Showing 126001 words to 129000 words out of 132766 words

Chapter 43 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87946

lafiya cikin takonta na k'assaita tanufi cikin gida a parlour taci karo da madam Hindu tana fitowa daga d'akin da Haleesa take ciki madam Hindu ta washe hak'ora ki k'araso daga ciki Dr madam Hindu tak'arasa magana had'e da juyawa cikin d'akin na Haleesa yayinda Dr Khaleesat ta Mara mata baya Haleesa na kwance kamar yanda madam tafita tabarta a kwance Haleesa nagani Dr Khaleesat ta mik'e zaune tana yatsinar fuska, Dr Khaleesat ta nemi kusa da ita ta zauna tayi mata ya jiki daga bisani tashiga watsa mata tambayoyi meke damunki"?
"Jiri da tashin zuciya
tsawon wane lokacin ki ka dauka kina jin wannan yanayi"?
Yau da safe
Yaushe rabonki da ganin period d'inki"?
''Rass.......rasss..... Gaban Haleesa yagad'i tad'ago a rikice tana kallon Dr Khaleesat daga bisani ta sadda kai k'asa cike da jin kunya tace almost 2 months"
Murmushi Dr Khaleesat ta yi ta bud'e briefcase dinta tafito 'yar k'aramar roba ta mik'awa Haleesa tashi ki Shiga bathroom ki yi fitsari a ciki inaso na k'ara tabbatar da abunda nake tunani jikin Haleesa a sa6ule tasauka daga kan gado tashiga bathroom bata jima da shiga ciki ba tafito rik'e da robar mai d'auke da fitsari ta mik'awa Dr Khaleesat "pregnancy test strip Urine Dr Khaleesat tadauko ta tsoma cikin fitsarin ta ajiye a gefe after 3- 5 minutes tadauko yanuna jajaye layi guda biyu alama ce da ke nuna positive Dr Khaleesat tafad'ad'a murmushinta ta dube madam Hindu congratulation! Madam kin yi kusa samun maigida ko kishiya tak'arasa magana cikin dariya.
Masha Allah! Masha Allah! Abunda madam Hindu ke maimaitawa kenan ta rungume Haleesa, tana mata sannu yayinda Dr Khaleesat ta rubuta mata magunguna masu k'ara kuzari da k'arawa abunda ke cikinta lafiya ta mik'awa madam Hindu takarda ta mik'e tsaye had'e da cewa madam ni zan k'arasa gida insha Allah zuwa jibin zan leqa gidan amarya Hannah mu gaisa madam tabi bayanta tana zuba mata Godiya.
''Suna fita Haleesa ta kifa kanta a pillow tashiga rera kuka, tsananin kunya ya lullu6e ta yanzu da wane ido za ta kalli mom saboda mom tasan cewa yau tsawon watani biyu kenan da kafawa Habeeb sharad'in sai gashi cikin wata biyu ya baiyana a jikinta kenan yanzu mom za ta gano tana kula Habeeb duk da gargad'in da take mata akan karta kulashi har sai yacinye Watani 3 kuka Haleesa tashiga rerawa sanadin kuka da ta yi ya janyo mata ciwon kai.

