Showing 102001 words to 105000 words out of 132766 words
sai kawai ya yi shiru
"Hello yaya Habeeb"!
"Wani sanyi dad'i mai gaske ya ratsa bones d'inshi ya lumsashe idanu.
"Hello, Hello yaya Habeeb can you hear me"?
"Yeah! Inajinki yafad'a adak'ile
Uhm.....uhm.....Haleesa tarasa abunda za ta ce da shi sai fama uhm....take
''Abunda ya harzuk'a Habeeb kenan ya tsani yana bacci a tashe shi gashi kuma, da alama leesa batada abun fad'a kawai ta kirane don ta katsi masa baccinsa mai dad'i.
Tsawa yadaka mata wannan wane irin wulaqancin ne leesa"?
Ki rasa lokacin da za ki kirani sai a tsakiyar dare kin katsi mini baccina mai dad'i kuma kin k'asa fad'ar dalilin kiran naki.
"In za ki iya magana just go straightforward ba wai kin dinga wani uhm...uhm..ba.
Tayi ajiyar zuciya tana mamaki masifa irinta Habeeb Lamido dama na kiraka ne na nemi izzininka zan tafi sokoto biki.
"Da k'arfi yaja iska a tunaninshi leesa ta kirashi ne saboda ta huce daga fushi da take yi da shi ashe ba haka bane ya tuna yadda yayi missing d'inta yatuna yadda sonta yake azabtarda shi ya matsu ya kamalla abunda yakawo shi Japan ya je gareta ya sanarda ita irin d'ibin son da yake mata.....
"Hello yaya Habeeb bakace komai ba"?
Muryata ce ta katsi masa zance zuci ya ja iska yafesar zuciyarsa na tafarfasa yace _sai yanzu ki ka gano cewa ina da matsayin da sai an nemi izzinina kafin ayi tafiya"?_
to ban amince ba ko main gate 'kafarki ta taka kuma ki tanadi hujojji masu k'arfi da za ki gabatar min da suka sa kika baro Lagos batare da izzina ba ki tabbata kin 'kure tunaninki ta hanyar nemo dalilai masu k'arfi da yasa in nakira phone d'inki bakya d'agawa sannan kuma ki tabbata kinada dalilin da za ki gabatar min da yasa ki ka kashe phone d'inki tsawon wannan lokacin.
"Ranar Wednesday zan dira 9ja Leesa ina mai tabbatar miki da cewa zan zo miki da abunda zai firgita ki watakila har ki fita hayyacinki.
''Yana k'arasa magana ya yi hanging up.
Yabar Haleesa cikin rud'ani tad'ago ta dube Hannah wance tuni bacci yayi awo gaba da ita.
"Jikinta a mace ta ajiye waya ta ja blanket ta rufi rabin jikinta ta afka tunani me Habeeb yake nufi zai zo mata da shi rass.....rass...gabanta yafad'i ta dafe k'irjinta da hannayeta duka biyu kadai yaya Habeeb yana nufi zai sakeni"?
Wani irin tsoro ya lullu6e ta tafara hawaye kuka take yi marar sauti bacci ya kauracewa idonta.
********************
A washe gari Haleesa tashi sukuku kamar marar lafiya, Hannah taga shiru-shiru nata yayi yawa yini ranar ko parlour bata fito ba tana k'unshe a bedroom har Hannah tashigo d'akin ta zauna kusa da ita batasaniba saboda tayi nisa, a tunani annurin zuciyarta Habeeb Lamido.
"Haleesa wai me ke damunki ne kwata-kwata yau narasa gane kanki tell me whats problem"?
''Huh.....Haleesa tayi ajiyar zuciya ta dube Hannah a sanyaye kema kinsan in har ina da problem to bara wuce na yayanki ba.
''Ni dai shawara da zan baki Haleesa kidaina matsantawa kanki da tunani kada yaje ya shafi lafiyarki.
Murmushi Haleesa tayi tace na gode Hannah insha Allah zan yi amfani, da shawararki amma kinsan me"?
A'a Sai kinfad'a"?
Yaya Habeeb yace bai amince naje sokoto ba.
''Hannah ta yatsine fuska tace share shi kawai shi da yake uwa duniya yaushe zai wani kafa miki doka.
