Showing 3001 words to 6000 words out of 132766 words
ba tare da kin gaji ba.
Yaya Habeeb yace ke banaso iskanci ki ja min ita a hankali kada ki ji mata ciwo, zainab ta taro baki had'e da cewa to so kake yi mu k'ara yi latti a dake mu.
A dakeki dai domin ita ba Wanda isa yata6a ta, zainab ta kalle Haleesa suka kyalkyale da dariya zainab tace kinji wani sabon fi'eli koh"?
Haleesa tayi murmushi had'e da cewa yaya Habeeb kenan yana matuk'ar ji da ni tamakar tsoka d'aya a miya kamar ance Hal tajuya yaya Habeeb yananan tsaye Inda suka barshi yana, kallonsu ya d'aga takarda da ta bashi ya sumbace ta had'e da mannata a k'irji daga bisani ya bud'e takarda idanu shi suka hasko masa abinda Haleesa ta rubuta cikin d'aga murya yace ```I love you too Haleesa ``` da sauri ta rufe fuskarta zainab tace soyayyarku na matuk'ar burgeni Haleesa narasa gane tsakani ke da yaya Habeeb wayafi son wani"?
Haleesa tayi murmushi daga bisani tace zainab kenan ni kam ina da tabbaci son da nake ma yaya Habeeb yafi Wanda yake mini ina tsanani, son yaya Habeeb tamkar yadda uwa takeso d'anta duk buguwa numfashina, yana bugawa ne tare da kwayar son yaya Habeeb in har narasa shi tabbas rayuwata za ta tagaryara zan shiga k'unci mafi muni a rayuwa, ina sonshi wallahi zainab ina tsanani son yaya Habeeb soyayyarshi za ta iya jefani a kowane irin hali tak'arasa magana hawaye na zuba daga idanuta.....
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S```
Jeeddah Aliyu🌹
[24/08 8:51 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [24/08 7:16 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```6```
Haleesa ta lumshe idanu ta tsanani son yaya Habeeb yacigaba da ratsa jijiyoyi jikinta ya ziyarce sassan jini jikinta dama haka takeji a duk lokacin ta, taga yaya Habeeb ko kuma taji murya sa ya durk'usa ya gaida baffa.
Baffa amsa cikin sakin fuska yaya Habeeb yace baffa baba yace na fad'a maka yafito kai kadai yake jira"
Da sauri baffa ya ajiye rediyo shi ya mik'e tsaye had'e da cewa masha Allah dama shi nake jira Ammi tace adawo lafiya baffa yace Allah yasa yafice yayin da yaya Habeeb yajuya wurin Ammi ya gaidata ya zuguri yaya salman cikin tsokana yace sarki ci me aka sa mu ne da ba'a tayawa mutane"?
Yaya salman yayi dariya yace wallahi Habeeb ka rena ni ko manta da matsayi na, na siriki ka ne"?
Yaya Habeeb ya tabe baki yace ae ni banida siriki yajuya ya kalle Ammi ya d'an zaro ido yana dariya yace wai ashe Ammi na kusa"? Ammi ce kadai suruka ta Ammi ta kyabe baki had'e da cewa _Allah_ ya tsare ni da yin sarakuci da kai na barma inna mairo watakila ita za ta iya Ammi tak'arasa magana had'e da mik'ewa tsaye tashige d'akinta.
Yaya Habeeb da yaya salman suka kyalkyale da, dariya yaya Habeeb yace Ammin mu kenan.
yaya Habeeb na gani Ammi tashiga d'aki yasa k'afarsa ya d'an shuri k'afar Haleesa nan take taji wani irin yarrr tsigar jikinta ya tashi da sauri ta, rintsi idanuta.
Yaya Habeeb yace _babylove_ ba gaisuwa"?
Haleesa tayi murmushi cikin 'yar k'aramar muryarta tace ina wuni yaya Habeeb"?
Rik'e abarki banaso tun da sai da na rok'a.
Kamal ya kyalkayale da dariya yace _yeeee yau yaya Habeeb da aunty Haleesa sunyi fad'a I'm so happy dama ina jira ranarda za kuyi fad'a ni kuma nayi rawa har da tsalle_
Yaya Habeeb ya gallawa kamal harara yace wa yagaya maka anta da jini suna, fad'a"?
Ya juyawa wurin Haleesa yace ae mu bama fad'a ko Haleesa naa"?