_14 minutes later_

Madam Hindu ta turo k'ofar d'akin Haleesa tashigo hannunta rik'e da ledar magani d'ayan hannunta d'auke da robar ruwan Faro da glass cup jin motsinta yasa da sauri Haleesa ta rufe idanunta, madam ta zauna kusa da ita Haleesa, Haleesa tashi ki sha magani, a kunyace ta tashi madam ta balle tablets d'in ta mik'a mata ta tsiyaya ruwa a cup tabata batare da Haleesa ta dube ta ba kar6i ruwan tashanye maganin.
"Kwanta ki yi baccinki saboda kina buk'atar hutu madam tafad'a had'e da mak'ewa tsaye Haleesa ta kwanta sannan madam tajuya tafita.
''Haleesa nagani madam tafita tararume Hijab tasaka ta zura bathroom slippers ta bud'e k'ofa a hankali ta leqa parlour, tak'arewa mutane da ke parlour kallo taga madam Hindu bata cikinsu wuf.....ta yi tafito tanufi k'ofar fita cikin sauri tanufi gate ta bud'e k'aramar k'ofa tafita tana tana k'arasawa titi ta tare mai adaidata Saida tashiga suka d'auki hanya sannan tafad'a masa sunan unguwar da za ta je.
"Tun daga shigarta unguwarsu tafara cin karo da abun mamaki _Ni da yaya Habeeb tailoring center_ yadawo babban shago painting shagon kadai abun kallo ne bata k'ara shiga rud'u da firgitarwa ba saida takai k'ofar gidansu daga gidansu har na su margayi Yaya Habeeb ya sauya, a rikice tafito daga adaidaita tasaki baki da hancinta tana kallon gate d'in gidansu jin an turo k'ofar yasa takara ware idanunta sosai taga mai fitowa addu'a take yi a zuciyarta Allah yasa iyayyenta ba siyarda gidajensu suka yi ba kamal tagani yafito yana ganinta yadaka tsalle ya rungumeta muryarta na rawa tace kamal me ke faruwa ne naga sauyi a gidanmu da na baba Audu"?
"Kamal ya yi dariya yace aunty Haleesa ki sallame mai adaidaita ki barshi tsaye sai lokacin Haleesa ta tuna da bata fito da ko fika ba ta mayarda ganinta ga hannun kamal, N500 tagani rik'e da hannunshi tace kamal ban fito da k'udi ba ko za ka iya biyanshi"?
Kamal yajuya yanufi wajen mai adaidaita ya biya shi kud'inshi sannan yadawo wajen Haleesa, wance ke tsaye da d'ibin mamaki lullu6e da ita muryar kamal ce ta yi nasara dawowa da ita natsuwarta.
"Duk wannan sauyin da ki ka gani aikin yaya Habeeb ne.
"Zaro ido ta yi wane yaya Habeeb ka ke nufi"?
Yaya Habeeb d'inki mana
Hum....kamal kana k'ara jefani cikin rud'ani yaya Habeeb Lamido nake nufi shine ya gyara mana wannan gyara da ki ke gani ba ma wannan kadai ba ya ba wa yaya salman aiki company shi ya bashi gida da mota wai za'a dinga cirewa cikin salary shi, ya gyara _ni da yaya Habeeb tailoring centre_ ya zuba Kwararin mad'inka ya kuma biyawa Baffa, Ammi ,Baba Audu da inna mairo makka sai kin Shiga cikin gida za ki ga yanda ya gyara miki d'akinki.
"Har kamal yadasa aya a zancenshi Haleesa na kallonshi baki bud'e Kamal yace aunty Haleesa ki Shiga ciki ni zan tafi Inda Ammi ta aikeni.
"Jikinta a sanyaye tashiga gida ta yi sallama shiru ba Wanda ya amsa kaitsaye tanufi d'akinta duk da taga sauyi tare da d'akin hakan bai hanata gane shi ba ta murd'a handle k'ofar ta bud'e tashiga tsaye ta yi tana k'arewa d'akin kallo everything's dake cikin d'akin red & yellow colour ne a hankali ta mayarda idanunta kan bed Wanda aka qawata shi da bedsheets red & yellow ga wasu teddy bear's jere akan gado murmushi ta yi tanufi bed d'in ta kwanta tad'auki teddy guda ta rungume a k'irjinta
[25/12 1:40 pm] aliyujeeddah: "Ta lumshe idanu tashiga tunanin Habeeb Lamido nan take wani irin sonshi yak'ara samun mafaka a zuciyarta ta k'udiri anniyar kyautata masa za ta guji duk wani abu da zai 6ata masa rai saboda yanzu tak'ara amincewa da irin soyayyar da yake mata ta bud'e idanu da sauri tadauko wayarta ta rubuta mishi text.
_my handsome Don narasa Kalmar da zan yi amfani da ita domin na gode maka saidai zan cigaba da yi maka addu'a ubangiji ya baka masauki a gidan aljanna Firdausi ina mai maka albishir Imaan ta yi kusa samun k'ani ko k'anwa tsananin kunyar mom nakeji yasa na fito batare da saninta ba a yanzu haka ina gidan Ammi. Thanks for everything's tauraro naa_
Ta tura masa ta gyara kwanciyarta tasoma hango irin soyayyar da za su zuba in takoma gidan Habeeb a haka bacci yasud'ad'o ya sace ta.

"Ta6angare madam Hindu kuma tana fitowa daga d'akin da Haleesa take ta lalla6o digit d'in Habeeb ta danna masa kira, yana d'agawa ko gaisuwar shi bata tsaya amsawa ba tace duk abunda ka ke yi ka ajiye ka zo inason ganinka yanzu nan tana k'arasa magana ta hanging up.

