Showing 36001 words to 39000 words out of 80390 words

Chapter 13 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

156

jikina zubar da gumi take, naji duk duniya na tsani mata amma madadin soyayyarki ta ragu a zuciyata wallahi sake k aruwa ta yi, hakan yasa nasan lallai son ki it s part of my destiny. Zuciyata ta kulle gaba d aya na rasa mafita, zazzafan zazzab i ya rufe ni a gidan su Shareef.

A yammacin ranar kuma duka bak i suka cika gidanmu. Ban ji zan iya fasa aurenki ba Aysha a lokacin, don zuciyata gaba d aya ta Riga ta mamaye da k aunar ki sai dai na saka a raina dama kafin na tara da ke zan saka a bincika min ke a asibiti, hakan na yanke a zuciyata na ji kuma koda ya kasance ke mazinaciyace zan hak ura na aureki na kuma rufa miki asiri. Ba zan gayawa kowa ba.


A haka aka shiga biki sosai, kowa ya ganni sai an min kirarin ango, ni dai kawai murmushi nake na dinga jin zuciyata na wani irin duka a duk sanda na tuna wancan hoton. Sai dai na bar shi as evidence a cikin wayata ban goge ba.


Da yamma muka sake zuwa gidan da ka ce min kuna zuwa a lokuta da dama ke da wancan saurayin. Sanda muka je muka nuna hotonki sai wasu y an mata Suka tabbatar min sun sanki sunanki Aysha ina jin sun fa di haka na runtse ido na kawai don bana son maganar, bayan su mutum daban daban muka tambaya suka kuma tabbatar da magana d aya sunanki AYSHA&

Sharif ya ce  Ka gani ko Ahmad? Shi yasa sam ba a yabon mace&  Da sauri na  d aga masa hannu na ce  Ba ita bace Sharif, ba AYSHA ba ce wallahi sai dai idan wani coincidence d in ne ya faru& . Sharifs ya girgiza kai ya ce  Haka ne Allah ya kyauta.. Ranar kam sai Shariff ne ya jani zuwa gida don bana jin zan iya driving a irin tashin hankalin da nake ciki, gashi a ranar za a kai ki&


Da yammacin ranar Mommy ta shigo cikin d akina tana kiran sunana Ahmad me ke damunka ne? Na girgiza kai na ina furta bakomai Mommy. Sai naga ta yi murmushi ta ce  Allah yasa bakomai d in. Wayata da take ta ringing na k i d agawa ta kalla sai naga ta saka hannu ta  d au wayar ta ce  Ba kiranka ake ba Ahmad? Da sauri na mik a hannu zan amsa wayar sai ta ce  Ai ta ma mutu, yauwa bari naga vedion gidanka da ka ce ranar ka  d auko jama a basu bar ni na gani ba ance iyayen yarinyar sun yi k ok ari& . Ko kafin na yi wani yunk uri naga Mommy ta waro ido ta ce  Ahmad me nake gani wannan kamar hoton matarka tsirara da wani mutum!




5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA& . 43


NAZEEFAH SABO NASHE&
'?



08033748387.


Ganin idanun matar zube a kaina ya sa na gagara yi mata musu, a hankali na saka spoon na fara Shan romon da din da romon ya yi ne yasa na shanye shi tas ba tare da sani na ba. Na d ago ina kallon matar da take ta kallona tana sakin murmushi. Ta ce  Ko ke fa? Yanzu kinga Maminki zata ji kyakykyawan labari. Ban amsa mata ba na mayar da kaina na kwanta saboda barci da na ji yana fisgata. Hakan yasa ita ma bata sake min magana ba, ban San lokacin da ta tafi ba sai tashi na yi naga bata nan. Na mik e cike da kasala ina kallon Aunty Doctor da take tsaye a kaina tana min murmushi ta ce  Inlaw jiki ya yi kyau ko? Ma sha Allah hope ba inda ke Miki ciwo? Na  daga kaina ina d an sakin murmushi duk jina nake wani ido ga wata kunyar mutane da na tsiri ji, na San dai by now kowa ya San me na aikata. Ta dafa Kai na a hankali ta ce  Gaskiya jiki ya yi kyau, zuwa da safe zan sallameki Amma Akan shara dai sosai, kada ki yi wasa da lafiyar ki,kada ki sake koda wasa ki sake yarda da shi sai nan da 2 weeks na San kafin nan jikin ki ya sake kyau, don haka a shawarce ma zan iya cewa Inna ku tafi da ita gida, ko a samu me zama da ita&  Inna da take gefe tana Shan tea d inta. Ta gyara zama da sauri ta ce  Yo ni zaman me nake? Da ba zan bita can gidan na kula da lafiyar ta ba, ai dole na ne shi wannan wajen ai dole sai an bashi kulawa sosai don shine martaba da mutuncin y a mace, ke dai likita Allah ya saka Miki da alheri. Aunty Doctor ta amsa da Ameen tana sakin murmushi sannan ta saka Kai ta fita daga d akin.