Haleesa na murmushi tace kwarai kuwa ```NI DA YAYA HABEEB ```
Jini da anta ne bugun zuciyarmu d'aya mtss yaya salman yaja tsoki had'e da mik'ewa yace kai indan kagama shiririrka ina shago yad'auki buta ya wanke hannusa yafice yaya Habeeb ya kalle Haleesa suka kyalkyale da dariya ya bud'e kwano tuwon da ke gabanta yace babylove baki cinye abinci ki ba"?
Kai nake jira yaya Habeeb sanin kanka ne komai tsanani yunwa da nakeji, bana iya cin abinci ni kadai dole sai tare da kai.
Yayi murmushi mai sauti gaske Wanda ke nuna ya ji dad'i kalamanta daga bisani yace shiyasa na matsu ayi aure mu Haleesa domin nasan zan sami kyakyawan kulawa daga gareki, Haleesa ina sonki farin cikina burina shine naganki a d'akina a matsayin matar aure na da ranar sai na kwana ina godewa mahalicina da nufi ni da samun babbar ni'eema.
Cikin yanayi na jin kunya Haleesa ta sada kai k'asa cikin sigar shagwaba tace yaya Habeeb ka wank'o hannunka mu ci abinci saboda ni yunwa nakeji
Ni kuma _babylove_ duk lokacin da na kasance tare da ke ko da ace inaji yunwa neman ta nakeyi narasa, kallon wannan kyakyawar fuskarki ta k'osar da ni.
Haleesa tad'ago dara-dara idanuta tasauke su bisa fuskar yaya Habeeb cikin shauk'i so suke kallon juna, tamkar yau ne suka fara gani junansu, Haleesa ce tafara sauke idanuta k'asa daga bisani ta mik'e tadauko buta tace yaya Habeeb ga ruwa ka wanke hannuka ya tara hannushi ta zuba masa ruwa ya wanke sauran ruwan hannushi ya yarfa mata a fuska.
Tasaki sanyaye murmushi had'e da cewa kai koh yaya Habeeb kana so na k'ara jik'aka da ruwan wanke-wanke"?
Yaya Habeeb yayi murmushi yace _nop babylove_ banaso saboda ko d'azu saida inna ta tsare ni da tambayoyi.
Murmushi Haleesa tayi had'e da ajiye buta a gefe daga bisani ta koma wurin zamanta yaya Habeeb ya bud'e kwano suka fara cin tuwon Haleesa ta tsinci kanta cikin nishad'i marar misaltuwa tun lokacin suka fara cin abinci.....
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu🌹
[24/08 7:16 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```7```
Idanu su na manne da juna ta hanyar aikawa junansu kallon _so_ Haleesa na jefa hannuta cikin kwano da suna, ta gutsiri tuwo shima yaya Habeeb yasaka nasa hannu sai kawai hannaye su sukayi karo sakamako tuwo, yak'are sai lokacin suka fahimci cewa , sun ciye tuwon yaya Habeeb ya kalli Haleesa ta sada kai k'asa tana dariya ya dungure mata kai yace yarinya nan kinada wayo shine kika tsare ni da idanu kin ka cinye tuwonki koh"?
A shagwabe tace Allah yaya Habeeb kai ne ka cinye loma uku kawai nayi tak'arasa magana tana murgud'a baki, yaya Habeeb ya zaro idanu yace _umhh babylove ba wani nan kedai kin cinye tuwonki kin hanawa yaya Habeeb d'inki_
Batare da tace komai ba tattara kwanuka takai _kitchen_ ta wanke hannuta ta mik'a masa buta ya wanke nasa hannun, daga bisani ya mik'e tsaye had'e da yin miqa, Haleesa ta tsare shi da ido ya hura mata iskan baki sa akan fuska, ta lumshe idanu yaya Habeeb yayi dariya yace _babylove ni zan koma shago akwai d'iki wata amarya da na fara ban k'arasa, kuma nayi mata alqawali gobe ta zo ta kar6a_
Haleesa ta turbune fuska kamar za ta yi kuka, tace yanzu kenan tafiya za ka yi yaya Habeeb"?