_After 13 minutes_
Sai ga Habeeb ya zo a bedroom yatarar da madam gani yanda take ta zabga fara'a ya zauna kusa da ita yanda naga kina wannan fara'a sweetheart wani abun farin ciki yasamemu koh"?
Sosai ma kuwa Haleesa batada lafiya na...a rikice Habeeb ya katse mata hamzari ta hanyar mik'ewa tsaye marairarice murya kamar zai yi kuka haba sweetheart don Leesa batada lafiya shine ki ke farin ciki"?
"Murmushi madam ta yi kai ni fa banaso shirme ae kajira na k'arasa fad'ar abunda zan fad'a, batare da tajira jin ta bakinshi ba tacigaba da cewa Haleesa batada lafiya na kira Dr Khaleesat ta duba ta sakamako gwajin da ta yi mata tagano tana d'auke da juna biyu har na tsawon watani biyu.
"Zaro ido Habeeb yayi I can't believe Leesa na d'auke da baby naa tsantsar farin ciki ya lullu6e shi ya rungume madam yayinda ita ma tashiga taya shi murna da fatan Allah ya sauke Haleesa lafiya Madam tad'ago fuskarshi ka je tana d'akin Hannah in ka tarrarda ita tana bacci kada katashe ta ka jira har ta falka da kanta.
"Cikin zumud'i Ya mik'e yanufi d'akin yana shiga ya yi tsaye turuss.....sakamako hango gado da ya yi ba Haleesa akai sai ya yi tunani ko tana bathroom, phone d'inshi ya yi ringing alamar shigowar text yafito da wayar daga aljihunshi Lessa! Yafad'a a baiyane hannunshi na rawa yashiga karanta text d'in yana gama karantawa yajuya da sauri a parlour ya had'u da madam ya zaiyane mata abunda ke faruwa dariya ta yi sosai tace, ae ni tuni na hal6o jirginku kawai dai na zuba muku Ido ne naga iya gudun ruwanku tun da kun shirya kanku shikenan saidai ina rok'onka son ka lalla6a ta kasan masu juna biyu basason 6aci rai kai kuma ga ka da 'yar banza zuciya sai ka saka hak'uri al'amuranka Ku zauna lafiya.
"Insha Allah sweetheart ba za'a k'ara samun matsala tsakaninmu ba wance ma Akasi ne madam ta yi dariya tace ka gaida Ammi saboda nasan can kanufa Habeeb ya yi dariya had'e da juyawa a compound yatarar da Bala yana cin abinci, hannu kawai ya mik'a mishi bani car key"
''Da mugun mamaki Bala yace lafiya boss ina za ka je ne"? Bara ka jira na gama cin abinci mu tafi tare ba"?
"Murmushi Habeeb ya yi kai dai bani key na hutashe ka ka zauna ka ci abincinka cikin kwanciyar hankali, Bala ya mik'a masa key ya kar6a yanufi mota da sauri ya yi mata key ya fizgeta da k'arfi yafice matsiyacin gudun da Habeeb yake tsulawa yasa ya iso gidansu Haleesa cikin d'an k'ank'anin lokacin.
Direct parlour Ammi ya wuce zaune yatarar da ita bayan sun gaisa suka shiga firar duniya sama-sama yake jin abunda Ammi take fad'a tunani yake ta ina Haleesa za ta 6ullo kuma yana jin kunya ya tambaye Ammi ina take.
Kamal ya yi sallama yashigo hannunshi rik'e da baqar Leda yana ganin Habeeb yashiga murmushi ya mik'awa Ammi Leda Ammi ta katse shi ta hanyar cewa ina canji na kamal"?
''Ammi na biya mai adaidaitasahu da yadauko aunty Haleesa da chanjinki.
''Ammi ta zaro ido tace wace Haleesa"? ba dai tanan gidan ba domin ni banganta ba "A rikice Habeeb ya mik'e yarik'o hannun kamal muryarshi na rawa yace kamal ta ina ka ga Leesa ta bi"?
"Kwantar da hankalinka yaya Habeeb aunty Haleesa ba za ta 6ace ba tana nan cikin gidanan.
Tana cikin gidanan a ina"? Ammi tafad'a had'e da mik'ewa.
D'akinta mana kamal yafad'a yana dariya da sauri Habeeb yajuya yanufi d'akin har yana had'awa da tuntu6e Ammi tace kai Habeebu ka yi hankali mana kad'a garin sauri ka cire 'yan yatsunka yayinda Habeeb bai Masan me Ammi take fad'a ba muradinshi ya yi tozali da Leesa yana shiga d'akin ya bango ta kwance tana sharar bacci abinta. Ajiyar zuciya ya yi yanufi wajenta ya zare teedy bears d'in da rungume ya maye gur6in teddy ta hanyar shigewa jikinta kamar a mafalki ta shak'i k'amshin perfume d'inshi a hankali ta ware idanunta akan kyakyawar fuskarshi yasaki mata tsadad'en murmushi k'ara shigewa ta yi jikinshi ya rungume ta d'ayan hannunshi na cikin rigarta yana shafar cikinta _Leesa kin haifar mun da farin ciki marar misaltuwa Allah yaraya mana abunda ke cikinki ya sauke ki lafiya_
