Showing 12001 words to 15000 words out of 80390 words

Chapter 5 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

150

addara ta samu jinina ashe Mariya ba mai iya rufa min asiri ba ce? Jikanta take cewa ba zai auri Jikata ba wani irin Zamani muke ciki?  Irin wanda Manzon Allah ya bamu labarin zai zo, don haka ki saka a ranki ba lallai yarda zuciyar ki take ba ta kowa ta zama haka fak at! A yi addu ar Allah ya kawo mata Miji na gari kawai. Zuciyata ce take wani matsanancin bugu wai ni yau Ayshah ni ake talla da ni ana k in aure na? Wace irin k addara ce wannan tabbas jarrabawar nan zata min wuyar answer don ina jin karaya tun daga zuciyata har gab ban jikina& .




5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA 29.

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.



&&
'?

Umma ta juya ta fita ta bar d akin ba tare da ta sake min second look ba. Jikina a sanyaye na mik e na bi bayanta ina fatan duk da abinda za su zo min yazo min da sauk i.

Sanda na yi sallama duka a ciki suka amsa min sallamar. Fuskarsu a mutyuke musamman Baffa Mutari sai ka rantse da Allah bai tab a dariya ba. Ina zama Baffa Mutarin dai shi ya fara magana muryarsa a kaurare ya ce  Ke duba nan, duk nan kin san ba abokin wasanki ba kuma sa anki ko? To ki bu de kunne ki ji da kyau abinda za mu gaya miki, bana son wasa da hankali kuma, a ina zamu samu abokin shai danancin ki? Abu na gaba mun yanke hukuncin aurar da ke da zarar kin gama iddar da ta zama dole a kanki, duk da shi ya ce bai d ora miki idda ba sai dai mutane ba su san wannan ba& ba zaki mayar da mu mutanen banza ba, kina ji ko? Jikina a sanyaye na  d aga kai. Ya girgiza kai yana yin k wafa ya ce a haka kamar wata mutuniyar kirki, ki gaya mana a ina zamu samu wancan mutumin banzan? Hawaye ne ya fara son zubo min na yi k arfin halin hana shi zubowa. Wata tsawa da ya saka min ban san sanda na runtse ido ba na furta  Zan fa da wallahi. Baffa Yahya ya yi wata dariya ya ce  Kin ceci kan ki don wallahi da ba ki fa da ba yau idan na dinga dukanki a gidan nan sai kin kasa tashi. Wani irin huci suke fitarwa hakan ya sake tsorata ni a hankali na ce  Wallahi Allah ban san shi ba& "  wani irin mari Baffa Yahya ya kai min suka cigaba da zagina. Ni dai ina durk ushe ina zubar da wasu irin hawaye ina kallo suka gama ci min mutunci suka fice. Na mik e tun kafin Abba ya bani dama na shige d akina cikin rawar jiki da bugawar zuciya.



Haka rayuwa ta cigaba da gargara min, wasu abubuwan tuni na saba da su yayin da wasu abubuwan har a kullum sake firgita ni suke yi. Ta gefe guda na samu sassauci a wajen Umma da Abba suna amsa gaisuwata duk da dai ba sakin fuska a tare da su. Yayyena ma su kan d an kula ni ka dan. Hakan ya saka na d an samu sauk in zuciya. Sai dai ba dama na fita an dinga zun dena kenan a cikin unguwa hakan yasa na rage fita. Dama ba Bari na fitar ake ba Umma dai ta daina gallaza min da kaso talatin cikin d ari. Hakan yasa na d an samu nutsuwa ta wani b angaren.



Wani dare Abba ya dawo tun daga yanayin yarda yake tafiya na san ba lafiya ba. Kamar jiri yake ka dan fuskarsa ba walwala ko ka dan. Na masa sannu da zuwa ya  dan amsa min yana d auke kai na karb i ledar hannunsa shi kuma ya shige cikin sasansa. Ina zaune a tsakargida Umma ta fito tana kallo na ta furta ki je In ji Abban ku. Da sauri na mik e duk da zuciyata ta yi wani irin bugawa na isa wajen Abban.


Yana zaune idanunsa akan t.v ya zuba ido yana kallon labarai. A gefe na durk usa nima ina kallon t.v  din ba tare da ya kalleni ba ya ce  Ki je waje zaki gana da bak on da na zab a miki a matsayin Miji, kada kuma ki sake ki bujircewa Umarnina a yayin da idanunki suka yi tozali da abinda bai gamsheki ba&  Zuciyata ce kawai take bugu na mik e jikina a sanyaye ina tunanin waye Abba ya zab a min a matsayin Miji, sai dai ina tunanin koma waye zan jure zan kuma yi biyayya na amsheshi da hannu biyu ba don komai ba sai don na faranta ran Abba.


