wajen wanke shi ba. Ina gama wankin waken aka yi kiran sallah. Na zame jiki da k yar na je na tada sallahr ina hawaye saboda matsanancin ciwo da jikina yake yi.

Ban bar gaban murhu ba sai k arfe goma na safe zuwa lokacin duk wanda ya ganni sai ya tausaya min, lokaci guda duk na fita daga hayyacina kamar ba Ayshan Mami ba.


Sha d aya na kwanta, bayan na idar da sallahr walaha. Barci awa guda na yi Umma ta shigo wannan karan hauri na tayi da k afa na bu de idona da k yar ina kallonta.  Uban wa zai d aura abincin ranar? K asa na yi da kaina kawai, ina jin wani irin k una da zuciyata ke yi. Sai naga ta fita kawai tana furta na baki 30 minutes ki fito ki d aura abincin. Tsabar yarda zuciyata ke suya ma bai saka na yi hawayen ba, idona kawai na lumshe ina jin wani irin tsanar Ustaz na zagaye jiki da zuciyata, duk shine Sila da bai shigo rayuwata ba da duk haka bata faru ba, tabbas ha duwata da shi ba abinda ya jawo min sai tashin hankali ya wargaza farin cikina ya wargaza na ahalin gidan mu. Wannan masifa har ina? Me yasa idan na ma aikata Ustaz ba zai min uziri ba sai kawai yazo gidanmu ya tona min asiri? Na dinga ha diyar zuciya ina jin kamar zuciyar tawa zata daina aiki. Haka na mik e ganin mintuna talatin da Umma ta bani sun cika, sauk in abin ma girkin ranar na iya gida ne kawai kuma akan gas ake yin sa. Amma ina fitowa sai Umma ta kalleni ta ce Sakwara za ki yi. Da sauri na ce  Sakwara kuma? Ta zuba min harara ta ce  Eeh pounded Yam, ita Abbanku yake so kuma dakan turmi ba engine ba&  Jingina na yi kawai da bango ina bin bayanta da kallo ina sake tambayar kai na Anya kuwa Umma ita ta kawo ni duniya?

Tun daga ranar ban huta ba, Umma jibga min aiyuka take masu yawa da suka fi k arfina. Tun ina jin ciwon jiki idan na yi har na saba ganin bata da ranar dai nawa kamar ma k ara ingiza ta ake. Na yi bak i na rame na yi wani irin lalacewa, idanuna suka shige lungu kamar ba AYSHA y ar gayun Mami ba.

Sam Umma bata barina na yi wanka sai bayan kwana biyu abinda yafi damuna kenan daga izayar da take min, don ni kam ina da son wanka a lokutan baya kafin abin ya faru na kan yi wanka Three times a day wallahi. Yanzu kuwa babu damar haka na zama kamar wata y ar fursuna tsanar yarda jiki na ya lallace don ma fatata mai kyau ce.


Rabona da na saka Abba kuwa har na manta, balle su Yaya Muhammad. Ya.Usi ne sam baya fushi da ni, ya kan zagayo duk. Dare ya mik o min d an abu a leda ko nama ko yoghurt sai dai baya min magana, hakan kuma da yake ban damu ba don na san yana bin umarnin Umma ne.


Da safiyar wata juma a, lokacin sati biyu cif da faruwar lamarin,
Ina zaune a tsakargida Jummai ce take gyara min kai, sai jin sallamar mutane na yi, ko ba a fa da ba na san wacece zuciyata ta buga da k arfin gaske don na san wacece Muryar Kakata ce da ta haifi Abba, wacce muke kira Inna. K asa na yi da kaina ina jin yarda zuciyata ke harbawa. Jummai ce ta amsa sallamar, ta amsa a ciki sai sannan na  dago na ce  Inna sannu da zuwa&  wani irin kallo ta watso min da yasa hantar cikina ta ka da na santa sarai mace ce mai zafin gaske, don ko wasan jika da kaka ita ba yi take ba, kullum girarta a tsare ta ke da k yar ta kan yi murmushi shima ba ya zarce gefen lab b anta.

Ta yi k wafa ta shige parlorn Abba ba tare da ta amsa gaisuwata ba. Umma jikinta na rawa naga ta fito daga d aki. Ta shiga parlorn Abban itama.


K walla min kiran da ta yi ne yasa hantar cikina juyawa jikina kamar mazari na mik e na shiga parlorn Abban. A gefe ba durk ushe tun kafin ma ta ce min na durk usa  din. Masifa ta cigaba da yi.  Dududu A in nawa take da za ace kun kasa bata tarbiyya, Mace guda d aya jal da Allah ya baku a ce baku san hanyar da zaku tarbiyyantar da ita ba! To dama da nazo bai saki annamimiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login