Showing 87001 words to 90000 words out of 132766 words
ta gyara masa bed ta feshe d'akin da freshener tana tsaye har yafito daga wanka ya zauna a gefen bed yana mata kallon k'asan ido wani irin abu yakeji yana ratsa jinin jikinsa can! Ya yi gyaran murya daga bisani yace........
Note:- _I'm sorry readers nasan za Ku ce page d'inan yayi kad'an wallahi yau nayi typing mai yawan gaske basan ya akayi ya fita gaba d'aya, ba da kyar na yi wannan a halin yanzu kaina yadau zafi ina cikin yanayi na jiyar zuciya_
Jeeddah Aliyu🌹
[28/11 6:20 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```80```
~~ke! Bud'e wardrobe ki dauko min fari jallabiya{white colour} yak'arasa magana had'e da lumsashe idanu.
Haleesa ta tabe baki a zuciyarta tace huh...daga farfad'owarsa yafara kirana da suna nan da na tsana, a maimakon ta dauko white colour kamar yadda ya umurceta sai kawai ta dauko mishi black colour, k'i kar6a ya yi yabarta tsaye rik'e da rigar, Haleesa tasake mik'a masa rigar tace yaya Habeeb gashi katashi ka yi sallah lokacin yana k'urewa.
"Ya yi kici-kici da fuska very slowly yafara magana Fari nace ki dauko ba black ba.
"Umhh....fari kace na dauko ni kuma a ganina white da black duk d'aya ne muradi kawai ka suturta jikinka ko...ya kace"?
Tak'ara sa magana tana kallon fuskarsa, saida ya tsotsi bakinshi sannan yafisge rigar daga hannunta daga zaune ya zura rigar yayinda Haleesa ta shinfid'a masa pray mat yana fara sallah tafice daga d'akin a parlour ta tararda madam Hindu da Hannah suna breakfast mom tace kin had'a masa ruwan wanka ne"?
''Eh mom har yafito daga wanka yanzu ma na barshi yana sallah abincinsa zan dauko masa.
Da kyau 'yar albarka haka akeso mace tagari ta kasance, murmushi Haleesa ta yi tanufi kitchen hannunta d'auke da k'aton tray ta tura k'ofa tashiga, yana zauna inda ya yi sallah da sauri yad'ago yarame sosai idanunshi sun k'ara girma fuskarshi ta yi wani fiyau ga wata irin k'asumba da yacika masa fuska.
Tadire tray hannunta ta zauna a gabanshi tana magana tana zuba masa kunun gyad'a kafara da wannan saboda hanjinka ya warware tak'arasa magana had'e da mik'a masa cup ya kafe ta da idanu ko kintawa ba bu Haleesa ta kad'a eye's ball d'inta ta marairaice murya ka daure kasha koda d'an kad'an ne.
Idaunshi a lumshe ya mik'a hannu ya kar6i cup d'in daga hannunta a hankali, yake kur6a kunun har ya shanye tass...ta kar6i cup ta bud'e food flask k'amshin faten dankalin turawa ya daki hancin Habeeb ya hadiye yawu, ta yi masa serving sai ga gogan naku ya lamshe fate tass....ya ajiye plate yana wani yatsinar fuska Haleesa tace uhmm....ciwonka yana burgeni yaya Habeeb saboda bai hanaka cin jagwalgwalen Haleesa ba tak'arasa magana tana murmushin tsokana.
Habeeb ya daure fuska kema kinsan saboda mom tana gidanan yasa naci abunda ki ka sarafa da hannunki.
''Haleesa ta tabe baki tace uhmm.....yaya Habeeb kenan a wasu lokuta in kana magana kamar da gaske sau ina kama ka kana satar jagwalgwale tak'arasa magana tana dariya.
''Da k'arfi yafisgota tafad'a kansa ya yi mata bak'ar matsa tasaki 'yar k'ara, yadaura bakinshi dai-dai k'ofar kunnenta yace ke! Waye barawo"?
