Showing 57001 words to 60000 words out of 80390 words

Chapter 20 - NAGA RAYUWA BOOK 2

02 Dec 2025

153

idonsa Naga ya yi. Ya k i sakar min hannun kuma a hankali ya bu de idonsa da suka juya zuwa wani launi murya cike da kasala ya ce  You hated me but I love you AYSHA, na gode je ki gida. Daga haka ya sab ule hannunsa ya juya ya tafi. D an tab e baki na nayi duk da wani sashen na zuciyata yana son tausaya masa sai dai na k i barin hakan ya yi tasiri.




    ZAMAN KOTU    -


Ranar da za a koma kotu da wuri muka tafi. Da kam na ce ba zan je ba, amma Ya Usman ya ce dole na ne na je. Ina kallo Umma jikinta a sanyaye take shiryawa har muka je kotun kuma yanayin walwalarta bai dawo ba. Mu ne a sahun farko a kujerun kotun. Fuskata sanye da bak in glass kuma don na bawa Ustaz haushi yau ma ban saka Hijab ba, rolling na yi da mayafin abaya ta, na sha kwalliya a bina. Bakina har da chewingum ina tauna shi kamar da gayya haka nake satar kallon Ustaz yana ta zuban harara.

Kotun ta d inke da jama a, kowa na son jin k arshen shari ar da zan kira mai sark ak iya. Ina ta hango Ahmad yana ta sakar min harara ni rabon ma dana gansa tun ranar da na gasa masa magana a harabar gidanmu. Ko waya ya daina yi min.

Tsawon mintuna Ashirin muka d auka kafin Alk ali ya shigo aka buga gudumar kotu hakan ya bawa Kotun damar yin shiru. Aka kasa kunne saurarar Alk ali. Su SHANY aka shigo da su kowacce sanye cikin dogon Hijab sai dai fuskokinsu a bu de suke. Sai dai a fuskarsu zaka hango Sun rame ka dan da alama a duk inda aka aje su basa jin da di.

Alk ali ya kallesu d aya bayan d aya kafin naga ya gyara glass d insa yana kallon lawyoyin da suke zaune kowa da takardu a gabansa. Alk ali ya kalle su gaba d aya kafin ya ce  A fito da Atine&  kowa ya zuba idon son ganin wacece Mama Atine. Kanta a k asa ta fito tana yatsina fuska kana kallonta kaga cikakkiyar y ar duniya mai ji da iskanci. Kowa zuba mata ido ya yi Kotu ta fara k ananan surutai daga bakunan jama a Wanda majority nasu tsinewa Atine ake. Ni kaina tsanar matar ce ta shiga zuciyata Farat d aya na dinga Allah wadarai da ita. Allah dai ya shirya musulmi. Shi na ji Umma ta ce cikin raunanninyar muryar da ta saka ni kallonta da sauri. Alk ali ya dubeta ya ce  Ke ce Atine Harka? Ba tare da b ata lokaci ba ta d aga kai tana cije bak in leb enta.  Ni ce Atine. Alk ali ya jinjina kai ya ce  Ko zaki gaya min alak ar ki da wa dannan yaran? Kin san su? Cike da confidence ta kalli Alk ali ta ce  K warai na san su&   Menene ha dinki da su? Ta d an tab e baki ta ce  matsayin Uwa nake garesu tun daga jarirantaka Har kawo yanzu. Alk ali cike da mamaki ya ce  Matsayin Uwa? Kamar yaya? Kina nufin yaranki ne ko na y anuwanki kike rik o? Anan kam tsit Atine ta yi, ta yi k asa da kanta tana murza hannayenta alamar rashin gaskiya k uru k uru a fuskarta a zuciyata na ce Munafuka.

