Showing 66001 words to 69000 words out of 132766 words
galla masa harara da jajaye idanunta har da laifinka yaya Hasheem me yasa ka sanya JC d'in da yaya Habeeb yake amfani da shi baya kuma kasan kun yi kama saida yafika kyau tak'arasa magana tana murgud'a baki
Hasheem yarufe baki yana dariya bisa wannan dalili naki zai sa na fasa amfani da JC da raina yakeso"?
Ammi ce takar6e zance ta hanyar cewa rabuda ita kawai Hasheemu tsabar shirme ta ne, ya motsa
Hasheem yana dariya ya mik'e Ammi ni zan wuce gida na ji amfara kiran sallah magariba har ya juya yak'ara dawowa Ammi ba fa Haleesa ita kadai bace tare take da Habeeb Lamido yana k'ofar gida''
A tsorace Haleesa tad'ago sai lokacin ta tuna da Habeeb Lamido nan take gargad'i shi yafad'o mata a rai.
"Ammi ta girgiza kai had'e da cewa Allah yaye miki wannan matsala Haleesa don lamarinki sai addu'a Hasheemu kace da shi yashigo Hasheem yafice a k'ofar gida ya tarar da Habeeb yana alwala da roba ruwan faro Hasheem yadanne zuciyarshi yace "Yalla6ai da ka bari na kawo maka buta
Fuskar nan a had'e yad'ago karka damu abokinaa na gode
Bala ya yi karaf yace ni ka kawo min a matse nake ina so in kama ruwa
Wani mugun kallon Habeeb ya watsa masa da sauri Bala yadauke kai tamkar bai ga kallon da Habeeb yake masa Hasheem yashiga gida bai jima ba yafito sanye da jallabiya hannunshi d'auke da buta ya mik'awa Bala
Habeeb yace abokinaa ina zan sami masallaci mu je na nuna maka yana farko layi watakila don ba ka lura bane da za Ku shigo da ka ganshi
Humm....Habeeb yafad'a a takaice
Ammi ta dube Haleesa tace har tsawon wane lokacin za ki dauka kafin ki dawo mutum"?
Haleesa ta sada kai k'asa tarasa amsa da za ta ba Ammi
Wannan ya ba Ammi dama tasoma yi mata fad'a mai had'e da Nasiha daga bisani tace tashi ki je ki yi sallah Haleesa ta tashi jiki a sanyaye Imaan tashigo da 'yar sallama ta Haleesa tariko hannunta
Ammi na ganinta tagane ita ce 'yar Habeeb Lamido
Akan hanyar su Habeeb na zuwa masallaci idanunshi suka sauka bisa symbol na ```Ni da yaya Habeeb tailoring center ``` rubutu ya ja hankalinshi har yatuna da zobe Haleesa da ta ta6a yarwa a Lagos yatsinta, a zuciyarshi yace _Humm..... Wannan Habeeb d'in yana da matuk'ar mahimanci a rayuwa Haleesa ya riga yagama da zuciyarta shine ni kuma mom ta had'ani da ita yaushe na ke da lokacin soyayya da k'aramar yarinya ae sai ajina ya zube_
Ya wani tabe baki a haka suka k'arasa masallaci saida ya jira akayi sallah isha'e sannan yafito, a k'ofar masallaci yatarar da Bala da Hasheem sai kuma salman da yazama ciko na ukunsu suna fira, yadda a kullum abinci Kara tsada yake rayuwa talaka Nigeria tadawo abar tausayi, abunda ya ji Bala yana fad'a kenan Habeeb ya girgiza kai a zuciyarshi yace su Bala an sami abunda akeso kalli yadda ya karkace baki yana zuba yak'arasa wurinsu ya gaisa da yaya salman daga bisani suka dunguma zuwa gida akan hanya Habeeb yake sanarda yaya salman tafiyar Haleesa abuja cikin sigar zolaya yaya salman yace _yalla6ai kace za ka k'ara nisantani da k'anwataa"?_
Murmushin k'arfin Hali Habeeb Lamido ya yi a cikin zuciyarshi yace dama za ka rabani da ita da ka taimakawa rayuwata, a baiyane kuma sai yace mafi yawa hark'oki na nafi yi su a abuja da Lagos ka ga bai kamata ina abuja k'anwarka tana yola ae sai ka zargeni da rashin bata kulawa yaya salman ya yi 'yar dariya had'e da cewa wannan gaskiya ne yalla6ai da haka suka k'arasa k'ofar gida, yaya salman ya yi wa Habeeb iso zuwa cikin gida har k'asa Habeeb ya durk'usa ya gaida Ammi yaya salman yace Ammi ina Haleesa"?