Ban koma d aki ba da dogon Hijabi na na fita harabar gidan. Ba kowa a harabar daga Idi mai gadi sai Tanimu driver. Isa wajensu na yi ina furta  Sannunku, don Allah ina wanda ya zo wajena. Sai na ga Tanimu ya mik e yana washe baki, ya furta  Ai ba wani ba ne Hajjaju ni ne&  Cak na tsaya ina kallonsa sanye yake da koriyar shadda da hula orange sai yage hak ura yake kamar me, babu aji sam a tare da shi, ni da nake son mutum d an gayu miskili mai ilimi mai iya soyayya da kalamai masu kwantar hankali ta ina zan iya da Tanimu? Na dinga cijar leb ena ba tare da na san ina yi ba. Ya kuwa cigaba da gyara tsayuwarsa yana furta  Anan zamu tsaya ne Hajiya Aisha, akwai maganganun da nake son na rattabo miki& . Samun kaina na yi da tafiya da baya da baya ina girgiza kai na. Hawaye kuwa suka fara zuba kamar famfo& ina ji Tanimu na kira na sai dai nan tsaya na saurareshi ba na shige cikin Gida da sauri. Karaf na ji na yi karo da mutum& da sauri na ja baya ina mayar da numfashin da naji yana min wuyar fita kamar ana shak e min mak ogwaro. Da sauri na ji Yaya Usman ya rik e hannuna yana furta  Nutsu Aysha menene me ye ya baki tsoro haka? Hannuna na saka na dinga nuna masa waje sai dai baki na ya kasa furta abinda nake son fa da masa. Gani na yi kawai ya ja hannuna mun nufi cikin gida. Sai da muka isa d akina ya zaunar da ni, sannan ya tsiyayi ruwa a cup ya saka min a baki. Ruwan na sha sosai kafin na saki ajiyar zuciya ina kallonsa na lumshe idona hawaye yana zubo min daga ido na ce  Yaya Usman wai Tanimu Driver Abba ya bawa aure na. Wallahi Yaya Usman wannan karan ba zan jure ba, da na auri Tanimu gwara na bar gidan nan na bi duniya ka& . Da sauri ya saka hannu ya rufe min baki, yana furta  A uzubillah!!! Kina da hankali kuwa AYSHA kin san abinda kike fa da kuwa? Ba kya cikin hayyacinki ko? Ki nutsu ki min magana yarda zan gane, waye ya ce miki za ki auri Tanimun? Cikin shashshek ar kuka na ce masa Abba ne Abba ne da kansa ya ce ya bashi aure na&  Yaya Usman ya zaro ido ya ce  Ah haba wallahi wannan karan hakan ba zai yiwu ba, ko kisan kai kika yi Ai sai haka? Akan wani dalili ina matching a aurenki da wani Tanimu? Ina zuwa zauna anan yanzu zan dawo&  ya fita da sauri duk ransa a b ace binsa na yi da sauri na rab e a jikin windown parlorn Abban ina jin abinda Yaya Usman d in yake fa da. Ina ji Abban ya amsa sallamar yana furta  Usmanu yaya dai? Yaya Usman ya gyara zama ya ce  Abba wata magana na ji AYSHA ta gaya min, wai ka bawa Tanimu aurenta, Haba Abba Ai abin zai yiwa AYSHA yawa, sam babu matching a ha din, Abba ka yi tunani da kyau, Tanimu mara ilimi AYSHA mai ilimi Tanimu d an k auye Ayshatu y ar birni, Tanimu marar wayewa AYSHA mai wayewa, ta ina wannan ha din gambizar zai hadu fisabilillah, Haba Abba ku tausaya mata don Allah dama itace namijin shi mace sai a ce ha din zai tafi don Allah Abba ka yi hak uri kamar hukuncin ya yi tsauri da yawa&  wani murmushi na ga Abba ya saki ya ce  Ka gama Usmanu? Na ce ka gama? Duk na ji abinda ka ce abu guda da ka manta baka fa da ba a banbancin na su shine Ayshatu y ar iska Tanimu kamilalle, ashe ba Tanimun aka cuta ba da za a lik a masa ragowar wani? Idan ba mu godewa Tanimu ba bai kamata mu tozarta shi ba, don haka maganar aure babu fashi fak at bana son na sake jin wata magana bayan ta ta amince da zab i na, idan ba haka ba d aga kai Har AYSHA wallahi za ku har gidan nan&  wata irin harbawa zuciyata ta yi da sauri na bar wajen cikin matsanancin tashi hankali.



