Showing 15001 words to 18000 words out of 80390 words

Chapter 6 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

142

kafin mutane su farga da abinda kika aikata, although dai maganar duniya bata b uya..Wallahi AYSHA da tunanin matsalarki nake kwana nake tashi, ga shi shi kuma shegen an ce har yanzu bai dawo garin ba, bari mu tuntub eshi mu ji ko biyansa aka yi don ya b ata miki suna.

Murmushi na saki, irin murmushin da na da de ban yi irinsa ba, jin abinda Ya.Usi ya ce da gaske shi ka dai ne mutumin da zan bugi k irji na ce ya yarda ban aikata ba. Ya saka hannu ya share min hawayen da suke zuba a idona duk da ni ban san zubar su ba saboda har ga Allah murmushi nake. Murmushin na sake yi ina kallon cikin idonsa na ce  Ya.Usi na gode sosai da kulawarka gare ni ya sunan amaryar tamu?  Sadiya ya furta yana lumshe ido.  And I love her very deeply& . Murmushi na saki ina ajiyar zuciya a hankali na tuna Ustaz da dukkan kalamansa ashe akwai abinda zai saka Ustaz ya rabu da ni, ko wai wayata bai sake yi ba tun bayan afkuwar lamarin nan, ashe duka soyayyar Ustaz a baki take. Na girgiza kaina kawai kafin na mik e na bar cikin d akin saboda kukan da ya taho min& .


Da safiyar wata laraba ina zaune a d akina sai ga sallamar Asma k awata. Da wata irin murna na tareta. Ita kuwa hawaye naga ya fara zuba daga idonta. Ta saka hannu ta ja hannuna muka fita harabar gidanmu.  Zo mu je AYSHA, zo mu je kada Umma ta fito ta gan ni ita ta hana ni zuwa duk sanda nazo sai ta ce na tafi kawai.. Na bita muka fita harabar gidan mu. Hawayen kawai take ta kasa ce min komai. Sai da na girgiza ta na ce  Wai Asma u meye haka zuwa kika yi ki sake d aga min hankali? Girgiza kai ta yi tana rungume ni a jikinta ta ce  AYSHA Ustaz ya ci amanar soyayya wallahi, abinda ya miki bai kyauta miki ba, ni fa ban san me ya faru ba sai jiya Umma na take gaya min wai an fara zagaya unguwa da cewa da wani k ato Ustaz ya kama ki ranar auren ki. Waro ido na yi zuciyata na bugu na ce  Waye ya fa da Asma? Ta sake runtse idonta hawaye na zuba a idonta ta ce  Ba wanda bai ji ba AYSHA zancen nan har Islamiyya wallahi& . Tunda abin ya faru sai yau hankalina ya sake masifar tashi jin ashe zancen ya isa har Islamiyya wajen Malaman da suke ganin mutunci na.  Ki gaya min Aysha ya aka yi kika canja daga Ayshan da na sani? Runtse idona kawai na yi ba tare da na mata magana ba, don bana jin zan iya furta ko kalmar  a saboda rawa da dukkan jikina yake yi&  na mik e dai na shige cikin gida a cikin wani irin yanayi da ni kai na ba zan iya cewa ga yarda na kai kaina d aki ba.



A yammacin ranar still ina kwance, Umma ta lek o ta ce  Ke ki zo in ji Abbanki da y an uwansa&  wani irin tsawa na ji kaina ya yi don ban san da me suka zo ba& Kai NI AYSHA NA GA RAYUWA INA KAN GANI MA& .





5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5?+?5??5?0?5?%?5?"?&
'?[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa >?p?: https://chat.whatsapp.com/EuW3Jn8UkDrJudA1ThiH23

Kina buqatar kayan kitchen Masu kyau da rahusa?
Kina buqatar inda zaki dinga samun kaya Masu quality?
Uwar gda Amarya Duk ku tawo =؃?
Quality shine takenmu =?;? Muna maraba da masu sayan daya ko sari =?o?
B&? Muna tura kaya ko ina da yardar Allah cikin Aminci=?;? muna zauna a garin Kano cikin kwaryar birni=?o?
B&? masu sayan kayanmu Mina godia=?o?
B&?



NA GA RAYUWA& 31.

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?

08033648387.



&&&


Ina ji Alhaji ya ce  Amma daga yau maganar Miftahu ta kau? Inna ta ce  Ta kau mana, ba dole ta kau ba tinda kakarsa ta nuna bata so, sai a yi addu ar Allah ya bata mafiyinsa, ita kuma tata jarrabawar kenan..

