Showing 15001 words to 18000 words out of 132766 words

Chapter 6 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87940

touch's d'in brown_ d'ikin Riga da siket bata d'aura d'an kwali ba ta yafa _kashkha veil brown colour_ tayi matuk'ar kyau jikinta na fitarda k'amshin _explore white body splash_ kaitsaye d'akin Ammi tashiga Ammi nagani ta ta zaro ido had'e da cewa Haleesa ke ce kuwa"?
Haleesa tayi murmushin mai sauti daga bisani tace kinga wani sabon sauyi a tare da ni Ammi"?
Ammi tak'ara bud'e baki da hanci tace ba sauyi d'aya ba Haleesa sauye-sauye
Haleesa ta kyalkyale da dariya tace kai Ammi dama fa ina wanka.
Miye amfani wanka da ko _versiline_ ba ki shafawa Kai Alhamdulillahi! Allah ya kar6i addu'a da muka share tsawon watani muna yi, Allah ya yi miki albarka Haleesa Allah yakawo miki miji nagari tamkar Habeebu ki.
_Ameen Ammi Haleesa tafad'a idauta cike da kwalla_
Da sauri tadanne hawayeta saboda bataso Ammi tagano cewa har yanzu da sauran rina akaba cikin sanyi murya tace Ammi _N100_ za ki bani na siyo awara,
Ammi tasaki murmushin farin ciki tace awara kuma Haleesa"?
Haleesa tad'aga kai Ammi tace bara kamal yadawo yasiyo miki
Dan Allah Ammi ki barni naje da kaina so nake na d'an mik'a 'kafata.
Ammi ta bud'e kwano samira ta d'auko _N200_ ta mik'a mata had'e da cewa kidawo mini da chaji kuma in kinje kin tararda layi ki bar kudi kidawo in kamal yadawo ya kar6o miki.
"Haleesa tace to! Ammi sai nadawo adawo lafiya Ammi tafad'a had'e da bin ta da kallon tausayi......
[28/08 5:17 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```25```

Haleesa na fitowa gidan baba Audu tashiga inna mairo na zaune tana yanka kunbewa, ta ji sallama Haleesa ta amsa had'e da d'agowa saura kiris inna mairo ta yanke yatsanta kasa hank'uri tayi saida ta furta abunda idanuta suka hasko mata wa nake gani haka kamar Haleesa"?
Haleesa ta rufe fuskarta da tafin hannuta tace ba kama bace inna nice'
Ikon Allah Haleesa sai yau aka fita daga takaba"?
Na ga anci kwalliya abunda muka jima bamu gani ba, masha Allahu _Allah yasa karshen damuwarki kenan_
Haleesa ta sada kai k'asa had'e da cewa _Ameen._
Inna ina zainab"?
Zainab na aike ta
To inna na tafi tajuya had'e da ficewa yayinda inna mairo ta share hawaye tausayin Haleesa da suka zubo mata.
A hankali Haleesa take tafiya tana sharar hawaye tasoma tunani rayuwar da tayi da yaya Habeeb abaya tun da da yaya Habeeb ya fahimce Haleesa na matuk'ar son awara, duk yamma sai yasiyo mata awara taci tun lokacin da yarasu ta daina cin awara don kawai yaya salman yafaranta mata duk yamma sai yasiyo mata kamar yadda Habeeb yake mata amma ta k'i ci ta aza kuka dalilin da yasa salman yadaina siyowa kenan.
Yau d'in ma da tayi wanka har da su kwalliya tayi ne don ta faranta ran Ammi, domin ta fahimce irin damuwa da Ammi take shiga a duk lokacin da taganta cikin damuwa.
