Showing 42001 words to 45000 words out of 80390 words

Chapter 15 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

136

tabbatar ba, to wallahi a yanzu nima sai ka sake ni ko na maka ka a kotu& . Bakina ya bi da kallo yana d an sakin murmushi ba mamaki ganin yarda bakin yake tsiwa yake ko kuma ya d auki magana ta wasa. Don haka a zafafe na ce  Wallahi d a gaske nake, ba mai saka ni na canja abinda na yi niyya&  Ya mik e tsaye ya  dan rankwafo da kansa saman fuskata ina jin hucin numfashinsa ya manna min kiss a lab b aina duk k amshin turarensa ya bi ya baibayeni&  Har abada ba saki a auren mu, wancan ma k addara ce aure na da ke Mutu ka raba ne Madam& . Na ce  ko? Ya d aga min gira yana lumshe ido. Na yi k wafa na ce  Za mu gani. Dariya ya yi ya sake manna min deep kiss a goshi ya ce  Mu ga alheri, na lura rigima kike ji bari na tafi ga wayata zan kira na dinga jin lafiyar K alb&  na wurga masa harara bai bi ta kai na ba ya shafi kumatuna da inda ya tsole masa ido ya fita da baya da baya yana blowing min kiss& yana fita naji wani hawayen takaici ya zubo min haushinsa nake ji sosai a raina, musamman auren can da ya yi na tabbata yanzu ma can wajenta zai je, a hankali na ja tsaki na furta  Mayaudari kawai, mai k aton kai&  sai kuma na saki murmushi ni ka dai ganin yarda Ustaz yake neman saka ni na zauce. Umman Zinatu ce ta shigo don haka na ja baki ja tsuke don bana son mata magana sam, na lumshe idona kamar mai barci ina ji tana furta  Ba dai barci kika yi ba tun Mijin naki bai tafi ba. A zuciyata na ce  Almunafuk ati ban sani ba.


Tun biyun dare ya dinga kirana a wayar ina ignoring d insa. K arshe don dole na d aga wayar ganin ba zai bar kira na ba. Ina ji ya saki wata ajiyar zuciya, ya furta  Na kasa barci K alb. Zuciyata a tunzire na ce  Ko? Me zai hana ka barci bayan ga ka ga matarka& . Ina ji ya katse wayar bayan ya yi dariya sai kuma ga kiran vedio call ya shigo. Haka kawai na ji ina son sanin a inda yake wata ballagazar mata ce mai barin mijinta waya cikin dare& na d aga kiran sai na ganshi a d akin da muka sha budiri jiya.  Kin ganni, rungume da rigar barcinki mai d umbin tarihi a wajena sai shinshinar k amshin turaren jiki nake amma ya kasa kawar min da feeling d in da nake ji a raina. Jikina maha dinsa kawai yake buk ata, ga Tasleem ta ce sai na baki koda 1 month ne kin warke sosai&  k aramin tsaki na ja, ganin yarda yake wayar jikinsa ko riga babu sai wani lumshe ido yake.  Ka koma wajen matarka mana. Ya d an bu de ido yana kallo na ka dan cikin wata irin murya ya ce  Eehsha, are you jealous? Na zabga masa harara na ce  Allah ya kiyaye na yi kishinka, kawai shawara na baka ko ka manta ita ce y ar mutunci, y ar gidan mutane masu mutunci ba ni da na watsar da martaba da mutuncin iyaye na a idonka ba& . Ina kallo ya runtse idonsa ya na jijjiga kai kafin ya yanke kiran. Sai ga msg d insa ya shigo.  Idan na zo gobe, I will explain to you clearly&  na yi tsaki na cillar da wayar& ina jin haushin Ustaz ne zai kashe ni, zan jira gobe na ji da wace k aryar zai zo&


