Showing 66001 words to 69000 words out of 80390 words

Chapter 23 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

132

jikinsa ina sakin wani irin wahaltaccen kuka. Shima kukan yake kafin ta janye ni daga jikinsa Naga ya juya da sassarfa ya bar wajen da sauri. Na lumshe ido na, na yi kuma saurin goge hawayen don bana son Mai tulun ya ga lagona.


Muna hawa jirgin na nemi mai tulun na rasa don ni ban sani ba ko ya shigo ko bai shigo ba. Haka kawai sai na dinga jin wani irin feeling a raina. Ga zuciyata ta na wani irin bugu kamar zata fito daga k irjina. Na dai daure na zauna a kujerar da take daf da ni. Bayan tsawon mintuna guda sai ga wani mutum yazo yana nuna min boarding pass d insa ya ce  Am sorry Madame, Seat d ina ne. Ban yi magana ba na mik e na isa inda na ga kamar nan ne nawa. Wani mutum ne cikin wasu irin k ananan kaya masu masifar kyau. Kansa sanye da p.cap ya rufe fuskarta sa bayansa jingine da kujerar jirgin kamar mai barci. Na d an bi shi da kallo kafin na tab e baki na zauna. Sai zabga k amshi yake kunnensa kuwa headphone ne a mak ale. Zama na ke da wuya aka fara sanar da tashin jirgin. Hakan yasa gaba na y a dinga fa duwa musamman ganin yarda jirgin yake kamar gargada. Ina kallo kowa ya fara fastening seat belt d insa amma ni hannu na ma rawa yake don rabo na da jirgi tun ina k arama. Ji na yi mutumin ya zura hannunsa kawai don saka min belt d in a masife na ture hannun nasa cikin bala i na ce  Mahaukaci ne kai ko na ce maka ina da buk ata? Hannu ya saka ya d auke p.cap d in fuskarsa wata irin fa duwar gaba ce ta same ni ganin Wanda nake zaune a kusa da shi& &




5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA& .59


NAZEEFAH SABO NASHE&
'?



08033748387.



Zuciyata idan banda matsanancin bugu ba abinda take yi. Na dinga ganin wani irin bak in duhu a idona. Ji na da gani na ya d auke d if. Bayan nan ban sake sanin inda nake ba sai farkawa na yi na ganni a gadon asibiti. Na bu de idona da suka min nauyi sosai na tarar da jama a birjik a cikin faffad an d akin asibitin. Dukkansu attention d insu na ga ya dawo kai na. Umma ta k araso bakin gadon da sauri. Tana kama hannuna cike da kulawa ta ce  AYSHA, me damunki? Lumshe ido na na yi kafin na dafe kaina da yake min matsanancin ciwo. Fuskar wancan mutumin kawai nake gani a idona. Tunda na fara girma na d orawa kaina son auren kyakykyawan namiji ashe ba zan samu ba. Ko kuma Allah ne zai nuna k udirar sa a kaina ta hanyar hukuntani da laifin tozarta Ustaz. Allah na tuba na fa da Wanda furucin iya busassun leb ena suka tsaya. Sake kwatantoshi da ganin surar sa a zuciyata nake. Mummuna ne sosai wallahi irin munin da kana gani zaka furta kai tsaye. Ban da munin yana da k aton baki, k aton ciki. Sai dai daga ganinsa ka San Naira ta zauna daga yarda ya baza babbar rigar shadda mai tsada. Ga k amshin turare yana ta bazawa. Kana ganinsa kaga irin mutanen nan da suka yiwa ku di taka haye ba asalin wa danda suka gada ba. Hawaye ne kawai y a fara zuba daga kwarmin ido na. Umma na ji tana Shafa min kai daidai lokacin da Abba ya ce  Humaira taje ta kira Doctor maza ta sanar masa na dawo hayyacina. Ba a d au lokaci ba Doctorn ya shigo a d an hanzarce yana duba na yana Zare robar da take Sadar da ruwa cikin jijiyata. Ya kalleni cike da kulawa ya ce  Yanzu me ke damunki? Muryata a dashe na ce  Ba komai. Don kuwa ni kaina na zance ga abinda yake damuna ba gwara kawai na ce masa bakomai d in don bashi da maganin damuwata. Ina kallo ya jinjina kai yana kallon Abba ya ce  A kula sosai, Alhaji don idan ba haka ba akwai yiwuwar ta iya samun hawan jini. Don a yanzu ma Allah ne ya kiyaye Allah ya bata lafiya. Zamu rik eta anan for 2 days zuwa abinda ya yi hali, don muga yanayin jikin nata da abinda yake damunta. Abba d aga kai kawai ina kallon yarda yake komai a sanyaye. Daga haka likitan ya fice yana sake rok on a barni na huta sosai kada a dameni da hayaniya.