''Ni fa bance maka barawo ba tafad'a cikin rawar murya d'ago fuskarta ya yi yana mata kallon ido cikin ido kasa jurewa ta yi ta sunne fuskarta a k'irjinshi, jikin Habeeb Lamido na 6ari yak'ara rungume ta tsanm....ya daura kanshi bisa wuyanta yana sauke numfashi can! K'asan mak'oshi Haleesa tace ka sakeni kada su mom su shigo su ganmu a haka Allah kunya zan ji tak'arasa magana cikin sigar shagwa6a.
'Maganar tace ta katsiwa Habeeb hamzari da sauri ya yakice ta daga k'irjinshi a kunya ce ya mik'e yanufi gefen gado ya zauna, Haleesa bata k'ara kallonshi ba ta tattrara food flask tafita da su.
Koda ta koma d'akin ta tarar da mom da Hannah na ciki Habeeb ya daura kanshi, akan cinyoyin mom tana shafar gashin kanshi Haleesa tabe baki tanemi kujera da ke cikin d'akin ta zauna cikin sigar rarrashi mom take masa magana _please son ka sanarda ni ainihin abunda yake damunka sanin kanka ne bara ta6a samu peace of mind matuk'ar kana cikin damuwa_
''Idanun Habeeb suna lumshe yace c'mon sweetheart I told you hundred time's ba abunda ke damuna so stop worry yourself.
Madam Hindu ta girgiza kai tace shikenan son, amma Dan Allah ka dinga cin abinci, kuma daga yau na hana peter ya girka abinci da kai ga matarka nan duk abunda ka ke so kafad'a mata za ta girka ma.
"Sai lokacin ya bud'e idanunshi ya mik'ewa zaune madam Hindu ta juya wurin da Haleesa take zaune tace ni zan tafi Haleesa ki tabbata yana cin abinci sosai ya kuma dinga shan maganinsa in time.
''Haleesa ta gyad'a kai a zuciyarta tace kai wannan matar akwai iya yi hatta da magani tace sai na bashi sai kace k'aramin yaro ae kuwa overdose zan dinga d'irka masa.
Madam Hindu tariga Hannah fita daga d'akin Hannah ta matsa daf da kunnen Haleesa ta rad'a, _yar uwa karki sake ki yi wasa da wannan damar da ki ka samu ba Dr saleem yace cutar ulcer da hawan jini yake damunsa ba ke Kuma ki yi k'ok'ari ki k'ara masa da cutar so_
''A lokacin d'aya suka kyalkyale da dariya had'e da tafawa Habeeb Lamido ya zaro ido a zuciyarsa kai lallai yara nan sun rainani da alama gulma ta ce suke yi ya murtuk'e fuska ya gallawa Hannah harara yace ke wai uban me ki ke jira ne da ba ki tafi ba kin bar mom tana jiranki"?
Hannah ta turo baki tace mom tare take da direbanta, ni kuma da motana nazo.
"Whatever! Habeeb yafad'a a harzuk'a.
Tsabar tsokana irin na Hannah saida tak'ara rad'awa Haleesa _yar uwa kada wannan muzurai da yake yi yabaki tsoro domin hakan zai iya rusa miki plan_
Haleesa ta yi murmushi ita ma ta rad'awa Hannah _don't worry 'yar uwa ke dai ki zuba ido ki sha kallo_
Suka k'ara kwashewa da dariya Hannah tajuya wurin Habeeb tana dariya tace bros ni zan ware sai gobe in nazo shan farfesu.
Tsaki Habeeb ya ja yace wannan kuma matsalarki ce munafuka kawai.
Hannah ta dube Haleesa ta yi mata signal karaf akan idon Habeeb, sai kawai ya ga Haleesa ta tintsire da dariya Hannah ta bud'e k'ofa tafice.
''Habeeb ya d'aure fuska yana kallon Haleesa a d'age yayinda ita kuma ta sadda kanta k'asa, tsawon dak'ik'a uku ta dauka kanta na sunkuye daga bisani tad'ago ta sace kallon Habeeb idanunshi na kafe akanta, batasan lokacin da tasake masa murmushi ba. harara ya galla mata yace ke zo nan
Saida anta cikinta ta kad'a ta dake kamar bata tsorata ba ta mik'e a sanyaye tanufi wurinshi Saida yak'are mata kallon wulaqancin yace jikina yabani cewa wannan rad'e-rade da Ku ke yi da ni Ku ke don haka fad'a min abunda Ku ke cewa"?