Kashegari kuwa da safe aka sallamemu. Na dinga rok on Inna Akan mu tafi can gidan mu Amma Inna ta kafe akan gidan Ustaz zata Kai ni, gidan da idan na tuna zan koma nake jin wani irin b acin rai. Ban ce mata komai ba har Ustaz d in ya shigo fuskarsa fal fara a yana kallon Inna da ta gama parking duka Kayan mu a gefe. Yaya Usman ne ya shigo tare da matarsa hakan yasa na mayar da hankalina kansu. Ya.Usman yana kallon Inna ya ce Ashe an yi sallama? Ta  daga kanta tana furta  Ai yau sai gida, ja irar yarinya tun  dazu nake fama da ita Akan gidan mijinta zata koma, amma atabau ta k i wai gidan Ubanta zata koma, gata nan Usmanu sai ka gaya mata ko zata ji. Yaya Usman ya juyo yana kallona. Kamar yarda Ustaz ya yi cak shima yana kallona ta cikin idonsa na hango rashin nutsuwa da tashin hankalin da yake tattare da shi. Na turo baki ina kallon Yaya Usman da yake cewa Inna ai bata isa ba, dole a bi abinda mijinta yake so, idan shi ya amince ta koma gidan sai a k yaleta&  Inna ta ce  Kuma fa haka ne, shine mai yanke zance, duk da ko gidan nasa ta koma ba tafiyar da zata tsinana masa, don likita ta jaddada lallai ya tsahirta mata idan ba haka ba d inkin zai b alle, don haka ina ga gwara kawai ya bari a tafi da ita can gidan Imamun& . Ina kallon Ustaz ya yi saurin sauke idonsa k asa kafin ya fice daga  dakin na San kunya ce ta dame shi. Dariya na so yi ni kaina maganar Innan taso ta bani kunya amma ita ba abinda ya dameta ta juya ma gaba d aya tana sake yiwa Yaya Usman bayani shi dai ina kallo shima ya fice da sauri na San bayan Ustaz ya bi. Bai wani jima ba sai gashi ya dawo. Yana kallon Inna ya ce  Ki k yaleta ta tattara ta bi mijinta ai shi ba mahaukaci ba ne zai kula da lafiyar ta. Inna ta kalleshi a kaikaice ta ce  A barta ta bi shi ita ka dai kake nufi? Usman ya d aga Kai, Inna ta ce  Ah to wannan ne baku isa ba, idan yarinyar ta lalace Baku da asara ko? To k afata k afarta haba wa ina dalili wannan mijinnata da ko kunyata baya ji a gabana yake bata sumbata ko ya rungumeta yana zaton barci nake, shi kake cewa zai d aga mata k afa&  Usman shiru ya yi yana kallon matarsa ya ce  Bari na wuce dear, idan zasu tafi ki bi su ki  d an taimaka mata da gyaran gidan. D aga Kai ta yi tana murmushi a hankali. Shi kuma ya fice. Bayan mintuna sai ga nurse ta dawo ta ce Ustaz ya ce mu fita yana jira a mota. Dariya abin yaso bani ta yarda duk rashin kunyar Ustaz yau Inna ta k ure masa maleji. Suka d ebi Kayan ni kuma na zura Hijab d in da Ustaz kullum sai ya kawo min wani. Muka fita zuwa wajen mota. Aunty Doctor na tsaye da Ustaz a gaban motarsa ina kallo har mur da masa kunne take yi da alama kashedi take sake jaddada masa. Na ga ya tab e baki yana ganin mu ya yi saurin bu de min gidan gaba na shiga. Su Inna suka shiga baya. Aunty Doctor ta mana sallama muka tafi. Karatu kawai Ustaz ya saka Amma cikin dabara sai da ya lalubi hannuna ya rik e a nasa hannun yana murzawa hannu gudan kuma yana driving. Lokaci lokaci sai ya juyo ya kalleni ya saki murmushi ko ya murza hannun idan na juyo kawai sai ya lumshe ido ya ce  I LOVE YOU&  tsaki nake masa na d auke ido na.