Ammi tace tana d'akinta
Yaya salman yanufi d'akin ya tarar da ita tana sallah yajuyo yace Ammi sallah ta ke yi in tagama ki ce da ita zan kirata a waya saboda sauri nake zan koma shago akwai Wanda yake jirana yaya salman ya sake mik'a wa Habeeb Lamido hannu sukayi musabaha salman yafice
Imaan da ke zaune a gefen Ammi tana ci tuwo tace Daddy Ammi tabani tuwo mai dad'i
Habeeb ya yi murmushin yak'e yace to yi maza ki cinye karki ragewa Bala
Ae kuwa da sauri Imaan ta yaki katuwar loma Ammi na mata dariya
"Shiru-shiru Haleesa bata fito ba yayin da Habeeb yake duba wrist watch d'in ke daure a hannunshi Haleesa kuwa tana gama sallah ta haye mattress ta kwance rub da ciki ganin Hasheem da ta yi yataso mata da tsohu mik'i na rashin yaya Habeeb a hankali take rera kuka
Habeeb yak'ara duba agogo hannunshi ya ga _9:00pm_ ta yi ga shi kuma yanada appointment da manager company shi sun yi da shi za su had'u k'arfe _8:30pm_ duk duniya ba abunda Habeeb ya tsana irin sa6a alk'awali yana matuk'ar girmama lokacin yawan duba agogo da yakeyi ya ankarar da Ammi tace wai wace irin sallah ce Haleesa take yi"?
Da sauri Habeeb yace Ammi bara na duba ta ya mik'e yanufi d'akin a dai-dai k'ofa ya tsaya kamar mai shawara daga bisani ya yanke shawara shiga ya bankad'ala curtain{lubulle} yana shiga idanunshi suka sauka bisa bango d'akin hotuna marigayi yaya Habeeb ne birjik kowane hoto Haleesa ta yi rubuta kalamai soyayya masu zafi a k'asa shi a hankali Habeeb Lamido yake karanta rubutu _I love you yaya Habeeb I can't live without you_
_you are d only men I love live without you is miserable_
_I love you yaya Habeeb more than my own life I will continue to love you for d rest of my life_
Da sauri Habeeb Lamido yadauke idanunshi ya mayarda akan mattress ke! Ya kira Haleesa shiru ko motsi bata yi ba jin yake yi kamar ya narka mata mugun bugu a gadon bayanta, amma yana ji tsoro kada ta kurma ihu Ammi ta ji sannu a hankali yakai hannunshi kamar Wanda zai ta6a kashi ya d'an bubbuga bayanta ke! Bacci ki ka yi ne"?
A firgice Haleesa ta mik'e zaune rigarta ta yaye cinyoyinta suka baiyana ta ja baya ta jigina a bango ta yi duru-duru da jajaye idanuta
Habeeb ya kafa wa cinyoyinta ido take ya tuna da mafalki da yata6a yi ya ja iska yayin da Haleesa ta kafe shi da ido yad'ago yana tsotsa bakinshi kamar mai tsotsa sweet kallon ido cikin ido su ka yi wa junansu Haleesa ce tafara d'auke idanunta saboda bara ta jure cigaba da kallo eye's ball d'in shi yana mata kwarjini matuk'a a zuciyarta tace ina mamaki wannan d'abi'a ta yaya Habeeb sai dinga Jan iska kamar Wanda yaci yaji ga wani tsotsa baki da yake kamar mai sha sweet kuma da alama wannan d'abi'a ta bi jikinsa amma fa wannan d'abi'ar tashi tana burgeni kuma tak'ara masa kyau kai Habeeb Lamido kyakyawa ne ajin farko "Habeeb Lamido yak'ara yadda ganinshi akan jela gashin kanta da ke reto a bayanta a cikin zuciyarshi yace _ashe yarinya nan 'yar duniya ce hadda attachment take sakawa na tsani mace mai saka gashin doki_