Kashegari around 10:45 Inna ta shigo asibitin kallona kawai take tana murmushi kafin su gaisa da Umman su Zinatu, Inna bata yi shiru ba sai da ta ce kuma Laraba sai al amari ya canja, wancan labari duk k anzon kurege ne, ai kuwa Ubanta ya ce ba zai yarda ba tunda ya tabbatar sharri aka ma y arsa ba abinda zai hana shi d aukan mataki, kuma nima ina bayansa Eehe, ba kunyar da baa saka ni cikin ta ba, musamman a k aramin gari irin potiskum Allah ya tsinewa Wanda ya ha da wannan kirumurmura&  Shiru Umman Zinatu dai ta yi kanta a k asa ta kasa komai, sai da Inna ta yi son ranta sannan ta ce  Ai yaran yanzu ba wai lallai sai an kawar musu da budurci ba, suna soyayyar shan minti Allah dai ya shirya mana kawai&  Inna ta watsa mata wani kallo kafin ta furta  Laraba, na ga ba alheri ne ya kawo ki asibitin nan ba, sai tsabar sharri to ha de kayanki tsaf ki bar nan wajen, tunda nema kike dole sai kin lalubo sharrin da za ki lik a mata. Umman Zinatu kamar jira take ta yi saurin fara ha da karonta ta yi mana sallama murya a cunkushe ta fice Inna ta ce Allah ya raka taki gona dama tun tana yarinya uwarta ke fama da ita akan rashin fa dar alheri& ki ga shan minti akan ki da zuri arki muguwar banza da wofi kawai. Ta gyara zaman ta tana kunce k ullin da ta zo da shi. Flask ne ta bu de sai ga kunun gya da mai zafi ta zuba min a cup d aya kwanon kuwa chicken pepe soup ne da ya sha kayan k amshi ta zuba min ta cika bowl da shi.  To maza tashi, irin wannan lalurar sai an tashi tsaye da gyara idan ba haka ba ki zama lusarar mace kina ji kina gani zaki dawo salaf ba  dand ano ko ka dan kamar kaza na dafa ta ba maggi, ah to ni dai ba ruwana sai an dage haik an da gyara da cima mai kyau sai ki ga wajen da ya raraka ya dawo. Na mik e a hankali na karb i bowl d in da cup na fara shan kunun dama ni na San Inna ba k aramin iya girki ta yi ba. Ina cikin sha sai ga Ustaz ya shigo k amshinsa gaba d aya ya gama mamaye d akin, duk da hassada ta ba zan k i fa din ya yi kyau ba, cikin black jallabiyar da take ta shinning kansa ba hula sai hirami da ya saka a kan ya d an yafa shi kamar yafen d an kwali. Kallo na yake yana murmushi kafin ya mayar da hankalinsa wajen Inna da yake zaune tana lazimi tana gyangyad i. Da sauri ta kalleshi kafin ta amsa gaisuwarsa ganin ya zauna saman gadon da nake daf ya ja hannuna yasa ta mik e tana fa din  Rasa kunya, kai yaran Zamani sai dai fatan shiriya&  Shi dai murmushi ya saki tana fita kuwa ya kwantar da kansa a jikina yana murmushi ya furta  I really missed you Baby. Na tureshi ka dan fuskata a yamutsa na ce  Ni fa ba matarka ba ce, ta mai rabo ce. Sai jin lips d insa na yi kan nawa yana gurza son ransa kafin ya d ago na turo baki na ce  wace irin mugunta ce wannan da zafi fa. Ya lumshe idonsa sai da ya kai bakinsa kunnena sannan ya ce  Bana son na ji an k ara maganar sakin nan K alb, kin san me yasa na dinga jingina ki da wa dancan maganganun bakomai ba ne kawai don Naga reaction d inki, anan zan gane za ki aikata ko baki aikata ba, Alhamdulillah irin yarda kika dinga nuna b acin ranki a fili idan na fa da Miki magana ya tabbatar min baki aikata ba&   ko? Na ce masa ina turesa daga jikina ya  d aga min kai yana saka hannu ya amshi cup d in hannuna ya kai bakinsa gani na yi ya lumshe ido ya ce  Ma sha Allah. Na yi tsaki na ce  Ka ajiye duk abinda za ka ce ba zasu yi tasiri a wajena ba, da gaske saki nake so&  Shiru ya yi yana cigaba da Shan kununsa bai kuma damu ba don sai sakin murmushi yake. Har ya gama sha tsaf ya mik e yana lakace min hanci ya ce  Rigimaty, Am leaving, don naga yau a kusa kike bari na tafi Neman na kai, ki adana rigimarki ba yanzu ba sai second night, ban sani ba ko a lokacin zata Miki amfani&  Daga haka ya bani feck a kumatu ya fice da baya da baya kamar yarda ya Saba. Lumshe ido na na yi kawai ina murzar goshi na a zuciyata kuwa tunani nake Ustazu ya gama mayar da zancena wasa.