Daidai lokacin mayataccen k amshin Ustaz ya cika Ilahirin d akin Asibitin. Ina kallo AYSHA ta mik e tana furta  Ustaz ya zo Umma, ga k amshinsa nan. Na runtse idona da sauri takaicin Humaira yana sake nakasta wani sashe na zuciyata wato itama ta San k amshinsa kenan.

Ina jin sallamarsa cikin Husky Voice d insa da take bayyana zamowarsa jarumin namiji.

Da sauri na runtse ido na. Don bana son a fahimci cewa ba barci nake ba.
Bayan ya gaishe da su Abba. Ina jin takunsa zuwa bakin gadon da nake, yarda yake taku haka zuciyata take bugu da k arfin gaske. Ya d an tsaya kafin ya ce  Abba ai barci take bata farka ba. Abba ya ce  Ta farka fa Ahmad, sai dai idan sake komawa ta yi. Humaira ce ta k araso don ta k asan ido na nake hango tahowarta, ina kallon kuma yarda Ystaz ya bata duk attension d insa da kulawarsa. Wani irin hawaye na ji ya zubo min a gefen ido na. Ina ji ta ce  Lah, Abba mafarkin kuka ta ke yi. Abba ya ce  Wani irin mafarkin kuka kuma Humaira ke me yasa baki da kai ne. Matsa na gani. Abba ya saka hannu y a shafi hawayen gefen ido na yana furta  Tabbas, da gaskiyarki Humaira sai dai mafarkin kuka take ba, zahiri ne kukan take. Wato AYSHA kina jin abinda Likita ya ce ko? Ba zaki cire damuwa daga ranki ba ko? To wai ma me aka Miki da y a tsunduma ki a wannan halin? Na ga dai duk abinda kike so shi muke yi Miki. Humaira ce ta ce  Abba ka mata a hankali, ba mamaki wancan abinda aka mata ne Har yanzu bai bar ranta ba. A hankali komai zai wuce. Abba ya ce  To abinda ya riga ya wuce ba ya wuce ba, meye na dawo da abu baya. Allah ya mana magani shi yasa fa nake ta lallab ata gidan Ahmad ma ban tilasta mata komawarsa ba.


Gaba d aya jin magangansu nake suna k ara harzuk a zuciya ta. Na mik e da sauri fuskata a tsuke na mayar da gashina da ya kwanto saman fuskata. Ustaz yana gefe ya zubo min ido ni kuwa wata harara na zuba masa. Madadin na ga b acin rai a tare da shi, sai naga ya saki murmushi ya ce  Aysha, ya jikin? ban ko amsa ba na shige toilet duk da ban san me zan yi a ciki ba. Amma har ga Allah kawai su d in ne bana son gani gaba d ayansu har su Abban.


Ina shiga toilet na saki kuka a hankali. Irin kukan nan me cin rai. Ba na so su ji muryata don haka na toshe bakina da d ankwalina. Don har abada na daina nuna musu karayata.