"Ameen Haleesa tafad'a ta zare jikinta daga nashi tadauko bisa gado tashiga bathroom ta wanke bakinta da fuskarta tadawo kusa da Habeeb ta zauna ta daura kanta bisa kafad'arta _yaya Habeeb naga abun arzikin da ka yi wa zuri'ata na go........da sauri yarufe mata baki da hannunshi karki gode mun kin cancancin fiye da hakan agareni Leesa duk abunda na yi wa zuri'arki tamkar zuri'ana na yiwa.
"Hawaye farin ciki suka wanke mata fuska rungume ta yi yashiga bubbuga bayanta, kinsan kukanki yana d'aya daga cikin abunda yake d'aga mun hankali a duniya"?
D'agowa ta yi ta share fuskarta, cikin shagwa6a tace kukan farin ciki ne yaya Habeeb.
"Ba kuka za ki yi ba Leesa anan za ki nuna farin cikinki yanuna lips d'inshi da yatsa murmushi ta yi ta matsa daf da fuskarshi ta had'e bakinta da nashi tabbas salonta ya rikita Habeeb domin har yafara fita daga hayyacinshi, saida ta taro shi ta hanyar rad'a mishi _karka manta my Handsome Don kana gidan in-law d'inka fa_
"Saketa ya yi da sauri yashiga rufe bottoms d'in rigarshi sai dariya take mishi kallon k'asan ido yake aika mata d'auke da manufar zan kamaki ne.
''Mik'ewa ta yi tafita ya bi bayanta da gudu tashiga parlourn Ammi tafad'a jikinta Ammi, Ammi naa nayi kewarki tureta Ammi ta yi kin yi kewa na shine ki ka shigo gidanan batare da nasani ba"?
''Am sorry Ammi naa koda nashigo gidanan bacci nakeji sosai ina baffa naa da yaya salman"?
"Baffa yafita shi kuma ban inda yake ba kinsan yatarkato aure zaman gida ba nashi bane Murmushi Haleesa ta yi wai nikan Ammi sai yaushe za ki fara fad'ar sunan yaya salman"?
"Bansaniba Ammi tafad'a tana hararar Haleesa kyalkyalewa da dariya Habeeb da Haleesa su ka yi Ammi ta mik'e tsaye tace bari nabar muku parlourn tun da na fahimcin abun naku iya shege ne tafice tabarsu suna kwasa dariya abinsu daga bisani Haleesa ta dubi Habeeb tace my handsome Don zan shiga gidan baba Audu na gaishe su.
''Mu je na rakaki kada kitafi ke kadai dodo yakamaki, dariya Haleesa ta yi had'e da cewa uhum....su dodo manya a tsakar gida suka isko Ammi zaune tana gyara alayahu Haleesa tace Ammi mu tafi gidan baba Audu"!
"Ammi tad'ago had'e da cewa Adawo lafiya Habeeb ya yi k'asa da murya yace Amminmu yau miyan alayahu za'a yi mana"?
"Murmushi Ammi ta yi eh! Amma kuma bansa da Ku ba saboda bansan da zuwanku ba.
"Habeeb ya Sosa k'eya yace fad'a kawai ki ke yi Ammi nasan baffa ne za ki bamu koh Leesa naa"?
Dariya Haleesa ta yi had'e da gyad'a kai suka juya yayinda Ammi ta yi murmushi tace in Ku je gidan inna mairo tabaku ni kan ban girka da Ku ba.
Mamaki Haleesa take yi yaushe shaquwa mai k'arfi tashiga tsakanin Ammi da Habeeb nan take ta tuno da margayi yaya Habeeb haka yake wasa da Ammi idanunta suka ciko da hawaye da sauri ta mayarda su tun kafin Habeeb yagani ya tuhume ta a haka suka shiga gidan baba Audu sallama Haleesa tashiga rafkawa Zainab ta leqo tana arba da Haleesa ta daka tsalle ta rungume ta Habeeb ya matsa kusa da su yace a hankali zainab kinsan ba ita kadai bace.
"A shagwa6e Haleesa ta turo baki uhum... Yaya Habeeb Kadàina tona min asiri mana harararta Habeeb ya yi Zainab ta kyalkyale da dariya tace yaya Habeeb ashe musame k'aruwa shine baka fad'a min ba"?
Bashine yanzu nake fad'a miki ba Leesa na k'ok'arin hanawa wai Karna tona mata asiri da wannan drama suka k'arasa shiga parlour inna mairo ta yi matuk'ar farin ciki da ganin Haleesa musanman da ta fahimcin Haleesa na zaune lafiya da mijinta cikin tsokana Habeeb ya dube inna mairo yace innataa, Allah yasa kinada fura a gidanan"? saboda nasan ke ba irin Ammi bace a koda yaushe za'a tarar da fridge d'inki da fura.
Harara inna mairo ta zuba mishi had'e da cewa banida fura.
Zainab ta tashi da sauri tanufi fridge tadauko jug mai d'auke damamiyar fura ta mik'awa Habeeb tun safe ta dama maka tana zuba idon zuwanka Zainab tak'arasa magana tana kallon inna mairo tana dariya,kiran sallah magarib ne yafitarda Habeeb daga gidan yanufi masallacin bayan Haleesa ta yi sallah inna mairo tashiga yi mata nasihar zaman aure daga bisani inna mairo tasa kuka saboda ta tuno da marigayi yaya Habeeb da yanzu cikinan da Haleesa take d'auke da shi nashi ne da kyar Haleesa da zainab suka rarrashin inna tadaina kuka Haleesa tayi mata sallama takoma gida....