''Haleesa ta rusa yar da kai ya za'ayi yaya Habeeb kana zaune mu yi gulmarka"?
Karaf yarik'en mata hannu ya shiga murza yatsunta da k'arfi, Haleesa tafasa ihu _wayyo yatsuna Yaya Habeeb karka yi min targad'e_
Saida yagaji don kanshi yasaketa, ta koma gefe tana 'yarfe hannu a zuciyarta tace mugu kawai nan take ta tuna da bai sha maganinsa ba ta yi murmushin mugunta tace nima anan zan rama yanzu nan za ka ga kalar nawa mugunta.
Tajuya ta dube shi ta ga har yanzu ita yake kallo ta turo baki tanufi bedside tadauko ledar magunguna sa, robar ruwa da cup tadauko ta ajiye bisa dressing mirror tasoma 6alle tablets saida ta cika hannunta duk abunda ta ke yi Habeeb ya kafenta da ido murgud'a masa baki ta yi ta mik'a masa hannunta karaf ya d'anke hannunta tace kai bawan Allah magani za ka kar6a ba hannuna ba.
''Yatsine fuska ya yi Can! K'asan mak'oshi ya furta kina nufi ni zan sha wannan tulin magani"?
Kwarai kuwa ko bara ka sha bane na kira mom a waya
Tsaki ya ja yace amma dai kinsan banason magani koh"?
Ta tabe baki tace oho...ni bansaniba cike da jin haushi ya mik'a mata hannu ta bashi maganin kamar zai fashe da kuka yace duk tulin magani nan ace ni kadai zan shanye shi, sai kace d'an kwaya.
Saura kiris Haleesa ta tintsire dariya sai kawai ta hadiye abarta Habeeb ya runtsi idanunshi da kyar ya shanye maganin yayinda Haleesa take aikin kallonshi saboda yatuna mata da marigayi yaya Habeeb shima haka yake Sam bayason magani duk lokacin da bashida lafiya sai tasha artabo da shi kafin yasha magani.
"A zuciyarta tace huh....kenan duk mai suna Habeeb bayaso magani batasan cewa maganar da tayi yafito fili ba.
Tsananin kishinta ya lullu6e Habeeb cikin zafin rai ya wanka mata raguwar ruwan da yasha magani.
A tsorace Haleesa tad'ago tana kallonshi yayinda shima ya kafenta da idanunshi da ke baiyanar da b'acin ranshi a fili.
Nan take wani tunani yafad'owa haleesa sai kawai ta hadiye b'acin ranta, ta mik'a hannunta ta d'auki robar ruwa kamar za ta sha ta balle murfi ta kwara masa a jiki ta balla da gudu ta nufi k'ofar fita har tafita ta d'an lek'o kanta ta yi masa gwalo tasaki k'ofa ta kwasa da gudu tashige part d'inta direct ta wuce bedroom tafad'a bisa bed tad'auki pillow ta manna a k'irjinta wani irin nishad'i, takeji Wanda rabonta da ta tsince kanta cikinsa tun yaya Habeeb d'inta yana raye ta runtse idanuta fuskar Habeeb Lamido ke mata gizo.
Ta6angare Habeeb kuma Haleesa na ficewa ya tsurawa k'ofa ido daga bisani ya sulale ya kwanta rabin jikinsa na bisa bed yayinda k'afafunsa ke k'asa wani irin tafiyar tsotsa yakeji a jininsa, sai kawai ya afka tunani yafara aikawa kansa tambaya batada amsa.
_me yasa lokacin da yarinya nan ta yi zancen marigayin sarauyinta naji mashahurin kishinta ya turnuke ni"?_
Ya mik'e zauna wani 6angare na zuciyarsa yace hakan yana da nasaba da tsananin sha'awarta da ka ke yi ya tabe baki had'e da mik'ewa yacire rigar jikinsa Yana tunanin in ya kama Haleesa irin hukuncin da zai yi mata.
