Showing 27001 words to 30000 words out of 132766 words

Chapter 10 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87933

ka fita ne batare da Bala driver ko kana nufi kai za ka yi driving da kanka"?
Whatever! yafada kaitsaye
Look son I known you can't drive musanmman yadda ababe hawa suke cikoso a gari Lagos kayi han'kuri kutafi da Bala.
Dafe goshi ya yi da alama yafara gajiya da surutu mommy nashi mom bana bukatar Bala I can managed with myself amma ke za ki iya d'aukar shi aiki "Co's I don't need him anymore madam Hindu tayi murmushi tace banaso fitarka kai kadai Habeeb ka yi hankuri kutafi tare da sauri Bala ya zube gabanshi yace am sorry Boss nasan nayi laifi amma ba zan 'kara ba Haleesa ta ja tsoki a zuciyarta tace dube yadda ake rarrahinshi sai kace Wanda aka yi wa wani laifi, d'an reni wayo kawai wallahi na tsini mutum mai girman kai muryarshi ta katsiwa Haleesa zance zuci ta baza kunnenta domin taji abunda zai fada mom na tsani mutum mai surutu a rayuwata sai kuma gashi shine halaya Bala duk abunda idanushi suka gane mishi, sai yafallasa yak'arasa magana had'e da gallawa Bala harara madam Hindu tace duk abunda bakaso daga yau zai kiyaye Habeeb ya mik'e kafad'a had'e da cewa mom I have to go!
Yajuya yafice daga parlour madam Hindu tajuya wurin Bala tace tashi kutafi Bala da sauri Bala ya mik'e yabi bayanshi, Haleesa ta tabe baki tacigaba da zance zuci ta kai amma wannan guy ya kware da wulaqaci sunanshi Sam bai dace da shi ba saboda yaya Habeeb d'ina is very simple man da kyar ka ga yaya Habeeb d'ina yayi fushi amma wannan He is always angry fuska a muturk'e so arrogant.
Haleesa! Da sauri Haleesa tad'ago tace Na'am mommy!
Da alama kema zaman gidanan yafara isarki koh"?
Murmushi Haleesa tayi batare da tace komai ba madam Hindu ta mik'e tsaye had'e da cewa ina zuwa tanufi upstairs yayinda Haleesa tasaki ajiyar zuciya tace Allah yasa mayarda ni gidan aunty juwairiyya za tayi saboda jin kai na nakeyi tamkar prisoner ga zuciyata ta hanani sukuni na zama _heart restless_ musanmman duk lokacin da idanuna sukayi tozali da Habeeb, nakan tsince kaina cikin matsananci fad'uwar gaba.
Har madam Hindu tafito Haleesa bata sani ba saida tadafa ta a tsorace Haleesa tajuya, cikin tausayawa madam Hindu tace Haleesa kidaina yawan tunani Kada ya shafi lafiyarki murmushi Haleesa tayi madam Hindu tacigaba da fad'ar mu je ki rakani unguwa saboda na fahimce cewa kin gaji da zama guri d'aya tana gaba Haleesa na biye da ita har suka isa parking space da gudu "Driven madam Hindu yak'araso ya bud'e masu mota kirar _BMW 6 series_ Haleesa da madam Hindu suka parke a owner's corner yawo sukayi sosai Haleesa ta ga gari Lagos sai d'an banza go slow tsiya madam Hindu ta yi wa Haleesa shopping nagani nafad'a "ready made da jallabiya's masu matuk'ar kyau da tsada sai around 10:30pm suka dawo gida Aderwale ya yi parking ya bud'ewa madam k'ofa yayinda Haleesa ta bud'ewa kanta Aderwale yataya ta kwashe bag's had'e da ledoji da suka yo shopping a parlour suka zube kayan madam Hindu tace Haleesa ki k'arasa da kayanan ciki duka naki ne, Haleesa ta duk'a k'asa tayi wa madam godiya da sauri madam ta d'agata haba! Haleesa miye haka"?
Duk abunda nayi miki bana buk'atar godiya saboda na dauke ki tamkar Hannah Haleesa tayi murmushi tace duk da haka na gode mommy Allah yasaka miki da alkhairi.
Ameen Haleesa ki je ki kwanta madam nak'arasa magana ta nufi bedroom d'inta Haleesa ta kwashe kayan tanufi bedroom d'in Hannah, tsanani gajiya da ta de6o ga kuma bacci fal idonta yasa ta haura wrong stairs a maimako ta haura left wanda zai sadata da room d'in Hannah sai ta haura right na part d'in Habeeb kaitsaye ta murd'a handle tashiga...
[10/09 9:37 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```46```