Alk ali ya girgiza kai ya ce  Atine, muna sauraron ki. Ko zargin da ake Miki ya tabbata ne kamar yarda yaran suka fa da babu kowace alak a tsakaninku dukkansu y an tsintuwa ne?. Da sauri Atine ta d aga Kai ta zubawa SHANY idonta da suka bayana tashin hankalin da take ciki. SHANY ta turo bakinta tana karka da ido cike da tsiwa.  Y an tsintuwa ne? Muryar alk alin da ya yi magana ta kara de kotun Atine ta d aga kai hankalinta tashe ta furta  Haka ne. Alk ali ya jinjina kai Kotu ta b arke da hayaniya da k yar aka tsawatar aka samu suka shiru. Alk ali yana kallonta ya ce  Ikon Allah! A wani gari kika tsinci Har mutane 35? Banda wa danda baa sani ba? Musamman waccan da tayi kama da wancan baiwar Allah. Don haka ake tunanin suna da alak a mai k arfin gaske, ko zaki gaya mana inda kika tsinceta? Idonta ta kai kaina inda Alk ali ya yi pointing da yatsarsa. Hankalinta tashe ta waro ido wani irin gumi ya dinga tsatstsafo mata. Alk ali ya dubeta ya ce  Muna jin ki Atine kuma zancen gaskiya muke so. Sab anin haka kamar kina rub anya hukuncin da za a zartar Miki ne. Gaskiyarki ce hanya mafi sauk i da zata sauk ak a miki hukuncin kotu.. k arya kuwa itace zata tsundumaki kogin nadama da dana sani& . Ido ta runtse tun daga nesa nake hango yarda k irjinta yake hawa da sauka, murya a raunane ta d ago idanunta da suka fara ambaliyar hawaye ta ce  Kamar yarda na fa da, da gaske nake wasu tsintar su na yi wasu asibiti na same su wasu kuma siyar min aka yi& . ihu aka shiga yi a Kotun& da k yar aka tsawatar  nima a k ark ashin wata mata nake, Wanda ita aikinta kenan safara da satar yara mata don tana fataucinsu zuwa k asashe daban daban idan Sun girma. Asibitoci take bi wajen samun yara jarirai ko marasa galihu ta siya ko ta sata ko kuma wa danda iyayensu suka Mutu ta hanyar accident aka rasa makusantansu Har gidan marayu tana ha da baki da mutane ta yi adopting yara. Ni kaina a irin haka ta same ni, ma ana ni shegiya ce. Duk abinda ta kashe maka kana yaro sai ta ninkasu sau d ari kafin ta barka ka samu y anci. Ko dai ta mayar da mutum karuwa ko tayi fataucinka zuwa wata k asar. Idan kuwa shekarun tsufa suka zo maka sai ta sallameka kaima ka kafa naka gidan karuwan. Don tana fa da ba a aikin banza a kano. A irin haka ni ma na fito a cikin wa danda aka sallama na kama gidan kai na sai na tsunduma irin harkar da take yi na shahara sosai Har na so na fita. A asibiti nake zagaye na siyo jarirai da ku d ade masu daraja a cikin k asashen Nigeria. A irin haka wata rana yawo na ya kai ni jihar kano inda na isa Har asibitin Nasarawa. A ASIBITIN NA SIYO SHANY, hannun wata mata da ba zan tab a manta fuskarta ba, ana ce mata FAD IMA& &


Daga Abba har Umma a wane irin firgice suke kallon matar Umma da k arfi ta ce  Asibitin Nassarawa? Wane rana kuma wane kwanan wata?



Tab gwarama!


Wash Allah na na sha dogon typing don haka Har da na gobe>?#?>??.



5?
?5?&?5?(?5??5?/? 5??5??5?0?5?%?5?"?&
'?[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa >?p?: NA GA RAYUWA& ..51

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.