*************************
_8:30pm_
Habeeb yana zaune a falonshi ya kafe akwatin talabijin da ido Haleesa ta yi sallama sai kawai ta ja ta yi tsaye cikin tsokana tace _yaya Habeeb in shigo ko in koma inda na fito"?_
Murmushi Habeeb ya yi had'e da shafa sajen shi, ya ja iska wani irin dad'i ya ziyarcenshi jin yake yi tamkar yana yawo a sararin samaniya, amma tsabar zafin kanshi ba zai barshi ya baiyanar da jin dad'i nasa ba.
"Ya yatsine fuska yace duk yadda ki ka za6a.
Haleesa ta mak'e kafad'a tak'arasa shiga falon a fakace yak'are mata sanya take cikin lemon green colour gown iya guiwanta ta yane kanta da d'an k'aramin white colour veil fuskarta tasha light make-up matsananciyar sha'awarta ta lullu6enshi har ta haddasa masa kasala yasauke zazzafar ajiyar.
Kaitsaye ta zauna bisa hannun kujerar da yake zaune, k'amshin turarenta ya baibaye shi ya tsincin kanshi cikin wani hali Wanda a tarihin rayuwarsa bai ta6a riskar kansa a ciki ba.
Kafin yadawo daga duniyar tunani muryar Haleesa ta daki dodon kunnenshi _yaya Habeeb your food is ready_
Habeeb ya tabe baki yana mamaki me Haleesa take nufi da wannan sabon salo da ta zo mishi da shi ta na nufi za ta ja ra'ayinsa ne yafara sonta"?
Ya yi murmushi yad'ago kanshi sama yadda zai hango fuskarta yana mata duba mai cike da sha'awa, yace ki je ki juyewa Rahul da Rita ni na k'oshi.
Haleesa batasan time d'in da ta galla masa harara ba ta murgud'a baki.
yadda ta murgud'a baki ta yi mugun bashi dariya sai kawai ya basar, yad'age gira sama yana mai cigaba da kallonta.
"Haleesa ta narke murya tace haba! Yaya Habeeb karka yi mun haka mana karka manta mom tace na kula da cin abincinka yanzu dai ka yi hak'uri katashi mu je ka cin abinci kaji"?
"Ignoring nata ya yi ya mayarda hankalinshi wurin TV haushi ya turnuke Haleesa a zuciyata dallah! Dube shi ina rok'onshi yana wani jan aji duk lokacin da ka shigo hannunna sai na gasa maka gyad'a a tafin hannunka.
Saida ya gama ja mata rai ya mik'e yana gaba tana biye da shi bayan sun gama cin abinci ya mik'e ya koma falonshi.
_10:00pm_
Har Haleesa ta kwanta ta tuna Habeeb bai sha maganinsa ba da sauri tadiro daga kan bed ta zura Hijab bisa night gown d'inta, ta murd'a handle tafice kaitsaye ta murd'a k'ofar d'akin Habeeb tashiga yana kwance ya yi pillow da hannayenshi abun duniya yataru ya yi masa yawa a yadda yake ji game da Haleesa muddin bai ji d'umin jikinta ba zuciyarsa za ta iya bindiga ta tarwatsa yana cikin tunani yadda zai je mata da buk'atarshi sai gata ta zo a lokacin da yake da tsananin buk'atarta, ya lumshe idanu yasaki murmushin dad'i a zuciyarsa yace uhm....tsuntsu daga sama gashashshe.......
Jeeddah Aliyu🌹
[29/11 6:21 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```81```
~~suna had'a ido tasake masa murmushi Wanda ya haddasawa Habeeb mutuwar jiki ya ja iska, had'e da cizo lips d'inshi na k'asa Ya tsare ta da idanu kamar tsohon maye.
"Haleesa tak'arasa kusa da shi tana magana had'e da 'yar dariya yaya Habeeb na manta ba ka sha maganinka ba.
Tsaki ya ja Cike da takaici Yace dama shine dalilin da yasa ki ka shigo min room a wannan lokacin"?
Eh mana tafad'a had'e da dauko ledar magani ta zauna a gefen gado.