Tsawon sati na yi a asibiti kafin a sallameni, saboda likitan ya CE dole a bani kulawa ta musamman don jini na ya hau ka dan. Ranar da aka sallameni muka koma gida Inna ta dinga kula da ni sosai tana k ok arin Kawar min da b acin ran da nake ciki. Hakan yasa na samu nutsuwa na yi wani fresh tas da ni ba abinda ke damuna sai d an abinda baa rasa ba.

Sai dai wani abu da yasa na tsani zaman garin, sai aka fara yama di di da ni har da masu cewa cikin shege na yi a Kano shine aka dawo da ni nan. Abinka da k aramin gari tuni labari ya kewaye lungu da sak o aka fara shigowa kallo na. Inna kuwa ba dama ta fita sai a yi ta nunata wannan shi ya tashi hankalin mu da na Inna ta gayawa Alhaji Kano zata mayar da ni, don anan kam duk wanda yazo neman aurena ma gulmar da mutane zasu kai masa ba zai bar shi ya aure ni ba. Alhaji ya jinjina kai ya furta  Sharrin k aramin gari kenan, mayar da ita d in shine mafi alheri gaskiya, can birni ba lallai wani ya samu labari ba ma, nan kuwa madadin ta samu nutsuwa sai ta sake firgicewa, amma ki jawa Uwarta kunne ta san irin abinda zata saka ta, don wahalar da take bata ta yi yawa abu sai ka ce a gidan gyaran hali. Sanda Inna ta gaya min zata mayar da ni Kano ban wani damu ba, don ni kai na zaman garin ya fara isata ba don komai ba sai don kallon da mutane suke min na matsayin Karuwa! Na ha da y an kayana na bawa mai aikin Innan don dama ba wasu kaya ne masu yawa ba. Kwana biyu tsakani kuwa muka taho Kano.


Inna ta saka Umma a gaba da nasiha akan ta sassauta min, wannan k uncin da gallazawar ba shi zai gyara ni ba sai ma ya k ara tab arb ara ni, ki nutsu Kubra ki ja y arki a jiki ki san matsalolinta tun farko ke kika yi saken da kika nesanta kan ki da ita har ta fa da wannan halin garin kawaicinki na banza da wofi&  Umma ta jijjiga kai murya can k asa ta furta  In sha Allah Inna. Shikkenan na samu sassauci har ma na dawo sashen Umman da kwana cikin d aya d akinta da bata amfani da shi sai sauke bak i. Da farin ciki na gyara d akin na kuma dawo da duk wasu tarkacena da suke sashen Mammy na. Sai ga shi ya fito tas. Daga ranar kuma Umman ta rage hantarata ko saka ni aikin mai wuya. Na so na koma Islamiyya sai dai ban san da wani ido zan kalli Malaman ba. Hakan yasa na hak ura Umma take biya min karatu tunda ita tayi ilimin addini sosai. Fita ce dai ban isa na fita ko nan da waje ba, hakan yasa na sake wani shegen kyau fata ta tayi fresh sosai.