_Eh babylove nima ba'a so raina zan tafi ba sai don na cika alqawali da na d'auka kuma kinsan gobe akwai school banaso kiyi latti tashi_
Ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyi murya tace sai da safe yaya Habeeb, da sauri yatari numfashinta ta hanyar cewa, babylove tun da bakyaso na tafi nafasa, tafiyar domin ko na tafi ba abunda zan iya tsinana a dalilin na bar zuciyata cikin yanayi na rashin jin dad'i ina sonki Haleesa shiyasa nake adawa da duk wani abu da yake yunkuri Shiga tsakani ki da farin cikin ki.
Tasan duk abunda yaya Habeeb yafad'a gaskiya ne bata ta6a gani mahaluki da yakesonta irin yaya Habeeb, yafifita soyayyarta aka komai nashi yana matuk'ar sonta fiye da yadda yakeso kanshi, shiyasa ita ma ta ware masa fili mai matuk'ar girma da fad'i a cikin zuciyarta.
_Haleesa_ a firgice tadago idanuta ta kalle shi shima ita yake kallo tayi, murmushin tace _yaya Habeeb_
Sai da ya mayar mata da martani murmushinta sannan yace _ina sonki_
Haleesa ta kyalkyale da dariya tace kai yaya Habeeb wannan kalma nasha jin ta a bakinka, na kuma amince da ita D'ari bisa d'ari yaya Habeeb yayi k'asa da murya yace da gaske"?
Kwarai kuwa shiyasa na baka sarautar zuciyata domin ka shinfid'a mulki iya son ranka, yaya Habeeb ya tintsire da dariya mai d'auke da tsantsa farin ciki, daga bisani yace na gode da wannan sarauta da kika bani, tabbas samunki agareni Haleesa babban rabon ne burina kuma na waye gari na ganki a matsayin matata a ranar zan nunawa miki irin tsantsa son da nake miki zan nuna miki cewa _ke d'aya ce_ anan yanuna k'irjinsa da hannu.
Cike da jin kunya Haleesa ta juya za ta shige d'aki karaf yaya Habeeb yarik'o hannuta, yace yaya Habeeb naki ne ke kadai Haleesa, ki yi yadda kika ga dama da shi ba Wanda zai hanaki.
Wani irin dad'i ne ya ziyarce zuciyar Haleesa har takeji a jikinta cewa ba mace da takai ta ```DACE DA MASOYI```
Yaya Habeeb ya zagayo gabanta ya k'ura mata ido tsabar son da yake mata jin yakeyi tamkar ya hadiye ta yace _I love you Haleesa you are the only woman I love & I'll continue to loved you for the rest of my life_
Haleesa tayi murmshin tace yaya salman na jiranka fa bata fuska yayi kamar zai yi kuka yace k'ora na kike yi koh Haleesa"?
Da sauri ta girgiza kai ta wani marairace murya banaso ka kasance cikin masu sa6a alqawali, domin alama ce ta munafukai na kuma tabbata yaya Habeeb d'ina ba zai kasance a Jeri munafukai ba don haka katafi ka k'arasa aikinka sai da safe.
Yaya Habeeb yasakin hannuta yace sai da safe my wife kiyi baccin mai dad'i had'e da mafalkina yana k'arasa magana yafice daga gidan, Haleesa tajuya tashige d'aki zuciyarta cike da son da k'aunar yaya Habeeb....
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu🌹
[24/08 8:51 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [24/08 7:32 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```8```
```ASALIN LABARI ```
malam Usman mai kifi da malam Audu mai kifi su biyu kacal iyayye su suka haifa mahaifin su malam balarabe bashida wata Sana'a da tawuce sayarda kifi, kuma har ya mutu sana'arsa kenan, shiyasa 'ya'yasa Usman da Audu suka gadin wannan sana'ar tasa tasayarda kifi.
Tun suna cikin ganiyar kurciya mahaifiyarsu ta rasu, mahaifinsu malam balarabe yacigaba da kula da su yasanya su makaranta allo saboda a lokacin ba kowa yake saka 'ya'yasa makarantar boko Usman yanada shekara 15 Audu kuma yana 13 Allah ya yiwa malam balarabe rasuwa, tun daga lokacin suka fara fuskantar 'kunci rayuwa babu mai taimaka musu da ko lomar tuwo domin rankatakar zuri'a su talakawa ne talauci yayi musu kanta yahana su rawar gaban hantsi.