Washe gari kuwa Haleesa tayi fatali da maganar Habeeb ta had'a luggage d'inta suka dauki hanyar sokoto
"Da Misali k'arfe _10:30pm_ flight d'in su Habeeb yayi landing, farin ciki fal zuciyarsa zai ga leesa Shi a tunaninshi tun da yace kada ta je bara ta iya tsallake umarninshi ba.
In yaso ranar Friday in zai tafi sai su tafi tare, saboda Saturday za'a daura aure da wannan tunani ya isa gida.
''Kaitsaye ya zarce d'akinshi ya sakewa kanshi shower yana fitowa daga wanka yafashe jikinshi da perfumes sai faman murmushi yake, jin yake bara iya baccin ba sai ya shak'i k'amshin leesa ba abunda yakeso gani irin kyakyawar fuskarta ya bud'e k'ofar d'akinshi yanufi part d'inta da ya ke akwai shortcut daga part d'inshi da yake bi ya shiga part d'inta ya murd'a handle ya bud'e k'ofar palourta yashiga kaitsaye ya wuce bedroom d'inta.
''A hankali ya murd'a handle sai kawai yaji k'ofar a rufe ruf ba don ranshi yaso ba ya koma part d'inshi.
A washe gari Habeeb bai fito ba sai around _10:40am_ yana sanye da blue colour Jeans da t-shirt red colour takalmin k'afarshi rufafin suma red colour ya kwashe phones d'inshi yanufi part d'in Haleesa.
Mamaki yarufe shi naji k'ofarta a rufe nan take bugun zuciyarsa ya tsananta, kadai leesa ta tafi Sokoto"?
A rud'e ya yi dialling numberta wayar a rufe sai kawai yayi decided ya kira lambar mom ringing d'aya zuwa biyu madam Hindu ta yi picking mom _Good morning sweetheart_
"Morning son katashi lafiya"?
"Lafiya lau sweetheart na kira phone d'in leesa a rufe shine nace bara na kira ki naji ko lafiya.
Huh..son kace matarka ka yi missing shine ka kirani to tana nan cikin k'oshin lafiya bara na kirata na bata waya.
"No....sweetheart ki kyalleta kawai zan kira number Hannah watakil zan biyo sahunku a yau d'inan.
Ba cewa ka yi sai ranar Friday za ka zo ba"?
Uhm....sweetheart nayi missing d'inki sosai I really wants 2 you mom"
Madam Hindu tayi dariya saboda ta fahimce idan Habeeb yadosa matarshi yakeson gani.
"Allah yakawo ka lafiya.
''Ameen sweetheart amma please sweetheart karki fad'awa leesa zan zo Co's inaso nayi surprised nata.
Dad'i ya lullu6e madam Hindu ita a dole d'anta na zaune lafiya da, iyalinshi tana dariya tace shikenan son bara fad'a mata ba a haka sukayi sallama.
"Habeeb ya yi ajiyar zuciya lallai leesa ta rainani na hanata tafiya da yake ta raina shine ta kwashe k'afa ta tafi bara iya cigaba da juri rashinta a kusa da ni dole na bi bayanta da sauri yakoma part d'inshi a gaugauce ya had'a luggage d'inshi yafice zuwa, compound ya kwadawa Bala kira Bala da ke zaune a main gate tare da gateman yana zuba surutunsa da yasaba da gudu yanufi wajen Habeeb.
Ka yi warming mota za mu tafi sokoto yanzu nan.
Boss sokoto kuma"? Ba sai gobe ne tafiyarmu ba"?
"Banaso surutu banza da wofi Bala za ka fito da mota ne ko kuwa"?
Batare da Bala yace komai ba yanufi parking space ya yi warming mota kirar Range rover evouge ash colour daga bisani yanufi boys quarter ya canza kaya yafito rik'e da 'yar k'aramar jakka kayansa.
Habeeb yashiga mota Bala yaja gateman ya bud'e musu gate yana musu fatan Allah ya kiyaye hanya.