Muna isa gida kuwa tas Auntyn Useey ta gyara gidan ta  dora abinci. Inna kuwa ta kasa ta tsareni a  dakina ta hana ni fita. Sai ga Auntyn Useey ta shigo tana k unshe dariya ta mik o min wayar hannunta da na tabbatar ta Ustaz ce,  Ana Miki waya. Ta fa da tana dariya ta fice. Wayar na kara a kunnena ina jinsa ya saki ajiyar zuciya Jin muryata ya ce  Ba zaki zo ba ko? Kin bi ta maganar tsohuwar nan? Na turo baki a hankali na ce  Ba zan zo ba d in, me zan zo na maka?  Mhmn Ya ce, kafin ya  dora da  Allah idan baki zo ba zan shigo yanzun nan na aikata abinda tilas Inna ta bar min d akin&  Tab e baki na yi na ce  Bismillah idan zaka iya na kashe wayar na ajiye a gefe, abin haushin hatta da wayarsa k amshin mayen turarensa da ya riga ya huda jikinsa take. Nocking na ji a hankali kafin na yi magana Inna ta ce shigo mana. Ya kuwa shigo sanye cikin shigar jallabiya sai walwali take da alama wanka ya yi, don na lura akwai soyayya mai kyau tsakaninsa da wanka. Y a rusuna ya gaida Inna kafin ya tako zuwa bakin gadon gaba na sai fa duwa yake ganin kamar da gaske yana shirin kunyatani a gaban Inna. Na waro idona ina nuna masa Innar da idona. Ya tab e baki yana min nuni da ina ruwansa& . Inna kuwa ta zuba masa ido na San so take taga iya gejin rashin kunyarsa.  Tashi mu je za ku gaisa da abokaina Sun zo duba ki. Ya fa da yana mik e min Hijab. Ina mik ewa Inna ta mik e itama tana kallonsa ta ce  Banda abinka Ahmad Ai da sai ka ce su shigo, tunda ka ga ai ba zai yiwu ta yi ta zurga zurga ba wajen bai gama ha dewa ba. Mu je mu gaisa da su ita ta zauna kawai ba sai ta je ba&  Ina kallo Ustaz ya saka yatsa yana murza goshinsa kafin ya  d ago ya ce  Yanzu zata dawo ai, kuma basa jin hausa idan kin je ba ba gane abinda zaki ce za su yi ba&  Inna ta ce  Ai hikkenan, sai ku je Amma dai ta dawo yanzun nan saboda a kiyaye dokar likita. Ustaz ya  d aga mata kai kawai yana saka hannunsa cikin nawa muka fice daga bedroom d in. Tun a hanya na fara turje masa, ina turo baki na ce  Pls! Ustaz wai ina zamu? Ya juyo ganin zan b ata masa lokaci naga yasa hannu ya d aukeni cak, ya haye da ni step d in da zai kai mu  dakinsa.