Tun daga lokacin Usman da Audu suka duk'ufa da neman na Kansu, ta hanyar maye gurbi sana'ar mahaifinsu, a haka suke rayuwa, lokacin da suka kai muzalin aure kowane su ya yakin filin daga cikin ru6abe gidan da suka gada daga wurin mahaifinsu dama gidan d'akin d'aya ne da shi, da kyar kowane su iya gina d'aki d'aya shima na jar k'asa.
Malam Usman ya aure wata bafulatana da ke kai musu nono a kasuwa, mai suna Fatima yayin da malam Audu ya aure 'yar 'kanin mahaifinshi mai suna mairo, a haka suke rayuwa cikin rufin asiri mairo da fatima sun had'e Kansu suna zaman lafiya.
Bayan shekara d'aya da aurensu fatima ce tafara haihuwa inda ta haifo d'anta ranar suna aka rad'a masa suna salman ranar da akayi suna salman a dare ranar mairo ita ma tasami d'a namiji ranar suna na zagayowa aka sa masa Suna Habeeb.
Lokacin da salman da Habeeb suka isa shiga makaranta aka yasanya su makarantar allo da ta boko suna da shekara 3 a duniya mairo da Fatima suka K'ara haihuwa inda mairo ta haifi d'a namiji mai suna Hashim fatima kuma ta haifi 'ya mace juwairiyya.
Sai ya zamana kusan a lokacin d'aya suke haihuwa a wannan karo ma mairo ce tafara haihuwa 'ya mace aka rad'a mata suna Zainab, bayan wata d'aya da haihuwa Zainab fatima ta haifi Haleesa tun daga ranar da Haleesa ta zo duniya Habeeb yad'auki duk wata soyayarshi yad'aura akanta.
Da yadawo daga _school_ zai d'auketa yadinga yi mata wasa duk tsabar so da Habeeb yake yiwa _ball_ a dalilin reno Haleesa yawatsar da zuwa _training_ da sukeyi da yamma a lokacin da Haleesa ta isa yaye Habeeb ne yaye ta saboda a d'akinsu da ke zaure take kwana akwai wata rana da dare da ta falka tana, kuka salman da ke kwance bisa gadonsa yana bacci kukanta ne ya tayarda, shi cikin zafin rai da k'unar zuciyar yace Habeeb katashi ka mayarda yarinya nan wurin Ammi kana matsayin namiji ina kai ina yaye
Wani mugun kallo Habeeb ya watsa masa, yacigaba da jijiga Haleesa da kyar yasamu ta koma bacci ya rungume ta tsanm a k'irjinshi yana shafar suma kanta a hankali,
Wai ba magana nakeyi da kai ba Habeeb"? salman yafad'a cikin d'acin rai
Don kana magana da ni akace da kai dole sai na tanka ma"?
Ba zai yu ba duk dare kukan Haleesa yahanani baccin in kai za ka iya ni ba zan iya ba wannan ae d'aukar alhaki ne.
Mtsss...Habeeb yaja tsoki yayi kwanciyarshi yabar salman yanata faman fad'a shi kadai.
A dalilin Haleesa salman da Habeeb suka raba d'aki tun da Haleesa tayi wayo batasan kowa ba sai Habeeb, ko rashin ji takeyi da Ammi tace sai na fadawa yaya Habeeb yanzu zata fara kuka tace Ammi nadaina kuma karki fad'awa yaya Habeeb yace bayaso na.
Wata rana mal Usman da d'an uwansa mal Audu suna zaune a k'ofar gida suna fira Habeeb yafito d'auke da Haleesa, Habeeb ya rusuna ya gaida su mal Usman ya tsare shi da kallon tuhuma daga bisani yace Habeebu me kake jira ne da har yanzu ba fita shagon koyon d'iki ba"?
Habeeb ya Sosa kai alama rashin gaskiya yace wallahi baffa yau rigimar Haleesa ce ta motsa sai faman kuka takeyi shine nayi, zamana saboda ko naje _tailoring raining centre_ d'in ba abunda zan fahimta.
Baffa ya girgiza kai yace haba Habeebu miyasa za ka za6i kadinga wasa da damarka"?
Karka sake kace za ka dogara da karatun boko, a matsayinka na d'an talaka zaka k'are karatun ne kanemi aikin yi karasa domin a wannan zamani aikin gwamnati na 'ya'ya masu da shi ne ba na 'ya'ya talakawa ba, kadage kanemi Sana'a hannu kadogara da kanka.