Tsawon lokaci ina cikin toilet d in da ban san me nake ba banda kuka. Har sai da na ji ana buga min toilet Umma tana kiran suna na. Hakan yasa na watsa ruwa a fuskata na goge fuskar don bana son a ga alamun na yi kuka.  Fito AYSHA ga mijinki ya zo. Shine abinda na ji Umma ta fa da wani irin tarnak in b acin rai na ji a zuciyata. Da wani irin k arfin hali na murza lock d in k ofar na fito fuskata ba yabo ba fallasa. A tsaye na ganshi da k aton cikinsa wayoyinsa manya a hannunsa. Gefensa kuma abokinsa ne me irin kamanninsa. So nake na danne abinda yake raina don na nunawa Ustaz hundred percent na amshi Mijina da hannu bibbiyu. Sai dai gabban jikina Sun k i bani ha din kai musamman idona da ya sake kawo ruwan hawaye, da gaske ko ganin mutumin bana son yi. Tuni hawaye suka fara zubo min batun bawa Ustaz mamaki ya kau. Na zauna a gefen gadon ina share ido na da handkerchief d in da yake hannuna. Ina kallo Ustaz ya mik awa mutumin hannu suka yi musabiha. Ustaz d in Naga ya kalleni sai kawai ya tab e baki ya saka kai ya fice daga d akin. Abin haushin haka duk mutanen d akin suka dinga ficewa da sauri kamar ha din baki. Mutumin da ko sunansa ban sani ba ya kalleni ya ce  Amaryata, ku gaisa da babban abokina mana.  Amaryar Ubanka&  Haka naso na furta a zahiri sai dai na kasa, sai ha diye wani irin yawu mai d aci nake. Na tsuke fuskata ban kuma gaishe shi ba, ji nake kamar na kashe shi ko na daina ganinsa balle har ya kira ni da amaryarsa mutum kamar wani basamude.  Ku gaisa mana. Ya fa da da y an muryar hassala hakan yasa na d ago na zabga masa harara. Sai na ji abokin nasa ya ce  Ka mata a hankali Mamuda, ai yarinya ce sai ka bi da ita a hankali kafin ku saba. Duk maganar duniya da suka yi na k i amsa musu ko guda ina ji gajiya suka yi suka mik e suka min sallama ha de da ajiye min bandir d in dubu guda biyu. Na bi bayansu da kallo duk a maganganunsu ba Wanda ya min ciwo kamar cewar da suka yi wai matarsa ce ta Mutu a haihuwar d ansu na biyar wato ma zuwa zan yi rainon yara. Kasa jurewa na yi na saka kuka sosai. Wannan karan ban toshe baki na ba don ban k i kowa ma ya ji ba sai me? Gwara ma su sani Da gaske ba zan auri wannan abin ba.



Kwana biyun da na yi a asibiti na yi su ne cikin wani yanayi da zan iya kira na ciwon zuciya. Hakan kuma ya kasa b oyuwa gareni. Ni ka dai na San zafin da nake ji a zuciyata. A haka dai likita ya tattara ya sallame ni don ana shirin fara biki jibi. Bikin da naji suna cewa wai har da d aurin aure na da tariya ta za a ha da, wai mijin zai wuce da ni Abu Dhabi. Inda a can yake gudanar da dukka harkokinsa. Ba irin abinda ban kissima a raina ba na son gujewa auren mutumin nan sai dai duk inda na b ulla sai naga hanyar ba mai b ullewa ba ce.


Ranar da aka sallame ni ko na ce Abba ya nemi sallama ina shiga bedroom d ina Humaira ta shigo a guje ta fa da jikina tana furta  Oyoyo My sisi an sallamoki ashe? Bari na kira Ustazu na na gaya masa& . Wata Uwar harara na watsa mata a kufule na ce  Ke bana son munafunci ki kira shi ya min Uban me? Ta marairaice ta ce  Shi fa ya ce idan an sallamoki daga asibiti na kira shi ku gaisa. Na ce  Ni kuma na ce bana buk ata, Humaira ki shiga taitayinki. Ki kuma fice min a d aki bana son hayaniya idan ba haka ba daga ke Har Ahmad d in wallahi zan ci muku mutunci. Ta wani irin waro ido ta ce  Ustazun? Na ce  Ko Ubansa ne, Munafukan banza kawai. Na kuwa shiga zuba masifa kamar zan ci Babu. Ina kallo ta fita daga d akin jikinta a sanyaye. Na bi bayanta da harara da kallon jin haushi. Bata wani da de ba sai na ji an turo k ofa. Umma ce fuskarta a ha de take kallona ta ce  AYSHA me ke faruwa ne? Humaira ta je min da wani banzan zance, wai ta lura kina son mijinki don haka ita ta fasa aurensa, da gaske ne abinda ta fa da? Kamar zan k aryata Humaira sai dai ina ga wannan ce gab ar da ta dace na gayawa Umma abinda ke damuna a hankali na furta  Eeh Ina son sa Umma. Wani irin zabura na ga Umma ta yi ta ce  Kina son sa fa kika ce AYSHA? Wani irin zance ne wannan? Gobe fa za a kawo lefe kuma goben ne kamu ta ya kike son na je na sanar da jama a an fasa da Humaira ke za a mayar d akin Mijinki, kamar fa hakan bai dace ba Aysha mu yi ta yin abu kamar wasu k ananan mutane, mutumin da yake son ki Har fa an karb i sadakinsa, shikkenan kullum a aurenki ke sai an samu irin wannan matsalar?





5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA 61.


NAZEEFAH SABO NASHE&
'?



08033748387.


UBANGIJI ALLAH YA JI KAN AHMAD ISA KOKO MAI KARATU NA RAI DANGIN GORO, ALLAH YA GAFARTA MASA YA SANYAYA MAKWANCINSA DA IYAYENMU BAKI DAYA.