Ya ja tsoki yak'ara murtuk'e fuska ke ki tashi mu tafi mana gaba d'aya Haleesa ta rikice jikinta na rawa ta d'auki mayafinta yana gaba tana biye da shi a bakin k'ofar Ammi ya tsaye ya yi mata sallama yaciro bundle na 'yan N1000 ya ajiye mata yafice da sauri domin yasan halin Ammi za ta iya cewa bara ta k'ar6a ba Haleesa tadauke imaan wance tuni ta yi bacci Ammi tak'ara gargad'i Haleesa ta bi mijinta sau da k'afa a k'ofa gida Haleesa ta tararda Habeeb da baffanta suna fira ta runsuna ta gaida baffa a gurguje tashiga gidansu marigayi yaya Habeeb ta gaida inna mairo zainab ta yo mata rakiya sai fama tsokana ta take yi ita ma kyautar kud'i Habeeb ya yi mata Ya kuma bata bundle gudu biyu yace bayan yatafi ta ba wa baffa da baba Audu domin yasan matuk'ar ya basu da kanshi bara su k'ar6a ba Bala ya bud'e musu k'ofar mota Haleesa ta zauna a seat d'in baya tana rungume da Imaan tun lokacin da suka d'auki hanya sanyi Ac ya ratsa Haleesa tafara gyagyadd'i a k'ofar gidan Alhaji bashir manager Bala ya yi parking Habeeb yafice yanufi cikin gidan yabar Haleesa da Bala a mota Bala yana ta zubawa Haleesa surutu tun tana bashi amsa har bacci ya yi nasara d'auke ta sai misali karfe _10:30pm_ Habeeb yafito daga gidan Bashir manager a lokacin tuni Haleesa ta yi nisa da bacci "Bala ya dube Habeeb yace Boss mutane nan naka gaba d'ayansu sun yi bacci
Habeeb ya mak'e kafad'a alama I don't care har suka isa gida Haleesa batasaniba tana ta sharar bacci Bala ya yi parking Habeeb yafito dauke Imaan daga jikin Haleesa yasoma tayar da ita ke tashi mu iso gida Haleesa ta yi wani juyi ta gyara kwanciyarta
Bala yayi karaf yace Boss yadda ka ga amarya ta gyara kwanciyata za Ka iya kai gobe kana tayar da ita bata tashi ba kawo Imaan na shiga da ita ciki ka dauki Haleesa Habeeb ya galla masa harara angaya maka ni d'an dako ne da zan d'auke ta"?
boss ba fa yau kafara daukarta ballatana nace abun zai zo maka banbarankwai
Cike da jin haushi Habeeb ya ja tsoki ya sunkuya yadauke Haleesa ya ji kamar yadauki Imaan Sam bata da nauyi a parlour ya shinfid'e ta bisa 3 sitter ya karbi Imaan yakaita bedroom Bala ya yi masa sai sa safe yafice Habeeb ya yi tsaye yana kallon Haleesa nan take ya kudurta wani Abu a cikin zuciyarshi yasaki murmushi mugunta...........
Jeeddah Aliyu🌹
[14/11 5:46 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```69```
~~kitchen ya shiga ya bud'e fridge ya d'auko roba ruwan Mr V masu sanyi gaske, fuskarshi d'auke da wicked smile yadawo wurin Haleesa.
''Baiwa Allah tana ta sharar baccinta ya balle murfi ruwan ya juye mata su a jiki Wani irin zillo Haleesa ta yi kamar za ta shed'e ta mik'e zaune bakinta d'auke da kalma shahada, tasauke ajiyar zuciya mai k'arfi ta tsurawa Habeeb ido sosai ranta ya b'aci da wannan wulaqanci da Habeeb ya yi mata.
Habeeb ya yi flinging da empty roba ruwa saida yak'are mata kallon wulaqanci, yace ke wannan kallon na menene ko za ki rama ne"?
"Girgiza kai ta yi A'a ta furta a sanyaye amma inaso kasani wulaqanta d'an Adam ba abu ne mai kyau d'an Adam yanada matuk'ar daraja bai kamata ya zama abun wulaqantawa a gareka musanmman ni da nake matarka ta sunnah tak'arasa magana had'e da sada kai k'asa.
"Habeeb ya ja iska jikinshi ya yi sanyi sai kawai ya tsince kanshi da rashin jin dad'i abunda ya yi mata kalamanta sunyi masifar ratsashi amma bayaso ya nuna mata kada ta yi tsanmani tafara samun matsayi a zuciyarshi.