Tana kaiwa dai-dai _Ni da yaya Habeeb teilorings center_ ta ja tayi tsaye ta tsurawa shagon ido kuka na 'ko'kari kunbce mata da sauri ta bar bakin shagon tana tafiya batare da tasan Inda take jefa k'afafuta sai da tayi tafiya mai nisan gaske sannan tagano har tafita cikin unguwar su ga kuma duhun magariba yayi domin a wasu masallatai an gama sallah gashi lok'o da tashiga babu mutane sosai take taji wani mashahuri tsoro ya lullube ta tajuya da sauri tanufi bakin titi wasu samari biyu da ke zaune a bakin wani ru6a6e d'akin jar kasa jerin kwala6e tutolin birjik a gabansu suna ta kwakwad'awa cikin su ga kuma tabar wiwi a hannaye su duba d'aya Haleesa ta yi musu ta kauda fuska d'ayan saurayin ya zunguri d'an uwansa yace baaba kalli wata tsalleliya cikaa, da alama za tayi zafi d'ayan na d'agowa ya hango Haleesa ya hadiye yawu cikin muryar 'yan kwaya yace mu je mu latsa 'yar banza, a lokacin d'aya suka mik'e had'e da bin bayanta Haleesa nagani haka ta kwasa da gudu yayinda samarin suka Mara mata baya gudu Haleesa takeyi iya k'arfinta har tayi kusan fita daga lok'on ko tsuntsun bata had'u da shi ba tak'ara 'kaimi wurin gudunta tana fita daga lok'on ta hango wani mutum tsaye fuskarsa na _facing_ titi yana waya hannushi guda cikin aljihun wandonsa na _dark blue colour suit_ a hargitsi Haleesa ta isa wurinshi bayansa ta rungumo had'e da cewa........


```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```


Jeeddah Aliyu🌹
[28/08 9:58 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [28/08 6:48 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```26```

Dan Allah mallam ka taimake ni 'yan iska ne suka biyoni, ta'karasa magana had'e da 'kara chukuikuiye shi batare da yajiyu ba yasa hannu yajanyota suna facing juna ya kalle ta ya kawar da kai yayinda Haleesa ta zaro ido kafin kace kwa6o ta fara hawaye jikinta yad'auki rawa numfashinta yafara kai da kawo daga bisani ta tsalla ihu ta langwa6e da sauri yataro ta tafad'a bisa 'kirjinsa a some samari nagani Haleesa tanufi wurin wannan mutumi suka arce na kare yadauke ta chak yanufi inda yayi driven shi _parking_ da sauri _driver_ nashi ya bud'e masa k'ofa ya shinfide ta a _seat_ d'in baya ya rufe k'ofa ya zauna a _seat_ d'in gaba yayinda _driver_ yaja mota suka halba kan titi saida sukayi tafiya mai nisa driver yajuya ya dube ubangidansa cikin girmamawa yace _boss_ ina mu ka nufa"?
Tsawon _5 minutes yadauka kafin yabashi amsa cikin husky voice yafara magana guda-guda kamar mai bita_
_mu tafi gida kawai_
Boss" gidanka ko na maigida"?
Wannan karon saida yaja d'an k'arami tsoki da ke nuna yafara gajiya da tambayoyi driver nashi.
A yatsine yace _gidana_
_okay boss_
Wani tsalele gida mai matuk'ar kyau _driver_ yadosa _horn d'aya yayi sai ga gate d'in yana bud'e kansa kaitsaye yanufi parking space yayi parking_ da sauri ya yafito ya budewa boss k'ofa saida ya gama shan 'kamshinsa sannan yafito _drivern_ yasada kai k'asa yace "boss ya za'a yi da wannan yarinya"?
Shiru ya yi kamar mai nazari daga bisani yace kai zan tambaya Bala saboda kai kasan yadda za'ayi da ita.
Bala ya zaro idanushi masu kama da na 'yan _Philippines_ yace "boss ni kuma"?
Tsawa yadaka masa ta hanyar cewa dallah mallam zo bud'e mota da gudu Bala driver ya zagaya ya bud'e k'ofa kamar yadda yasakata mota haka yadaukota yanufi cikin gida da ita Bala driver yana biye da shi bisa _three star_ ya shinfid'e ta yajuya wurin Bala driver _yace kira Dr yazeed_
Cikin rawar murya Bala driver yace _boss suma na tayi ruwa kawai za'a Shafa mata ta tashi_
Cikin tafarfasa zuciya yace _you're very stupid Bala dama kasan ruwa kawai za'a Shafa mata tafarfado kasa na dinga dakonta"?_
"Sorry boss nayi tsanmani akwai wani amfani da za tayi maka
Wani mugun kallon ya watsawa Bala tuni Bala yagano abunda yake nufi jikinsa na rawa yace _ayi han'kuri boss subul da baka nayi_
Cikin zafin rai yace za ka zo ko za ka tsaya bani hank'uri ne"?
Da kyar Bala ya ja k'afafushi yanufi wajensa zara-zara yatsun sa yasaka ya wankawa Bala mari, yace kuma nayi _increase salary_ ka a wannan wata magana na karshe ka tabbata kafin na sauko yarinya nan tafarfado ka maida ta inda ka d'auko ta.