Kotun zuwa lokacin tuni ta d au hayaniya da cecekucen jama a da suke ta yi ba k akkautawa da k yar aka samu bak uncin shiru bayan buga gudumar Alk ali. Umma a razane ta cigaba da kallon matar ita kanta bata San lokacin da ta yi wannan furucin ba murya a sama ta sake maimaita maganar tata, har sai da Alk ali ya tsawatar mata. A hankali ta ce  A ranar lahadi 17 ga watan july 2000 wata irin razana UMMA ta yi tana nuna ta da yatsa ta furta  Na shiga uku, kada kice min wannan yarinyar
jinina ce don ranar da na haifi Aysha kenan! Gaba d aya kallo ya koma wajen UMMA shi Kansa Abba jijjiga kai yake ni ma duk na bi na ru de don exactly ranar da aka haife ni kenan. Alk ali ne ya dakatar da Umma da take niyyar zuwa wajen Atine da k yar aka samu UMMA ta zauna hankalinta tashe tana sake nuna Atine Harka. Ni kaina bugun zuciyata a lokacin ya k aru sosai ba abinda nake sai zaro ido, glass d in ma na ajiye sa. Alk ali ya ce  Muna Jin Ki Atine wacece ta siyar Miki da Aysha? Ta yi shiru har sai da ya sake daka mata tsawa sannan ta ce  Idan har ban manta ba sunanta Fa dima ko Hajiya Fateema&  na dinga nanata sunan kamar mai son sanin ya ake fa dar sunan, bakomai nake tsoro ba sai kada abinda zuciyata take tunani ya zama gaskiya, kada dai ace Mami na itace Fateemah da ake zargi. Ina ji UMMA a hankali ta ce  Ba yafiya tsakaninmu a wannan karan Fateemah matuk ar na tabbatar da saka hannunki a cikin sace min jaririya. Na d ago ina kallonta itama na samu kallona take tana furzar da numfashi hankalinta tashe ta d aga min kai.  Haka nake nufi Aysha, matuk ar na samu Maminki ce da aikata wannan abin da gaske ba zan yafe mata ba, shari a ni da ita har Kotun k oli. Zuciyata ta dinga wani irin tsalle cikin tashin hankali na dinga addu a a raina kada Allah ya tabbatar da wannan lamari& . Alk ali ne ya ce  A ina zamu sameta? Kafin mu ji su kuma sauran a inda kika samo su. Ta girgiza Kai a hankali tana fincikar leb enta ta ce  Ba zan ce ga inda take ba a yanzu dai kam, Amma idan na ganta tabbas zan shaida ta. Bayan rubuce rubuce Alk ali ya yi jawabi kamar haka.  Dole ne duk inda take ki gaya mana, kafin zuwan wannan lokacin za a cigaba da rik eki a kurkuku ba tare da zab en tara ba. Samun matar da kuma zuwa asibitin wajen bincike ranar da aka haifeta da wacece ta haifeta idan ma baa samu Matar da ta siyar Miki ba na tabbata zamu samu record na wannan ranar In sha Allah. Umma ta mik e da sauri tana kuka ta ce  Wallahi ranka ya da de y ata ce wannan idan baku yarda ba aje asibiti a yi gwajin k wayar halitta (Genetics) zaku tabbatar da haka. Shiru Alk ali ya yi kafin ya yi rubutu ya d ago yana kallon UMMA ya ce  Duk wannan zai biyo daga baya, saboda kada ki manta har yanzu mai laifi ce ba zai yiwu mu naku ita ba. Alfarma guda zan muku shi likitan yazo ya d ebi samples nata, da sauran duk abinda ake buk ata aje a yi gwajin daga ranar da aka dawo kotu aka tabbatar taku ce za a baku ita bayan hukuncin da Kotu ta zartar a kanta. Jikin UMMA ya yi sanyi sai kallon SHANY take da dukkan idanunta da suka ka da suka yi jajur. Ganin yarda hankalinta yake Neman fita daga jikinta sai kawai na damk a hannunta cikin na Abba. Shi Kansa sam hankalin nasa kamar ya yi nisa daga jikinsa Amma haka ya yi k ok arin rik e mata muka fita waje. Bayan UMMA ta sake fashewa da kuka ganin yarda aka fita da SHANY, itama Shanyn tana waiwayenta.


Koda muka isa gida jikina a sanyaye nake jan k afata. Bakomai yake dagula min lissafi sai tunanin MAMINA. Fatana kada Allah yasa Mami tana da hannu a cikin wannan abin da zan iya kira son zuciya. A raba d a da Uwarsa a ranar da yazo duniya& . Idan har ya zama da saka hannunta a ciki ya makomar Mamin zata kasance? Wasu hawaye masu zafin gaske suka dinga bin idanuna.


&&&


Haka na kwana da zancen a zuciyata. Da safe ko karyawa ban yi ba na nufi Umma da zancen. Da ido ta dinga bina da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya ta ce  Tunani na yazo d aya da naki, da na Abbanki ma duka. Shima zargi da hasashen da yake kenan. Sai dai zan kwab eki kamar yarda shima na kwab eshi. Kada ku kuskura ku furta wannan zancen ga kowa har sai gaskiya ta bayyana, kada a zo a sake jin kunya don ba lallai ne abinda muke tunanin ya zama haka ba. Amma ya rantse wannan karan idan ya samu Fateemah ce silar salwantar yarinyar sa ba zai yarda ba sai ya yi shari a da ita. Ba zai mata sassauci ba. Burinsa kawai a yi gwajin k wayar halitta ya samu k wakwkwarar shaida a kotu&  A hankali na ja numfashi na fesar murya a raunane na ce  Kai jama a! Wallahi duniya abar tsoro ce. Umma ta jinjina kai kawai. Na gyara zama na ce  Umma don Allah zan je gidan Ahmad akwai wasu kaya na da books da nake son na d auko. Ta d an kalleni kafin ta ce  Ahmad d in ai yana nan gidansa mai kallon gidan nan, ki masa magana mana ya kawo miki, balle ma meye na d ebo kayan ke da zaki tattara ki koma gidanki, ko shikkenan kina nufin kin barwa Kishiyarki Mijinki kenan? Na turo baki na kamar yarda na Saba ya zame min jiki na ce  Ni fa Umma ba zan koma ba, don Allah ki bar ni na je yanzu zan dawo. Ta d an kalleni sai kuma Naga ta saki ajiyar zuciya ta ce  Ai shikkenan, sai ki buga waya ki sanarwa Mijinnaki ko ki gayawa Abbanki zaki fita don ni dai ba zan baki izini ba kin sani. Na marairaice fuska na ce  Allah Umma yanzu zan dawo. Baba driver ne ma zai kai ni. Umma ta kafe ba zan fita ba sai na sanar da Ahmad ta mik a min wayarta  Maza ki tura masa text, ai ba a garin mahaukata muke ba. Dole na tura masa message. Sannan Umma ta barni na fice da sauri.