A daren ranar dai ban sake ganin Yaya Usman ba, yarda na ga dare haka na ga rana zuciyata ba abinda bata sak a min ba na aikata sai dai na kasa yarda na gudu na bar gida. K arfe shidda n???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a safe Yaya Usman ya shigo d akina yana kallona ya ce AYSHA tashi& Tashi tashi mu tafi potiskum don Abba ya rantse a gobe zai d aura miki aure da Tanimu da zarar manema auren sa sun zo& ki tashi ba mu da lokaci& . Wani irin kallo nake masa ido na ko blinking basa yi tsabar ka dawa da zuciyata ta ke. Ji nake kamar wasu abubuwan basa aiki a Gangar jiki na& AURE DA TANIMU? Shine abinda zuciyata take ta nanata min&






5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA 28.

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.



A razanen ta cigaba da nuna ni muryarta na rawa ta furta  Sharrin da za ki min kenan Aysha, wallahi k arya take Sam ba ni ba ce a jikin hoton nan kuma ba ni da alak a da duk wani abu da ya shafi hoton&  Bori na hau yi Anty Khadija na rirrik eni na hau nuna su ina fa din wallahi su ne, na gaji na gaji don me za a dinga jingina min laifin da ba nawa ba ne,Hakn ya isa! Ya isa!! Ya isheni!!! Runguma sosai Anty Khadija ta kai min ta saka hannunta ta toshe min baki. Ki yi shiru Aysha Allah yana bayan mai gaskiya kuma tabbas shi zai saka miki. K ananan maganganu ne suka cigaba da tashi a d akin kowa yana fa dar duk kalmar da yaga dama a kaina. Umma dai na tsaye tana bin kowa da ido. Zannira ta turo baki.  Ah to yarinya kada ki sake kama suna na, abin kunya ne dai kin janyowa familyn mu, kuma kina nema ki lik a mana, nan kika dinga kwanaine kina hura hanci wai ke za ki auri mai ku di ke da ake gani kamilar mace ake murnar ta samu Miji d aya tamkar da dubu sai ga shi kin ba dawa iyayenki k asa a ido an tashi ba wan ba k anin abinda Bature ke kira 2-0&  Kowa na  d akin cike da mamaki ake kallon su Zannira jin irin kalaman da suke fita daga bakin su. Umma dai tana tsaye idanunta sun ka da sun yi wani irin jaa. Anty Khadija ce ta kalli Zannira da Zaituna a zafafe ta ce  Ah to lallai ta bakin AYSHA akwai lauje cikin na di a cikin wannan habaicin da kuke zubar wa, ashe dai tabbas hassada da bak in ciki kuke mata, idan kuwa ya tabbata hakan ne ba abinda ba zaku iya aikatawa ba wajen son ruguza maganar auren, don haka dole an bincike ku ku fa di gaskiya don ba k ira ba abinda zai kawo gawayi& . A zafafe Umma Sa a ta ci burki a gaban Anty Khadija ta nuna ta da yatsa..  Kada ki fara Khadija, kada ki sake ki jawo mana waruwar kai a cikin dangi, mu kan mu a ha de yake abinda bahaushe ke kira tsintsiya mad aurinki d aya don haka ki cire hasashenki akan su Zinatu me ye ribarsu idan suka yi silar waruwar auren AYSHA? Bu de baki Anty Khadija ta yi zata yi magana Umma da ke tsaye ta furta  Khadija ya isa! Kada ki sake magana, idan ma abinda kika fa da d in gaskiya ne Allah zai bayyana cikin girma da d aukakarsa&  Shiru Anty Khadija tayi tana mayar da numfashi hawaye na zuba daga idonta, sai dai bata sake maganar ba duk da irin maganganun da suka cigaba da tashi na mita da habaici. Ta yi shiru kawai her face looking so worried. Jan ajiyar zuciya kawai take tana buga baya na. Tsit da d akin ya yi ne ya sata mik ewa tana kallo na, ta furta  Ki yi hak uri AYSHA Allah yana bayan mai gaskiya, zan yi shiru da wannan maganar amma anan kawai ba don komai ba sai don bana son yin jayayya da umarnin Umma, amma zan gayawa Yayanki zaku ma mu cigaba da bincike ta k ark ashin k asa amma tabbas zato na akan yaran nan yake.. Na girgiza mata kai. Ta fice daga d akin bayan na tabbatar ba zani wajen kai lefen ba. K una zuciyata kawai take da wani d aci da nake ji a mak ogaro na.