Bala driver yace _"yes boss_
Cikin tafiya kassaita ya haura _stairs_ yayinda Bala driver yabishi da kallon takaici daga bisani yanufi _fridge_ yadauko robar ruwan faro ya bulbulawa Haleesa a jiki a firgici ta mik'e zaune had'e da kurma razanane ihu daga bisani tafara zarar ido tayi wuk'i-wuk'i ta k'arewa _parlourn_ kalli jikinta na makyarkyata cikin matsananci tsoro tace "Bawa Allah me nayi muku kukeso Ku cutarda ni"?
Bala driver ya kwada mata harara yace dallah tashi mutafi tun kafin boss yafito yak'ara tafka mini tsiya
Haleesa ta'kara tsorata kafin tasami abin cewa bala driver yafisgo hannuta suka fice yayinda Haleesa ke ta faman yi masa magiya kada ya cutarda ita mota yajefa ta kaitsaye unguwarsu Bala driver yanufa, Haleesa nagani ankawo unguwar su tace ajiye nan tun kafin bala driver yak'arasa parking ta balle k'ofa tafita tun daga nesa ta hango yaya salman da hasheem da su baffa tsaye a k'ofar gida gabanta ya yi munmuna fad'uwa........
[28/08 8:02 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```27```

Cikin yanayi na mutuwar jiki tak'arasa wurinsu jikinta na rawa harara salman ya galla mata, had'e da cewa don gidanku ina kika fito"?
Haleesa ta zube k'asa tasaki kuka mai matuk'ar ta6a zuciya cikin bacin rai baffa yadaka mata tsawa tashi maza ki shiga gida mutuniyar banza marar tawakalli da gudu Haleesa tashige gida kaitsaye d'akinta tashiga ta rufe k'ofa tayi kwance rub da ciki tasoma zance zuci naga takaina ni Haleesa miyasa nake masifar tsoron mai siffa larabawa"?
Da gani fuskarshi mugu ne in banda mugunta na soma a maimako ya kaini asibiti sai yakaini gidanshi kuma da na farfado ban ganshi ba to ina ya shiga"?
Ta aikawa kanta rashin sani amsar tambyarta yasa ta lumshe idanuta tafara hango kyakyawar fuskarsa, da sauri ta bud'e idanuta hawaye suka ziraro mata tasaka bayan hannuta ta goge tana cikin wannan halin Ammi da baffa suka shigo sukayi mata tass dare ranar Haleesa batayi baccin kirki ba da tarufe idanuta _Handsome_ take gani sabon suna da ta rada masa kenan saboda sai yau ta'kara tabbatar da tsantsa kyau da yakeda shi.

```WASHE GARI ```

Haleesa ta tashi sukuku kamar marar lafiya alhani tsabar damuwa da fargaba had'uwa da _Handsome_ ne suka jagoranci Shigarta cikin wannan hali take taji garin Yobe ya yi mata zafi kamar daga sama ta ji muryar aunty juwairiyya da gudu tafito daga d'akinta ta rungumeta aunty juwairiyya tasoma yi mata kallon mamaki daga bisani tace Haleesa wai har yanzu baki dangana da rashin yaya Habeeb ba"?
Haleesa tayi rau-rau da idanu hawaye suka cika mata idanu, tasaki juwairiyya ta sunkuce 'karamin d'ata mai sunan baffa da suke kira Abba tashige d'akin Ammi tun zuwa juwairiyya suke ta faman fira da Ammi Haleesa na gefe bata ce 'kala ba Ammi tace wannan karon zuwan bazata mai sunan mallam yayi mana domin bamusan da zuwansa ba sai gani sa kawai mu kayi.
Juwairiyya tace wallahi kuwa nima bansan da tafiyar nan ba sai jiya masa'ud yake gayamin wani zai zo Yobe bikin bud'a sabon _company_ maigidansa shine na biyo shi.
Ammi tace ikon Allah dama maigidansa d'anan gari ne"?
"Eh Ammi d'an gidan marigayi Alhaji Muh'd maJeed lamido ne
Sai lokacin Haleesa ta tsoma bakinta cikin firar tasu ta hanyar cewa shine mamallaki _MAJEED LAMI'DO AIRLINES"??_
Kwarai kuwa shine wallahi mahaifiyarsa na da matuk'ar kirki baki yadda takeso ne tamkar ita ta haifeni.
Haleesa ta tabe baki ta yatsine fuska tace _Humm_
Ammi tace yaushe za Ku koma"?