''Ke wannan dad'i bakin naki bara sa nafasa yi miki abunda na yi niyya _so you better keep quiet & listen to me_
Idanu Haleesa suka ciko da hawaye bata yi k'ok'ari hana su zubowa saboda ita ma tana buk'atarsu a wannan lokacin.
D'aya bayan d'aya yafara magana kamar Wanda aka yi wa dole _Do you think zan yi dakonki tun daga compound har izuwa parlour a banza"?_
Sai lokacin Haleesa tafara raba-raba idanu har ta yi nasara gane Inda take tasauke eye's ball d'inta a fuskarshi ta yi k'asa da murya tace ka yi hankuri yaya Habeeb bansan lokacin da na yi bacci a mota ba.
"Yakara had'e fuska kin ga malama ni ba hankuri nace ki bani kawai ki biyo ni a bedroom d'ina, ki sauke Hakke na da yarataya a wuyanki
"Numfashin Haleesa yadauke chak tana wani muzu-muzu da ido tsoro ya baiyana k'arara akan fuskarta
Cikin gadara ya daka mata tsawa ke! Bara ki tashi ba"?
Babu shiri ta mik'e zubur ruwan da zuba mata suna d'iga daga jikinta, wuce mu tafi yafad'a chan k'asan mak'oshi Haleesa tana gaba yana biye da ita a rud'e take haura stairs ta zame saura kiris ta fad'i ta rike karfe.
''Habeeb ya ja tsoki yace ke ki yi hankali fa karki je wurin tunaninki na banza ki illata kanki a wofi.
Haleesa ta kasa gane inda kalamansa suka dosa hannunta na, rawa ta bud'e k'ofa ta jigina a wardrobe tana muzurai.
Habeeb ya dube ta ya tabe baki ya matsa daf da ita a rikice ta matsa yak'ara matsa ''very close to her har ya na ji heartbeat d'inta ya yatsine fuska k'asa-k'asa yafara magana kamar mai rad'a ke wace irin bad thinker ce ga ki 'yar ta tsutsuwa amma sai d'an banza tunani ke me kike tunani za ki yi min a wannan k'anana shekaru naki"?
Haleesa ta yi shiru gabanta na cigaba da fad'uwa Dallah! matsa ki bani wuri yafad'a had'e da tureta Haleesa ta koma gefe tana kallonshi ya bud'e wardrobe yace ke dama luggage d'ina nakeso ki had'a min gobe around _7:30am_ flight d'inmu zai tashi in nace da safe ki had'a za ki iya b'ata min lokacin saboda na fahimce siririta a jininki yake yak'arasa magana had'e da kallon fuskarta.
''Haleesa tasauke sanyayar ajiyar zuciya tanufi wurin wardrobe da sauri Habeeb ya matsa yace ke kafin na fito daga bathroom ki tabbata kin cire wannan rigar naki karki jik'a min rugs yanuna rugs carpet d'in da hannunshi Haleesa ta yi masa kallon mamaki a zuciyata tace dube shi dallah sai kace bashi bane ya jik'a ni tana kallonshi har yashige bathroom ta Ciro d'aya daga cikin jallabiya shi ta cire rigar jikinta tasaka 'yar k'aramar trolley ta janyo ta loda masa kayanshi tana yi tana gyangyad'i bacci yaci k'arfinta a hankali ta sulala k'asan rugs bacci mai dad'i ya yi awo gaba da ita Habeeb ya gama wanka yafito ya yi tsaye sororo yana kallon Haleesa yadda ta yi kwance ta dunk'ule a wuri d'aya ya yi bala'e bashi dariya da shi gwanin dariya ne da abunda zai hanashi kyakyatawa, kawai ya yi murmushi a zucyarshi yace kai wannan yarinya akwai bacci tsiya ya gyara mata kwanciya sai lokacin ya lura da jallabiya shi a jikinta yak'ara sakin murmushi mai sauti ya bud'e wardrobe yadauko blanket ya rufa mata ya sanya kayan bacci ya haye bed.
*********************
Kiran sallah asuba ne ya falkar da Habeeb ya yi mik'a had'e da addu'a tashi daga bacci, ya zuro k'afafu shi har ya tsallake Haleesa sai kuma yadawo ya shiga bubbuga hannunta ke, ke ki tashi asuba ta yi a hankali ta bud'e idanunta ta ware su akanshi a tsorace ta mik'e zaune.