*************************
_some hour's later_
Tun lokacin da Habeeb ya isa Sokoto yanemi Hotel mai tsada ya yi musu booking room shi da Bala da yake ya kwaso gajiya ba kad'an ba shiyasa bai nemi Haleesa a time d'in da ya iso ba sai misali k'arfe 9:30pm yanufi masaukin su Haleesa da yake gidan ba bakonsa bane saboda mijin Aunty Mami Dan asalin Sokoto ne, aiki yakawo shi Yola har Allah yahad'a shi da Aunty mami suka yi aure Sageer ne first born d'in Aunty Mami auren zumuncin ne za'ayi masa da 'yar Qanin mahaifinsa{idan mai karatu bai mata ba Aunty Mami Qanwar mahaifin Habeeb Lamido ce sannan kuma babbar Aminiyar Madam Hindu}.
Bala yanemi waje yayi parking a compound d'in gidan Aunty Mami yayinda 'yan mata ke ta tururuwa shiga mota suna tafiya zuwa Hall d'in da za'a gudanarda mother nights.
Haleesa da Hannah suka fito sanye da anko kowace su tasha makeover, sun yi matuk'ar kyau musanman Haleesa da fito tamkar ita ce amarya tun daga nesa Habeeb ya hango ta yasaki Qayatance murmushi, yafito daga cikin mota yanufi wajensu tun kafin yak'arasa ya hango madam Hindu tafito daga cikin gida.
''Cak.......Haleesa ta tsaya numfashinta yafara fita da sauri ta rik'on hannun Hannah da k'arfi cikin rawar murya tace na shiga uku Hannah kamar yaya Habeeb nake gani"?
"Zaro ido Hannah tayi tace wallahi ba kama bace shine wai yaushe yadawo daga Japan ne"?
Oho! Ni ina nasani Haleesa tafad'a cikin pity face.
Madam Hindu ta washe baki had'e da fad'ar oyoyo my son
''Habeeb yana murmushi yak'araso yana zuwa yayi hugging mom I miss you mom
_I miss too son ya gajiyan hanya duk da nasan yanzu gajiyar ta bi jiki"?_
"Yasake mom yajuya wurin da Haleesa da Hannah suke tsaye suna kallonshi da yake akwai 'yar tazara kad'an tsakanin idan suke tsaye da inda madam take tsaye.
"cikin tafiya nan tashi k'assaita yanufi wurinsu jikin Haleesa yadauki rawa.
Yana zuwa yaja birki a gabanta yana mata mai cike da shauk'in so da sauri ta sadda kai k'asa da k'arfi yafizgo ta tafad'a k'irjinshi yayi mata kyakyawa runguma _I miss you leesa I really miss you duk da nasan ke d'in ba ki yi missing d'ina ba_
Tsoro mai cike da d'inbin mamaki ya lullu6e Haleesa takasa koda kwakwaran motsi har Habeeb ya gama bidirinshi yasaketa batasan duniyar da take ciki ba.
"kuttt...ta hadiye wasu miyau fargaba gani yadda ta tsare shi da ido yasa hura mata iskan bakinshi tasaki ajiyar mai k'arfin gaske muryar mom ce tak'ara dawowa da Haleesa natsuwarta Hannah zo mutafi kad'a wannan sarkin lice mata ya6ata mana lokacin.
''Hannah tajuya ta bi bayan mom ta bar Habeeb da Haleesa a tsaye suna kallon-kallon.
''Mamaki ne sosai yacika Haleesa yadda Habeeb ya iya hugging d'inta a gaban mom tabbas Habeeb yacika cikakken pretender.
''Ta yatsine fuska tajuya batare da tace da Habeeb uffan ba kafin tak'arasa ta hango har drivern madam Hindu ya ja mota sun nufi gate sai kawai taja tayi tsaye.
"Habeeb ya lashi lips d'inshi yana shafar suma kanshi had'e da murmushi juyawar da zai yi ya bi bayan Haleesa yaji an kwada masa kira ya tsaya cak....batare da yajuya ba maryam tak'araso tana dariya.
Yaya Habeeb yaushe kadawo ne"?
Jiya ina angel d'ina"?
Tana Yola tare da hajiyarmu da nasan zan had'u da kai anan da na zo da ita.
Yayinda Habeeb da Maryam suka jera zuwa wajen matarshi sai surutu take zuba masa, yaya Habeeb kaima za ka je wurin party ne"?
''Uhm...ko za ki je ne mu tafi tare Habeeb yafada a kasalance saboda yafara gajiya da surutun Maryam.