Juwairiyya tace kwana biyu kachal za mu yi mu koma kinsa aikin _company_ ba hutu.
Haleesa tayi karaf tace aunty Juwairiyya in za Ku koma zan biki Ammi da Juwairiyya suka bud'e baki cike da mamakin furucin Haleesa da sauri Haleesa ta kauda fuska Saboda sunsan Halinta na rashin so zuwa wani gari sai gashi yau da bakinta tace za ta bi juwairiyya Lagos Ammi kan tsanani dad'i ne ya lullube ta lokacin da baffa ya ji labari, tafiyar Haleesa Lagos kaitsaye ya amince.


Jeeddah Aliyu🌹
[28/08 9:58 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [28/08 9:21 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹


```28```

Haleesa ta had'a kayanta tass na tafiya Lagos domin bata tunani, zata dawo garin Yobe da wuri so take ta nisanta da garin ko za ta rage damuwa da tunani yaya Habeeb.
Ranar da za su wuce Lagos tayi kuka tamkar ranta zai fita har suka je _Airport_ tana kuka wannan shine karo na biyu da ta6a zuwa Lagos shine kuma Karo na farko da ta6a shiga jirgi a rayuwata.

```LAGOS```
Yau kwana Haleesa biyu a garin Lagos duk da tun zuwa ta ko k'ofar gida bata lek'a ba amma yanayi gari yayi mata dad'i ta tsince kanta cikin farin ciki Wanda rabonta da shiga irinshi tun yaya Habeeb yana raye.
Haleesa tafito daga d'akin da aka ware mata tanufi _kitchen_ tana taya aunty juwairiyya aiki.
Aunty juwairiyya kinada _visitor's_ ne
naga tun safe kike ta faman girke-girke"?
Mahaifiyar maigida masa'ud daga Abuja za ta zo Lagos duk lokacin da ta zo Lagos sai na girka mata abinci kala-kala na kai mata saboda tana matuk'ar jin dad'i girki na.
_"Humm aunty juwairiyya tana jin dad'i girki ki ko dai kuna neman gidin zama Haleesa tak'arasa magana cikin dariya_
Juwairiyya ta kyalkyale da dariya daga bisani tace kai Haleesa kin shiga uku ko ma gidin zama muke nema ae muna da gaskiya zamani nan dole sai ana had'awa da hakan musanmman shugaban _company_ nasu akwai zafin rai tsiya Sam bayason wasa da aiki Haleesa tayi murmushin had'e da cewa ae shima yanada gaskiya.
Bayan sun kamalla girkin kowane su yasha _make up_ musanmman Haleesa da takeji jin kanta kamar sabuwa rayuwa za tayi a Lagos shiyasa lokacin da juwairiyya tace ba za ta bita ba sai tayi kwalliya batare da tace koma ba ta ca6a adonta cikin 'karamar atamfa _super Holland_ dark green da touch's din yellow tayafa _veil yellow colour_ ita kanta da ta dube mirror saida ta yabawa kanta.
Tana fitowa suka shiga mota masa'ud yaja mota suka d'auki hanyar _Victoria island_ masa'ud yafara tsokanar Haleesa ta hanyar cewa wannan irin kyau Haleesa ko d'an Lagos za ki samo mana"?
Haleesa ta turo baki had'e da cewa Allah ya kiyaye me zanyi da bayarbe"?
Masa'ud ya kyalkyale da dariya yace wayagaya miki yarbawa ne kadai a Lagos"?
Ni dai banaso Haleesa tafad'a kamar za tayi kuka
Masau'd yace to wa kike so"?
Haleesa ta galla masa harara tace kai!
Masa'ud da juwairiyya suka kyalkyale da dariya daga bisani masa'ud yace ni kan na juwairiyya ne kiyi 'ko'kari ki nemo naki ko kuma mu ba da sadakarki.
Haleesa kamar za tayi kuka tace Ni yaya Habeeb kadai nakeso tun da narasa shi saidai in mutu banyi aure ba ko kuma Ku bada sadaka ta.