Bedroom d'in Hàbeeb tana shiga ta jefarda kayan hannuta da yake d'akin akwai duhu Sam bata lura da, Habeeb da ke kwance wani juyi tayi tacire mayafinta had'e d'an kwalinta ta jefa bisa bed suka fad'a akan fuskarshi daga bisani tanufi switch ta kunna wuta haske yagauraye d'akin karaf idanuta suka sauka akan bed Habeeb na kwance ya yi matashi{pillow} da hannaye shi fuskarshi na lullube da mayafinta da jefa akan bed Haleesa ta zaro ido jikinta yadauki rawa tasoma ja da baya a hankali yacire mayafinta da ke kan fuskarshi ya jefa mata batare da bud'e idanushi yafara magana, d'aya bayan d'aya sai kace mai koyon magana _hey what's are you doing in my room at dis time"?_
Cikin sark'ewa halshe Haleesa tace I'm so..rry I made a mistake am looking Hannah's room but I'm so sorry.
_hey shut up I don't wants any apologies from you just pack your things & leave my room right now_
A tsorace Haleesa ta tattara kayanta jikinta na rawa ta bud'e k'ofa tafice tsanani rud'ewa yasa Haleesa takasa gane inda za ta dosa dole ta koma downstairs parlour anan tayi tsaye daga bisani ta haura stairs d'in zai sadata da room d'in Hannah tana shiga d'akin ta jefarda kayan hannuta, tafad'a kan gado tasoma zanci zuci wai gari yaya naje room d'in yaya Habeeb"?
Gaskiya nagaji da gidanan gaba d'aya naji garin Lagos yafita min a rai, tun zuwa na banyi waya da Ammi ba gashi na baro phone d'ina gidan aunty juwairiyya ballatana na kira yaya salman ya had'a ni da Ammi, mtss gidanan ban had'a komai da su ba yakamata zuwa yanzu ace nasan lokacin da zan dauka a gidanan, domin ba zan iya cigaba da zamansa, banaji ko 1week zan iya k'arawa a garinan.
Ta b'angare Habeeb kuma Haleesa nafita ya ja tsoki ko uban me yarinya nan ta zo yi a d'akina oho"?
Na tsani yarinya nan Sam banaso ganita duk lokacin da idanu sukayi arba da ita sai naji tsanarta na 'kara yad'uwa a zuciyata.

```washe gari ```

Tun misali 'karfe 10:44am Haleesa ta falka tayi wanka ta shirya cikin d'aya daga cikin jallabiya's d'in da madam Hindu ta siya mata rigar _black colour ce anyi mata ado da blue colour stone's_ tayi rolling da mayafin rigar duk da batayi make up ba she look very beautifully ta nemi gefen bed tayi zaune ta zabga d'an uban tagumi, zuciyarta cike da tunani yadda za'ayi tafita saboda tana masifar tsoron had'uwa da Habeeb idanuta suka cika da kwalla jin karar bud'e k'ofa yasa tayi maza ta goge hawaye fuskarta madam Hindu ce tashigo jikinta sanye da atamfar Sheraton tayi matuk'ar k'ar6a fatarta Haleesa me kikeyi a d'aki da har yanzu baki fito kiyi breakfast"?
Haleesa tayi murmushin yak'e tace mommy yanzu nakeso fitowa sai kuma ga ki'