Ina ji duk aka fice kai lefe. Ya zama gidan ya yi wani irin shiru. Ina kwance idona a lumshe na ji maganar Umma a kaina.  Ke ki zo in ji Abban Sadik. Ido na na bu de ka dan ina kallonta cikin dishi-dishin hawaye na. Itama kallon nawa take sai naga ta juya ta fita daga d akin. Da k yar na mik e saboda matsanancin ciwo da kaina yake. Na yafa mayafi na fita kiran da Abba yake min.


A zaune yake fuskarsa sam ba walwala, ba mamaki Umma ta gaya masa duk abinda ya faru. Gefe ya nuna min bayan ya amsa gaisuwata murya a hankali ya kalleni ya ce& .  Me yasa kike zargin su Zinatu da duk abinda ya faru? A hankali na yi k asa da ido na ina wasa da hannu na.. Magana nake miki. Ya fa da wannan karan muryarsa a sama ka dan.. shashshek ar kuka na fara yi ina furta  Nima ban sani ba Abba, kawai ina tunanin zasu iya aikata min hakan daga yanayin kalamansu a kai na. Ido ya k ura min kafin ya ce  Wasu maganganu suka gaya miki? Tsaf na kwashe na gaya masa, sai naga ya yi shiru, idanunsa sun yi wani irin jaa fiye da na Umma. Murza hannunsa kawai yake kafin ya ce  Akwai inda kika je da su ne a satin bikin ki? Da sauri na d aga kai na. na ce Eeh Abba akwai, na je gidansu har ma na yi barci a can, mun je kuma gidan Anty Falmata da wasu gidajen na cikin dangi. Shirun ya sake yi tsawon mintuna biyar kafin ya furta  Tashi ki tafi ki ba ni wuri, Allah ya bayyana gaskiya. Tunda abin ya faru yau ne kawai Abba ya min magana cikin kwanciyar murya. Sai na ji wani abu ka dan ya gushe daga b acin ran da yake cunkushe a zuciyata.



Tara na dare na jiyo Yaya Usman ya shigo gidan da sauri na mik e na nufi har sashensu don tun yamma nake jiransa am eager na ga ha du da shi.


A parlorn dukkansu suke zaune, Ya Usi Ya Umar da Ya Ali. Na gaishesu suka amsa fuskar ba yabo ba fallasa. Ya Usi kam da fara a sosai ya tare ni. Ya ja hannuna ya zaunar da ni gefensa yana furta  Ya aka yi AYSHA gayu? Koda yake yanzu wannan sunan tsaf ya tashi daga kan ki, duk kin bi kin sukurkuce kamar ba Ayshan Mameey ba&  murmushi kawai na yi ina tuna Mamee a raina. Na ce  Dama murna na zo maka Yaya Usi, duk da dai baka sani a cikin lamarin ba, congrats to you and am happy for you& . Na fa da wata y ar k walla na son zubo min. Kama hannuna ya yi yana furta  Okay Okay na gane, mu je d aki mu yi maganar har ma na nuna miki hotonta. Ina mik ewa muka ha da ido da Ya.Umar sai na ji bakina kawai ya furta  Congratulations Ya Umar.. Hannu kawai ya  d aga min ina ji Ya.Ali ya zabga tsaki.


Muna shiga na zauna gefen kujera ina kallon hoton da yake mik o min. Yarinya ce k arama ba zata zarce sa ata ba.  Ma sha Allah, gaskiya ta yi ina tayaka murna once again, duk da dai baka saka da ni ba. Hannuna ya matsa yana furta  Am sorry Aysha kwana biyu kin ga bana damuwa nazo inda kike, wallahi zuciyata bata iya wa tausayi kike ba ni, ina so ki tsaya ki nutsu ki ajiye zuciyarki waje guda ki yi aure, da zarar na yi aure zan mayar da ke can waje na, don naga duk gidan nan ba mai tausaya miki na yi magana da Abba akan ya barki ma ki cigaba da karatu ya nuna min sam ba zai yiyu ba, Miji ma yake nemar miki ya miki aure tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login