"Habeeb yashige bathroom da sauri ta mik'e tanufi bedroom d'inta sai da ta sauya kayan jikinta sannan tashiga bathroom ta yi brush had'e da alwala tana gama sallah ta bud'e Qur'ani ta yi tillawa.
_7:15am_
"Habeeb Lamido yafito cikin shirin tafiya yasha black suit sunyi matuk'ar yi masa kyau jikinshi na fitarda fitinane k'amshi kaitsaye ya murd'a handle bedroom d'in Haleesa tana kwance akan pray mat d'in tagama sallah ga Qur'ani ajiye a gefenta.
"Habeeb ya girgiza kai sleeping sickness yafad'a a baiyane chan k'asan mak'oshi yasoma kiran sunanta da yake baccin nata baiyi nisa ba nan take ta falka yana tsaye hannaye shi zube cikin aljihu.
Muryarta na rawa tace _ina kwana yaya Habeeb"?_
Tafad'a had'e da d'an runsunawa.
_Lafiya lau_
Yafad'a a takaice
Tsawon _10 second's_ yadauka yana nazari daga bisani ya aza briefcase d'inshi a gefen bed d'inta ya zuge zip yaciro 2 bundle na 'yan N1000 ya mik'a mata zaro idanu ta yi ta k'asa k'ar6a''.
K'ar6i mana yafad'a ciki angry voice ya za'a yi na baki abu ki ce bara ki k'ar6a ba"?
Jiki a ma ce Haleesa ta mik'a hannun biyu ta k'ar6a.
"Ajiye su a hannunki koda buk'ata ta taso miki sai ki yi amfani da su yak'ara Ciro ATM ya ajiye a gefen gado yaciro farar takarda ya rubuta code d'inshi yadaura akan ATM wannan ATM d'ina ne inda k'udin Hannunki suka k'are sai ki je bank ki ciro in kuma bakisan yadda ake yi Hannah ta rakaki tanuna miki yadda ake yi.
Har ya dasa aya kan Haleesa na sunkuye Yaya Habeeb duk me zan yi da wad'annan kud'i gaskiya sun yi yawa katafi da ATM d'inka wad'annan da kabani har kadawo bara iya kashesu. harara ya galla mata ba shawararki nake nema ba abunda nakeda ra'ayi ne, _11:30am_ flight d'inku zai tashi ticket d'inki yana wurin mom ki had'a kayanki driver da zai wuce da su shi zai sauke mu a airport kafin yadawo kin had'a.
"Haleesa tad'aga kai har Yajuya yasake dawowa ina phone d'inki"?
Haleesa ta yi duru-duru da idanu tace tana ciki wardrobe mamaki ya lullu6e shi me kuma waya yake yi a ciki wardrobe"?
''cikin sanyi murya tace basan yadda ake operating d'inta shiyasa na ajiye.
"murmushi Habeeb ya yi yace village girl kawai je ki dauko nagani ta bud'e wardrobe taciro kwalin wayar ta mik'a masa ya bud'e yaciro charger ya jona wayar a charging.
Yace ki bawa Hannah wayar za ta koya miki yadda ake operating d'inta kinji"?
Haleesa tad'aga kai had'e da cewa _Allah ya kiyaye hanya_
"Ameen Habeeb yafad'a yadauki briefcase da sauri Haleesa tace kawo na rik'a maka jakkar batare da yace komai ba ya mik'a mata ya wuce gaba tana biye da shi a compound suka ci karo da Bala.
Habeeb yace Bala sa'eed ya iso kuwa"?
"Eh Boss tun da asuba ya iso yana main gate yana jiran fitowar ka
"Shiyasa nakeso aiki da sa'eed Sam baya wasa da lokacin
Gaskiya ne "Boss
Habeeb ya juya wurin Haleesa yace kawo briefcase d'in ki koma Imaan tana bedroom d'ina tana bacci ki dauko ta ki rufe min d'akin.
Jikin Haleesa a sanyaye tajuya kaitsaye tanufi bedroom d'inshi ta tayarda Imaan ta yi mata wanka ta gyara masa room d'in tarufe k'ofa tanufi d'akinta ta had'a kayanta.
*******************
_11:30am_
Flight d'in su Haleesa yad'aga zuwa Abuja lokacin da flight d'insu ya yi landing driver madam Hindu ya zo, ya yi picking nasu zuwa gidan