A cikin wannan yanayin aka fara shirye shiryen bikin su Ya.Usman shi da Ya.Umar. Bikin ya rage saura sati guda don haka gaba d aya hankalin Umma ya koma kan bikin. Nima ina ta shiri na na bayar da d inkuna na. Umma dai ba wani sake min fuska take ba duk da dai bata gallaza min. Kullum su Yaya Muhammad da matansu sai sun zo gidan jin tsare tsaren biki. Yau ma tun bayan magriba suka zo. in daga cikin d aki na ji Muryar Anty Khadija tana cewa  Wai Umma AYSHA bata nan ne? Naga kullum idan muka zo ba ma ganinta. Na kuma lek a d akin tsakargidan nan ma bata nan. Ina ji Umma ta yi shiru sai kuma na ji ta ce  Tana cikin d aki, ni na hanata fitowa cikin mutane tunda dangi suna yawan zuwa bana son ta jawo raina ya b aci. Na lumshe ido kawai ina daga cikin d aki ina sakin murmushi. A.Khadija ta ban ka da labulai ta shigo, idonta a kaina ina aikin taje gashin da ya bi ya dameni Saboda tsabar yawansa da tsaho. Ga shi na da de ban yi saloon ba. Baki ta bu de tana kallona tana dariya  Ah! Lallai AYSHA kin samu kan ki dole ki manta da ni, irin wannan kyau da kika yi haka? Turo baki na na yi ina furta  Wani kyau kuma? Ni da ko man arziki Umma ta hana ni shafawa ta hanani saka ko kwalli. A.Khadija ta saki ajiyar zuciya tana karb ar comb d in hannuna ta ce  Wallahi kin yi kyau AYSHA fiye da zatonki, ko don dama can ke mai kyau ce.. Ta taje min kan tsaf ta kama ta tufke, sannan ta jawo babbar ledar hannunta  Tashi kiga Kayan bikin da na siya miki. Ido bu de nake kallon ha daddun kayan di nkuna masu kyau na zamani. Ban san sanda rungumeta da k arfin gaske ba. Itama dariya ta yi ta rungume ni. Na kwashi kayan na fita da su parlor wajen Umma. Kayan Umma ta Kalla Kafin ta kalli Anty Khadija ta ce  An gode k warai Khadija, amma da baki wahalar da kanki ba, don Aysha Ba Zata zauna a gidan nan lokacin biki ba& can gidanki ma zan turata su zauna da mai aikin ki da k anwarki&  Cikin wani irin yanayi nake kallon Umma sai dai bata ba ni fuskar ma da zan mata musu ba, hakan yasa na ja k afata na koma cikin d aki, zuciyata ta min rauni na zauna kawai bakin gado na zuba uban tagumi, duk d okin bikin nan da na ci ashe ma Umma ba zata bar ni na je ba. Anty Khadija ce ta shigo ta zauna kusa da ni. A hankali ta ce  Ki yi hak uri AYSHA, na san Umma tana dalilin hakan, kada ki ce zaki yi fushi da ita ba Uwar da zata guji d an ta fa hakan da take miki soyayya ce&  d aga mata kai kawai na yi ina murmushin da sam bai kai zuciyata ba& Anty Khadija ta min sallama da cewa sai na taho. Na d aga mata kai.




Kashegari jikina a sanyaye na mik e Umma ta shigo tana kallona  Ki ha da kayanki, za a kai ki can gidan Yayanku da yamma. Na d aga mata kai kawai.


Da yamma kuwa ina zaune a harabar gidan Abba ya saka ni shara don dama haka kawai idan ya bushi iska sai ya ce na fito na share harabar gidanmu. Duk girmanta kuwa haka nake shareta tas, yau ma sharar nake, na ji k arar shigowar mota, gaba na ya yi wani irin fa duwa. Tsabar kyan motar ban san sanda na d aga ido ina kallonta ba, Mai motar bai fito ba kamar yarda nima ban fasa shara ta ba, sai dai ina ji a jikina kallona yake yi. Don haka na ji na bi duk na daburce. Fitowar Yaya Muhammad ne yasa ni ajiye tsintsiyar na zauna a saman wani dakali ina kallon yarda Yaya Muhammad ya nufi inda motar take. Tsawon minti guda na ga an bu de motar mai Motar ya ziro wasu takalmansa masu kyan gaske, ina d aga kai na idanuwa na suka fa da cikin na USTAZU yana tsaye idonsa a kai na& Da sauri na ajiye tsintsiyar ina sakin tsaki na juya na bar wajen& cikin wani irin k unar zuciya da b acin rai& .




5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA 33&

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?

08033748387.