Cab ko kun san wa na gani? Da sauri na sake ware ido na don son na gasgata abinda idanun nawa suka nuna min. Amma still shi d in ne dai yana sakar min murmushi idanunsa na wani kalar lumshewa. Sanye cikin kayan da suka masa bala in kyau maroum shirt da wando black. Saman kansa kuma p.cap ce. Dole zan kasa gane shi don ban saba ganinsa da irin kayan ba. Sun masa masifar kyau. Ya gyara zamansa sosai yana facing d ina ya ce  Ba mafarki kike ba, ni ne dai Ustazunki. Wani irin sanyi na ji yana shiga duka sassan jikina, bak in cikin da ya cunkushe a zuciyata ya dinga yayewa da ka dan ka dan. Hankalina ne ya dawo jikina tunanin ko dai suna tare da Humaira tunda da idona naga sanda danginsa suka zo d aukarta. Don haka murna ta ta koma ciki na ce masa  Ina Humaira? Kuma tafiyar za ku yi?  Ban ji ya min magana ba sai kusanto da jikinsa da ya yi daf da nawa na ji ya manna min wani irin deep kiss a baki. A hankali ya zare jikinsa yana lumshe ido ya mayar da kansa baya cikin husky voice ya ce  You get your answer right? Wannan ka dai ya isa ya tabbatar min Ustazu na ya dawo gare ni tunda na San ba zai tab a aikata hakan gareni ba sai da k wakwkwarar hujjar zamowata halaliyarsa. To ya aka yi haka ta faru? Shine abinda yake min kai kawo a zuciyata. Sai dai farin cikin da nake ciki ya danne tasirin tambayar tawa. Ganin yarda na saki ido da baki kamar wawuya yasa Ustaz ya bu de lumsassun idanunsa na ga ya jawo hannuna ya ce  Ko still baki yarda ba? Humaira na gidan Mijinta ni Mijin AYSHA ne. Ya fa da yana nutsar da idanunsa cikin nawa. Hakan da ya haifar da wani lamari mai girma cikin zuciyata, wasu irin abubuwa suka dinga min yawo a sassan jikina. Na lumshe ido kawai bayan Ustaz ya saka kai na a gefen shoulder d insa a kunne ya ra da min.  Na san kina son jin komai but for now ba abinda zan ce Miki is a long story ki yi barci na San kwana biyu ba kya samun barci kina kukan Humaira ta k wace Miki Miji ko? Ban ji kunya ba na d aga kai ina sakin murmushi Ustaz y a danna clip d ina da yake hab ata ya furta  Ana so ana kaiwa kasuwa.. murmushin na sake yi don bani da bakin da zan bu di ido na k aryata shi.


Na lumshe idona kawai ina hango mu a wata duniya mai girman gaske, na kasa barcin zallar soyayyar Ustaz da Muradinsa ne kawai a cikin zuciyata. Ina sake kuma jaddada godiya ta ga Allah da ya sake mallaka min shi a karo na uku bayan na cire rai da samunsa. Ko ina Mamuda mai tulun?


A zaton Ustaz barci nake don haka bai tashe ni ba, ni kuwa bakam na yi ina shak ar k amshin jikinsa cikin wani irin yanayi. Sam bana son ko kwakwkwaran motsi na yi don kada gangar jikina ta nesanta da shi. Sosai na shige jikinsa nasa shi kuma ya saka hannu cikin rigata yana Shafa baya na a hankali. Ban san sanda barci ya d auke mu ba daga ni Har shi.


Sai Asubar can k asar muka isa. Gaba d aya Ustaz ya rik eni gam a jikinsa kamar wani zai k wace ni.


Ba mu sha wuya sosai da yake tun A Nigeria aka masa booking na hotel da komai da komai. A 5star Hotel muka sauka da yake garin na Dubai. Zuciyata fari k al nake mayar da k afata duk inda Ystaz ya saka tasa. Shima kuma bai yarda ya yi nesa da ni ba yana mak ale da ni sosai a jikinsa Har muka isa D akin da muka sauka. Bedroom ne da parlor da fa dar k ayatuwarsu ma b ata baki ne, wani irin cool k amshi suke fitarwa. Gadon ya sha gyara na musamman. Gani na yi kawai Ustaz ya fa da toilet bayan mintuna ka dan ya fito sanye da bathrobe hannunsa da towel yana goge jikinsa. A gaba na ya tsaya hakan yasa na yi saurin runtse ido saboda har yau ina jin kunyarsa musamman ha duwa guda muka yi muka sake rabuwa. Hannu ya mik o

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login