To tashi mu tafi Haleesa na kamalla breakfast ta nufi 'karamin parlour ta zauna k'asa kamar yadda tasa6a, hankali madam Hindu tajuya wurinta, Cikin murmushi tace Haleesa har yanzu kin k'i kisaki jikinki sai wani d'ari-d'ari kikeyi Haleesa tayi murmushi had'e da sada kai k'asa 'kamshin turare intense man yacika parlour da sauri Haleesa d'ago idanuta suka sauka akan fuskarshi yana sanye da coat red colour da black colour trouser hannushi na cikin aljihu yayinda d'ayan hannun rik'e da file's fuskarshi a had'e Sam ba alama fara'a a tare da shi kaitsaye yanufi kusa da madam Hindu ya zauna kamar mai rad'a yace _Good morning mom_
Morning son da fatar katashi lafiya"?
_lafiya qalau mom_
Batare da Haleesa tad'ago tace ina kwana yaya Habeeb"?
Yayi ignoring nata tamkar wani kurma, yacigaba da maganarshi mom ga wad'anan documents za ki yi sign nasu zan wuce da su Abuja.
Madam Hindu ta bata fuska tace Habeeb bakaji Haleesa tana gaidaka"?
Ya yatsine fuska a wulaqance yace lafiya sani halinshi da mom tayi yasa batayi masa complain akan yadda ya amsa gaisuwan da Haleesa tayi masa sai kawai tayi ignoring nashi had'e da k'ar6a documents d'in tayi signing phone d'inshi yayi ringing ya mik'e cikin yanayi tafiyarshi ta k'asaita yafice, yayinda a fakace Haleesa tabishi da kallo, cikin zuciyarta tace banza d'an girman kai shi wannan da Allah yayi shi gidan sarauta da bansan iya adadi iskanci da zai dinga tsulawa mutane, madam Hindu ta katsita ta hanyar kiran sunanta Haleesa kar6i file's d'inan ki kai ma Habeeb nasan halinshi da mantuwa zai iya tafiya ya manta da su daga baya yadinga yi min k'orafi cikin sanyi sanyi jikin Haleesa ta kar6i file's d'in tafice tana fita ta hango shi a parking space Bala driver ya bud'e mishi mota zai shiga tazara da ke tsakaninsu zai iya tafiya kafin tak'arasa sai kawai tayi decided ta kwala masa kira yaya Habeeb tafad'a da k'arfi batare da yajuya ba ya tsaya chak gani haka yasa Haleesa ta kwasa da gudu Habeeb da ke tsaye zuciyarshi tamkar za ta kama da wuta jin sautin gudunta, yak'ara harzu'ka ya tsani ya ga mace na gudu da sauri yashige mota Haleesa ta'karaso tana sauke numfashin gudu da tayi, tadafa k'ofar mota tace yaya Habeeb gashi mommy tace nakawo maka,
Da k'arfi yafisge file's d'in har yana had'awa da yatsun Haleesa garin fisgar file's zobenta na azurfa yasa6ulle sakamako ramar da tayi zobe yadaina tsayuwa a yatsanta Haleesa ta matsa daga jikin motar tana yarfe hannu cikin k'unar zuciya yace da Bala kai! tsayuwar me kake yi ne"?
Jiki na rawa Bala ya bud'e k'ofa ya zauna a sit d'in gaba yayinda Aderwale driven madam Hindu yaja mota yanufi gate Haleesa tabisu da kallo daga bisani tanufi cikin gida zuciyarta cike, da d'ibin tsanar halaya Habeeb airport Aderwale ya ajiye su fitowar da Habeeb zai yi daga cikin mota zobe yafad'o daga jikinsa ya duk'a yadauki zoben yana jujuya shi ras-ras gabanshi yafad'i sakamako ganin sunan da ke rubuce a jikin zoben ```NI DA YAYA HABEEB ``` Yafad'a a baiyane me wannan sunan yake nufi"?
Meyasa gabana yafadi anyya kuwa yarinya nan ba bibiyana takeyi ba"? nan take, yatuna da haduwarsu da kuma ganin da yayi mata a gidansu......