Ko Drivern ban nema ba, don ba gaskiya na gaywa Umma ba, ba wani gidan Ahmad da zani gidan su Mami na zan tafi. Na k agu an gano koda. Saka hannunta a ciki.


Wannan karan Mama da fara a ta tare ni Har mamaki abin ya bani. Duk wannan d acin ran da bak in ciki Babu shi. Mami na kuwa tashi ta yi ta rungumoni sosai jikinta tana furta  Oyoyo Ayshatu na. Ni dai murmushin yak e kawai nake saboda yarda zuciyata take dukan tara-tara. Daga haka Mami ta jani cikin d akinta har da turo k ofa muka zauna a gefen gado. Kawai na ji Mami ta jefo min tambaya.  Ayshatu y a aka k are da zaman kotu? Wannan karan ai k in zuwa na yi tunda Naga kin yi free na ce me zan je na yi.. D an murmushi na jefeta da shi. Zuciyata na sake kambama zarginta da nake. Murmushin nawa San bai kai zuci ba na ce  Ai kuwa Mami da kin sha kallo, SHANY dai ana zaton ni da ita Twins ne, don rana guda aka haife mu, a kuma asibiti guda&  Da sauri Mami ta zaro ido ta ce  In ji Uban wa kuma? Na gyara zama cike da mamakin firgicin ta na ce  In ji matar da ta raine su ita ta fa di inda aka yi tazo hannunta, matar ta tabbatar da cewa siyanta ta yi a asibitin bisa jagorancin wata mata&  A hanzarce ta ce  Wata mata kuma? Wacece ta fa di sunanta? Na yi shiru ina nazarin yanayinta kamar dai tun yanzu zuciyata na son tabbatar min da zargi na. Na jinjina kai na ce  Ta fa da mana, sunanku d aya da matar da ta ce ta yi hanya an siyar mata da y ar. Wani irin kallo naga Mami tana min kafin ta mik e tana zagaye d akin hannayenta sak ale da bayanta. Jikina ya yi sanyi k alau ko Mami bata fa da ba na San tana da hannu dumu dumu a cikin wannan lamarin. Wata k walla ta kawo ido na. Na mik e ina d aukan handbag d ina. Na k arasa gabanta idanunta a lumshe suke na ce  Mami zan wuce. Da k yar ta bu de idanunta da suka juye lokaci guda ta d an lashi leb enta ta ce  Ki gaida gida AYSHA. Ta fa da da wata irin murya da na rasa yarda zan kwatanta. Ina fita na ratsa bayan gidansu Mami na zauna na ci kuka na sosai don na San Mami ce da wannan laifin bana haufi.


Sai da naje k ofar gida Sannan na tuna k arya na shiryawa Umma akan zan je d ebo kaya. Hakan yasa na juya na nufi gidansu Asma da sauri. Ashe rabon na yi mugun gani don Ustaz na gani tsaye da zank alak ok in matarsa a daidai k ofar gidansu da alama fita za su yi. Muka yi four eyes da shi. Wani abu na ji ta tokare min k irji. Na zabga masa harara na shigesu ba tare da na musu magana ba. Muryarsa na ji a daf da ni yana furta  Ban yafe fitar da aka yi ba da izini na ba. A masife na juyo na masa wani irin kallo mai nuna bala in da zuciyata take ciki ba. D aga min gira ya yi yana lumshe ido ya ce  Abinda na ce kenan Mara kunya. Wani yawu mai d aci na ha diya na kasa furta masa komai saboda takaicin da yake cike da zuciyata. Kuma muddin na tsaya zan iya saka masa kuka a wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login