Rik e wajen ya yi da sauri ganin har jini ya fara zuba, amma hakan bai saka shi ya fasa isowa inda nake ba, yana sakin wani kalar murmushi da na rasa fassarar da zan ba shi. Hannu nake  d aga masa ina furuci a zafafe  Don t come closer Ustaz ka tsaya inda ka ke I hate you& . I hate you whole heartedly& . Murmushin yake kuma bai fasa isa inda nake ba. Na runtse idona zuciyata na wani irin bugu kamar numfashi na zai bar jikina tsabar masifar da take cin zuciyata. Ina ji ya kira sunana da muryar da na kasa yarda tasa ce.  Open your eyes ki kalle ni, ina son mu yi magana&  Ba zan bu de ba Ustaz, kada ka saka na maka illar da har abada ba zaka manta ba&  na furta da wani irin rawar harshe  Illa? Ya furta cikin alamar tambaya hakan ya saka ni ware idona a kansa na ce  Ko kana shakka? Sai naga ya girgiza kai ya lumshe ido ya waresu duka a cikin second d in da basu fi na k irga ba& ya ce  Bana mamaki, Saboda komai aka ce za ki aikata yanzu ba zan musa ba, illa kuma ai kin Riga kin gama min illa da kika bari son ki ya Riga ya shiga raina, duk da yanzu ba son ko ka dan, am just& . Sai naga ya cije leb ensa ya saki huci ka dan na ware idona a kansa cikin masifa na ce  You just what? Ka fa da mana.  Ina tausayawa Abba da Umma saboda an rasa mai jihadi ya aureki That s why na yanke shawarar sake aurenki whether you want it or don t, kawai zan yi manage na aureki& .  Kan Uba! Na furta cikin tsabar mamaki  Uban waye ya ce na rasa mai so na? Murmushin ya sake yi ya kuma murza goshinsa ya fice daga  dakin yana sake furta  Am not begging you if you wish ki gaya musu ba zaki koma gida na ba, and so what waye ya zama looser& . Ya fita daga d akin har da y ar wak arsa ta larabci. Wasu irin hawaye ne kawai na ji suna zuba a k unci na zuciyata na wani irin harbawa ina jin kamar na bi Ustaz na kama shi na yi ta duka ko na huta da zafin da zuciya take yi& .. Gashin kaina kawai nake ja ina zagin ustaz a fili da zuciyata Samira ta shigo tana kallona kafin ta zauna a gefen gadon ta furta  AYSHA me ye haka, control your self mana, ko kina son wani ciwon ya kama ki nake?  Na fi so Samira, wallahi ina so saboda ko zai zama Ajalina I hate this world and all the things around it& .. Na fa da ina sake fincikar gashi na kamar wata mahaukaciya sabon kamu. Ina ji Samira ta ja ni jikinta da k arfin gaske ta rungume ta fara karanto min addu oin da suke bakinta. Da k yar ta samu ta ji na saki ajiyar zuciya ta ja min pillow na kwanta a hankali. Mik ewa naga ta yi ta fita sai gata ta dawo da magani a hannu.  Tashi AYSHA ki sha magani.. Bu de idona kawai na yi ina kallonta ta min alama da kai nuni take min tashi na mik e a hankali ina dafa kai na da yake wani sara min. Na zauna sosai ta saka min maganin a baki ta saka min ruwa, ina runtse idon na ha diye maganin.


Ban farka ba sai sha biyu da rabi na dare. Da sauri na mik e tunawa da nayi ban yi sallahr Isha ba Samira da take waya ta juyo tana kallona ta kashe wayar. Tana furta  Kin tashi AYSHA? Na d aga mata kai kawai na shiga toilet da ke d akin duk zuciyata ba da di na d aura alwala na fito. Ko da na idar da sallah har Samira ta kawo min tea mai zafin gaske da shortbread biscuit.  Ki ci AYSHA na san dare ya yi ba zaki iya cin abinci mai nauyi ba. Ruwan black tea d in kawai na d auka na kai baki na na dinga sipping d insa kamar magani ina runtse ido na. Samira dai sai kallona take da k yar na sha Rabin cup na ajiye ina lumshe idona saboda yarda nake jin zuciyata ta yi nauyi kamar wacce aka sakawa dutse. Turo k ofa muka ji an yi Anty Khadija ce ta shigo idonta a kaina ta ce  Kin tashi AYSHA sannu. Na d aga mata kai kawai. Ta zauna da k yar saboda cikin ta da ya fara girma ka dan. Ta dafa ni tana furta  Ki daina yawan damuwa AYSHA, kada ki causing ma kan ki wani problem d in. Samira ta gaya min duk abinda ya faru, abinda nake so da ke ki saka nutsuwa a ranki, ki cire tunanin komai idan Ustaz kome yazo nema ki amince kawai kin&  Wani kallo da na wurga mata ne ya sa ta ha diye Sauran maganar ta mik e jikinta a sanyaye tana furta  Shikkenan, Allah ya zab a mafi alheri. Ban amsa ba illa mayar da kaina da na yi na sunkuyar. Zuciyata na zafi ni fa gani nake duk wanda zai ce na koma gidan Ustaz baya so na baya k aunata. Samira ce ta taso ta kama hannuna muka hau gadon ta kwantar da ni. Sai da ta ga na lumshe ido sannan ta ce  AYSHA ki yi hak uri da abinda zan ce miki, amma wallahi kada ki yi sake Ustaz ya kufce miki, don ya ha du ta kowane fanni ga kyau ga gayu ga ku di ga ilimi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login