```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[15/09 12:29 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [14/09 10:56 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```47```

Haleesa na Shiga cikin gida ta koma mazaunita ta zauna, madam Hindu ta dubeta cikin kulawa tace kin bashi file's d'in Haleesa"?
Haleesa tad'aga kai madam Hindu tacigaba da kallon tv yayinda Haleesa ta sada kai k'asa tasoma aikin nata{tunani} madam tajuya ta tsurawa Haleesa ido gani yadda ta zurfafa a tunani tausayinta yakamata nan take ta k'udiri anniya sai takawo karshen matsalar Haleesa saboda yarinya ta shiga ranta matuk'a.

```ABUJA```

Misali 'karfe _12:15pm_ flight d'in yadauko passengers daga Lagos yasauka a airport na Abuja, a hankali Habeeb Lamido yake saukowa daga stair's na jirgi Bala driver yana biye da shi a baya driven madam Hindu na Abuja ne ya yi picking nasu kaitsaye gidan Habeeb Lamido da ke Garki driven yadosa yayinda Habeeb Lamido ke ta fama da zance zuci na hadu da 'yan mata kala daban-daban ban ta6a haduwa da very smart girl irin Haleesa, zuciyata tana bani cewa Haleesa ta zo d'aukar famsa abunda na ta6a yi mata ko kuma ta fad'a a tarko sona shiyasa take bibiyana in kuwa d'aya daga ciki ya kasance gaskiya lallai sai na wulaqanta ta Co's ban ta6a haduwa da yarinya da naji farat d'aya na tsaneta irinta, kamar daga sama ya ji sautin muryar Bala driver yana fad'ar Boss mu iso gida Habeeb yasauke ajiyar zuciya had'e da yafito daga cikin mota.

```BAYAN KWANA BIYU ```

Haleesa na kitchen tana wanke plate's da cups d'in da sukayi amfani da su kasancewa yau Sunday Janet tana church, madam Hindu kuma tafita ba yadda batayi da Haleesa su fita tare Haleesa ta k'i a cewarta bataji dad'i cikin sanyi jiki take wanke plate's d'in K'amshin turare intense man da tashak'a ya haddasa mata fad'uwa gaba, Habeeb Lamido ne tsaye a k'ofar kitchen yana aika mata kallo mai cike da tsana Cikin tsanani tsoro Haleesa tajuya karaf suka had'a ido, da sauri ta sada kai k'asa Habeeb ya ja tsoki yak'arasa shiga kitchen d'in cikin muryarshi mai matuk'ar dad'i yafara magana kamar mai rad'a ke! Uban me kike jira a gidanan da har yanzu baki tattara komaitsa ki kibar mana gida"?
Wani irin shock yaja Haleesa jikinta yafara sharking, takasa furta uffan yadaka mata tsawa ke! Ba magana nakeyi da ke ba"?
Yak'arasa magana cikin k'unar zuciya muryarta na rawa tace Dan Allah kayi han'kuri ba laifina bane mommy ce har yanzu bata bani izzini tafiya gida.
_You're very stupid kina nufi mom ce mai laifi ashe bakida mutunci"?_
A lokacin d'aya mamaki had'e da tsoro sukayi nassara lullu6e Haleesa ko kwakwara motsi takasa yayinda haushinta yak'ara turnuk'e Habeeb a harzuk'e yafisgo hannuta yace wai ke me kike tak'ama da shi waye ubanki duk fad'in African da har zanyi miki magana kiyi ignoring nawa"?
Hawaye suka wanke fuskar Haleesa tsanar Habeeb ta kanainaye zuciyarta, da k'arfi ta fincike hannuta saidai kash takasa kwace hannu nata ranta a 6aci tace dallah malam kasake min hannu, kallon uku saura kwa6o ya watsa mata ya yatsine fuska cikin sigar wulaqanci yace ki kwace hannunki mana Haleesa ta girgiza kai tace kai kanka kasan da zan iya kwace hannun nawa ba bazan tsaya ina rok'a mutume da baisan daraja da k'imar d'an Adam irinka.......
[14/09 11:02 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```48```