Jeeddah Aliyu🌹
[8:35PM, 28/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [27/12 1:50 pm] aliyujeeddah: 💝```NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa shehu Aliyu🌹

*®NWA*

*°°°°In Dedication°°°*
*Shehu Aliyu Family's*

*100*

_the End_

~~A parlour ta iske Habeeb da Ammi zaune Habeeb ya yi rashe-rashe suna zuba fira shi da Ammi Haleesa ta zauna asanyaye Ammi ta tashi ta kawo musu abincin, loma 1-2 Haleesa ta yi amai yataso mata ta mik'e da gudu tafice tsakar gida tadinga kwara amai Habeeb yabi yarud'e sai faman yi mata sannu yake. Ammi na mishi dariya yanda Haleesa bataci abincin ba shima kasa ci ya yi Ammi ta dubi Haleesa cikin tausayawa tace mekikeso a nemo miki"?
"A kunyace Haleesa ta furta d'an wake murmushi Ammi ta yi had'e da fita kamar jira Habeeb yake yi Ammi tafita ya matso kusa da Haleesa ya rungumo rabin jikinta sannu Leesa babynaa yana wahalarda ke koh"?
"Lafewa ta yi tana shaqar k'amshin jikinshi ta gyad'a kai alama eh! A shagwa6e tace ina mamaki yanda nakejin tashi zuciya alhali ada ba haka nake ba.
Karan hancinta Habeeb ya ja laifi babynaa ne so take kowa yasan tana kwance anan yak'arasa magana yana Shafa cikinta.
"Ture hannunshi ta yi kai yaya Habeeb kana nufi har kafara za6e abunda zan Haifa"?
"Ba za6e nake yi ba Leesa amma inaji a jikina kamar baby girl za ki haifa.
Uhm.. Uhm... Ni gaskiya nafiso baby boy saboda muna da Imaan.
Kafin yabata amsa Ammi ta yi sallama da sauri yasaketa ya koma wajen zamanshi plate Ammi ta mik'a mata mai d'auke da d'an wake yasha yaji da mangyad'a ga yankake cabbage a sama nan take yawun Haleesa ya tsinke yayinda Habeeb ya yatsine fuska cikin kyankyami yake kallo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login