Dad'i ya lullu6e Maryam ta bud'e mota tashiga, Habeeb yajuya wurin Haleesa yace ke! Zo mu tafi kad'a ta yarfa shi a gaban Maryam yasa ta bud'e mota tashiga nesa da Maryam ta zauna ta muturke fuska yayinda Habeeb yake zaune a seat d'in gaba Bala kuma na driving Maryam kuma sai labarin Imaan take zubawa Habeeb.
Kishi ya turnuke Haleesa har wani duhu-duhu take gani a haka suka isa Hotel d'in da za'a gudanarda party.
Bala nayi parking Haleesa ta bud'e k'ofa tafita da sauri tashige Hall tanemi wani sak'o ta la6e tana lek'en Habeeb da Maryam da ke tsaye a jikin mota.
''Yaya Habeeb bara na gwada maka pic d'in boy friend d'ina very Handsome da shi kamar kai saidai gaskiya kafi shi kyau tana magana ne had'e da scrolling d'in pic's d'in wayarta.
Duk surutu da take yi hankalin Habeeb baya wurinta yana wurin leesa ya matsu ya ji muryarta.
Ihun Maryam yadawo da shi daga natsuwarshi.
"Wayyo yaya Habeeb idona!
Menene a idonki"?
Wani kwaro ne yashiga min a ido Dan Allah yaya Habeeb ka busa min.
Yatsine fuska yayi oya kawo idon nagani yajanyo ta yarik'o kanta ta baya yashiga busa mata idon.
Da sauri Haleesa ta runtse idanunta a tunani Habeeb yana pecking d'in Maryam ne.
Hawaye suka wanke mata fuska tasaka bayan hannunta ta goge da sauri tak'arasa shiga Hall d'in.
Har aka tashi daga party bata saka Habeeb a idon ba yayinda shed'an yacigaba da zugata Habeeb na can! Cikin mota yana soyewa da Maryam.
Tana fitowa kallon gefen da Habeeb yake bata yi ba tanufi motar mom har ta bud'e k'ofa za ta shiga madam Hindu ta dakatarda ita ta hanyar cewa Haleesa ki bi mijinki kutafi tare a masaukinsa ba don ran Haleesa yasoba tajuya tanufi motar Habeeb ta bud'e k'ofa tashiga Habeeb ya dube Maryam yace Maryam sai gobe insha Allah" za mu k'arasa maganar mu.
''Maryam tayi wani fari da idanu tace "yes boss
Habeeb yayi murmushi yace kinganki ko Maryam wallahi bakida dama yana magana ne had'e da shiga mota yarufo k'ofa cikin kwarewa da driving Bala ya yi wa mota key yaja suka tafi..........
Jeeddah Aliyu🌹
[9:47PM, 13/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [10/12 4:51 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```90```
~~Suna isa Hotel d'in Bala yayi parking a sanyaye ta balle k'ofa tafito, tayi tsaye jikin mota tana jiran Habeeb yafito saida 6ata lokacin kafin yafito.
''Ko kallon wajen da take tsaye bai yi ba yawuce ta yanufi cikin receptionist ta had'e yawun takaicin tana mamakin wannan jijji da kai da Habeeb Lamido yake mata ta juya ta bishi a baya.
"Tana tsaye ya kar6i key card na room sai taga kamar mutane da ke receptionist d'in ita kadai suke kallo, a zuciyarta tace yanzu mutane nan kallon 'yar iska suke min sun ganin da k'ato a Hotel mtwww.....Ta ja tsaki wani sabon haushin Habeeb yak'ara lullu6eta.
Batare da ya dube ta ba yace mu tafi koh''? Yana magana ne had'e da juyawa yabi wani dogon corridor ta juya ta bi shi kamar kazar da kwai yafashewa a ciki.
''Zuciyar Haleesa tacigaba da tafarfasa musanman yadda taga Habeeb yana tafiyar k'assaita yasaka hannunshi d'aya cikin aljihun wandonshi d'aya hannun kuma yana rik'e da key card yana wata tafiya kamar mace mai ciki wata tara.
''Saida suka kai karshen corridor d'in yanufi upstairs yashiga haura staircase da suka kai karshen staircase 'yar gajeriya tafiya sukayi dai-dai d'akin mai number 406 ya tsaya ya yi using key card d'in hannunshi k'ofar ta bud'e.