Da k'arfi Habeeb ya murde mata hannu yace kin tafka babban kuskure na shigowa rayuwata tuni nagano cewa kina bibiyana, kuma sai na tabbata miki da cewa bansan daraja da k'ima mace banza 'yar iska irinki mai bin d'an namiji har gidansu da wannan Neman gindi zama da kike yi a wurin mom da fitowa kika yi kika fad'a mata gaskiyar dalili zuwanki gidanan.
Haleesa ta zaro manya idanuta masu cike da tsoro ta hadiye miyau masu masifar d'aci ta rushe da matsananci kuka tace karka jefeni da mummuna kalma yaya Habeeb don ina zaune a gidanku bashi zai baka damar ka fad'a mini magana son ranka, ka tambaye mahaifiyarka za ta fad'a maka dalilin zama na a gidanku. Habeeb ya galla mata harara had'e da cewa ke! Munafuka ni fa nagano cewa abu biyu ne yakawo ki a gidanan kodai kin zo daukar famsa wulaqanci da nayi miki a baya ko kuma kin zo neman soyayyata jin wannan furuci na Habeeb yak'ara rud'a Haleesa ta runtse idanuta tana kuka kamar ranta zai fita saboda zafi biyu Habeeb Lamido yahad'a mata ga zafin murd'e mata hannu da yayi ga kuma na magaganu da yake ta faman gasa mata, yayinda Habeeb yacigaba da cewa bara na fad'a miki ko a k'afa aka daura min ke zan kwance na yar Co's nafi k'arfinki infact ban ta6a jin na tsani wata 'ya mace sai akanki don haka kidaina yaudara mom ta hanyar ihun da kike yi kina cewa yaya Habeeb ya mutu ba zai ta6a dawowa gareki wai ke ga ki 'yar duniya Haleesa ta bud'e idanuta tasoma watsawa Habeeb kallon mamaki daga bisani tace tir da wannan duk'usashiya kwakwalwa taka da har ta tasanya maka tunani cewa ni Haleesa ina sonka me zanyi da kai bana d'aya daga cikin shashashu 'yan mata da kudinka da kyakyawa surarka za su rud'a kuma yau d'inan zan bar maka gidanku bara ka k'ara ganina ba har abada Habeeb Lamido ya ja tsoki wulgar da hannunta da k'arfi ya juya cikin tafiyarshi ta k'asaita yafita daga kitchen d'in Haleesa ta dur'kushe 'kasan tile's tafashe da kuka tasoma danasani zuwa garin Lagos da kyar ta mik'e tsaye ta nufi room d'in Hannah tafad'a kan bed tafara zance zuci ashe Habeeb Lamido mahaukaci ne in banda hauka don kawai ya ganni a gidansu zai ce ina sonshi mtss shashasha kawai mai k'aramar kwakwalwa nan take tafara tunina rayuwarta da yaya Habeeb da yaya Habeeb yana raye me zanzo yi a garin Lagos da har wannan arrogant zai same damar wulaqantani, Haleesa tacigaba da shashekar kuka madam Hindu ta murd'a handle tashigo d'aki ta hango Haleesa kwance tana kuka da sauri tanufe ta Haleesa lafiya me kike yi ma kuka"?
Cikin muryar kuka Haleesa tace mommy gida zan tafi, inaso gani Ammi naa nagaji da garinan tak'arasa magana had'e da rushewa da kuka madam Hindu ta rungume ta tace haba Haleesa don kinaso zuwa gida shine za ki dinga kuka"?
Yi maza ki share hawayenki ki tashi mu tafi na ajiye ki gidan Juwairiyya gobe masa'ud yasaka ki a flight ki koma Yobe da sauri Haleesa ta k'ank'ame mommy tace na gode mommy Allah yasaka miki da alkhairi, madam Hindu tad'ago ta tana murmushi tace Ameen Haleesa 'yar gidan mommy jiki na rawa Haleesa ta had'a kayanta madam Hindu sai faman dariya take yi mata had'e da tsokanarta a haka suka fice daga gidan zuciyar Haleesa cike da farin ciki tabar ma Habeeb gidansu, suna isa gidan Juwairiyya tun kafin Aderwale yabude mata k'ofa ta bud'e da kanta tafito Aderwale yabud'ewa madam Hindu k'ofa tafito tana dariya tace Haleesa sai murna kike yi za ki tafi kibar mommy koh"?
Haleesa ta rufe fuskarta da tafin hannuta Juwairiyya nagani su tafara washe hak'ora saboda kullum sai yaya salman ya kira waya ya tambayi Haleesa, madam Hindu ta zauna a parlour yayinda Haleesa tanufi d'akinta juice da ruwa masu sanyi Juwairiyya takawowa madam Hindu ta tsiyaya mata, a glass cup ta mik'a mata kur6a d'aya zuwa biyu madam tayi ta ajiye cup d'in bisa stool tajuyo tana facing Juwairiyya, tace Juwairiyya akwai magana mai matuk'ar mahimmanci da nakeso zanyi da ke akan Haleesa.....

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```


Jeeddah Aliyu🌹
[15/09 8:00 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [15/09 4:50 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```49```

Tun daga lokacin da nadaura idanuna akanta naji tashiga raina matuk'a, nayi matuk'ar tausayawa Haleesa a dalilin labari rayuwarta da yaya Habeeb da tabani gani halin da take ciki da Kuma yabawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login