Habeeb yace insha Allah baffa zan kiyaye baffa yace masha Allah tashi ka mayarda ita wurin Fatima
Habeeb ya sada kai k'asa cikin raunaniya murya yace Dan Allah baffa in Haleesa ta girma za ka bani ita na aura"?
Baffa ya kalle d'an uwansa mal Audu sukayi dariya, daga bisani baffa yace Habeebu ae Haleesa taka ce matuk'ar ina Raye Haleesa bata wani miji sai kai cikin tsanani farin ciki marar misaltuwa Habeeb yasoma zubawa baffa godiya Yayinda baffa da baba Audu, suke masa dariya tun daga ranar Habeeb yak'ara ririta soyayyar Haleesa tsanani so da shak'uwa ya shiga tsakaninsu.
Da Haleesa tayi laifi hukunci d'aya Habeeb yakeyi mata shine yace Haleesa banasonki ranar tadinga ihu da birgima kenan, har yaran unguwa suka ganota da sun ganta a k'ofar gida sai su fara tsokanarta ta hanyar cewa Haleesa yaya Habeeb baya sonki, kawai sai ta daka tsalle tayi fad'uwar 'yan bori tana taratsi kuka in kuma tsautsayi yagita salman yaganta ya dank'e hannu 'yar banza ya ta duka shi kuma ranar sai sun kwashe 'yan kallon da Habeeb tun lokacin da Haleesa ta mallaki hankalin kanta, ta fahimce tsantsa son da Habeeb yake mata, ita ma tana sonshi tamkar ranta ta kuma fifita shi akan kowane d'a namiji.
[24/08 7:32 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```9```
A kwana atashi asarar mai rai ga shi har Habeeb da salman sun kamalla karatun sakandire _{secondary school}_ a lokacin Haleesa da zainab suna aji biyu a _primary school_ jawairiyya kuma tana aji uku a sakandire, zuwa wannan lokacin sun kware da d'ikin tela, hakan yasa iyayyesu suka zauna suka yanke shawara bud'e musu shago, d'an tanadin da suka jima sunayi suka fito da shi, suka nemo haya shago, a cikin unguwar tasu aka zuba musu telolin.
Habeeb da salman na zaune a tsakiyar gida sai faman shawara suna da za su sakawa shago nasu sukeyi, duk suna da salman yakawo Habeeb yace baiyi masa ba, cikin bacin rai salman yace nagaji Habeeb na fahimice cewa so kake yi ka haddasa mini ciwon kai don haka na baka za6i, Habeeb yayi murmushi had'e da cewa dad'i na da kai salman saurin fushi girgiza kai salman yayi daga bisani, yace banaso damuwa shiysa na baka za6i kafin Habeeb yabashi amsa ya ji 'yar siriiyar muryar Haleesa tayi sallama, sun dawo daga _school_ ita da zainab yad'ago yana kallonta fuskarshi d'auke da murmushi Haleesa na kyala ido taga Habeeb tadaka tsalle had'e da jefarda _school bag_ d'inta ta kwasa da gudu ta nufi wurin Habeeb da sauri ya mik'e tsaye ya ware mata hannaye shi tafad'a jikinsa ya k'ank'ameta yace _oh my baby I miss you so much_ ya sumbace kuma tun ta ina fatar _babylove_ tayi karatu sosai"?
Turo d'an karamin bakinta tayi cikin shagwaba tace nayi karatu sosai yaya Habeeb har da _sweet_ auntymu tabani tasake shi tajuya tad'auko _school bag_ d'inta da ta jefar ta zuge _zip_ tafito da _sweet d'in splash_ ta6are leda tafito da _sweet_ ta jefa baki ta gutsirawa Habeeb yunwa ta duk ya lullube, sweet tasakawa Habeeb a baki da sauri salman ya kauda fuskarsa yana wani yatsina fuska, Habeeb yad'aga ta sama suna kyalkyale dariya, daga bisani yadireta, yaja karan hancinta yace zo mu je _babylove_ ki cire _uniform_ da kanshi yasauya mata kaya, sai faman zazzaga masa surutu takeyi shi kuma yana kwasan dariya, salman ya gallawa Habeeb harara had'e da cewa _look malam karka maida ni soko irinka tun d'azu ina jiranka sai yawo da hankali kake min_
Murmushi Habeeb yasaki yace _sorry in-law