Ana idar da Sallahr azahar, Inna tana zaune tana lazimi muka ji nocking na amsa da k yar da cewa Come In& Matar ta shigo sanye cikin dogon hijabi fuskarta sanye da nik ab. Kallo na bita da shi ina son sanin wacece. Har ta iso gado na bata cire hijabin ba bayan ta gaishe da Inna da itama ta bita da ido. Sai da tazo bakin gadon nawa sannan ta d aga nik ab d in. Ta d an sakar min murmushi. Da k yar na mayar mata don ban Santa ba, kamar ta shiga zuciyata sai Naga ta ajiye kwandon abincin a gefena ta ce  Ga sak on da na kawo na San baki sanni ba, bari na baki wayar ki ji wacce ta aiko ni. Ta latsa wayarta sannan ta kara min a kunne, muryar Mami na na ji tana furta  5?h?5ؚ?5ؔ?5؉?5؂?5ؕ?5ؐ?5ؖ?, ya jikin? Ga sak o nan na bayar a kawo miki, ki tabbata naman ke kika cinye ko romo ba a san wani ya lasa, shi yasa na sako a roba daban pls kada ki wasa da shi zaki gan shi a roba mai blue murfi d aya mai Jan murfin kowa ma zai iya sha, ki kula sosai Allah ya bada lafiya&  Kafin na ce komai ta katse wayar. Jiki na na rawa na kalli matar da ta bu de basket d in ta Ciro exactly robar da Mami ta ce ta saka min a cinya a hankali ta ce  Maza ki cinye, don umarni ta bani kada na matsa ko nan da can sai kin gama tas, na tafi mata da robar& . Jikina ba inda ba ya rawa duk na shiga ru dani& .



5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?




A yi hak uri Kakata ce ta rasu, shi yasa gobe da jibi ba zan yi
Posting ba wannan ma don kada ku ji shiru ne. Kuma already ina da shi a k asa. Na gode sosai da adduoinku gareni Allah ya saka da alheri=?L?
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa >?p?: Wani irin Sarawa kaina ya yi, sarawar da na ji shi Har tsakiyar k wak walwata na runtse idona ina jin jiri na d ibana. Tunani na guda menene wannan yaushe na aikata wannan abin da ko a mafarki ban san zan iya rik e bindiga ba. Amma yau gani dumu dumu rik e da bindiga. Kasa motsin kirki na yi don bani da k arfin da zan iya motsa koda gashin idona ne balle wata gab a ta jikina. Ina ji suka sanya min hand cuffs suka tasa k eyata zuwa motarsu ta shiga ba biya fita da Allah ya isa. Da jiniya sosai muka bar cikin harabar gidan. Tuni zuciyata ta cunkushe waje guda. Bana iya tunanin komai sai na dama Allah ya d au raina na huta da irin wannan rayuwar daga wannan masifa sai wannan, me yasa? Ni dai na San koda wasa bani ba ce a jikin Hoton nan Amma na San ko zan Mutu ina rantsuwa ba yarda za a yi ba. Tsabar tashin hankalin da nake ciki yasa ko k walla babu a idona illa iyaka idanun nawa Sun fito waje.