Bai dire ni ko ina ba sai saman gado, ya kalleni yana murmushi kafin yabi jikina ya kwanta ya rungumeni sosai yana sakin ajiyar zuciya. Zan yi magana naji bakina a cikin nasa sai da
Ya yi son ransa sannan ya sake ni yana mayar da ajiyar numfashi ya ce  Ba abinda zan
Miki matsoraciya barci kawai nake son yi a jikinki& . Hawaye ne ya kawo idona na ce  Kada ka sabawa kanka abinda ba zai d ore ba, am serious ba zan zauna a gidanka ba, ka cika ni na koma kada Inna ta yi fa da&  Bai cika ni ba sai ma sake shiga jikina da ya yi sosai ya ce  Kina sake magana kuma, zan canja mind d ina na sake bu de d inkin can&  Shiru na masa ina jinsa yana wasu irin abubuwa a jikina
Kafin barcin gaske ya d aukeshi. Wayarsa da take vibrating ce tasa nima na farka daga barcin da ya fara fusgata ina kallon wayar naga an saka Hayateey sai kawai naji ina son sanin wacece don haka na kara wayar a kunnena ba tare da na yi magana ba. A zafafe na ji Mommy ta ce  Wato Ahmad ka
Mayar da ni abokiyar wasanka ko? Wannnan ne dalilin da yasa fa da farko na k i amincewa da auren nan don naga gaba  d aya hankalinka na wajen yarinyar can son da kake mata ya yi yawa, to bu de kunnenka ka ji
Da kyau wallahi gobe sai kun tafi da Hameeda ba fashi idan
Kuma ka k i bin umarni na ban yafe maka ba, zan kuma yi sanadin da zan raba auren naku Har abad&  Ji na yi ya zare wayar daga kunnena ransa a b ace ya mayar kunnensa yana
Cigaba da sauraran Mommyn tasa& idanunsa kafin ya gama wayar sun ka da sun yi jajir. A hankali ya sauke wayar daga kunnensa yana lumshe ido. Wani abu mai kama da tausayinsa na ji yana fisgata sai dai ban yi magana ba na d au Hijab d ina na zura da niyyar tafiya na ji ya rik o hannuna da sauri na fa da jikinsa. Bakina ya kama da k arfi yana kissing cikin wani irin yanayi. Bai daina ba har sai da leb ena suka yi jajur sannan ya saki murya a raunane ya ce  Wa ya ce ki d aga min wayata K alb? Na turo baki na ban yi magana ba. Sai na ga ya saki murmushi ya ce  Am& na San kinji abinda kike so ki ji. Fine&  Ya fa da yana murza goshinsa a hankali ya mik e daga gadon gani na yi ya d auke ni cak mun shiga wata k ofa sai a lokacin na tabbatar toilet ne. Da sauri naja na tsaya ina furta  Me.. Me zamu yi anan? Ya lumshe idonsa a hankali ya furta  Love bathing& . Ya fa da yana bu de jirkitattun idanun cikin nawa. Na waro ido ina furta  Ni a a&  Matsowa ya yi daf da ni ya ce  Pls! K alb, mu yi ko don na dinga tunawa da ke, kin dai ji Mommy ta ce tilas mu tafi da Hameedah gobe kuma na San zan iya kaiwa 8weeks ban dawo ba, ban san yarda zan yi da rashin ki ba, gashi sau  d aya na yi tasting amma kin zautar da ni. Ko da yake ina zuwa zan fara Miki processing Visa kema ki biyo ni&  Tab e baki na yi na ce  Allah ba inda zan bika, ai yanzu ma na sake jin aurenka ya fita daga raina tunda Babarka bata sona, ba zan zauna a inda ba a so na ba na San ko nan gaba wahala zan sha, don haka dole kafin ka tafi ka sake& . Ji na yi ya jani jikinsa ya ha de bakinsa da nawa kafin na ce komai sai jina na yi a cikin bathtub da ya cika da ruwa, ranar kam ni Naga wanka a wajen Ustaz duk da bai yi min komai ba amma jikina ya wahaltu.


Da kansa ya sauka sai ga kaya ya taho min da su. Ina kallonsa kamar na yi kuka na ce Inna fa? Ya tuntsire da dariya ya ce  Tana can tana barci, Allah dai ya yiwa matar Usman albarka da ta kawo idear saka mata maganin barci&  na waro ido ya d aga min gira yana sake jana jikinsa a kunne ya ce min  Yau kin sake gigita ni da surar jikin ki Eehsha! Anya nan gaba akwai wata macen da zan sake yiwa kallon mace&   Har ita y ar mutuncin da ta San martabar iyayenta& . Goshinsa ya goga da nawa ya ce  Har ita Eehsha, Har kowa ma ke ta daban ce a cikin mutane na daban& . Na tabbata a cikin mata dubu da k yar a samu biyar irinki, Wai Zuma kenan&  Turesa na yi ina tab e baki na yi nufin sauka ganin yarda lokaci ya ja. Ina ji ya saki ajiyar zuciya ya ce saura dare zan zo d aukan ki mu yi bankwana& . Tsaki na ja a hankali na ce  Wallahi kada ma ka fara&  ina ji yana dariya na sauka a hankali. Gidan shiru da alama Auntyn Useey ma ta tafi. Ta dafa mana abinci kuwa na lek a ko ina ban ganta ba sai takardar na gani akan dinnig ta yi rubutu ka dan. Ki yi hak uri AYSHA Yayanki yazo mun tafi a sha amarci lafiya na tausayawa Ustaz ne shi yasa na taya shi samun abinda yake so.. Na yi k wafa na yaga takardar na cilla dustbin kafin na tura k ofar cikin d akin. Inna ce ta motsa a hankali ta mik e tana kallona ta furta  Kin dawo kenan?




Na gode

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login