''Yasa kai ya shiga d'akin Haleesa ta yi ajiyar zuciya gabanta na fad'uwa ta jefa 'kafarta cikin d'akin.
"Jikin bango ta koma ta lafe Habeeb yayi switch on d'in light d'akin ya gauraye da haske, ya juya a hankali yana kallon Haleesa da take jingine da bango sai wuk'i-wuk'i take da idanu ga mamakinsa sai ya ga ta galla masa ta yatsine fuska ta dauke kanta zuciyarta naci gaba da bugawa.
"Ya tabe baki yasoma balle buttons d'in rigar jikinsa yacire rigar yayi saura daga shi sai white vest da trouser Haleesa na satar kallonshi ta 'kasan idon.
''A cikin zuciyarta tace wannan d'an duniyar yana nufi zai dawo half necked a gabana"?
"Habeeb da bai masan tana yi ba aikin gabansa kawai yake, yasoma warware belt ya zare shi a hankali ya jefa akan bed.
''jikin Haleesa yadauki rawa ta runtse idanu gam......ta tuna ko lokacin da suka yi wanka tare a Lagos runtse idanunta ta yi.
"Yacire trouser yadawo daga shi sai white vest da Boxer Haleesa ta bud'e idonta kad'an ta ga yana k'ok'arin cire vest yarage daga shi sai boxer, ta tsurawa fad'adde k'irjinshi mai d'auke da Lallausar suma idon _kutt..... Ashe guy nan mai k'arfi ne kalli jikinshi a murd'e sai kace d'an wrestling_
Ba dole ya zama k'aton ba kullum yana cikin gyms machine abunda d'ayan 6angare na zuciyar Haleesa yace da ita kenan.
"Habeeb yajuya ya dube ta gani yadda ta rufe idanu yasa ya tabe baki yataka a hankali yanufi wurinta ya yi tsaye a gabanta, jin saukar numfashin mutum a gabanta ya firgitata babu shiri ta bud'e idanu da mugun mamaki take kallonshi, tukuna ma yaushe yak'araso kusa da ni"?
''Shima kallon nata yake da gira a d'age da sauri ta d'auke kanta da barin kallonshi cikin sark'ewar halshe tace ma....mal.....malam me ye haka"?
"Hannunshi yasa yadawo da fuskarta yak'ara matsawa daf da ita yayinda numfashinsa yake sauka, akan fuskarta ta matse idanunta gam.......can! K'asan mak'oshi yafara magana ban gane me ye haka ba"? Kina nufi baki ta6a gani namiji a half necked ba"?
"To ae ni ba 'yar iska bace da zan dinga gani maza a half necked tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
"Shu'umin murmushi yayi had'e da kallon lips d'inta kina nufi hadda wannan gajere bak'in mutume mai kirar mutane Ghana duk da shaquwar da ki ka yi da shi baki ta6a ganinshi a haka ba"?
''Gaba d'aya Haleesa ta gama tsorata da lamarin Habeeb Lamido me yake nufi da wannan kurman bak'i nashi"?
"Ni ban fahimce abunda ka ke nufi ba?
"Ya ja tsaki karka nemi ki raina min hankali mana tun da ki kaji na lissafa wa'annan siffofi ae kinsan da wannan margayi sarauyin naki mai d'ikin tela nake.
"Rass-rass!!..... Haleesa ta ji gabanta yafad'i yau kuma da wannan Sabon samfari yaya Habeeb ya tsiro da shi"?
Ran Haleesa yayi matuk'ar sosuwa cikin k'unar zuci tace kaga yaya Habeeb karka nemi ka cin zarafin mutume da yake kwance a kabarinsa idan wulaqancin ka ya motsa ya tsaya iya ni.
''Ya ja tsaki nasan har yanzu zuciyarki bata daina bagensa ba saidai kina yi a banza ne saboda tuni na haura stage d'in da shi d'in har ya kwanta dama bai haura ba.
''Hawaye suka wanke mata fuska cikin zafin rai tace shima d'in yashiga idan kai d'in bara ka ta6a shiga ba. Tana k'arasa magana ta ture hannunshi daga jikinta ta d'uka za ta bi ta k'asan hannunshi ta wuce ya matsa hannunshi yahana ta wucewa, yafizgo ta ya mayar da ita jikin bango ya matse ta sosai ta yadda duk yunk'uri