Muna zuwa Office d in y ansanda suka tasa ni a gaba da tambaya. Tambayoyin da suka dinga saka zuciyata wani irin harbawa da k arfin gaske. Har ban San sanda na runtse idona na furta  Ko ke ake tuhuma ta ni na aikata a yi min hukuncin da ya dace&  Tsit station d in ya yi ina kallon Yaya Usman da su Abba suka runtse idonsu. Sam ban damu da tashin hankalin da suka shiga ciki ba damuwata a yanzu bata wuce ta barin duniya ba. Na gaji da rayuwar gaba d ayanta. Dpo ya k ura min ido ya ce  Kika ce ke ce kika aikata? Na d aga kaina kawai ba tare da na yarda na kalleshi ba. Ya ce  To ina sauran y an uwa naki su bakwai da aka ce tare kuka aikata? Na datse leb ena da k arfin gaske na ce  Ban San inda suka tafi ba&  ina kallo ya yi rubuce rubucensa yana kallon wasu y an sanda mata guda biyu ya ce su je da ni su tuhumeni sosai na fa di inda sauran y an uwa na suke. Suka kuwa ingiza k eyata muka tafi. Tambayar duniya da izayar duniya ba wacce basu min ba Amma na ce ban San inda suke ba. To ina zan sani tunda su kansu ban san su ba, asalima ban tab a ganin fuskarsu ba, ban sani ba ko Aljannu ne suke siffata su aikata son ransu. Ba yadda za a yi na yarda Biladama ne, saboda idan ana kwaikwayar fuskar mutum, ba ta yarda za a yi a kwaikwayi komai da komai na jikin mutum ace hatta da farce ba banbanci. Abu d aya da na tambayi kaina, me na yiwa Wanda ya min wannan sharrin da yake son ganin baya na? Aka ajiyeni a cell cikin kyakykyawan matakin tsaro da ba a barin kowa ma ya ganni. Ina ji Dpo na yiwa Abbana bayani  Alhaji ba Wanda zai sake ganinta sai ranar shari a, ku nemar mata lawyer kawai. Ina kallo Abba da Yaya Useey suka saka hannu suka share k walla suka bar wajen. Na ji wani irin Abu ya tsaya min a mak oshi. Tun daga ranar kuwa ban sake ganin kowa ba har tsawon kwana uku kafin zuwan lokacin kuwa na ji gata sosai, jigatar da ta bayyana har a saman idona. Ranar ina zaune a d akin mai duhu sosai na dinga Jin murya kamar ta Ustaz tana dumfaro d akin. Ina Jin muryarsa sama sama yana furta  Wallahi, idan ba a sameta da laifin komai ba, sai na yi shari a da Dpo d inku& matata za a tozarta don wulak anci kuma ance mutumin da ake zaton an kashe d in ma bai Mutu ba, to saboda me ba zaku saketa ba? Ban ji amsar da wancan ya basa ba, naga dai an bu de k ofar Ustaz ya shigo tun daga fuskarsa har gangar jikinsa Sun bayyana tsagwaron tashin hankalin da yake ciki. Idanunsa tuni suka ka da suka yi jajur. Ya fara cizon leb ensa yana k arasowa inda nake, ya zube a gabana murya a sark afe ya ce  Ke ce a haka K alb? Kuka yake sosai ya kama hannuna ya ce  Sai jiya labari ya isar min wai an kulleki a station, how come Aysha da gaske ke ce a jikin hoton? Na runtse idona tunda abin ya faru sai lokacin naji kuka yazo min Amma na yi dakiya na share na k i kukan muryata a raunane na ce  Idan ka yarda nice a Hoton shikkenan ba abinda zan ce sai ni na aikata su yi min abinda ya dace Ahmad&  Murzar hannuna kawai yake ya kasa furta komai sai huci da yake furzarwa goshinsa sai fitar da zufa yake, ya ce  I wish I was dreaming& .. bana son wannan abin ya zama gaskiya, kin fita ne da ba nan? Ban amsa ba illa rufe idona da na yi kawai ina kokawa da numfashi na da naji yana fita ba daidai ba& Ustaz muryarsa a k asa ya furta  Stop it Aysha! Na yi alk awarin ko duka dukiya ta zata k are sai na wankeki daga wannan laifin& . Zan kuma tsaurara bincike har sai na hango waye ya Miki wannan sharrin&  Da sauri na girgiza Kai na ce  Ba na so Ahmad, ka bari kawai su min duk abinda ya dace, ba Wanda zai ce ba ni ba ce a jikin hoton nan don haka wahalar da kanka kawai zaka yi&  Kuka na saki sosai, kukan da tuntuni nake son yinsa bai zo ba sai yanzu& na dinga kukan har Ahmad ya jani jikinsa bai damu da dau dar da take jikina ba ya manna min Hot kiss Wanda hakan yasa naji zafin zazzab in da jikinsa ya d auka& Da k yar ya cikani sanda aka zo aka ce lokaci ya cika. Ya harari d an sandan sai kuma ya mik e yana tsane hawayen da suke zuba masa a ido. Na bi bayansa da kallo hawayen na cigaba da yi min suntiri a idona. K irjina ya min nauyi sosai kamar an saka min block ten inches a kaina.





ZAMAN KOTU (COURT)& .


Kaina a k asa yake saboda na kasa yarda na ha da ido da dandazon jama ar da suke zube a court d in. Hannayena duk a gark ame da handcuffs. Lawyoyi ne birjik a gaban court d in sai a sannan nake jin ma mutumin da aka kusa kashewar aka kwashe musu American dollars wai Minister ne.


Shigowar Alk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login