"Ranshi a 6ace ya mik'e zaune yafisge ledar daga hannunta ya jefar ya rik'e hannayenta duka biyu can! K'asan mak'oshi yace ke! Wannan magani da za ki bani bashida amfani a tare da ni bara iya warkarda cutar da nake d'auke da ita saboda haka ko kin bani bara sha ba yak'arasa magana yana kallon cikin idonta.
Haleesa tarausayar da kai had'e da marairaice murya tace ba don kace na yi maka shishshigi ba da nace wane irin cuta ne yake damunka"?
''Har Habeeb ya bud'e baki da sunan ya zaiyano mata buk'atarsa sai kawai wani 6angare na zuciyarsa ya kwa6e shi _haba Habeeb kai fa jarumin namiji ne Wanda ba ya sauya magana ko ka manta da irin furucin da ka yi akanta ne"?_ _kana furta mata abunda ka ke da buk'ata za ta d'auka kamar kana sonta ne alhali kai ba sonta ka ke yi ba karka sake ta fahimce halin da ka ke ciki domin girmanka zai zu6e a wurinta_
"Habeeb ya dawo daga duniyar tunani ya sauke ajiyar zuciya ya tsayar da idanunshi akan fuskar Haleesa, wance tun lokacin da ya afka tunani ta kafenshi da ido jikinsa a sanyaye yasake mata hannu ya juya mata baya.
''Haleesa ta yi shiru tana kallon bayansa tsawon lokacin ta dauka a haka daga bisani cikin sanyin murya ta kira sunansa, _yaya Habeeb_
A fusace ya mik'e zaune ya galla Mata harara _look I don't want any disturb now so leave my room_
Haleesa ta kad'a kai batayi mamakin jin wad'annan kalamai daga bakin Habeeb ta mik'e tsanm! Sum-sum tafice Batare da ta furta uffan ba
yayinda Habeeb yabita da kallo ya ja iska yafesar yana tsotsan bakinshi, ya koma ya kwanta da yarufe ido Haleesa yake gani yakasa bacci sai fama juyi yake akan bed bacci ya k'auracewa idonsa, ji yake yi kamar ya mik'e ya je room d'inta ko k'amshin jikinta yashak'a ya tabbata zai same sauki abunda yake ji a game da ita a haka bacci ya sud'ad'o ya sace shi batare da ya nemawa kansa mafita ba.
''Ta6angare Haleesa kuma ita ma hakan ce tafaru da ita da ta rufe idanu Habeeb Lamido take gani, yayinda wani bak'on al-amari yake ziyartar jininta da kyar tasamu baccin yadauke ta.
**********************
_WASHE GARI_
_10:15am_
Haleesa na tsaye a dining area tana jejjera breakfast akan dining table, tana kamallawa tanufi part d'in Habeeb.
"Kwance ta tararda shi akan _3 seater_ idanunshi a rufe jin sallamarta yasa ya bud'e idanu kallo d'aya ya yi mata yadauke kai _ina kwana yaya Habeeb ya lafiyar jiki"?_
"Lafiya! Ya amsa ya a dak'ile.
Breakfast na jiranka tafad'a cikin murmushi
Tabe baki ya yi a tsarina sai 11:00 o'clock nake taking breakfast yak'arasa magana had'e da lumshe idanu.
"Haleesa ta yatsine fuska tanemi kujerar da ke facing d'inshi ta zauna, ta rafka tagumi.
''Ke! Ya kira sunanta a nitse da sauri Haleesa ta dube shi, still idanunshi a rufe ke! Zo nan yak'arasa magana had'e da yafito ta da hannu jiki a sanyaye Haleesa ta mik'e tanufi wurinshi.
''Ganin idanunshi a lumshe yasa tace yaya Habeeb gani
Na ganki mana ko angaya miki ni makaho ne da za ki ce min ga ki yana magana ne had'e da bud'e ido d'aya
"Um.....Haleesa tafad'a tana turo baki ya gyara kwanciyarshi cikin isa da tak'ama yace tausa za ki yi min ina fatar kin iya"?
A tsorace ta waro ido umh......umh....a wane waje zan tausa ma"?
"Bayanshi