Masa'ud da juwairiyya sai dariya suke mata har suka shiga had'adiyar unguwar nan ta masu kudin Lagos _Victoria island_ tafiya mai nisan gaske sukayi daga bisani suka nufi wani had'ad'e gida _gate_ d'in gidan kadai abin kallo ne _horn_ masa'ud yadanna bayan kamar _5 minutes_ gate d'in ya bude yadanna hancin motarsa yana shiga _securities_ suka taso saida sukayi _checking_ d'in motar masa'ud daga bisani suka barsu shiga gate na biyu saida bai kai tsaruwa na farko ba Haleesa sai zarar ido take tacigaba da kallon inda masa'ud yadosa wani karamin _parkin space_ yanufa yayi parking cikin zuciya Haleesa tace wannan shine na ba'ki a hankali ta mayarda idanu ta wurin k'aton _parking space_ mai d'auke da tsalatsala motoci lullube cikin _tenfold_ Haleesa bata sha kallo ba saida suka shiga cikin _main parlour_ gidan wata munmuna mata suka fara cikin karo da ita tana sanye da _black colour mini skeet da farar Riga gashi kanta lullube da attachment da sauri ta nufo waje su ta kar6i warmer d'in hannu masa'ud tanufi cikin wani karamin parlour yayinda su Haleesa suka Mara mata baya_
Kujera ta nuna musu masa'ud ne kadai ya zauna Haleesa da juwairiyya sukayi tsaye suna jiran matar tadawo ta kar6i Warmer's d'in hannu su........
[28/08 9:55 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```29```

Bayan matar mai kirar katti tazo ta kar6i Warmer's d'in sannan su Haleesa suka zauna bayan tadawo tace da su madam na zuwa tajuya ta koma inda tafito, a hankali madam Heendu take taka matakala bene fuskarta tadauke da murmushin da ke baiyanar da farin cikinta nagani bak'inta{visitor's} 'kamshin turare ta yadaki hanci Haleesa da sauri tad'aga kai ta dube ta kyakyawar fara mace kamar kata6a fatarta jini yafito kamanu matar kadai ya Haleesa ta kalla tagano cewa balarabiya ce tana sanye da tsadadiyar _combination shahada da material d'inki Senegal wuyanta yasha gold kirar Dubai_
Tana k'arasa shigowa _parlour_ masa'ud da juwairiyya suka mik'e tsaye gani Haleesa tak'i mik'ewa tsaye yasa juwairiyya ta galla mata harara dole Haleesa ta tashi tsaye madam Heendu ta rungume juwairiyya ta sunbace kumatu ta hagu da dama tajuya wurin Haleesa ta rungumo ta ta sunbace ta kamar yadda ta yiwa juwairiyya a zuciya Haleesa tace kutt yau kuma ga wata sabuwa bidi'a cikin girmamawa masa'ud da juwairiyya suka kwashe gaisuwa dole Haleesa tayi yadda ta ga sunyi daga bisani madam Hindu ta zauna sannan suma suka zauna a zuciyar Haleesa tace kai jama'a duniya ina za ki damu _kudin bala'i ne ita wannan ba matar President ba ba kuma matar governor ba amma don tsabar girmamawa sai ta zauna mutane suke zaunawa_ ta dube Haleesa tana murmuahin ras-ras gaban Haleesa yafadi domin tayi mata kama da wata halitta da ta6a gani kafin ta lala6o inda ta ta6a gani mai irin kamanu madam Hindu sai ta ji sautin murya madam Hindu tana cewa juwairiyya amma wannan sister ki ne" koh"?
Juwairiyya tace eh madam Hindu tace saidai tafi ki kyau 'yan mata ya sunan ki Haleesa ta hadiye yawu da kyar tace......



```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeddah Aliyu🌹
[29/08 8:09 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [29/08 12:13 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```30```

"Sunana Haleesa, _madam Hindu_ tace sunanki mai dad'i har yaso yafi na Juwairiyya dad'i tak'arasa magana cikin dariya Juwairiyya tayi murmushin tace _Allah mommy nima sunana yana dad'i_
Nima bance sunanki bai dad'i ba Juwairiyya amma na Haleesa yafi dad'i saidai matsala Haleesa bata magana.
Juwairiyya da masa'ud suka kyalkyale da dariya, Janet ta shigo hannuta rike da _tray_ da kwalaye _juice a sama had'e da glass cups ta ajiye bisa stool ta tsiyayawa su juwairiyya Haleesa ta kar6i cup d'in_ tana jujuya shi yayinda suka cigaba da firar su Haleesa kanta na sunkuye tana saurare firar tasu, tsawon _2 hour's_ suka share suna fira daga bisani masa'ud ya mik'e tsaye yace madam bara mu barki ki huta sai gobe insha Allah zan shigo mu yi magana akan wance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login